Showing 156001 words to 159000 words out of 403653 words
sauke, cikin sanyin murya ta ce. "Ina kwana". Da alama zuciyarta ta yi sanyi dayawa, dan ta fara yarda son da take yi mashi wasa ne a kan wanda yake yi mata. "Sai da aka gama jera mun tambayiyin ne za'a ce mun ina kwana?". Cikin zolaya ya yi maganar.
Siririn murmushi ta saki tana sanya tafukan hannayenta ta rufe face ɗinta. Wani irin daɗi ya ji na ganin murmushinta, lallai wannan safiya tasa ta fara da kyawawan abubuwa.
Ta tafi da tinaninsa har ya sanya hannunsa ya kamo hannayenta da ta rufe, ya buɗe dan ya ji daɗin ganin kyakkyawan murmushinta, yarinya mai kyan gani, dik wanda ya ganta sai ya ji daɗi a ransa. Yunkurawa ta yi da sauri ta miƙe tana cigaba da murmushi. Zama ta yi kusa da shi suna fuskantar juna, har lokacin wutar bai mutu ba, a hankali ya saki hannayenta da ya rike yana kallan gefe.
"My Hero". Ta ambaci sunansa kallanta a kansa. Kin ɗagowa su haɗa ido ya yi, amma ya amsa kiran. "Idan har da gaske kana sona, abu ɗaya zaka mun in tabbatar da hakan".
Jinjina mata kai ya yi alamar to ba tare da ya yi magana ko ya yi wani motsi ba. "Kalli cikin idona sai mu yi magana"......... Kamar ba zai yi hakan ba, sai kuma ya daure ya ɗago da kallansa a kanta. Ya subhanallah, sarkafe juna da kallon kauna mai tafiya da imani suka yi, gabaɗayansu sun lula wata duniya, dik sun kasa yin magana. Sun macewa juna a kallo, ita kanta ganin cikin kwanciyar idanunsa yasa ta rasa nitsuwarta bare kuma shi.
Sai da suka ɗauki good 5 mins a haka, sannan ya yi ta mazan lumshe idanunsa yana jin wani abu na mashi yawo daga tsakiyar kansa izuwa tafin ƙafarsa. Cool voice ɗinta ya ji a kunnuwansa tana faɗin. "Na yi fatan mu kasance ma'aurata da wuri".
Waro idanunsa a hankali ya yi ya kalleta. "Na fiki yin wannan fata my Hoonaira". Nisawa ta yi kafin ta ce. "Yanzu misali a ce yau daddy ya ce ya mallaka maka ni ya zaka ji?"........... Wani irin lumshe idanunsa cikin salo mai jan hankali ya yi tare da yunkurawa ya miƙe tsaye. Binsa da kallo ta yi. Hannu ya sanya a cikin sumar kansa, a hankali ya ɗan watsa gashin nasa haɗe da ɗan ciza laɓɓansa kaɗan, wani irin nisawa ya yi ya ƙasa magana.
"My Hero lafiya kuwa?". Ta yi maganar tare da miƙewa tsaye ita ma........ Kai kawai ya girgiza mata, ya ƙasa magana, wato baki ya yi kaɗan wajen zayyana irin farincikin da zai shiga dik ranar da aka mallaka mashi ita, wow abin ba'a magana, soyayyarsu soyayya ce kafun Allah, ba aba bace da aka ginata yau ko jiya, shekaru ake magana, zuƙatansu sun narkewa juna dayawa da jimawa, a yadda suke ji zasu iya aikata komai a kan junansu.
Hannunta ya riƙo cikin nasa, wajen ruwan da suka yi alwala daren jiya suka nufa. Sai da ya duƙa gaban ruwan zai fara taɓa ruwan ne ya yi karfin halin cewa. "Ki dai'na yi mun irin waɗan nan tambayoyi, saboda baki ba zai iya faɗar yadda girmanki yake a rai'na ba, watarana zaki iya sanya zuciyata ta aikata wani abin da ya saɓawa shari'a idan kina irin waɗan nan tambayoyi".
Jinjina mashi kai ta yi tare da duƙawa ita ma dan ta ɗauro alwala, kamar zai ce mata tana bukatar yin tsarki kafin alwala, sai kuma ya yi shiru saboda kada ta yi mashi wata mummunar fassara, yasan halinta sarai.
Yana ganinta ta yi alwala, shi kuma ya tsaya bai yi ba, har ta gama ta miƙe, baya kaɗan ta ɗan ja ta tsaya wai tana jiransa, ganin hakan yasa ya miƙe tsaye, cikin sanyin murya ya ce. "Jeki ki tashi Pretty, sannan ki yi sallarki ina zuwa"........ Bata yi mashi musu ba ta wuce tana waigosa, shi ma kallanta yake yi har ta kure mashi. Sannan ya matsa daga in da yake zuwa gaba dan ya yi tsarki.
Zaune ya isko Auta kusa da wuta, ita kuma Pretty tana sallah. Matsawa ya yi kusa da ita, a gabanta ya zube gwiwowinsa, cike da so da kauna ya miƙo mata flowers da ya ciro mata yana kallan face ɗinta............... Ai tsabar farincikin bata san lokacin da ta saki ɗan kara mara sauti sosai ba. Hannunta har yana kerma wajen sanyawa ta karɓi flowers ɗin, jikinsa ta faɗo unexpect tana murmushi. Rungumeta ya yi yana jin daɗin ta yi farinciki.
A hankali ta ɗago kanta daga saman kirjinsa, sumbatar flowers ɗin ta yi, lokaci guda ya ji tamkar kumatunsa ta sumbata, har wani ajiyar zuciya ya sauke, shi kaɗai yasan me yake ji a ransa, cikin ƙanƙanin lokaci ya ji ya kwaɗaitu da san sumbatarta.
"My Hero nagode sosai, farkon kyautarka a gareni, ba zan taɓa manta wannan rana ba, ina sanka fiye da yadda ma'aunin tunanin mutum zai iya aunawa". Tana magana idanunta suna ciccikowa da kwallah.
Hannu ya kai saitin gemunta, hawayenta da suka cika idanunta ne suka zubo har kan tafin hannunsa, nisawa ya yi, calmly ya furta. "Ki dai'na mun asaran hawayena, please my Hoonaira, kada ki sake bari su zuba kin ji?".
Kai kawai ta gyaɗa mashi, Allah mai juya dare ya zama rana, rana ya zama dare, wai yau ita ce tare da masoyinta a nan suke zuba soyayya wa junansu?. Pretty ce ta katsesu da cewa. "Ina jin yunwa sosai Zunaira".
Zame hannunsa Hoorain ya yi daga kusa da ita, sannan ya miƙe yana faɗin. "Ku tashi mu fara tafiya, a gaba zan sama maku abin da za ku ci". Ya kai karshen maganar tare da nufar in da ya ɗaure dokinsa daren jiya. Kwantota ya yi ya zo ya ɗaukesu da dik abubuwansu, a yanzu sai ya sanya Pretty a baya Auta a gaba, shi a tsakiyarsu kenan, saboda a jiya da ya sanyasu dikka a gaba sun haifar mashi da matsala ta rashin gudu sosai, dole ya rabasu idan yana san su yi gudu sosai su samu damar isa da wuri kafin rana ta faɗi.
Daga haka suka kutsa cikin daji da gudun gaske........ To Allah ya tsare hanya our love birds.
🔥🔥KINGDOM OF POWER🔥🔥
After some days. A waɗan nan ƴan kwanaki da suka wuce abubuwa sun faru wanda suka haɗa da ganin Khadijah da su uncle Jahiz suka je, and jiya da daddare Khadijah ɗin ta farfaɗo baiwar Allah, amma ta ji azaba ba karya, dan ma ta samu kulawar likitoci sosai ne yasa, sai dai bata magana dik da ta farfaɗo ɗin ma.
Time da uncle Jahiz ya ganta sai da ya ɗan razana kaɗan, dan a fili ya furta tabbas ya taɓa kallan wannan fuska, sai dai ya manta a ina ne.
(Anya ba raina mana hankali yake san yi ba kuwa?🤔 Shi da yake Tunisia a ina ya taɓa ganinta ita da take Nigeria bata taɓa fita ko'ina ba, ko Abuja bata taɓa zuwa ba sai sanadin Hauwa bala'i, to aina ya taɓa ganinta? Anya zarginmu a kansa ba gaskiya bane kuwa? Mu je dai zuwa, lokaci ne zai warware mana komai.)
Abu na biyu da suka faru kuma shi ne su commander Zafar sun ci nasara a yakin da suka tafi, sai dai kuma da kyar suka sha, saboda commander mayakan Queen Zarina wato mai kama da Hoorain namu ya kawo masu babban barazanar da sai da dangerous warriors suka girgiza, sun kasa iya taɓa jikinsa, saboda suna tsoron su taɓa jikinsa a matsayinsa na assistant commandernsu. Shi kansa commander Zafar ƙasa taɓa shi ya yi saboda kowa ya san yana kaunan ɗansa over. In short sai da commander yaga da gaske wannan zai iya hallaka shi idan shi bai kashe shi ba to shi zai kashe shi, sannan ne fa ya bawa warriors ɗinsu umarni da su kashe shi koda Hoorain ɗin ne tin da kashesu shi ma yake ƙoƙarin yi.
Sosai mayakan suka yi mamakin jin furucin commander, Allah sarki basu lura ƙoƙarin kashe commander ɗin shi ma yake yi ba, da ciwo mai kama da ciwon zuciya commander ya dawo Kingdom of power, Allah sarki, ya ƙasa yarda Hoorain ne, sannan ya gargaɗi mayakansu da kada su yarda su sanar da King Zuhair abin da ya faru, su rufa mashi asiri su bashi lokacin zai binciko gaskiya, dan ya tabbatar ba Hoorain ɗinsa bane, idan kuma shi ne to tabbas akwai wani abin da aka yi mashi, ba haka kawai ba.
To tin da suka dawo wannan yaki commander yake kwance yana jinya, ya kasa samun kwarin zuciyar iya ɗaukar wannan balai'n bare har ya iya tashi ya binciko gaskiya, sai zargi zuciyarsa take ɗarsa mashi, ya yi tinani ya fi dubu a kan hakan, sai faɗi yake yi dama kenan da Hoorain ya gudu daga nan bayan Zarina ya koma ne ko yaya?...... MY PEOPLE'S GASKIYA ABIN DA ƊAURE KAI, ALKALAMIN PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA CE KAWAI ZAI IYA WARWARE MAKU WANNAN CAKWAKIYA, KU DAI MU JE ZUWA.
Abu na uku da ya faru a kingdom of power kuma shi diransu Omaid and Obaid, sun samu hutun karshen shekara, azumi ya kawo kai, sun samu hutun dawowa gida su yi azumi, shi kuma guyson yanzu result ɗinsu ya fito har ya yi registration, yanzu guyson namu zai shiga hundred level, ya zama babban yaro, yanzu jami'a yake, sai sakalci da kukan ciwo kam har yanzu tana nan.
A ɓangaren su Mammie kuwa suna can suna aikin kullace kullacensu, sai shirya ta yadda zasu taimakawa Fanan suke yi, ita ma Fanan yanzu ta bi bayansu, a kan soyayyar Jaish ta yarda dik abin da suka sanyata zata iya aikatawa. Babbar magana, mu je zuwa.
Shi kuwa King, yanzu hankalinsa yana can yana kan neman Auta, tin yana ganin abin kamar da sauki har ya fara ganin abin fa ya zarce tinani, ya baza mayakansa a ko'ina nemanta ake yi, wasu har cikin dajin da su Hoorain suke suka shiga, amma basu samu haɗuwa da su ba.
Mahnoor and Mahreen suna ta shan gyara, wa'adin da momma ta ɗibawa King gobe zai cika In Sha Allah, yau sai busy momma take yi tana shirya masu oder kayayyaki na gani na faɗa wanda zasu tashi kai. Sarina dai dik balai'nta bata samu damar ganin Mahnoor ba, dole ta hakura suna jiran gobe a fito da ita su ga wace tsiya ce.
Wannan shi ne kaɗan daga cikin abubuwan da suka faru a ƴan kwanaki da suka shuɗe, to mu je zuwa.
•••••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥
7:30am. Agogon kingdom of power mai tsananin kara ta buga. Sanye uncle Jahiz yake cikin shiga ta ƴan kwallo na team ɗinsu, ya ɗaura jacket a kan kayan nasa saboda sanyi da ake yi, cikin nitsuwa yake takowa, daga part ɗin Akka ya fito izuwa part ɗin mama wajen Aneesa kenan.
Yanzu likitoci asibin kingdom suka yi mashi waya a kan Khadijah ta farfaɗo daren jiya, dan haka suna bukatar na kusa da ita wanda ta sani ya zo dan suka yanayin kwakwalwarta, ta ki yin magana, ta kuma ki yin motsi ƙwaƙƙwara, to shi suke buƙatar Zee, idan ta zo kila Khadijah zata yi magana ko wani abin da zai sa su fahimci tana cikin hayyacinta kuma aikinsu ya yi kyau.
Wannan dalilin yasa ya fito da safiyar nan zai je wajen Zee su tafi hospital ɗin, ga shi cikin satin nan yake san komawa Brazil, dan suna da wasa, hutun da ya ɗauka ta kusa karewa, zai je ya shirsshirta.
Bakinsa ɗauke da sallama ya afka cikin ɗakin Aneesa, bai yi tinanin sun tashi daga barci bama shiyasa ya afka kawai. Wani irin birki ya ja lokacin da idanunsa suka sauka a kan Zee dake tsaye gaban mirrorn Aneesa tana shafa mai, daga ita sai towel a ɗaure a kirji, ita kuma Aneesa ta fita izuwa kaiwa mummyn Chuchu labari...... KO LABARIN ME ZATA KAI MATA KUMA?🤔
MU JE ZUWA ZA DAI MU JI.
Zee har ta goge ta yi kyau, sai dai ko kaɗan bata jin daɗin zama da su Aneesa, suna tsangwamanta, bare ma Sarina da in dai ta shigo sai ta ci mata mutuncin da kare ma ba zai sinsina ba, amma tana hakuri tana dannewa dan gidansu ta zo, kuma ko ba komai sun taimaka mata, ita burinta Khadijah ta samu lafita su koma Nigeria abinsu.
Da yake uncle Jahiz ɗan duniya ne girma cikin turawa, sai ya fara binta da kallo tun daga kafafunta har izuwa kirjinta, sai da ya ɗan tsai da idanunsa a kan kirjinta ma kafin ya kai kallansa a kan face ɗinta. Ta yi ƙasa da kai ta takure jikinta waje guda, tana jin kunyar motsawa daga in da take, jin sallamarsa dama yasa ta juyo, ta yi danasanin ɗaura towel bata sanya hijabi kamar yadda take yi a gida ba, kuma saboda taga babu wanda yake shigowa ɗakin ne yasa bata saka hijabin ba.
Ko kaɗan babu kunya a idanunsa ya sake dawo da kallansa a kan kirjinta da suke cike fam, a hankali ya kalli santala santalan cinyoyinta da yanzu suka murje suka yi kyau saboda wanka da sabulai masu rai da lafiya na Aneesa da take yi.
Ya kasa motsawa ya kuma kasa kawar da kallonsa daga kanta, sai ma ƙara kurawa kirjinta ido ya yi, ita kuma ta kasa gudu ta bar wajen, to me kuke tinani zai faru? Shi dai uncle Jahiz ba kunya ne da shi ba, ni dai na tafi shan maltina idan na dawo zan ga shi da ita waye zai ɗagawa ɗan uwa kafa, shin zai hakura ya ja da baya ya koma ne? Ko kuma ita zata danne zuciya ta gudu? Su dai suka sani, ni na yi ta nan...............🥱
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
======🔥🔥🔥===========
MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
Cigaba da karewa albarkatun jikinta kallo yayi, kwata kwata babu alamar zai ja da baya ko ya kawar da kansa, ta gaji da tsayuwa taga alamar bafa dai'na kallanta zai yi ba, dan haka sai ta daure ta fara takawa a hankali kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta nufi dressing room na Aneesa.
Dik wani step ɗinta ɗaya a kan idanunsa take yi har ta kurewa ganinsa, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗan dukar da kansa ƙasa, shi kaɗai ya fara ayyana yadda kyanta yake a cikin ransa, saman sofa ya zauna yana kara jinjina kyan abin da ya gani, to da alama dai ransa ya biya.
Shi da bashi da fara'a ko kaɗan, sai ga shi yau ya sanya hannu saman arabs hairnsa, yana ɗan watsa gashin yana murmushi kamar wani sabon kamu......... My people's ni wai ba uncle Jahiz ba ne ya ce ba zai taɓa san mace ba sai ya kai 40 years? Sannan har da wani ce mana babu abin da zai yi da yar yarinya, shi mace daga mai 25 years ya yi sama yake so? Anyi haka ko ba'ayi ba? To inaruwansa da Zee ɗinmu? Zee dai 17 years take da shi, ko Khadijah bata kai 20 ba bare Zee bare kuma a kai ga 25 years, me uncle Jahiz yake nufi? Kada ma ya kuskura ya fara ce mana ya janye kalamansa, dan ba zamu lamunta ba, amma guy ɗin nan ya sha damu dama, to wai an faɗa mashi mata wasa ne?......…....🤔
Shiri Zee ta yi cikin abaya again, kunsan su Aneesa kaso 80 cikin ɗari na kayansu abayas ne, saura kaso 20 ɗin kuma irinsu riga da wando, riga da sket and gown ne. Abaya mai kyau da tsada launin purple color ta sanya, ta yi rolling mayafin a kanta, sai kuma ta ƙasa fitowa waje, saboda bata san haɗa idanu da shi, zuciyarta ta ja baya matuƙa da shi, dama kun san halin Zee ai, yanzu ma saboda Khadijah ta samu lafiya yasa ta yi sanyi take jure komai da ake yi mata, banda haka ai wlh ba sarauta ba, ko uban me uncle Jahiz yake ji da shi bai isa ya karewa albarkatun jikinta kallo haka ba.
A yanzu haka zuciyarta ta raya mata uncle Jahiz ɗan iska ne, kada ta yarda da shi ya je ya cuceta ya yi mata ciki kamar Khadijah, wannan shi ne babban dalilin da zuciyarta ya rike yasa ta yi baya sosai da shi, ta ji bata san sake haɗa inuwa da shi, amma kuma tana san ganin Khadija, kuma kun san dole sai ta hannunsa zata samu damar ganinta.
Ta kai 30 mins da kammala shiri, amma ta samu waje saman ɗaya daga cikin drawers dake cikin ta yi zamanta tana tinanin mafita a gareta, dan wlh bata ga abin da zai sa ta sake bari ya kalli surar jikinta har haka ba. Shi kuwa zama ya yi yana jiranta, tunanin kyan surarta da kwaɗaituwa da shi yasa bai ga tsawon lokacin da ta ɗauka bata fito ba, sai yake ganin kamar yanzu ta shige.
Sai da suka kara wani 20 mins a kan wancan 30, nan ma sai da yaga kiran Dr sannan ya miƙe tsaye ya nufi dressing room ɗin cike da mamakin me ya hanata fitowa? Shi bai san cewa mu ƴan Nigeria muna da alkunya ba, dan shi bashi da shi sai yaga kamar kowa ma bashi da, a'a mu Nigerians muna da shi sosaima.
Ya sha madarar mamaki na ganinta zaune shiru ta buga uban tagumi, tinanin