Showing 153001 words to 156000 words out of 403653 words

Chapter 52 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

39

da Pretty kafin ya fara tinanin im da zai samo masu abin da zasu ci.

Cike da mama Auta ta ce. "Kai kuma ina wajen kwananka my hero?".

Idanunsa a kan kyawawan hannayenta ya amsa mata da. "Ko lokacin da muke gida ma ai bana da wajen kwana, kullun ina kasancewa ne a kusa da family part dan gadin abin da zuciyata ke muradi".

Dik da tasan ita yake nufi, amma saboda ta ji ya furta ita ɗin da bakinsa yasa ta ce. "Wacece kuma ko mecece kuma abin da zuciyarka take muradi?".

Sarai ya fahimci Zunaira a kullum tana san ganin yana nuna irin zallar son da yake yi mata, hakan yasa take san jefa mashi ire iren waɗan nan tambayoyi. Allah sarki tana san taga yana nuna yana santa tare da yi mata kalamai masu zafi.

"Wata ce wadda zuciyata ke kauna". Ya bata amsa cike da tsoron abin da amsar zai haifar, dan yasan halin kayassa.

"Ban gane wata ba! Wakenan?". Ta yi maganar tana ɗan ɗaure fuska.

"Wata kyakkyawa mai kyan fuska dake ɗauke da lallausan murmushi mai kwantar da hankalin assistant commander, murmushinta yana sakani manta in da nike, murmushinta yana sawa in ji kamar an bani kyautar gida a aljanna, tauraruwar zuciyata wanda haskenta ya haske kirjina dikka, shekin haskenta ya wuci tinaninki, tin daga nesa idan ta doso haskenta yake disashe hasken dikkan wasu halittu dake gefenta, tauraruwar da bana jin za'a samu irinta".

Tin da ya fara waɗan nan zafafan kalaman ta tsaresa da idanu tana kallan kyawawan lips ɗinsa yadda yake ɗan motsasu, yana magana one by one, bata san tana sakin cool murmushi ba ma, ta nitsu tana jin ta a wani duniya da babu hayaniya babu wata yana da zata yi mata tsakani da farinciki. Haƙiƙa akwai tsananin daɗi masoyi ya aika saƙon kalamai ga zuciyar da yasan tana matsanancin kausarsa, tabbas zai ɗarsa bishiyar yarda da kauna mai zafi da bata da iyaka a wannan zuciya.

Ganin tana zuba sanyayyar murmushi ba tare da tasan tana yi bane yasa bai san lokacin da ya kashe mata ido ɗaya ba. Sai ganinta ya yi ta ɗan zaro idanu tana ɗage mashi gera ta kuma faɗaɗa murmushinta.

"Murmushinki abin so ne har ga makiyanki gimbiyata, dik wanda baya san murmushi tabbas bai ga naki bane sarauniya............".

Katse shi ta yi da cewa. "A fadar birnin zuciyar my Hero" . Wato sarauniya a fadar birnin zuciyarsa kenan, ta ƙarisar mashi da maganar.

Ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani irin sanyi tana ratsa zuciyarsa.

"My Hero kasan me?". Cike da farinciki ta yi maganar. Kai ya girgiza mata alamar a'a ba tare da ya yi magana ba. "Kalli cikin idanuna bari mu yi magana". Ta faɗa tana kallansa.

Girgiza mata kai ya yi kafin ya ce. "A'a ba zan iya kallan cikin idanunki ba". In a silent talk mai kama da raɗa ta furta. "Why?".

Ƙasa sosai shi ma ya yi da murya kafin ya amsa da. "Saboda sirrikan da kyawawan idanunki suke ɗauke da su zasu sa zuciyata ta kasa iya shanyewa, ba zan iya ɗauka ba"................. Pretty dai kallansu kawai take yi, yo ita da bata ma gane me suke faɗe, ai gani take yi wani sabon haukan ne suke yi.

"Kai da kake matsayin jarumi, namijin gaske, sadaukin da dauloli suke tsoron jin an ambaci sunansa a cikin mayakan da zasu kai masu hari, sadaukin da ya ciri tuta ya kafa tarihin da ba'a taɓa kafa irinta ba a kaf faɗin kingdom of power, sadaukin da sunansa ke firgita manyan maza yasa hantar cikinsu ta kaɗa, kai fa assistant commander ne na gabaɗaya dangerous warriors, shi ne zaka ce kana jin tsoron kallan cikin kwayar idanu na? Meyasa?". Cike da kwarin gwiwa ta yi maganar.

Nisawa ya yi kafin ya ce. "Ranki ya daɗe dik ajiye wannan a gefe, mata suna da kwarjinin da dik wani girman namiji da ji da kansa yana jin shakkarsu, ga su dai sune ƙasa da mu, amma Allah ya basu wannan dama a kanmu, wlh wannan gaskiya nike faɗa maki, dik namiji yana jin shakkar mace, sai dai ya danne kawai, dik bama wannan ba".............. Ƙasa sosai ya yi da murya kamar sillent talk, sannan ya cigaba da cewa.

"Ke idanunki daban suke da kowace mace, tsoron ganin cikinsu nike ji kada ki hanani yin barci yau". Cikin nitsuwa ya yi maganar................Siririn murmushi ta sakar mashi. "Zan iya samun sunan love apart from ranki ya daɗe?".

Unexpect garin amsa mata idanunsa suka sauka a cikin nata. Wani irin azabbabben shock ya ji tin daga tsakiyar kansa har izuwa tafin ƙafarsa dake cikin takalmarsu na mayaƙa. Cikin sauri ya zare idanunsa unexpext ya sake sauke kallansa a saman kyawawan laɓɓanta da ta ɗan ciza na kasan kaɗan hakan yasa ya kara pink sosai.

Oh god, zuciyar maza ne ta amsa, nan take ya ji shi a matse kamar yana ƙoƙarin shiga out of control, wani irin jan numfashi ya yi mai cike da fassarori dayawa. Ƙasa iya amsa mata ya yi, sai ya ji gabaɗaya kamar an ɗaɗɗaure mashi tongue ɗinsa.

"My Hero lafiya?". Ta yi mashi tambayar bisa famintar da ta yi na ya shiga wani hali. Nisawa ya yi kafin da kyar ya iya buɗan baki yana ɗan girgiza kai ya ce. "Babu komai Hoonaira". ......... Hoonaira ta maimaita sunan tana kallansa, har cikin ranta ta ji wannan lallausan suna mai daɗin ambato, sai ma da ya faɗa da bakinsa ne ta ji wani irin daɗi na daban. HOORAIN AND ZUNAIRA SHI NE YA BADA HOONAIRA LIKE WOW, ABIN YA ƘAYATAR.

"Zan iya tafiya in je in samawa gimbiyata abin da zata ci?". Ya jefa mata tambayar yana kallan gefenta a zahiri, amma a bayan fage face ɗinta yake kallah.

"Ni dai a'a ban yarda ba, ni sai ka kalli cikin idanuna sannan zaka tafi, idan ba haka ba ni bazan ci abinci ba". Kamar zata yi kuka ta yi maganar.

Ɗan jinjina kai kawai ya yi, shagwaɓaɓɓiyar nan tasa tana san ɓallo mashi ruwa ne yana zaman lafiyansa. "So kike yau ki hanani barci ko?"........... Kai ta ɗan girgiza mashi. "Zaka yi barci In Sha Allah in dai muna tare".

"To amin afuwa na je na kawo wa sarauniyata abincin dai tukun nan, idan na dawo sai ki tsareni ki sakani yin dik abin da kike so"........ Jin in ya dawo ta saka shi yin dik abin da yake so yasa ta aminta da ya je to. Cikin zafa ya wuce yana taku cike da jarumta.

Bayansa ta bi da kallo har ya kurewa ganinta, sannan ta riko hannun Pretty suka zauna a wajen da ya tanada masu, cike da tsananin kaunarsa ta fara bawa Pretty labarin irin tsantsar madarar san da take yi mashi.

Shi kuwa neman masu abin da zasu ci ya tafiyi dokinsa na biye da shi a baya. Dai'dai zai gifta tsakanin wasu dogayen bishiyoyi ya hango kamar mutun kuma mace tana ƙoƙarin jan abu a kwando. Da yake yana da zuciya mai kyau sai ya nufeta domin ya taimaka mata.

Ba kowa bace face mammar Kamran, ta ɗebo kayan lambunta dayawa a cikin irin wannan kwando da Kamran yake ɗebo mata ɗin, kwandon yana da girma sosai hakan yasa take jansa da kyar, dan ya yi mata nauyi. Allah sarki Kamran mai yi mata hidimar baya nan, daga ganinta bata da ƙoshin lafiya, da alama tsananin damuwan rashin Kamran ya haifar mata da ciwo, ta yi rama sosai tamkar ba ita ba, shiyasa ma ta kasa iya ɗaukar wannan kwando, jikinta har wani kerma yake yi.

Taimaka mata ya yi ya ɗauka mata suka haura saman tsauninsu, kun san Mamma bata yarda da baki, dan haka shi ma bata aminta da shi ba, sai dai shi ko da ya nufota bai yi mata magana ba, kwandon kawai ya ɗauka mata da hannu ɗaya ya haurar mata sama, a bakin kofar kogonsu ya ajiye mata ya juya ya sauka, bai yi mata magana ba ya wuce abinsa.

Dik yadda bata san mutane yau karo na farko da aka taimaka mata ta ɗan ji a ranta ashe ba dikka mutane bane na banza, ashe akwai na kirki? Ashe akwai masu taimako? Bata taɓa zatan akwai wanda zai iya taimaka mata ba a rayuwarta, Allah mai iko, yau ta ga sabon abu.

Shi kuwa yana sauka ya bazama nemanwa gimbiyarsa abinci, bai dawo ba sai da duhu ta fara yi, sannan ne ya dawo ɗauke da kala kalan kayan cima da za'a iya samu a wannan dajin. A lokacin Pretty da Auta sun yi alwala sun yi sallah suna zaune a waje guda suna hira.

Suna ganinsa suka miƙe, a gabansu ya dire masu kayan da ya kawo masu, Auta ce ta kallesa cikin ido. "My Hero muna godiya da kulawan da kake bamu, Allah ya barmun kai ya kare mun kai da kariyarsa".

Ƙasa ƙasa ya amsa da amin tare da miƙewa yana faɗin. "Zauna kici ko? Kinga tun ɗazun kika ce kina jin yunwa". "To kai ina zaka je ba zaka zauna mu ci ba?". A shagwaɓe ta yi maganar. "Ba zan jima ba, yanzu zan zo". Ya faɗa cike da san ya tafi.

Bata san sake jefa mashi wata tambayar, dan tasan halinsa sam bai cika san tambaya ba, tana kaucewa abin da baya so, sai kawai ta amsa da okey tare da komawa ta zauna suka fara ciye ciyensu ita da Pretty.

After some minutes. Hannunsa ɗauke da wasu itatuwa ya dawo wajen, wuta ya zo ya kunna masu sannan ya matsa gaba ya ɗauro alwalarsa a wajen ruwan gudun dake kusa da su. Sallar mangariba da isha'i ya haɗa dikka ya yi, saboda matafiyi ne shi wanda babu abin ganin lokacin a tattare da shi, hasalima bai iya gane gabas ba sai dai ya kintata ya yi sallar kawai.

Bayan ya idar ya yi addu'a sosai, dik Zunaira tana ta aikin kallan motsinsa, a yanzu basa iya ganin face ɗin juna saboda duhu, sai sun matsa kusa da wutar da ya kunna suke iya ganin juna.

Bayan ya kammala ya matsa kusa da wutar ya zauna tare da lankwashe kafafunsa yana kara wasu itatuwa a ciki dan wutar ta cigaba da ci har wayewan gari kada ta mutu. Auta and pretty kuma suka tashi suka gabatar da sallar isha'i bayan sun gama cin abin da suka ga zasu iya ci.

Shiru ya zauna yana tinanin irin kalubalen da zai fuskanta a kan soyayyarta, sai dai ya kudurta a ransa ko mutuwa zai yi ba zai janye ba tin da ya rigada ya sanar da ita cewa yana santa, sun kuma yi wa juna alkawarin ba gudu ba ja da baya.

Ya zurfafa cikin tinanin da yake yi, kamar daga sama ya ji saukar hannayenta a saman shoulders ɗinsa, ta zarosu ta gabansa ita kuma tana ta bayansa, tana durkushen a saman gwiwowinta, ta ɗan manna kirjinta da bayansa kaɗan, hannunta na rike da fresh apple jajir mai kyau da zaƙi.

Saitin ɗan bakinsa ta kawo mashi apple ɗin, a daidai saitin kunnensa ta tsayar da laɓɓanta, silent talk ta yi wajen furta mashi............ "My Hero kai fa baka ci komai ba, ni kwata kwata ban ga kaci wani abin na fa, ka karɓi wannan ka ci". Ta kai karshen maganar tare da kara matsar mashi da apple ɗin a dab bakinsa.

Rasa me zai yi ya yi, ya rasa a wace duniya yake, ya rasa a wani matsayi zai ajiye kansa, yau shi ne tare da abar da ya fi kauna sama da komai nasa, kuma ga su a ƙeɓaɓɓen waje, har da kulawa na musamman take bashi, bayan Abbonsa babu wanda ya taɓa damuwa da ya ci abinci ko bai ci ba sai ita, kai ba zai taɓa manta wannan rana ba a rayuwarsa.

Alhamdulillah ya rinƙa nanatawa a cikin zuciyarsa, ya ƙasa iya buɗe bakinsa ya karɓi kyautarta a garesa. Ƙasa sosai ta yi da murya, kamar mai raɗa ta sake cewa. "My Hero ba zaka ci kyautar da ya fito daga hannu na bane? Ko kuma sai na yi maka kuka ne? Da kaina fa zan baka".

Oh my god, wani irin nisawa ya yi, ajiyar zuciya mai daɗin gaske da bai taɓa sauke irinta ba ya sauke, a hankali ya buɗe ɗan bakinsa ta sanya mashi apple ɗin, kaɗan ya gutsira yana jin tamkar babu abin da ya kai wannan apple ɗin daɗi a duniya....... Oh soyayya ruwan zuma.

Sosai ta ji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta na ganin ya gutsira, har ajiyar zuciya ta sauke, wannan ajiyar zuciya da ta sauke ji ya yi tamkar ta kara lulluɓe zuciyarsa da bargon farinciki ne. Ita dai Pretty sai sanya kananan itatuwa take ta yi a cikin wuta, sam hankalinta baya ma kansu baiwar Allah.

Sake matsar mashi da apple ɗin kusa da bakinsa ta yi, dan farinciki haka ya rinƙa gutsira yana ci har ya cinye ba tare da ya sani ba, cike da zumuɗi ta zame hannayenta daga shoulders ɗinsa, tana ƙoƙarin barin wajen tana faɗin. "Bari in karo maka wani my Hero".

A hanzarce ya ɗan juyo ya rike hannunta a cikin nasa. "Please ba sai kin karo mun ba, wanda kika bani ya wadatar, na ƙoshi sosai saboda albarkan dake tattare da hannunki".

Ƙayatattcen murmushi ta sakar mashi, wutar tana haskasu gwanin ban sha'awa, bata yi musu da shi ba ta yi na'am da zancensa, sannan ya saketa. A hankali ta dawo gefen damansa ta zauna suna fuskantar wutar, kanta ta kwanto da shi a saman damatsan hannunsa tare da kamo hannunsa guda ɗaya.

Sillent talk ya yi wajen ce mata. "Baki jin tsoron dajin nan?"........ Ƙara yin lamo a jikin hannun nasa ta yi. "Ni da nike tare da kai kuma my Hero tsoron me zan ji?". Ɗayan hannunsa ya kai saman hannunta da ta riƙo nasa.
"Kina ƙara mun kwarin gwiwa sosai my Hoonaira".
A ɗan shagwaɓe ta yi magana ƙasa kasa ta yadda ita kanta tasan ba zai ji me ta faɗa ba. "Ban ji me kika ce ba". Ya tambaya yana ɗan juyo da face ɗinsa saitin tata, irin mutum ya juyo ya kalli gefen shoulder ɗinsa haka.

Sake yin maganar ƙasa ƙasa sosai ta yi, still dai bai ji me ta ce ba, hakan yasa ya ɗan kwanto da kansa kusa da nata kaɗan ya kara tambayar me ta ce.

"Barci nike ji kuma san yi nike ji". Shi ne abin da ta faɗa. Tabbas akwai sanyi sosai a wajen, shiyasa ma ya kunna masu wannan wutar dan wajen ya ɗan ɗumama.

"Tashi in ɗauko maki rigan sanyina na ɗazun ko?". ............ Make kafaɗa ta yi. "Ni dai a'a, ba zan iya tashi ba". Kallan Pretty dake ta doka hamma ya yi, da yake ita ta saba yin barci da wuri baiwar Allah, har idanunta sun yi ja alamar barci.

"Pretty ɗauko mun rigan sanyina a wajen kayanmu, daga nan sai ki je ki kwanta dan naga kamar barci kike ji"............ Da okey ta amsa mashi tare da miƙewa ta isa ga kayansu.

"ko kema zaki je wajen da na tanada maku ki kwanta ne?". Ya jefa mata tambaya yana zame hannunsa daga kan nata....... "A'a ni dai zan kwanta kusa da wutar nan dan in rage jin sanyi". .......... Jinjina kansa ya yi alamar to. Kawo mashi rigan sanyin Pretty ta yi, karɓa ya yi ta wuce ya je ya kwanta a wajen nasu tana yi masu good night.

Cikin sanyin murya haɗe da tausasawa da lallaɓawa ya ce. "Ɗaga in saka maki rigan kin ji?".
Jiki dik kasalar barci ta ɗan ɗaga shi tana turo baki. Sorry ya ce mata kafin ya ware rigar ya sanya mata, sannan ta sanya shi dole ya miƙe mata kafafunsa ta tada kai da laps ɗinsa tana daka hamma, lamo ta kwanta a laps ɗin nasa, wutan yana ɗan ratsata kafin wani ɗan lokaci barci mai daɗin gaske ya yi awon gaba da ita.

Shiru ya zuba mata idanu yana ta kallan face ɗinta, ya ƙasa zare kallonsa daga kanta, kamar yadda yaga rana haka ya ga dare. Tana kwance a kafarsa yana ta kallan face ɗinta har dare ya tsala, Pretty ta jima da yin barci abinta.

Asuban fari Auta ta farka, ta sha madarar mamakin yadda ta kwnata daren jiya ta barshi haka ta wayi gari ta same shi, cike da mamaki da tausayawa ta tambaye shi bai yi barci bane?. Kai ya gyaɗa mata almar e bai yi ba.

"Meyasa to?". Ta jefa mashi tambayar tana kallansa. "Tashi mu je mu yi sallah mu cigaba da tafiya, dan mu isa gida da wuri rana na ganin ido". Shi ne abin da ya faɗa a maimakon ya bata amsar tambayarta a garesa. "Ni sai ka bani amsata zan tashi". Kamar zata yi kuka ta faɗa.

"Kin manta jiya na faɗa maki cewa bana barcin dare? Kin kanta na faɗa maki gadin gimbiyata kawai nike yi ne?"............... Tina maganganunsu na jiya ta yi, abin ya kara bata mamaki, a tinaninta ya faɗa mata hakanne kawai saboda soyayya, bata san dik kalamansa hakikanin gaskiya ce wanda babu mix ba, baya faɗar kalamai dan jin daɗin soyayya ko kuma daɗin bakinsa, dikkan abubuwan da yake faɗa gaskiya ne kuma yana iya aikata fiye da hakan a kanta.

Sai yanzu ta kara tabbatarwa da kanta lallai ta yi babban sa'ar da samun irinsa abu ne wanda zai bada wahala, lallai Hoorain one in million ne. "Tashi to tin da na baki amsa".

Ajiyar zuciya ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login