Showing 39001 words to 42000 words out of 403653 words
"Beb ka yarda da abin da ta faɗa kenan?".
Dawo da kallonsa a kan Floris ya yi. "Ina ji a rai'na dik abin da ta faɗa gaskiya ne, amma ba zan yarda da hakan ba har sai na ga hujoji a zahiri ba a faɗe a baki ba, dan haka zan nemi Alqur'ani dan na karanta na tabbatar!".
A hanzarce Sweetie ta karɓi zancen da cewa. "Tabbas zan baka hujjoji a zahiri da zarar na bar nan".
Jinjina mata kai ya yi tare da miƙewa ya nufi hanyar shiga toilet.
"Yau muna da gagarumin party a empeir ɗin nan na fidda gwanar kyau, Sweetie ki shirya, yakamata ki shiga cikin wanna gasa fa nasan zaki fi kowa, zaki samu kyauta babba daga wajen yaya". Cewar Ronnie dake nufar toilet.
Jinjina kai Sweetie ta yi, a ranta ta kudurta cewa tabbas zata biyewa mutanen birnin nan dan ta rinjayesu izuwa addininta, dan haka zata rinƙa shiga cikinsu, zata bi al'adunsu dik dan ta yi masu mage mai kwamciyar ɗaukar rai, a cikin zuciyart ta furta.
"Ya Allah kasa kafin na bar garin nan ko da rabinsu ne na samu su musulunta, Allah ka tayani ka taimaka mun ka dafa mun".
Sosai Floris ta ji rashin daɗin cewa da Ronnie ya yi Sweetie ta shirya ta shiga cikin gasarsu da suke yi dik karshen sati, dan tasan Sweetie ta fita kyau nesa ba kusa ba, so tasan zata bugeta ta cinye mata number na farko da take zuwa, sai ta ji ta kara jin haushin Sweetie, dama can akwai sauran haushinta na zagin malamansu da ta yi, sai ya karu mata.
Ita kuwa Sweetie raba jikinta da jikin bangon ta yi ba tare da ta sake bi ta kan Floris ba ta nufi hanyar fita faga cikin ɗakin.
"Ina zaki je?". Ronnie ne ya jefa mata tambayar.
Da sauri ta juyo haɗe da kai kallonta in da yake, yana tsaye a bakin kofar toilet ta waje, ya harɗe hannaye a saman kirjinsa.
"Zan je wani ɗakin ne na yi amfani da toilet ɗin, lokacin sallar mangariba ta wuce".
Da hannu ya nuna mata hanyar cikin toilet ɗinsa.
"Zo ki yi amfani da wanna, daga nan ki yi wanka, Floris je ki kawo mata ɗaya daga cikin irin kayan da kuke sakawa dan yin gasa, mai kyau zaki kawo mata fa".............. Ya yi maganar ne idanunsa a kan Sweetie.
Ba musu ta dawo ta nufi toilet ɗin nasa, yanzu ba zata yi gardama da su ba, dan ta ɗaura ɗamarar musuluntar da su dikka birnin da izinin Allah, dan haka ta shirya tsab wajen shiga cikinsu sosai dan ta san takamaiman ina ma suka dosa tukun nan.
Sai da ta iso dab da shi sanna ya bata hanya ta shige ciki, shi kuma ya wuce ya nufi waje yana faɗawa Floris ta zo su je bari ya je wajen ƴaƴansa ya duba irin kyautar da aka tanadawa waɗan da zasu zo daga na ɗaya zuwa na goma, ita kuma ta wuce room ɗinta ta shirya ta kawowa Sweetie kaya sanna ta taimaka mata wajen shiryawa.
Da okey ta amsa mashi a fili, amma a cikin zuciyarta ta kudurci niyar shiryawa Sweetie mugunta ta yadda ba zata taɓa cin wanna gasa ba, har da shirya irin kwalliyar muguntar da zata yi mata, ga shi Ronnie idan ya fita yanzu sai dai su haɗu a wajen wasa kawai, so ba zai samu damar ganinsu ba bare idan Floris ta yi mata ba daidai ba ya ce ta gyara mata, sai a cikin mutane zasu haɗu.
Hakan ne ma ya bawa Floris kwarin gwiwar cewa zata ɓata mata fuska ta dishashar mata da kyanta.
Alwala Sweetie baiwar Allah ta ɗauro ta zo kamar yadda ta saba ta gabatar da sallar mangariba, tana idarwa lokacin sallar isha ta yi, hakan yasa ta miƙe ta gabatar da shi.
Sanna ta shiga cikin toilet ta yi wanka, tana fitowa ta isko Floris zaune a saman bed ta tsantsara kwalliya kamar wata amarya, tana shirye cikin wani doguwar riga mai kama da weeding gown, ta yi masifar kyau sosai, kwalliyar ya karɓeta matuƙa.
Sweetie baiwar Allah har da yaba kyalliyar tata ta yi, cikin sanyin murya ta ce. Floris kin yi matuƙar kyau sosai".
Tsabar haushi kamar ba zata amsa ba, sai kuma ta tina im bata amsa ba Sweetie zata fahimci ta shirya mata wani muguntar ne, dan haka sai ta amsa da thank u. Kawai.
A kusa da ita Sweetie ta zauna tana bin kayan jikinta da kallo, irin kayan ƴaƴan sarakuna ne, shigensu wannan sadauki mai taimaka masu a forest ɗin yake kawo masu ita da Pretty suna amfani da shi!.
Su hajiya Sweetie manyan ƙasa, girma ya fara zuwa ƴan kirgan danginta sun girma kamar na Auta Zunaira, hakan yasa yanzu take ɓoyesu, kamar dai yanzu yadda ta wani ɗaura towel ɗin Ronnie daga saman kirjinta, ita ma Floris dik da take krista bata taɓa yarda ta fito wanka kirji a buɗe, tana rufe kayanta, Floris ta fi Sweetie shekaru, amma Sweetie ta fita cikar halitta, dan tula tulanta ɗaya ya yi kusan biyun na Floris a girma.
In short kwalliya Floris ta tsarawa Sweetie kamar wata ta Allah, kamar dai da gaske take tare da ita, alhalin a karkashin zuciyarta ba haka bane, hasada take da kyan da Allah ya yi wa Sweetie da kuma iliminta, Floris an fara hasada da kishi.
Wajen da za'a gabatar da gasa ya cika makil, jama'a suna zazzaune cikin hall ɗin, ƴan matan da zasu shiga wannan gasa suna killace cikin ƙayatatcen ɗaki, dama haka suke yi, sai sun gama haɗuwa a cikin wannan ɗakin sanna sai su fito izuwa saman stage na hall ɗin dan bayyanawa duniya irin kyansu da surar jikinsu.
Dikkanninsu matasan ƴan'mata ne da babu wacce ta wuci 18 years a cikinsu, sai dai dikkansu daga 15 years suke, babu wanda take kasa da 15 sai Sweetie da zata shiga gasan a yanzu.
Kafataninsu kayan jikinsu irin kayan nan ne da ake cewa aunty tsirara, sun ɗame jikinsu dan fito da surar da Allah ya yi masu, idan ba ku manta ba a baya na gaya maku ƴan'matan birnin suna da sura mai matuƙar kyau da ɗaukar hankalin dik mai kallonsu, to hakance.
Sun yi kyau sun kuma saki gashi har baya, kowacce ji da kanta take yi, tana ganin tafi kowa kyau, anyi fente fenten kwalliya kam har an gaji, ga wani uban high heels a kafafunsu, wasu daga cikin sai taunar chewing gum suke yi suna yi wa junansu kallon ƙaskanci da matsayin basu kai ba.
Ronnie yana tare da Oxil a saman kujera suna hira a kan yadda gasan zai kasance da kuma wadda zata yi nasara.
Oxil dai ya ce Floris ce zata yi nasara dan yasan a kullum ita take bige kowa ta zo ta farko, saboda ko kayan da take sanyawa a jikinta ya take na sauran ƴanmatan kyau da tsada, bare a zo kan kwalliyarta, abin ba'a magana, hakan yasa take zuwa ta ɗaya.
Angama kimtsa komai ƴan'mata kawai ake jira su iso. Ga shi Floris ɓatawa Sweetie fuska, me kuke tunanin zai faru a wanna fasa? Ronnie zai yarda da hakan ko yaya?.
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
==========🔥🔥🔥===========
MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
A dab zasu shiga hall ɗin Sweetie ta tsaya bata shiga ba. Floris ta tambayeta dalili, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce.
"Kunyar shiga da irin wannan kaya nike ji Floris".
Binta da kallo Floris ta yi, nan take wani kululun bakinciki ya tokare mata maƙoshi, kamar zata haɗiyi zuciya, saboda tafa zaɓo kayan da bashi da kyau sosai ne ta bata, amma kuma sai ta yi bala'in yi wa kayan kyau, saboda tana da round butt, yadda kuka san ita ta yi wa kanta halitta.
Floris bata san cewa ba kaya ne yake yi wa Sweetie kyau ba, yanayin shape ɗin jikin Sweetie yake yi wa kaya kyau, in kina da kyau sai kaya ya zauna maki.
"Gaskiya Sweetie bai kamata ki shiga ba tin da kince addininku ya yi hani da fidda tsiraici, kinga wannan riga kuma ta kamaki sosai". Cewar Floris. Cike da hasada ta yi maganar.
Shiru Sweetie ta yi, sai ta ji kamar da gaske Floris ta gaya mata gaskiya ne, ta yi mata nasiha kanan, wani irin sanyi ta ji a ranta, sai taga kamar da gaske Floris take yi, kamar santa take yi, bata san ba haka bane.
"Tom shikenan Floris, zan koma ciki ni kam".
Tsabar farinciki ta kasa shanyewa har sai da ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, buƙata ta biya.
"To ki koma kam zai fi". Ta faɗa fuska ba yabo ba fallasa ba kamar yadda ta ɗaure face ɗin nata ɗazun ba!.
Juyawa Sweetie ta yi ta nufi hanyar komawa cikin gida, ita kuma Floris ta yi maza ta shige cikin room na hall ɗin, wai dan ma kada Sweetie ta canza shawara ta ce zata shiga ciki, shi ne ta yi saurin wucewa ciki ta yadda ko ta juyo ba za ta ganta ba.
"Ina kuma zaki je?". Daga bayanta ta ji wannan tambayar.
Juyowar da zata yi gabaɗaya komai na face ɗinta ya canza, kwalliyar mugunta da Floris ta yi mata maras kyau ɗin nan, dik kafin ta juyo ga Ronnie kwalliyar ya goge izuwa wani tsantsararren kwalliya na ban mamaki, ta yi balai'n haɗuwa, har da wani gashi dogo guda biyu ya bayyana a gaban goshinta wanda aka naɗa mata shi kamal indomie.
Ta yi masifar kyau wanda sai da ta sanya Ronnie zaro idanu, cikin second ɗaya magic ya canza mata kamannin kwalliyar face ɗinta.
Da yake ba ganin kanta a mirror take yi ba, sai ta ɗan sakarwa Ronnie murmushi wanda ya kara haukata ƙwaƙwalensa, dimples ɗinta dik suka lotsa.
Kamar wanda ya ga abinci Ronnie bai san time da ya haɗiyi yawu ba, ya kasa sake ce ko uppan.
"Ciki zan koma" ta bashi amsa tana kara faɗaɗa murmushinta.
Hannu kawai ya iya buɗe mata ba tare da ya yi magana ba. Tsaresa da ido ta yi tana kallan irin shigar jikinsa, ya yi kyau matuƙa shi ma, sai dai ya yi aske gera, ya raba gashin gerarsa har kashi uku, hakan ta yi mashi kyau kam matuƙa, sai dai a addinin musulunci Allah ya tsinewa masu haske gashin gyara da masu kankare hakwara su yi wishirya.
So hakan yasa Sweetie ta ɗan ji ranta ya sosu, meyasa zai rinƙa aske gerarsa haka? Ga ɗan kunne a kunne har saman kunnensa, bayan haka ga sarkoki a wuya kamar wani mace, har da wani ɗan pil a gefen bakinsa, sun yi mashi kyau kam over, sai dai Allah ya haramta, dole ta san yadda zata gaya mashi ya rabu da sakasu.
Kamar ba zata je in da yake ba, amma ganin irin shigarsa yasa ta ji yana da kyau ta je garesa dan ta shiga jikinsa sosai ta samu ya fita daga wanna irin rayuwa. Dan haka sai ta nufesa da sauri.
Tana isa garesa ya rikota ya rungume yana sauke ajiyar zuciya, ita ma bata zare jikin nata daga nasa ba, sai ta rungume shi da kyau tana ɗan murmushi.
"Kinga yadda kika yi kyau kuwa?". Ya faɗa kamar mai raɗa.
Kai ta girgiza mashi alamar a'a ba tare da ta yi magana ba.
"Kin yi kyau sosai da sosai, zo mu je an kusa fara gasar".
Kamar zata ce mashi ba zata je ba, sai tunani ya faɗo mata a kan tana san fa ta rinjayesu su musulunta, dan haka dole ta yi aiki tukuru, dole zata ɗan kawar da idanunta a kan wasu abubuwan ta shiga jikinsu sosai.
Dan haka sai ta aminta suka shige ciki a tare.
Tin da ta ɗaura kafafunta a cikin wajen idanun mutane suke a kanta, kallonta kowa yake yi babu kyaftawa, hakan ya ɗan sosa ran Ronnie, amma ya daure.
Floris ta kara jin haushinta sosai, dan tana ganin kamar Ronnie ne ya je ya gyara mata face ɗin nata a cikin room ɗinsa, sai ta kara jin wani irin kululun bakinciki ya tokare mata maƙoshinta, kamar ta shake Sweetie, amma ta girgiza sosai na ganin wanna halitta ƙayataccen kwalliyar, babu wata mace da ta taɓa yin irin wannan kwalliya a cikin birnin, zallar madarar kyau, ga yanayin gashin kanta dik cikin birnin babu mai irinsa, ita kaɗai ce mai irinsa.
Amma kuma da Ronnie ya kawo mata Sweetie ɗin kusa da ita, sai ta ƙaƙalo murmushin dole ta yi mashi tsabar iya makirci da munafurci.
Bai kawo komai a ransa ba ya haɗasu ya koma wajen zamansa.
Zubawa takalmar kafar Sweetie idanu ta yi tana kallon yadda suka ci uban nata a kyau, bata taɓa kallon irinsu ba, da duwatsun lu'ulu'u aka kawata kwalliyarsa, hakan yasa ya kara rinjayar jama'a dayawa wajen kai kallonsu a kan takalmar.
A tunanin Floris Ronnie ne ya ɗauko mata takalmar daga ɗakin Black Tiger, amma kuma ba haka bane, dan shi kansa Ronnie bai san da takalmar ba, ruhohin tsafinta suka canza mata komai!.
Dik fa abin da suke yi kada ku manta Black Tiger yana jinsu kuma yana ganinsu, sai dai this time bai wani mayar da hankali sosai a kansu ba, ya mayar da hankalinsa ne a kan katafaren ginin companyn motocinsa da ake yi, wato BLACK TIGER SUPER AUTO MOTORS, yana san su zama na ɗaya a duniya wajen kyara motoci waɗan da su suka fara kawo irin style ɗin, yana san su tashi kan duniya ne sosai.
So ya fi kayar da hankalinsa a kan ginin da kusan rabin aikin Robbot ne suke yinsa ba ƴan adam na, hakan yasa aikin yake kara sauri yake kuma tafiya yadda ya kamata, ga shi girman companyn gidan sama ne mai hawa goma, Robbot sun taka muhimmiyar rawa sosai wajen rage samu mace mace mutane a kan wanna gini, su suke hawa sama ƙololuwa su yi aiki, kunsan a gini irin haka laburas and engineers suna rasa rayukansu wajen faɗowa kasa daga sama idan aka samu akasi, so yanzu Robbot ke hawa sama wanda su idan ma suka faɗo sai dai su tashi su karkaɗe jiki su kara gaba abinsu, babu abin da zai same su!.
So yanzu an samu sauki sosai wannan fasaha ta Black Tiger wajen amfani da Robbot sosai a aikin da ƴan adam suke yi ya yi matuƙar birgewa, saboda ya taimakawa mutane matuƙa. Yanzu hankalinsa baya a kansu sosai.
Ko ban faɗa ba nasan kunsan dik faɗin birnin Black world babu wanda za'a samu ta iya doke Sweetie a kyau, dan faɗe ma ɓatawa ne, kun san in ta shiga fili dole mata su matsa mata, hakan ma yasa Floris ta kullah mata tuggun ta hanata shiga wajen, amma ina hakarta bai cinma ruwa ba.
Sweetie ta yi gasa kuma ta ci na ɗaya, Angela ta zo na biyu, sai Floris ta uku, ba komai yasa Angel ta zo na biyu ba kuma face alhakin Sweetie ne ya kama Floris, ta mata mugunta reshe ya juye da mujiya, ita da take zuwa na ɗaya kullum yau ta kare a na uku.
Idan ranta ya kai miliyan to ya ɓaci, zuciyarta ya sosu, tsabar kishi da kuka ta bar wajen taron, bata ma tsaya an shigar da mark na kowa a Idanta ba, ta wuce ciki da gudu.
Sai gobe da safe za'a bawa waɗan da suka ci gasar kyautarsu, hakan yasa Sweetie ta ce da Ronnie zata je ta yi barci dan zata tashi ta yi sallar dare.
Sam bai so hakan ba, ya so ta tsaya su yi casun rawar da zasu yi, ya so koya mata rawa, amma baya san shiga hakkinta, sai ya rakota har cikin room ɗinsa ya ce ta kwanta a nan shi zai je wajen rawar, in suka gama rawa kuma ba lallai ya dawo ɗakin ba, kila a ɗakin yayansa zai kwana.
Ko tsoro babu a tattare da ita ta amsa da to tare da wucewa ciki, yana tsaye har sai da ta canza kayan jikinta izuwa kayan barcin Floris da ya kawo mata, dressing room ɗinsa ta shiga ta canza kayan, sanna ta zo ta haye gado, da kansa ya rufeta da bargo kafin ya juya ya fita.
A tunaninsa Floris tana wajen gasa, dan bai ga fitarta daga wajen ba, hankalinsa na kan Sweetie, so bai san ta fice ba, hakan yasa ya koma can dan su yi rawa da ita.
Ita kuwa Sweetie Ronnie na tafiya ta miƙe zaune, dama ba wani barcin da take ji, so take ta dawo dan ta zo ta yi masu bincike a cikin gidan.
Kamar wata ɓarauniya haka ta saɗaɗa ta fito waje ta hanyar sanya password na kofar ta buɗe, ya gaya mata password ɗin yanzu.
Ko tsoro babu ga dare wajen karfe 12, ga kuma kanta ko ɗankwali babu, kuma tasan akwai ababen ban tsoro a gidan, amma ko ɗar bata ji ba ta nufi part ɗin Black Tiger.
Kunsan komai ilimin mutum in dai yaro ne to sai yarintar nan ta nuna, a shirmen yarintarta wai tunani take yi Black Tiger ya yi barci, hakan yasa ta lallaɓa dan ta je ta yi mashi bincike a part ɗinsa, Ronnie ya gaya mata akwai kofar sirri na fita daga cikin Daular nan a saukake, amma kofar tana cikin part ɗin yayansa,