Showing 330001 words to 333000 words out of 403653 words
ke ɗaukar hoton da haske ya samar, sai ta aika wa kwakwalwa ta hanyar jijiyoyin gani, ƙwaƙwalwa itake tantance menene a wajen ba ido ba!. To haka a camera ma, akwai image sensor, wato kamar CMOS ko CCD wanda ke ɗaukar hoton da haske ya samar sannan ya juya shi zuwa hoto har ma a iya adanawa kamar yadda ƙwaƙwalwa take adana hoton da ido ya gani, in kaga abu ai ka rigada ka gani ne, ya zauna a kwakwalenka".
"Na huɗu shi ne Autofocus, wato daidaita tsawo. Kamar yadda idon mutum ke daidaita mayar da hankali kan wani abu cikin sauri. To haka camera ma tana amfani da autofocus system dan tabbatar da cewa hoton yana cikin sharp. Abu na biyar shi ne HDR, wato high dynamic range da Contrast Perception. Ido yana iya bambanta haske da inuwa fiye da yawancin Cameras. Dan haka an ƙirƙiri HDR technology a camera ne dan taimakawa wajen ɗaukar hotuna masu daidaiton haske da duhu sosai, kuma har yanzu mun ƙasa iya kirkirar camerar da zata iya daidaita abu sak yadda ido zata iya yi, dik da kullum muna cikin kara faɗaɗa bincike ne dan gano manyan abubuwa masu amfani da zasu daidaita komai, shiyasa zaki ga duniya tana kara gaba Camerori masu karfin ɗauka suna kara fitowa, har yanzu ƙoƙari muke yi muga camera ta yi karfin ɗauka kamar ido dik da mun san babu wanda ya isa ya yi abu dai'dai da Allah, muna dai kwatantawa ne iya baiwar da Allah ya yi mana!".
"Dik da cewa camera ta zamani tana da fasahar da ke kama da yadda idon mutum ke aiki ko in ce maki mun kwaikwayi ido mun kirkireta, to har yanzu idon ɗan adam ya fi ƙarfi wajen fahimtar launi, haske, da zurfin hotuna fiye da kowace camera da muka ƙirƙira a duniya, muna dai iyaka bakin ƙoƙarinmu, amma Allah ya wuci tinanin mutum, babu wanda ya isa ya yi dai'dai da shi, sai dai mu yi ta kwaikwayo dan samawa al'umma saukin abubuwa!". Ya kai karshen maganar yana ɗan jan lallausan kumatunta, ta wani natsu tana suararonsa.
"To shi ne yanzu Yah Omerish kake kwaikwayon kunne?". Like wow ta yi tambayar, abin ya bata mamaki ne sosai, wato dai dik wani kimiya kwaikwayo ne daga Allah, sai dai su Allah ya basu baiwar iya zaƙulo halittun da idan sun kwaikwaya sun yi wani fasahar da shi zai taimakawa al'umma sosai, lallai su ƴan baiwa ne sosai!!...... Jinjina mata kai ya yi alamar e yana kirkiro naura mai karfin ji sosai ne, zubawa laptop ɗin nasa idanu ta yi tana kallan yadda yake ta ƙoƙarin faɗaɗa bincikensa, ya zuba tsantsar basira a kan aikinsa.
Suna a haka tiger ɗinsa ya shigo wajen da gudu yana gurnani. Ai daga Auta har Prettyn dikka haukace mashi suka yi, gabaɗaya suka rungumesa suna ihu. Sai suka sa ma ya rasa me zai yi, saura kaɗan su jefar mashi da laptop a ƙasa Allah yasa ya tare. Ya ƙasa yin komai dan sun nukunkume shi, ga ihun da suke yi. Cikin harcen farasanci ya rinƙa cewa damisan ya tafi, amma shi ma yaki tafiya, dan iskanci, sai ma tsalle da ya yi zai haye jikinsa. Ai wani ihun da Auta ta kurma sai da ta sanya damisan dakatawa. Daga bisani ya juya da gudu ya bar wajen, ajiyar zuciya Smart ya sauke kafin ya ce. "To sarakan tsoro, sai ku sakeni ai tin da ya tafi". Auta ce ta fara cewa. "Yah Omerish ka leƙa tukun nan ka tabbatar da ya tafi ko yana nan". "Matsoraciya kawai, ya tafi, kuje ku shirya ma ku zo mu je in kaiku yawo tin da weekend ne".
Ai da jin haka Auta ta yi gaggawar sakinsa, dama ta jima tana rokon ya fita da su, sai ya ce masu yana busy, to yau dai zasu fita, cike da ɗauki ta ja hannun Pretty suka nufi stair case dan su je su shirya. Da kyar Pretty ta yarda ta bita, sai da ta ce mata tiger fa ya sauka ƙasa gabaɗaya, yana harabar gidan, sannan ne ta yarda ta bita, suna shiga bedroom ɗinsu suka garƙame da key wai dan ma kada tiger ya biyosu ciki.
Shi kuwa komawa ya yi ya zauna yana jiran ya ga wanenen zai auro saman, dan zuwan da damisan nan ya yi wajensa labari ya kawo mashi a kan ya yi baƙi, yana fahimtar dabbobin nasa, kun san idan ka zauna tsawon shekaru da dabba kuka saba to fa zaka iya fahimtar dik abin da take ciki. Yana zama sai ga wasu zaƙwaƙuran matasa biyu sun hauro saman, ɗaya fari tas kaman madara, ɗayan kuma chocolate color, kusan kansu ɗaya, and ɗaya farin kaman bature ne, ɗayan kuma Africans ne, dikkansu kyawawan gaske ne, tsayayyun maza, dik in da ake neman namiji to sun kai, ko da yake tin da kuka gansu a tare da Smart kun san suma ba baya ba, dan baya abota da marasa fasali marasa ilimi.
Kai tsaye suka nufosa, da ido ya bisu har suka iso shi, hannu ya miƙa masu suka yi musabaha kafin su samu waje saman sofa suka zazzauna. Cigaba ya yi da aikin da yake yi tare da faɗin. "Zash yaush ka dawo?". Wannan handsome chocolate guy ɗin ne ya amsa mashi da. "Yesternigh". Jinjina kai ya ɗan yi kafin ya juyo da kallansa a kan ɗaya farin. "Bobo is there anything problem?".
Fuska ɗauke da damuwa Bobo ya amsa mashi da. "Yeah". Zuba mashi idanun suka yi suna sauraransa. Cigaba ya yi da cewa. "My baby, yau da kewarta na tashi sosai". Ɗan kawar da kansa Smart ya yi. "Sorry, komai zai wuce, abu kaɗan ya rage mana".... Nisawa Smart ya ɗan yi kafin ya kawar da kallansa daga kansu, a ransa yake faɗi shi bai ga amfanin damuwar da bobo yake yi a kan wani abin bama, yakama ne ma a ce ya manta da kowa da komai na rayuwarsa ta baya tin da yanzu komai ya canza.
Uhm wanenen bobo da ake so ya manta da komai na rayuwarsa ta baya? Mu ji tarihinsa kaɗan, dan shi ma yana daga cikin manyan stars na RAWANIN ZALINCI. RAWANIN ZALINCI labarine a kan ɓangarori biyar, dan haka manyan jaruman cikin littafin zasu iya kasancewa su bakwai ne, amma idan kuka san wanenen Bobo zan banbanta maku sani abin.
-------------------------------------🔥♥️
BLOOD CROWN. shi ne sunan masarautar su Bobo, masarauta ce da aka kafata a kan jini tin zamanin kakanni. A cikin masarautar BLOOD CROWN, a dokance dik wani sarki ko sarauniya da zai hau karagar mulki sai an zub da jinin wani a matsayin hadaya. Ana kiran wannan al'ada da suna kariya wacce suke ganin ita ce take kare masarautar daga lalacewa ko hare hare daga masarautu, ita ce take hana kowa iya tinkararsu, kuma suna ganin hakance ma ta hana King Zuhair yakarsu, a cewarsu sun rufe mashi ido da baki ba zai iya yin komai a kansu ba, dan suna sadaukarwar jini!!.
Bobo shi ne babban Prince na wannan masarauta, yana da kanne mata ƙanana guda biyu, ya shaƙu da kannen nasa matukar shaƙuwa, yana bala'in sansu fiye da kansa, sun taso cikin gata da kula, a lokacin da ya kai shekaru 22 sai mahaifinsu ya fara shirye-shiryen yadda za'a fara koya mashi sarauta, dan shi ne kawai magaji. Sam sam mahaifiyarsa bata so ba, yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa mutanen garin basa san haihuwar ƴaƴa maza, dan za'ace za'a basu mulki, kuma kafin su hau mulki sai sun zub da jinin wanda suka fi kauna. Shiyasa suke san haihuwar ƴaƴa mata, har murna suke su shirya shagali idan suka haifi mace, amma in suka haifi namiji, wlh kuka suke yi yadda kuka san gidan makoki, gidan suna sai ya koma gidan mutuwa!!.
Mahaifinsa jarumin gaske ne na bugawa ga jarida, kazalika mahaifiyarsa, zakanya ce sosai!. Sai dai masarautar tasu ƙazantar dake cikinta ya zarce tinanin mai tinani, suna bautar da mata, suna wahalar da su, sun ɗauki mace a matsayin abar sauke sha'awarsu kuma baiwa a garesu, mata basu da wani galihu basu da gata, dik wani aikin karfi mata ne ke yi, dik wani zalunci suna yi masu, a dik time da suka ga dama ko a cikin daji ne zasu haiƙewa matansu su biya buƙatarsu, noma mata ne suke yi, kai komai da maza zasu yi matan ke yi, a cewarsu ai mata bayinsu ne, babu tausayi babu imani, fyaɗe da zinace zinace ya yi over, ba zaku so tona ɓarnar da suke aikatawa ba wlh, amma a hankali idan tafiya ta yi nisa zaku ji komai!.
--------------------------------🔥🔥
Bobo ya fara karɓar dik wani horo da ya danganci mulki salum alum, sai dai a lokacin da aka zo kan batun sadaukar da jini kafin ya ɗale kan kujerar mulki, aka sanar mashi cewa dole sai ya kashe wanda yake tsananin so kafin ya hau gadon sarauta. Wannan ita ce hanyar tabbatar da biyayyarsa ga mulkin da aka gina a kan jini!. Tashin Hankali. Nan fa Bobo ya ce babu wannan magana, dan dik duniya mutum huɗu yake so, daga kannensa mata guda biyun nan, sai mahaifiyarsu da kuma mahaifinsu, dan haka ko mutum ɗaya ba zai iya kashewa ba, babban abin takaicin ma wai shi da kansa zai kashe mutumin da yake kauna, sannan ya lashi jininsa a kan harshensa, dik dan ya nuna zallar rashin imani, a cewarsu ta hakance kawai zasu iya gamsuwa da cewa namiji mai dakakkiyar zuciya ce yake mulkarsu. Sai dai kuma ba zai iya bada wanda ya taɓa yin mulki ba, misali ace ya bada mahaifinsa, hakan ba zai yiwu ba, dan already babansa yana da tsari ya ɗale dangerous seat kuma ya ɗaura blood crown a kansa.
Bobo ya shiga ruɗani da tashin hankali a in da ya fara bincike a kan masarautar tasu, gadan gadan ya shiga wannan bincike. A nan ne fa ya gano wani sirri mai ban tsoro, wato sarautar BLOOD CROWN tana da asirin duhu. Ba wai kawai ana kashe mutane ne dan cimma muradi ba, rawanin da kowani sarki yake sakawa a yayin hawa mulkinsa rawani ne da yake da wata asiri mai kyaucewa hankali. Dik wanda ya sanya rawanin nan a kansa, zuciyarsa ba ta ƙara jin tausayin mutum, daga nan ya rabu da imani da tausayi.
Bobo ya gano cewa dik sarakunan da suka gabace sa, rawanin ya mai da su masu mugunta, yana rage musu tausayi kuma yana ƙarfafa su su yi zalunci ba tare da rashin jin daɗi ko kunya ba. Wannan yana nufin idan har shi ma ya sanya rawanin to zai zama azzalumi kamar su. Babbar magana! Ya shiga ruɗani mai girma gano cewa yana da yaya namiji da mahaifinsa ya kashe domin ɗale kan kujerar mulki, ya sadaukar da jininsa ga BLOOD CROWN kenan, bala'i iya bala'i Bobo ya shiga a wannan lokaci, nan fa ya fara tinanin mafita a garesa dama ƴan uwansa bakiɗaya, dan ba zai taɓa iya bada ko mutum ɗaya daga cikin huɗun nan ba, ba kuma zai iya bari a cigaba da wannan ɓarna ba, saboda a lokacin shi ya musulunta ba tare da saninsu ba, a makarantarsu ya karɓi musulunci daga abokinsa wato Smart, tare suka yi karatu a ƙasar France, a lokacin da aka ce ya karɓi mulkinma hutun school ya dawo, daga nan suka rikesa wai karatun ya isa haka, lokacin hawansa gadan mulki ya yi! Dama shi ya matsa yana san karatun!.
Daga nan Bobo ya fara shirin wargaza mulkin zalunci. Sai dai hakan yana da gagarumin hatsari da barazana ga rayuwarsa da ƴan uwansa. Sama da sau goma ƴan majalisar masarauta tana yin zama a kansa, sun tursasa mahaifinsa a kan ya sanya shi dole ya ya zaɓi wadda ya fi kauna ya kasheta a karawa CROWN ɗinsu karfi, dan da alama zasu iya fuskantar marazana daga wasu masarautun idan basu yi gaggawar bada jini sun karawa RAWANIN karfi ba. Sai dai dik yadda za'ayi da Bobo anyi yaki buɗar baki ya ce ga wadda ya fi so, da zarar an yi mashi magana sai ya ce su ɗan kara mashi lokacin. Ya yi kokarin canza dokokin masarautar, amma ƴan majalisar masarauta sun dakatar da shi game da daka mashi zazzafar warning a kan zai iya rasa ransa idan ya yi kuskuren taɓa doka guda ɗaya daga littafan dokokinsu, dole ya bi komai kamar yadda ya ganta a rubuce, tsawon shekaru suke a kan wannan tsari. UHM ABIN TAKAICIN MA WAI WANDA YA FI KAUNA ITA ZA'A KASHE, WLH BASU DA IMANI KO KAƊAN MUTANEN NAN!!.
Bobo ya yi iya tinanin da zai yi, amma ya kasa samawa kansa mafita, saboda sun fi karfinsa, bai isa ya yi fito na fito da su ba, sun fishi yawa, hakan tasa ya koma gefe ya yi shiru dan tinani a natse ko za'a samu mafita. Daga karshe ya yanke shawarar fitar da sirrin familynsa ga abokai ko zai samu maslaha, hakan yasa ya kira Smart a waya ya sanar da shi ga halin da yake a ciki, ashe dama sarautarsu ba ta Allah da annabi bace, sosai Smart ya yi mamakin jin hakan, a lokacin suna a tare da Zash, dan su ukun a tare suka yi karatu.
In short dai Smart ya ce da Bobo ya ɗauki ƴan uwan nasa ya bar ƙasar, dan faɗa fito na fito da su lokaci guda ba zai yiwu ba, dole sai sun yi shiri, idan kuma ya ce zai zauna a tare da su har su yi shiru zasu iya matsa mashi, idan bai biya masu buƙatarsu ba zasu iya kashe shi, dan ya rigada ya san sirrin RAWANIN JINI. Wannan dalilin yasa Bobo ya shirya makirci cikin dare ya ɗauke mom ɗinsa da kannen nasa dikka biyu ya gudu da su zuwa kasar France, Smart ne ya tsaya mashi tsayin daka sosai, mom ɗinsa dama a tsananin tsorace take, hankalinta a mugun tashe, tana cike da fargabar waye ɗanta zai zaɓa ya fiso, tsoronta kada ace ita ce, kun san wanda baya tsoron Allah da shegen tsoron mutuwa, wlh billahi dik wanda baya tafarkin Allah shegen tsoron mutuwa ne da shi kamar me, dik wanda yake da karfin imani baya tsoron mutuwa, dan already yasan sai ya mutu, kuma idan na kwarai ne shi yasan lahira ta fi mashi duniya sau miliyoyin miliyoyi, dan haka zai so ya tafi lahira ma sai ta fi mashi.
Mom ɗinsa tana tsorace, dan ita tasan wannan al'ada, amma kannensa mata basu san wannan al'adar ba. Lokacin da ya shirya ya ɗaukesu daga kasar ba karamar daɗi mom ɗinsa ta ji ba, sai dai kuma taki ta musulunta har wa yau, ba yadda bai yi da ita ba, har ya faɗa mata cewa saboda addinin musulunci yasa bai yi sadaukarwar jini ba, musulunci yasa bai zaɓeta an kasheta ba, dan haka ta musulumta shi ne addinin gaskiya, amma matar nan ta ce babu wannan magana, ba zata musulunta ba, har da cewa Allah ya yi wa Musulunci albarka da ya kuɓutar da su, amma dai ita ba zata musulunta ba, Smart ya ce mashi ya cigaba da binta a hankali kamar yadda shi ma yake lallaɓa mom ɗinsa ta musulunta, idan suna da rabo watarana za'a dace, to haka dai suka yi, kunji kaɗan daga tarihin Bobo. Amma fa har yau har gobe neman Bobo suke yi dan su kashe shi, ya karya alkawari da dokokin BLOOD CROWN, suna nemansa kamar hauka, yanzu an dai'na tinanin ya hau mulki ma, tinanin kashe shi kawai ake yi, jininsa za'a baiwa BLOOD CROWN! Tashin sense, kai akwai cakwakiya fa, bamu fara wasan ba, ku jira bayan bikin Auta balbalin kura zai taso daga sararin samaniya, gobara zata taso daga kogi, wanda kwantar da wannan bala'i sai Allah kawai!!.
Kada ku ga laifin mahaifiyar Bobo na kin musulunta, saboda mijinta ya taɓa hawa gadan mulkin BLOOD CROWN, kamar yadda mijinta ya sanya wannan RAWANI imani da tausayi ya fita a ransa, haka zalika ita ma majalisar dokokin masarautar masu alhajin kula da BLOOD CROWN suka cire mata dik wani tausayi da imani, shiyasa bata yi wa su Bobo da sauki, wlh barema Bobo, yana shan wahala a hannunta, tana tauye masu hakkinsu, bata san barinsu su sarara, harta ƴaƴanta mata, tana da bakar zuciya na mugunta sosai, kafin su iya samu ta dawo na kwarai to fa sai ranar da aka ruguje BLOOD CROWN!!. UHM AKWAI RINA A KABA!!.
INTERMISSION. NAN SHI NE TAAKIYAR LITTAFIN RAWANIN ZALINCI.🔥♥️
--------------------------------🔥♥️
To fa, mun zo dai'dai wani gaɓar da dikka masarautu biyar na RAWANIN ZALINCI suka gama bayyana, zan lissafo maku su sai in baku aikin zaƙulo stars ɗinku daga kowacce masarauta. Na farko akwai KINGDOM OF POWER, na biyu CROWN OF INJUSTICE wato BLACK WORLD, na uku akwai KINGDOM OF JUSTICE, masarautar Queen Zarina kenan, na huɗu akwai EVIL KINGDOM, masarautar su Yusuf, na biyar akwai, BLOOD CROWN, masarautar su Bobo, dama na ce maku masarautu biyar ne, kuma dik mugan abokan gabane da basa shiri kwata kwata, kuna dai gani yakar juna suke yi, RAWANIN ZALINCI ya zo da sabbin salo na daban, stars na littafin nan su bakwai ne zuwa takwas, kowanne kuma zai fito daga ɗaya daga cikin masarautun nan, KINGDOM OF POWER ce kawai take bada stars guda biyu, yanzu aiki ya ragunmaku, dikka masarautu biyar sun bayyana, saura a fara ainahin yakin bayan bikin Auta kenan, dama in da nike ta fatan in iso kenan, kuma Allah ya kawo mu!. A yanzu ba zan kira maku Stars da kowacce masarauta zata bayar ba, daga matansu har mazansu, saboda kuna tare da dayawansu ne baku san daga ina suke ba, idan kuka san daga in da suka fito a nan ne zan bayyana maku kowani masarauta da stars ɗin da ta bayar, amma ku cigaba da canki cankanku...... 🥱😅
(Kam bala'i, gaskiya RAWANIN ZALINCI ya zo da salo na daban, wai har yanzu laluɓar stars ake yi! Tab to akwai show a nan gaba, ku mu je dai zuwa, zaku sha mamaki fa.😅 To amma a Black world dai mutum