Showing 6001 words to 9000 words out of 403653 words
iya zaɓa, nama kawai ta sani wannan ma dan wanda yake taimaka masu a forest yana kawo masu nama sosai, so tun kafin ta makance tasan ya kamannin namar yake.
"Ko dai in zaɓa maki ne?".
Ya yi magana idanunsa a kanta.
Ɗago kai ta yi suka kalli juna. "Ni fa Ronnie ban san waɗan nan abubuwan ba, amma dai ka bani naman ya fi tun da shi nasani".
Tun da ta fara magana ya kafe ɗan bakinta da idanu yana jin wani irin shaukin yadda take motsa laɓɓanta wajen furta word, har ji ya yi baya son ta dakata da yin magana.
"Namar jimmina ce da ta ɗawisu, sannan akwai ta ɓauna, wanne zaki ci".
Yadda ya yi maganar sai ya burgeku, saboda idanunsa a kan lips ɗinta ya yi, kuma ya yi maganar kamar wanda bakinsa yake ciwo.
"Dik abin da ka lissafan nan ban sansu ba, ni dai nama kawai na sani".
Hannu ya kai saman tray ɗin ya ciro mata wani haɗaɗɗe tsadadden plate mai shake da namar ɗawisu wanda ya ji gashi mai kyau, sai tashin daddaɗar kamshi yake yi ya ji kayan haɗi.
"Kin ki ki faɗa mun sunanki na ainahi ko Sweetie?"
Yana magana yana ɗauko kananan wukake haɗe da fork domin ya taimaka mata wajen yanka namar ta samu ta ci.
Ɗan siririn murmushi ta saki har sai da dimples ɗinta suka lotsa kafin ta ce. "Sunana na ainahi Sweetie".
"Ba gaskiya bane! Sweetie ba suna bane".
Shiru ta ɗan yi, wani zuciya yana ce mata ta faɗa mashi gaskiya, ta yarda da shi, shi ɗin ba mugu bane, wani zuciya kuma yana gaya mata kada ta yarda da shi, dan mom ɗinsu ta gargaɗesu a kan kada su yarda da kowa a duniya idan ba Kamran ba!.
"Don't restrict yourself, in baki son gaya mun ba sai kin sha wahalar tuna abin faɗa mun dan in ji daɗi ba, don't worry, a dik yadda kike zan ji daɗin kasancewa dake, so forget about the name, yanzu karɓi abinci ki ci".
Ya yi maganar ne bayan ya saita mata fork mai ɗauke da gasashen namar ɗawisu a saitin ɗan bakinta.
Sosai ta ji wani irin a jikinta na jin furucinsa, jikinta ya yi sanyi, bai kamata ace ya nemi sanin wani abin dangane da ita ta ɓoye mashi ba, amma ya zata yi to? Dole ta bi umarnin mom ɗinsu.
Buɗe ɗan bakin nata ta yi ya saka mata namar, suna aikin ganin juna ido cikin ido.
"Ka yi rashin lafiya ne Ronnie?".
Kai ya girgiza mata alamar a'a, sannan ya ɗaura da cewa. "Me kika gani?"
B komai ta bashi amsa tana ƙoƙarin ɗauko ruwan roba dake cikin tray ɗin. Hannu yasa ya karɓi ruwan tare da ɓalle mata bakinsa, sannan ya zuba mata a tsadadden glass cup da ya zo da shi.
"Yau zaki bini church ko?".
Ya yi magana yana miƙa mata ruwan.
Karɓa ta yi ta kafa a bakinta, kusan rabi ta sha kafin ta cire, tana ƙoƙarin ajiyewa a kasa ya kai hannu ya karɓa, bakinsa ya kai ya shanye ragowar tare da ajiye cup ɗin ya zuba mata idanu tana taunar namar da ya bata bayan ta cire cup daga bakinta.
"Mu bama zuwa church ai".
"Why?". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Coz I am a Muslim".
"Komai nace maki sai ki ce mun baki sani ba, to ya aka yi kika san church kika kuma san banbancin addininmu?".
Ya jefa mata tambayar yana ɗaga mata gera ɗaya, har lokacin idanunsu a kan face ɗin juna.
"Saboda shi abu ne wanda ya shafi addini, ko ban san church a ido ba na karanta labarinsa a litattafanmu na addini".
Ɗan zaro idanu kaɗan ya yi kafin ya ce. "Okey kenan in na fahimta addininku ya yi magana a kan namu?".
Jinjina mashi kai ta yi haɗe da cewa. "Kamar yadda ainahin littafin addininku yake magana a kan musulunci ba".
Ɗan girgiza kai ya yi. "Ban gane ainahin littafinmu ba? Ko so kike ki ce yanzu ba na ainahi muke amfani da shi ba?!".
Haɗiye namar dake bakinta ta yi kafin ta amsa mashi da. "Kusan hakance, ainahin littafinku ai annabinmu ne ya zo da ita, kuma magana take a akan musulunci da dokokin Allah da dai sauransu, amma yanzu gabaɗaya an canza littafin da rubutun cikinsa, masu son zuciya tun tsawon shekaru da suka gabata sun canza wasu abubuwa, a hankali hankali suka rinƙa zare wasu shafuka masu muhimmanci daga ciki, suna shigo da na san zuciyarsu dan su ɓatar da alumma, haka mom ɗinmu ta ce mana".
Tun da ta fara magana idanunsa yake a saman laɓbanta babu ko kyaftawa, sai dai kunnuwansa suna saurarenta da kyau, ƙwaƙwalwarsa kuma yana jujjuya mashi zantukan nata, lallai ba shakka ta zo da babban al'amari, ya za'ayi ta ce an canza masu littafi? Ƴar karama da ita da wanna zancen, lallai so take ta jawa kanta bala'i, dan kuwa ba zata iya wanna faɗar ba!!.
Sai da ta dasa aya a maganar ne ya sauke ajiyar zuciya tare da ajiye fork na hannunsa, sannan ya ɗan gyara zama kaɗan.
"Addininki ne ya ce maki an canza wasu shafuka cikin littafinmu ko kuma littafinku ne ya ce hakan?". Ya jefa mata tambaya.
"Ko ɗaya daga ciki, ba addinina bane, hasalima ni addinina kyakkyawar zato yake yi wa kowa".
"To ya akayi kika san and canza littafinmu domin a cigaba da gusar mana da hankali muna tafiya a kan ɓata?".
A gaskiya Ronnie yana da saukin kai sosai, kuma ga dikkan alamu yana bala'in jinta har cikin ransa sosai ne yasa har ya iya jure maganganunta, kun san ba kowa zai yarda acewa da littafinsa da kuma malaman da yake bi haka ba, ba wanda zai yarda a ƙaryata malamansa ko kuma ace suna cutar da mutane wajen canza maganar gaskiya izuwa ta karya, amma shi cikin kwanciyar hankali yake yi mata tambayoyi ta hikima haɗe da ilimi, gaskiya ilimi ta yi a rayuwa, tana sanya iya magana da zama da kowa lafiya sosai, jahili yake faɗace faɗace ba mai ilimi ba!.
"Zan gaya maka yadda aka yi na sani, zan kuma baka hujoji masu karfi da zaka yarda dani, amma sai na koma wajen mu tukun nan, dan dik hujojin suna forest ɗinmu".
Shiru ya ɗan yi yana tunanin yadda za'ayi ta bar empeir ɗin nan har ta je ta bashi hujojin, ga shi yana son waɗan nan hujoji ko dan ya gani da ido, to me abin yi? Dan dai Black Tiger ba barinta zai yi ta tafi ba tare da ta bada Spender ba!.
"Zaka taimaka mun na bar nan?".
Tambayarta da ya ji takmar saukar aradu kenan, har sai da ya ji kansa ta ɗan juya mashi tana wani sarawa.
Idanunsa a cikin nata bai iya bada amsa ba, dan bashi da ta cewa.
"Ronnie ina kewar ƴar uwata sosai, ina son komawa forest domin in je in ganta, please ka taimaka mun na bar nan ka ji?".
Tamkar zata sanya kuka ta kai karshen maganar.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ɗan jinjina mata kai haɗe da cewa. "Zan taimaka maki ki bar nan kamar yadda kika buƙata, amma da sharaɗi guda biyu, idan kika mun abubuwa guda biyun nan tabbas zan fitar dake daga nan koda kuwa hakan zai zama sanadiyyar mutuwata!!"....... BABBAR MAGANA!!.
A hanzarce ta ce. "Menene sharaɗin? Ka gaya mun kome ne zan yi".
Cigaba da yanka mata namar ya yi yana faɗin. "Zuwa dare zamu yi wanna magana, zan gaya maki sharaɗin, yanzu dai ci abinci ki je ki yi wanka".
Bata yi mashi musu ba, dan ta lura musu yana ɗaya daga cikin abin da baya so, tun zuwanta empeir ɗin ta fahimci hakan a tsakaninsa da su Floris, dan haka sai ta yi shiru tana karɓar namar da yake bata har sai da ta ƙoshi.
Sannan ya rakata toilet ɗinsa da kansa ya fito ya barta a ciki, ta yi tsaye tana ganin ikon god, duniya guda kamar ba za'a mutu ba.
Shi kuwa ya dawo ya kwashi kayan abincin ya nufi waje da su.
Yana fitowa babban parlourn kasa ya isko Floris ta ci kwalliyar sexy dress, ta yi kyau sosai, ɗan rigarta a iya cibiya ya tsaya mata, sai sket da bai gama rufe gwiwanta ba black color, rigar kuma white, da yake in baku manta ba mutanen birnin Black world suna da yelwar tsawon gashi sosai kamar turawa, haka ta sake dark brown hair nan nata har baya, sai sheki yake yi yana curlyn.
Ɗan bakin nan nata ya sha lips balm sosai sai sheki yake yi, ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya tana rike da wayar Ronnie tana latsawa, ta yi kyau irin sosai ɗin nan.
Tun da ya sako kafarsa a saman stair case ɗin yake binta da kallo har ya karisa saukowa. Jin motsin mutum yasa ta yi saurin ɗago kanta da kallonta a kansa.
Ganin shi ne yasa ta mike har da haɗawa da ɗan gudunta ta nufesa. Buɗe mata hannu ya yi ta faɗa saman Wrestling chest ɗinsa.
Tana faɗawa jikinsa wani Robbot ya kariso wajen ya karɓi kayan abincin dake hannunsa ya juya ya nufi hanyar kitchen da shi.
Shi kuwa kamar wata ƴar tsana haka ya ɗagata sama sai saman shoulder ɗinsa suka juya izuwa sama.
"I really missed u mine". Ta faɗa tana saƙalo wuyarsa.
Yau yana cikin farinciki ya ga Sweetie kuma Black Tiger ya barsu a tare, hakan ba ƙaramin farinciki ya haifar mashi ba, cikin sanyin murya ya amsa mata da.
"Missed u too babydoll".
Ɗan bakinta ta kai saman lallausan kumatunsa ta fara sumbata tana goge mashi lips balm dake saman lips ɗinta.
"Zaki fara ko?".
A shagwaɓe ya yi maganar.
"Ba kai ne ka barni sai da na yi missed ɗinka sosai sanna ka waiwayeni ba?".
Yana cigaba da tafiya ya nufi room ɗinsa ya gangaro da ita izuwa saitin wrestling chest ɗinsa, ya zama suna kallon juna. Fingerprint ya sanyawa door room ɗinsa ta buɗe ya shige ciki da ita yana ta kallon face ɗinta.
Saman bed ya sauƙeta, kamar mai jin barci ya furta. "Ki taya Sweetie ta sanya kaya ta shirya ina zuwa".
Ta ɗan yi mamakin jin yadda ya yi maga a kasale sosai, ta san shi ɗin shagwaɓaɓɓe ne idan ya yi ra'ayi, sannan tasan riƙaƙƙene ta ɓangaren iya kalaman soyayya, amma bata taɓa jin ya yi magana a irin wannan yanayi ba, bata san cewa yanzu ya fara girma yana jin feeling sosai bane, da ai sai dai ya yi dik abin da zai yi na shagwaɓarsa baya jin komai, amma yanzu girma ta fara zuwa, ya fara amsar sako.
Bai jira amsarta ba ya juya ya fita. Bai zame ko'ina ba sai room ɗin Black Tiger.
After some minutes. Ya fito sanye da sport wears ya nufi room ɗinsa.
==========🔥🔥🔥===========
ALKALAMIN
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
*Ina yi wa ɗaukacin al'ummar musulmi murnar shiga sabuwar shekara ta 2025, Ubangiji Allah ya sadamu da alkhairan dake cikinta, Allah ya nisantamu da sharrin dake cikinta, Ubangiji Allah ya shiga lamuranmu ya kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasarmu da ma dikkanin in da musulmi suke, ya Allah yasa mu cika da kyau da imani ya kuma kara mana kaunar manzon rahma manzon tsira.*
Wani birki ya ja a bakin kofar room ɗin ta ciki, idanu ya zaro waje yana kallonta, tamkar kwayar idanunsa zasu faɗi ƙasa. Sam bai san lokacin da bakinsa ya furta wow ba.
Like wow, ni ma dai sai da na furta wannan wow ɗin a lokacin da idanuna suka sauka a kan Sweetie sanye da kayansa na sport, kun san shi mayen wasanni ne, yana da dik sport wears na wasanni kala daban daban.
Floris da iya tsiya sai ta bata riga da wandonsa na football ta saka, wandon ya yi mata tsawo sosai, rigar kuma da yake roba ce kuma sababbi ne bai sakasu ba bare faffaɗar wrestling chest ɗin nan nasa ya buɗesu sai ya ɗan kamata kaɗan. Floris ta gyara mata golden white hairnta tare da sanya mata mayukan gyaran kansa, gashin ya yi bala'in kyau sai sheki yake yi, yanzu ne ma tsantsar kyan gashin ya kara bayyana da ya samu gyara, wlh kamar ka kwace gashin dan kyansa, dole ashe ya zama mafi tsada a duniya, ashe haka yake da balai'n kyau, gyara ne dama bai samu ba.
Kasa ƙarisowa cikin ɗakin ya yi, kawai ya harɗe hannu saman kirji yana binta da ido, dik sai ya ji wani irin wahalallen kasala ya kama shi.....................
"My ka shigo mana".
Cewar Floris dake dake mashi saman bed kamar wata matarsa, ita kuma Sweetie tana tsaye gaban mirrorsa tana ganin kayan yadda ya dace da ita, sai a yau ta tabbatar da ashe kyakkyawa ce ita fa, ta mace da kallon kanta.
Jin Floris ta yi magana ne yasa Sweetie juyo da kallonta izuwa door room. Ganin shi ne yasa ta saki cool murmushi har sai da dimple ɗinta suka lotsa.
Hakan ba ƙaramin kara jan hankalinsa ya yi ba, sai ya ji shi a wata duniya.
"Ronnie na yi kyau?". Cikin sanyin murya ta yi maganar.
Jinjina kai kawai ya yi bai iya furta uppan ba, saboda ta yi mugun tafiya da tunaninsa, yama rasa me zai ce.
Kara faɗaɗa murmushinta ta yi, ta ji daɗin ya ce ta yi kyau. Floris dai binsu da kallo take yi tana ta sakin uban murmushi abinta, da alama ta ji daɗin kasancewarsu a tare.
"Sweetie wai ke bakya shiga damuwa ne?".
Cewar Ronnie, bai yi zaton zai ga murmushi a kan face ɗinta ba, saboda a tunaninsa wannan wahala da ta sha zai sa dik wani sauran farinciki da ya rage mata ya kau daga fuskarta.
"Meyasa zan shiga damuwa Ronnie?". Still akwai murmushi a saman face ɗinta ta bada amsar. Ta yi maganar tana jingina bayanta da jikin mirror.
"Naga kin sha wahala ne shiyasa, a tinanina zaki shiga damuwa a kan hakan, kuma ga ƴar uwarki bata a tare dake, dik da haka baki shiga damuwa a kan hakan ba!".
A kasale sosai voice ɗinsa take fita.
Ko a jikinta kamar an yakushi kakkausa, cikin sanyin murya ta ce.
"Ni da nike da Allah da manzonsa meyasa zan ji wani damuwa dan wani bawan Allah ya cusguna mun? Dik abin da kaga ya faru dani mukaddari ne daga Allah, kuma mu mun yi imani da Allah dole mu karɓi kaddararmu hannu bibbiyu a dik yadda ta zo mana in ma mai kyau ko akasinta!".
Baiwar Allah tana magana tana murmushi.
Ɗan zaro idanu Floris ta yi tana kallon Ronnie, ta ji sabon karatu yau. Shi ma Ronnie zancen Sweetie ya taɓa zuciyarsa, dan haka ta wutsiyar idanu ya kalli Floris while ainahin kallonsa yana a kan Sweetie, tabbas har cikin ransa ya ji yana son sanin wannan Allah da manzonsa da idan ka riƙesu ka bi umarninsu ba zaka taba shi damuwa ba, dik wahalar da Sweetie ta shiga, ga makanta dik, uwa uba aka rabata da ƴar uwarta, ga rashin iyaye, dik bata taɓa shiga damuwa ba dan ta rike Allah da Manzonsa, dik azabar Black Tiger bai ɗaga hankalinta ba saboda ta rike Allah, hakika zai so shi ma ya san ta yadda zaka bi ka rike Allah har ka more haka, sai dai kuma da kamar wuya in dai yana Black world.
"Ya kayi shiru Ronnie?". Cewar Sweetie.
Girgiza kai ya yi ba tare da ya furta uppan ba, amma abin ya bashi matukar mamaki kuma ya ratsa zuciya da gangar jikinsa, sai nanata kalmar idan ka rike Allah da manzonsa, ka yi imani da su ba zaka shiga damuwar komai ba, Allah ba zai bari ka ji kunci ba, sai nanatawa yake yi a cikin ransa yake yi, like wow abin ya ƙayatar da shi ba kaɗan ba.
"Ronnie zaka je wasa ne?". Floris ta jefa mashi wannan tambaya.
Kai ya gyaɗa mata ba tare da ya yi magana ba, da alama jikinsa ya yi weak sosai, bawan Allah ya ji ɗaya daga cikin karfin ubangijin gaskiya!!.
Idanunsa a kan Sweetie, ita ma tana rike da wayarsa da ta karɓa daga hannun Floris dan ta gani, amma kallonta da nutsuwarta na'a kansa, Allah Ronnie ko baka son ganin kowa in yana waje sai ka ji sha'awar ɗaura idanunka a kansa, saboda kyau, sai ma idan yana murmushi tare da ƴanmatansa.
Ga shi ya karyawa Delisha kafa tana can tana jinya, wato Ronnie ma fa mugune wata sa'an, yanzu haka ta fara samun sauki tana koyan takawa da sanda, amma ta ji a jikinta kam, ta gane annabi Isa ba ɗan Allah bane manzon Allah ne ƴar banza.
"Ronnie zan bika wajen wasan ka ji?". Cewar Sweetie.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Zo mu je, time ya cika, tun da kuka zo gidan nan ke da Floris kullum nine bayan shiga wajen wasa".
Murya a kasale ya yi maganar.
"Meyasa to?". Sweetie ce ta jefa mashi tambayar.