Showing 231001 words to 234000 words out of 403653 words
tulanta, lokaci guda ya kara birkicewa sosai, cikin fitar hayyaci ya capki hannunta ya ɗaura a saman bananarsa.
A zabure ta kwace hannunta tare da kwace lips ɗinta, nan take tsoro da shakkarsa ya shigeta, narai narai ta yi mashi da ido, sai ta ji tana san gudu ta bar ɗakin ta koma nata, kamar zata yi kuka ta ce. "Yah Jaish ni cikina ya dai'na ciwo zan koma ɗakina".
Tamkar wanda yake a cikin maye haka ya rikota, cikin fatar hayyaci ya fara sambatu kamar haka. "Please don't go leave me, stay with me here, ki bani magani kin ji? Please and please". Tamkar ba yaron Mommarsa ba, lokacin guda ya zame mata kaman ƙaramin yaro, banbancinsa da guyson a lokacin da yake cikin ciwo kuka ne kawai, kun ga shi guyson yana kuka, shi kuma ya marairace murya ne kamar zai yi kukan kawai, amma bai yi ba.
Wani irin tausayinsa ne ya kamata, amma kuma akwai tsoronsa sosai a ranta, ƙasa ƙasa ta ce. "Yah Jaish to a ina maganin naka yake sai in ɗauko maka kasha kafin na tafi ɗin". A tunaninta da ya ce ta bashi magani ta zaci kyawa zata ɗauko mashi yasa, bata san ita ce maganin da kanta ba.
"Ai kece maganin, kanki kawai zaki bani zan samu saukin azabar da nike ji". Ya faɗa yana kara janyota jikinsa yana kuma dafe mararsa da hannunsa ɗaya.
Sai a yanzu ta gane nufinsa, yanzu ne ta fahimci in da ya dosa, haba wani irin tsoro ne ya dira a ranta, ina ba zata iya bada wannan magani ba, dan Jumma ta faɗa mata akwai wahala kuma akwai zafi........ Kun ji yar ƙaniya, tasan akwai wahala da zafin ne kuma ta ɗauki shawarar momma, mama Haulat da Chuchu ta rinƙa kwanciyan wa bawan Allah a jiki tana sanya mashi kayan anty tsirara tana yawo a bedroom ɗinsa tasa al'amura dik suka tattashi ta yadda ba zai iya shanyewa ba, sai da ya zo har wuya in da ba zai iya jurewa ba sannan ta ce wai ba zata iya ba? Tab aikuwa bata nemi zaman lafiya ba!.
Da karfi ta kwace kanta daga riƙon da ya yi mata, jikinta har ya fara kerman tsoro, hankalinta dik ya tashi, laluɓawa ta yi da sauri tana san sauka daga gadon. Shi kuwa da ya ga da gaske tafiya zata yi ta barshi, ga shi ba iya jurewa ya danne zai yi ba, sai ya capkota cikin zafa.
Ƙoƙari kwace kanta ta fara yi tana faɗin ya saketa cikinta na yi mata ciwo, haba ai da ya fahimci yana sakinta guduwa zata yi sai ya shareta, cikin zafa ya zare kayan jikinta ya kuma yi mata rumfa da faffaɗar kirjinsa. Tana ganin haka ta fara yi mashi ihu tana bubbuga kirjin nasa tana san miƙewa ta gudu.
Da ta hakura ya bita a hankali ma sai ta samu sassauci, amma ta gwada mashi gardama ta gwada zata kwaci kanta, shi kuwa yana hannu ya danneta ya yi mata ta karfin tsiya, hakan ya haifar mata da jin ciwo daga ciki ga zubar jini sosai da ta samu, dan ko kaɗan bai sarara mata ba, cikin fitar hayyaci ya yi abin, dan wlh kunga a yadda yake ai yama yi mata ƙoƙari da ciwon yana tsaya a iya haka, suma kuwa sai da ta yi sau biyu, dik kuma bai jitaba ya yi ta bidirinsa har sai da ya ɗan samu gamsuwa, da alama ya manta da cewa disvirjin yake yi ba wai an taɓa yi ba, sai da ya yi sau uku, nan ma tsabar jaraba bata wani isheshi ba, ya dai hakura ne kawai kada ya yi kissan kai.
Abin kuma kamar abin haɗin baki, a lokacin da yake disvirjin na Mahnoor a lokacin shi ma Jawad ya yi disvirjin na Jannawad ɗinsa, shima sai da suka kai ruwa rana sosai, daga karshe shi ma ta karfi kawai ya yi mata, dan ya kai two weeks yana binta tana yi mashi kuka ta nuna bata so, aikuwa yau kam ya saka mata karfi ya buɗeta, sai dai shi bai ji mata ciwo ba, dan bai fita hayyacinsa kamar Jaish ba, ya dai sumar da ita, shi kuwa Jaish mai gabaɗaya sai da ya jawa ƴar mutane jinya mai lasisi.
Tsabar tabbatar rashin kunya irin nasa kuma bayan ya dawo hayyacinsa ya mayar da kayan jikinsa, sai ya je ya kira mama Haulat, wai ba zai iya kiran momma ba, saboda ba zai iya haɗa idanu da ita ba, sai da ya gama rashin mutuncinsa sannan kunyar tasa ta rashin kunya ta dawo. Ita ma fa mama Haulat ɗin zuwa ya yi ya ce mata ta je bedroom ɗinsa Mahnoor tana kiranta, daga haka ya gudu garden abinsa, wai shi ba zai bari ya haɗa idanu da kowa ba.
Kuma fa tsabar rashin mutunci bai wani ji tausayin Mahnoor ɗin ba, shi dai ya biya buƙatarsa ya ɗan samu sassaucin abin da yake ji, so bashi da wata matsala da ita, wato ita ta sani kenan idan ta rayu ma........ My people's shin mu faɗawa Jaish ko dai mu kyalesa tun da ya ɗanɗana ya ji abin da ake ji? Ɗan rai'nin wayo da kanka zaka dawo nemanta, ba dai ka ɗanɗana ba, zaka gane baka da wayo, mu je dai zuwa, ranar da zaka ƙasa barci zai zo ne.
Innalillahi Queen Zarina ta tura a ɗauko mata shi dan samartakansa ga shi yau ya bawa Mahnoor samartakar tasa, innalilahi wa inna ilahir, shi mutum ne mai addini hakan yasa Queen Zarina bata iya ganin halin da yake a cikin ta madubin tsafinta, tab akwai cakwakiyoyi matuƙa.
Mama Haulat baiwar Allah, ita ta gasawa Mahnoor jiki da ruwa mai zafi da ta haɗa mata, sai dai kuma har ta yi mata dik abin da zata yi mata ta gama Mahnoor bata farfaɗo daga wannan doguwar suma da ta yi ba, kuma jinin yaki tsayawa dan ta samu rauni daga ta ciki, hankalin mama Haulat in ya kai dubu to ya tashi a wannan lokaci.
Jikinta na kerma ta tallabi Mahnoor zuwa cikin bedroom ɗin, ta fahimci ciwo ta ji sosai daga ta ciki, dan haka sai ta cire bedsheet ɗin da jinin ya lalata, ta kudundunesa, ta kwantar da Mahnoor a saman sofa ta ɗauki bedsheet ɗin ta nufi wajen momma da shi.
A lokacin momma ta dawo daga wajen King kenan, tana ƙoƙarin kwantawa mama Haulat ta shigo bakinta a ɗauke da sallama. Da kallon mamaki momma ta bita kafin ta amsa sallamar tare da kafeta da idanu alamar tana jiran jin abin da ya kawota.
A gaban momma ta zube gwiwowinta ƙasa, cikin girmamawa ta fara neman izinin magana. Kai momma ta ɗaga mata alamar ta yi magana tana jinta. A natse ta ce. "Ranki ya daɗe princess Mahnoor dai ta kawo budurcinta ga mijinta ga kuma shaida nan ina tafe da shi, sai dai an samu matsala sosai ta zubar jini da alamar ta samu rauni daga ta ciki". Ta kai karshen maganar tare da ware bedsheet ɗin ta nunawa momma shaidar da ta kawo na jinin Mahnoor dake jikin shi.
A lokacin da mama Haulat ta ce Mahnoor ta kaiwa Jaish budurcinta ba ƙaramin daɗi momma ta ji ba, a bayyane ta sauke ajiyar zuciya mai sanyin gaske, har ta ji dik wata damuwa tata ta gudu, amma a lokacin da ta ji zancen karshe na cewa Mahnoor ta samu rauni take farincikin nata ya tsaya cak, dama dai tasan Mahnoor zata sha wahala, dan dik ƴaƴanta babu rago, sai dai bata kawowa ranta wahalar har haka bane, hankalinta ya tashi sosai, da sauri ta fasa kwanciyar da take da niya.
Kasan gadan ta sauko, bata bi ya kan mama Haulat ba ta yi gaggawar nufar waje, kai tsaye ta nufi ɓangaren Jaish ɗin, hankalinta dik a tashe matiƙa. Da sauri mama Haulat ta miƙe ta rufa mata baya dan su je su san abin yi. Ko da momma taga Mahnoor ta tausaya mata matuƙa, dan ta ganta a wani irin yanayin da dik zuciya mai imani sai ta tausaya mata, sai dai kuma momma bata tambayi ina Jaish ba, dan ita kanta ta san ba zai tsaya ba, saboda shegen kunyar nan tasa ta rashin kunya in ji Jawad, so sai bata ma nemesa ba, da kanta kawai ta tsayawa Mahnoor ɗin ta yi mata komai ta hanyar kirar likitarta mace dan ya zo ta dubata.
Shi kuwa Jawad da yake iya suma Chuchu ta yi bata samu rauni ba, da kansa ya yi treating kayassa, sai dai fa akwai cakwakiya matuƙa, domin kuwa tun da ta farfaɗo banda kuka babu abin da take yi mashi, ya yi rarrashin duniya taki ta kula shi, ta dai ce wajen mummynta zata koma wlh ba zata zauna da shi ba tun da shi mugu ne. Dik abin da take faɗe he's not minding her word, hakuri kawai yake cigaba da bata yana rarrashinta dan yasan ya yi ɓarna.
•••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥🔥
A ɓangaren Smart kuwa, Sarina tana ganin ya shiga dressing room ta lallaɓa ta miƙe da nufin ta gudu, kasa iya taka kafafunta ta yi, dan haka sai ta koma ta zube ƙasa, da ciki ciki ta fara ja wasu zafafan hawaye suna tsere a saman ƙuncinta, wani irin azaba ta ji lokacin da ta gwada mikewan nan, da kyar ta cigaba da jan cikin nata har ta fice daga ɗakin. Ganin komawa part ɗinsu ba zai yiwun mata ba saboda nisa ne yasa ta nufi part ɗin King dan a ganinta shi ne kawai zai iya cetanta daga hannun Smart. Amma kuma sai da ta ɗauko alkyabbarta ta sanya a jikinya kafin ta fice tana ja da ciki. Tasan in ta je wajen King da irin wannan shiga zata yabawa aya zaƙinta ne, sai ta mayar da alkyabbarta.
A lokacin da ya fito bai sameta a cikin room ɗin ba, wani irin ɗaure fuska ya kara yi, a ransa ya ce lallaima wannan yarinyar ta jawa kanta bala'in da babu wanda zai iya tare mata, har kamar shi ta isa ya sakata kneel down ta tashi ta gudu? Tab ta ɗebowa kanta wutar gasa kanta da kanta. Auta dai tana zaune a saman bed, ta dai'na kuka amma bata iya mayar da barcinta ba, ya kuma ganta, sai dai ya mayar da hankalinsa a kan kamo Sarina, ya ce sai ya dawo zai rarrashi Auta.
Cikin takun jarumta ya bi bayanta, sai dai bai san ko'ina a cikin fam part ɗin ba, dan haka da ya fito sai da ya ɗan tsaya a bakin kofa yana tinanin ina yakamata ya bi.
Ƙasa ya yi da kansa domin yin tinani sai yaga jininta a kasa saman tiles, da ta ja jikinta a ƙasa jininta ya ɓata ko'ina, bin jinin da kallo ya yi ya ga hanyar da ta bi, ransa a ɗan ɓace ya bi wajen, ta ja ya kuduri niyar yi mata abin da bai shirya ba.
Dik abin da yake faruwa Mammie ɗinta tana ganinsu ta madubin tsafinta, ta so ɗaure hannun Smart a lokacin da yake dukan Sarina ta kafar mashi da hannun, sai dai ta kasa sage mashi koda jijiya guda ɗaya, saboda ni da ku dai dikka mun san yadda yake da riƙo da addini, ko jijiya guda ɗaya ta kasa sagar mashi, infact ko kusa da shi abubuwan tsafin nata sun ƙasa zuwa, wannan dalilin yasa ta baro part ɗinsu ta zo domin ta kwaci yarta.
A main parlour na part ɗin King Smart ya isko Sarina, tana jin motsi ta juya, tana ganin shi ne ta daddage ta kurma ihu mai amsakuwar da sai da ya daki kunnuwan dik wanda bai yi barci ba a cikin part ɗin except Jawad and Jaish da suke duniyar sama jannati.
Cikin zafa King ya fito daga bedroom ɗinsa sanye da arabs jallabiya saboda wannan ihun, ita ma Mammie da sauri ta karisowa wajen, da yake uncle Jahiz ma bedroom ɗinsa yana cikin part na King sai ya fito da gudu, dama Dr Raj yana kan hanyarsa na zuwa wajen King, so jin ihun yasa ya yi saurin karisowa. In short cikin short time gabaɗaya family suka haɗu a cikin parlon, kowa sai tambayar kansa yake yi me yake faruwa?.
Mammienta na ganin haka ta yi wa uncle Abbas sms a kan ya zo main parlour babu lafiya. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai ga shi ya zo, gabaɗaya kowa ya tsaya cirko cirko kaman masu shirin kaurewa da yaki, an rasa mai bakin iya tambayar Smart me yake faruwa?.
Da yake momma ce ta yi karshen zuwa wajen sai yazama sun ɗauki almost 5 mins babu wanda ya iya kallan Smart ya tambayesa dalili, sai King ne ma ya yi kokarin buɗan baki zai tambayesa sai ga momma ta kariso wajen da sauri tana faɗin meyake faruwa ne?.
King ɗin ma bai fasa tambayar da ya yi niyya ba, dan haka tana rufe baki ya ce. "Omerish meya haɗaka da kanwar taka kuma?". Shi King dama mamakin shigar jikin Sarina yasa ya ɗan yi shiru ma, dan ba kaya bane na hankali da musulunci, kaya ne na Allah wadarai, so abin ya bashi mamaki ganin irin wannan shiga a jikin ƴaƴansu. Ja da take yi da ciki yasa alkyabbar da ta sanya ya yi sama kayan suka bayyana.
A wannan karan har da su Zee and su Pretty, Auta dik sai da suka haɗu a parlourn, su Jaish da matansu ne kawai basa nan.
Mu koma baya kaɗan kafin mu ɗaura daga labarinmu, a lokacin da Zee ta baro garden ta baro Dr Raj kenan, tana kan hanyarta na nufar bedroom ɗin momma suka ci karo da mama da ta fito daga part na Akka. To kun dai san yadda halin mama yake da kyara haɗe da tsangwama, ga shegen walaƙanta mutane da ƙasƙanci. Hakan yasa tana ganin Zee ta bita da kallan walaƙanci kafin ta yi mata zagi ta uwa ta uba wanda ko kare ba zai ci ba dik da bata san wacece ita ba, daga karshe ma ta kirata da bola kazama, a tinanin mama ƴar aiki ce Zee momma ta kawo, dan haka sai ta rufe zancenta da cewa. "Kada ki kuskura na ganki ta arear side ɗina da sunan kin zo mun aiki, dan bana da buƙatar irinku a masu yi mun aiki".
Wato idan jininka bai haɗu da mutum ba fa bai haɗu bane kawai, ga shi dai babu gaira babu dalili mama ta tsani Zee, har ta yi mata wannan ƙasƙantaccen zagi mai muni haka. To ita ma dai Zee kun san ba shiru take yi ba, dan haka a karshe ta ce. "Ai ko zan yi wa kowa aiki a cikin gidan nan ke kam ba yi maki zan yi ba, banza ma irinki shashasha mara mutumci".
Amma da Hausa Zee ta yi maganar, hakan yasa mama bata fahimci abin da ta faɗa ba, ta daiga tana magana kawai. Hmmm Zee fa bata san mamar Dr bace wannan, haka kawai ta tsani mama ta kuma zageta fes har da ce mata shegiya mai idanun mujiya dik da Hausa, ta kara da cewa dik ranar da hannunki ya taɓa jikina zaki gane baki da wayo, dan sai na lillisaki wlh. Ta dai tsaya tana surutanta ita kuma mama ta kara gaba. Sai da ta gama babu mai bata amsa sannan tasa kai ta wuce part ɗin momma tana kunkuni ciki ciki.
Uhmmm rashin sani ya fi dare duhu, wato akwai cakwakiya matuƙa, mama bata kaunar Zee, haka zalika Zee bata shiri da Aneesa kanwar Dr ɗin, ga shi kuma Dr ya folawa Zee, ita ma ta fola mashi, baiwar Allah ga shi farkon soyayyarta kenan, kuna ganin zata cinwa nasara a wannan soyayya? Zata kai labari kuwa?. To mu je dai zuwa.
•••••••••••••••••••••••••••••••🔥
Shiru Smart ya yi har sai da momma ta sake jefa mashi tambayar me yake faruwa?! A maimakon ya bata amsa sai ya jefa mata tambayar wanenen uban Sarina a cikin ƴan uwan daddynsu?.
"Omerish ka faɗa mun meyafaru tukun nan ka ji?". Cewar momma, cikin sigar rarrashi da kwantar da murya ta yi maganar. Da yake a duniya babu wanda Smart yake kauna biyunta bayan Allah da manzonsa, yana san momma fiye da komai ɗinsa, kuma yana yi mata biyayya da dikkannin iyawarsa, dan haka sai ya sanar da ita dik abin da yake faruwa cikin kauna da girmamawa.
Salati gabaɗaya parlourn suka sanya a cikin zuƙatansu except Mammie da ta san komai ita. Shi kansa uncle Abbas and King the was very shocked da suka ji abin da ya faru, mamaki uncle Abbas yake yi na yaushe Sarina ta girma har ta yi wannan bushewar idanu bashi da labari.
Suna tsaka da mamaki Smart ya katsesu da tambayar wanenen uban Sarina?. A lokacin Akka ma tana wajen.
King ne ya yi saurin cewa. "Nine ubanta". Sam Smart bai so ace daddyn nasa bane ubanta, saboda bai yi niyar raga mata ba, amma dik da haka sai ya yi wasu daga cikin abin da ya yi niyya. Cike da izza ya ce.
"Daddy kenan dama haka kake tarbiyantar da amanar da Allah ya baka? Ko ka manta amana ce Allah ya baka kuma zai tambayeka? Nasan kasan da haka sai dai in ce maka ka mance ne?".
Akka ce ta ce. "Omerish yana da kyau kasan irin maganganun da zaka rinƙa faɗawa mahaifinka da kuma in da ya dace kayi magana da shi! Idan tarbiyarsu bata yi maka ba sai ka yi naka ai, nan gidan sarauta ne masu amfani da dokoki masu karfi wanda dole ka bisu, kuma kasan da cewa mahaifinka sarki ne ba wai irin mahaifin haka kawai bane!!". Cikin faɗa Akka ta yi maganar saboda ranta ya sosu sosai na yadda Smart yake gatsa magana ba tare da ya taunata ba.
Su sun kasa gane