Showing 210001 words to 213000 words out of 403653 words
face ɗin Khadija zaka kalli tana cikin bakinciki, dan damuwa na cunkushe a ranta, wai a hakan ma dan likitoci sun ce ta cire damuwar dake ranta in ba haka ba zata iya kamuwa da ciwon zuciya, shi ne fa ta ɗan rage.
••••••••••••••••••••••••••••🔥
"Aunty Khadijah tin da kin samu lafiya yakamata mu koma Nigeria ko?". Cewar Zee. Yadda ta yi maganar tasa Khadijah ta zargi wani abin. Cike da mamaki Khadijah ta ce. "Kina da matsala da nan ɗin ne?".
Kai ta jinjina da sauri tana amsawa da e tana da matsala. Nisawa Khadijah ta ɗan yi kafin ta amsa da.
"Meyasa Zee dik in da muka je sai kin yi wa wajen mummunar zato ne? A nan ɗin ma nasan cewa zaki yi kina zargin wani abin ko?".
Kai Zee ta gyaɗa. "To Aunty Khadijah ki faɗa mun wani waje ne da na yi wa mummunar zato bai zama sharri a garemu ba? Kina dai gani mai napep da ya ɗaukemu daga kawo Kaduna da nace ban yarda da shi ba, kin dai ga sace mu ya yi izuwa Abuja, Allah ya kuɓutar damu, muka sake faɗawa gidan matar can, ita ma na ce maki ban yarda da ita ba, haka kika matsa mu zauna da yanzu babu junior ta sacesa, nan ma Allah ya karemu da kariyarsa, muka tsallaka rijiya da baya, kinga kuwa ai ba kya tuhumeni a kan dan nace nan ma ban yarda da su ba, basu kwanta mun a rai ba".
Tun da ta fara magana Khadijah take binta da kallo tana sauraronta har ta kai aya, sannan ta ce mata. "To ke yanzu meyasa kike zargin wannan gida?".
Ajiyar zuciya Zee ta sauke, juya harshe ta yi izuwa turanci, sannan ta ce. "Saboda wannan ɗan kwallon, ina zargin yana shigo mana ɗaki da daddare, sannan kuma yana yawan sakawa dik wani motsina idanu..........."
A hanzarce Khadijah ta katseta da cewa. "Wani ɗan kwallon kenan?". "Jahiz mana". Ta bata amsa tana kara ɗaure fuska.
Zaro idanu sosai Khadijah ta yi zata yi magana daga bakin kofa suka jiyo muryar Aneesa cikin harshen turanci ita ma tana faɗin.
"My second dad ba yadda kika ɗaukesa yake ba, ke ba abin alfahari bane ma a wajenki ki ce kin taɓa ganin shi a zahiri? Na tabbata dik wanda zaki ce wa kin taɓa ganin uncle na a zahiri ma ba yarda zai yi ba, domin baki yi kalar wadda ta taƙa matsayin da zata samu damar ganinsa a zahiri ba".
Ɗan siririn tsaki Zee ta ja, a kule ta ce. "Then so what? Kuma da kike wannan magana ce maki aka yi wata tsiya ce shi? Ko an faɗa maki Nigeria irin nan ne da zamu yi alfahari da ganinsa?".
Zee ta samu Khadijah ta samu lafiya yanzu kuma su Aneesa sai sun sarara mata, dama saboda lafiyar Khadijah ta koma baya ta yi zaune, yanzu kuwa kowa zai sha mamakinta, ba ɗaga kafa.
Wani irin matsiyacin kallo Aneesa ta wurga mata kafin ta ce. "Ni ba mate naki bane okey? Ki rike words ɗinki da kyau kada ki bari su kubce maki a kai'na, dan zaki yi danasani, rubbish useless people kawai". Ta yi maganar tana dalla masu harara.
Da sauri Zee ta buɗe baki zata mayar mata da martani, a hanzarce Khadijah ta tareta da faɗin ta rufe bakinta a wajen. Ranta ne ya ɓaci sosai, ba zata iya yi wa Khadijah musu ba, dan haka sai ta miƙe da sauri ta nufi waje, Khadijah na kiranta amma bata tsaya ba, ta ce ita ta bar wannan ɗaki ma ba zata sake dawowa ba, gara ta kwana a waje da ta sake kwana a ɗakin, kun san mutuniyar da shegen zuciya.
Tana fitowa ta nufi elvator, ƙasa mai gabaɗaya ta yi domin ta fita waje. Ita da bata san ko'ina ba amma saboda zuciya sai gata a tsakar kingdom ɗin, ta ko'ina warriors ne suke shawagi dan tabbatar da tsaro. Shiru ta ɗan tsaya tana kallan yadda hasken bulb suka haska harabar kingdom ɗin tamkar rana, ko allura ka jefar zaka iya tsinta.
Wani ɓangare na zuciyarta ne ya zugata wajen ce mata ta ɗan yawata cikin kingdom ɗin mana ko zata huce kafin ta koma ciki ta je su kwana a tare da Pretty, dan ba zata sake komawa part ɗin mama ba, kun san zuciya da sake sake, sai ya rinƙa saƙa mata tabbas Aneesa ta ci mutumcinta.
A hankali ta fara taka kafarta tana tunane tunane ta fara kewaye cikin harabar family part. Wasu warriors guda biyu ne suka nufota cikin takun jarumta. Ta ɗan ji tsoro da ta gansu, amma haka ta daure ta cigaba da tafiya suna tinkarar juna.
A gabanta suka tsaya, cikin girmamawa suka ce ko tana buƙatar wani abin ne ta fito? Kai ta girgiza masu kafin ta amsa masu da bata buƙatar komai, shan iska kawai ta fito yi. Ɗaya daga cikin warriors ɗin ne ya nuna mata hanyar babban garden na family part, sannan ya ce mata ga wajen shan iska a can ai idan tana da buƙata.
Ta ji daɗi sosai, sannan ta nufi wajen tana yi masu godiya. Juyawa warriors ɗin suka yi suka koma bakin aikinsu........ Sosai Zee ta baza idanu tana kallan ƙawatuwar garden ɗin nan, ga wasu irin flowers masu kamshin daɗi, a hankali iska ke kaɗawa yana ratsa jiki, sai ta ji wlh zata iya kwana a nan wajen, haɗuwar wajen ya tafi da imaninta.
A hankali ta nufi karisawa wajen da luntsuma luntsuman sofas dake wajen wani ƙayataccen rumfa dan ta zauna a can, tana tafiya tana waige waige dan ta kurewa ko'ina kallo a cikin garden ɗin. Unexpect suka ci karo da mutum, a razane ta juyo da kallanta a kansa domin ta ga wanenen?.
Tana juyowa dai'dai lokacin ya ɗaga hannu zai dallah mata mari sakamakon cappuccino dake hannunsa ta buge mashi ya zube a white sleeping dress dake jikinsa,.hakan ya kona mashi rai sosai, ga wayarsa da ta buge ya faɗi ƙasa, ya ji zafin hakan natuƙa.
A fusace ya cire hannu zai dallah mata mari, da sauri tasa hannunta dikka biyu a face ɗinta domin ta kare lafiyar fatarta daga marinsa. Ta datse idanunta gam tana jiran ta ji saukar mari sai kuma ta ji shiru bai mareta ba. A hankali ta ɗan waro idanunta domin taga meya hana shi sauke mata wannan mari.
Tsaye yake ya mace da kallan face ɗinta, dalilin da ya dakatar da hannunsa ga isa fatar kumatunta kenan, da alama a kallan farko ya fola, idanunsa a kan dogon wuyarta mai kyau da ƙawa. Ganin ta waro kallanta a kansa ya sa ya dawo da kallonsa a saman face ɗinta.
Kara waro idanunsa waje ya yi yana kallan haɗuwarta, lokaci guda ya wani ja numfashi tare da mai da kallansa a saman kirjinta. Ita kuwa ganin face ɗinsa ba ƙaramin girgizata ya yi ba, ta ga kyau na jinin Akka tamu ta amana, sai taga kamar ya fi kowa kyau a gidan. Yo dama yana kanin Ramish ba dole ya yi kyau ba.
Slowly ta kai kallanta kasa saman kyawawan fararen kafafunsa dake cikin wasu kyawawan takalma na yawo a tsakar gida, a hankali ta fara binsa da kallo har izuwa sama dai'dai wuyarsa, sai ta ji nauyin karisa kai kallanta saman face ɗinsa dan kada su haɗa idanu.
Kasa Dr Raj ya yi da hannunsa ya fasa marin nata, sannan ya ɗan kawar da kallonsa a kanta yana maidawa kan wayarsa dake ƙasa, sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi. Ganin yana kallan ƙasa yasa ta kai kallanta wajen ita ma. Wayarsa yake kallah, ɗan satar kallansa ta ɗan yi kafin ta duka zata ɗauka mashi wayar.
Dai'dai lokacin shi ma ya duƙa zai ɗauki kayansa ya wuce, ba tare da sun ankaraba suka kai hannunsu kan wayar a tare, ta rigasa ɗauka, amma da hannunsu ya goge juna wani shock da ta ji ne yasa ta saki wayar, shi ma sai ya ja hannunsa baya kaɗan. A hankali ya ɗago da kallansa a kan face ɗinta, while ita ma dai'dai lokacin ta ɗago da nata kallan a kan face ɗinsa, wato wannan fa shi ake cewa soyayya a kallan farko, the most luckys persons.
So idan ta tashi shiga mutum fa wlh bata excuse, wani lokaci ma zaka haɗu da yarinya da rana, sai da daddare idan ka koma ka kwanta santa ya shigeka im ka tinata, so, so, so, a karshe dai ao ita ce silar kowa a duniyar nan, bari dai mu cigaba.
Sarkafe juna da kallo suka yi, Dr Raj ya ga jinin Nigerians ya rasa natsuwa da control of his heart. Ita ma Zee taga ɗan balarabe jinin modarawa jinin Akka tamu ta amana ta rasa natsa natsuwar. Sun ɗauki a kallah 2 mins a haka suka kallan juna ido cikin ido kafin ta yi ta mazan zare idanunta daga kansa, sannan ta miƙa hannu ta ɗauka mashi wayarsa.
Wai ni kam ba Zee bace ta ce babu ita babu maza? Har da wani cewa ta tsani maza! Ko dai ba ita bace nikam?! Kaina ya ɗaure, ina ƴan special grp kuzo ku warware mun kullin dake kai'na,...........🥱
Cikin sanyin murya ta ce. "Am so so sorry, this is ur phone". Ta yi maganar tana miƙa mashi wayar.
Miƙewa tsaye shi ma ya yi, a maimakon ya karɓi wayar sai ya harɗe hannayensa a kirjinsa yana binta da kallo. Ɗan ƙasa kaɗan ta yi da kanta, kamar zata saki murmushi saboda wani irin bargon farinciki da ta ji ya lulluɓe zuciyarta ba tare da tasan dalilin farincikin ba.
Ya ɗauki a kallah 2 mins again yana ta kallanta kafin ya miƙa hannu ya karɓi wayarsa, cikin natsuwa ya juya ya nufi hanyar fita, yana tafiya yana waigota, wai a haka ma dan King ne ya yi mashi waya da ya same shi a main parlour, da ba zai tafi ya barta ba, sao ya tsaya jin wacece ita, amma King na jiransa, dan haka ya wuce yana kara waigota.
Ita ma wucewa gaba ta yi, tana tafiya tana waigosa, da alama ta ya burgeta. Saman ɗaya daga cikin sofas na wajen ta zauna tana dawo da kallonta a wajen, ta fara rarraba idanu tana kara jinjina irin dukiyar da aka narka a wajen.
•••••••••••••••••••••••••••••🔥
Mammie and Fanan, zaune suke suna shawarin yadda zasu ɓullowa lamarin Fanan da Jaish, mammie ta ci alwashi kuma ta yi rantsuwa da Allah sai Fanan ta auri Jaish, idan ba haka ba Jaish ɗin ya mutu kowa ya rasa, sai tsara yadda zasu wahalar da Mahnoor suke yi, yanzu Mammie ta gama tsara yadda za'ayi Fanan ta koma part ɗin Jaish da zama tare da mama Haulat kenan, ta kuma tsarawa Fanan ɗin irin abin da yakamata ta yi wa Mahnoor idan ta koma can da zama.
Ita kuma Sarina ta gama tsara mata yadda zata buga barikanci wajen samun soyayyar Jaish ko yaki ko y so, har da faɗa mata wai idan dare ya yi ta rinƙa saka sleeping dress tana zama a parlour da sunan zata yi kallo, hakan zai rinƙa jan hankalinsa a gareta, Sarina dai ta bata shawarin zama karuwar cikin gida sosai,......... My people's me kuke tinani a kan wannan shawari na Sarina? Anya kuna ganin hanya ce mai ɓillewa Fanan kuwa?.
A gefe guda kuwa, Sarina and abokanan rashin mutumcinta ne suke zaune a rest parlourn uncle Abbas suna shirya wani makircin, Omaid dai sai chatting yake yi a Whatsapp da sabuwar budurwarsa, shi kuwa Obaid sai tsarawa Sarina yadda komai zai gudana yake yi, shiri suke yi a kan yadda zasu ganawa Mahnoor azaba, tana neman da su tayata tun da kunga su suna da kunama da kwari, shi ne ta nemesu a kan wannan harka, dama kun san mutanenta ne. Obaid sai tsara mata yadda za'ayi yake yi, shi kuma Omaid yana chatting.
Sosai Sarina ta so yi wa su Obaid wayo wajen tambayarsu wanenen Omerish? Sai dai bata fito ta tambayesu wanenen shi kai tsaye ba, gudun kada su zargeta, ta fake da ce masu.
"Obaid na yi mafarki wani kyakkyawan saurayi mai cikar mazantaka da jarumta, dogo mai kama da daddy, ga shi da fuskar kwarjini da haiba, fari tas kamar momma, yana da saje irin na daddy, sai dai kwayar idanunsa irin na Auta ce wato hazel, sannan sunansa Omerish".
Lokacin da ta ambaci sunansa sai da dikkansu suka ɗago da kallonsu a kanta, lokaci guda kuma ko me suka tuna suka yi gaggawar kawar da kallonsu daga kanta suka cigaba da abin da suke yi. Ta fahimci sun yi shock da jin sunan da ta ambata, hakan yasa ta kara tsananta zarginta a kan abin da suke zargi ita da Mammiensu.
Cigaba ta yi da yi masu zabara dan su faɗa mata wanene Omerish kuma me hotonsa yake yi a wajen momma da har ta iya ɓoyewa a kasan bed ɗinta bata san kowa ya gani (kun tuna envelope da ta ɗauka a kasan bed ɗin momma? Hotunan dake ciki kenan, a jikin hoton matashin ne aka rubuta Omerish, a nan tasan sunansa). Sai dai da yake suma A ne wajen dabara da kaifin ƙwaƙwalwa sai suka shashantar da ita, suka tsara mata labarin karya wanda dole in mutum ya ji ya yarda da su. Suma da wayansu ashe.
A ɓangaren guda kuwa, Chuchu and Yah Jawad sai kashe junansu da love suke yi, yanzu hankalin Chuchu ya kwanta dan Auta ta dawo, sai kashe Yah Jawad da salan soyayyarta take yi tana rikita mashi ƙwaƙwalwa, dik abin da ta iya dange da soyayya tana iya kokarinta wajen koyar da Mahnoor, amma ita Mahnoor wai kunyar kwatantawa Jaish take ji, ga tsaronsa dake ranta, yanzu sun dawo wasan ɓuya ne ma, in yana nan bata fitowa parlour, sai ta tabbatar ya fita, kuma bata zuwa bedroom ɗinsa, saboda ta samawa kanta lafiya.
Suna tsaka da zuba soyayyarsu King ya yi wa Jawad massages a kan ya zo main parlour ya samesa yanzun nan. Dan dole ba dan ya so ba ya fita zuwa parlourn a tare da Chuchu ɗin.
A wani ɓangare kuwa Pretty and Mahreen da mama Haulat ne suke zaune suna hira, mama Haulat na koya masu abubuwa dan kara wayar masu da kai. Daga gefen su mama kuwa, mama tana can kishi kamar zai kasheta, ita kuma mummyn Chuchu tana fama da takaicin abin da yake faruwa tsakanin Auta da commander Zafar, ita a ganinta ai ba laifi bane dan Hoorain ya so Auta, saboda Auta fa tana da kyan da dik wani namiji ya ganta sai ya kyasa, kuma kada ku manta mummy ƴar talakawa ce, so bata ga dalilin da zai sa a wulaƙanta talaka kaman ita kuma ta goyi baya ba.
Waɗan nan sune kaɗan daga cikin abin da yake faruwa a cikin kingdom of power ta kowani ɓangare kenan. Mu koma kan labari in da muka dosa kenan.
•••••••••••••••••••••••••••••••••🔥
Cigaba kuka Auta ta yi tana kara faɗa mashi zasu yi nasara, ya jure saura kaɗan ne, dama dik abin da bawa yake so sai Allah ya jarrabcesa a kansa, to suma su ɗauki wannan a matsayin jarrabawarsu. Suna tsaka da karfafawa junansu gwiwa unexpect suka ga haske ya gauraye cikin ɗakin. Kafin ta yunkura domin ganin wanene sai ji ta yi an damki hannunta. Da karfi aka figeta, ta kofa aka fita da ita.
Dikkansu biyu idan hankalinsu ya kai miliyan to ya tashi, bana kaman Hoorain da ya shiga tashin hankali kamar zuciyarsa zata buga, damuwarsa ɗaya shi ne za'a hukunta mashi ita, hakan yasa shi a damuwa.
Ita ma bata kanta take yi ba, hankalinta a kansa, ta kara ja mashi wani musifar, sai ta ji ta yi danasanin zuwanta wajensa, yanzu za'a kara mashi azaba kan azaba.
Ba kowa bane ya ja hannunta face King, idan baku manta ba na faɗa maku yasa idanu a kanta, dik wani motsinta yana sane da shi, so tin da suka fita ita da guyson suke a kan idanunsa, ya gansu sarai, yanzu haka ya kama guyson ɗin ma yana main parlour, shiyasa ya yi wa su Jawad dikka massages a kan su same shi a parlourn, dan zai ɗauki tsastsauran mataki a kan Auta da guyson, bawan Allah guyson dik ya sha jinin jikinsa.
King bai zame da ita ko'ina ba sai main parlour, sai kuka take yi tana yi mashi magiya a kan ya yi hakuri ta tuba ba zata kara ba.
Sam bai saurareta ba, yana zuwa ya tsayar da ita a tsakiyar parlourn, da karfi ya ɗauke fuskarta da mari sai da ta tafi ta kifa ƙasa. Da gudu Chuchu ta yunkura zata tashi ta nufi Autar. A miliyan Jawad yasa hannu ya riketa, tana ƙoƙarin kwace hannunta King ya daka masu wani irin tsawa wanda ya sanyata komawa jikin Jawad a miliyan ta lafe, tin da suke basu taɓa ganin King cikin ɓacin rai irin na yau ba.
Kowa yana cikin parlourn banda su Zee da suke ba ƴaƴan familyn ba, sannan Jaish ma baya nan, amma tin daga kan su uncle Jahiz da suke cikin kingdom of power har kansu Omaid dik suna parlourn, su Mammie, uncle Abbas dik kowa ya hallara. Dan ran King ya ɓaci.
Akka tana zaune saman sofa ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, ita kanta bata goyan bayan wannan alaƙa ta Auta and Hoorain.
Sai huci King yake yi, Auta and guyson dik suna zube a ƙasa suna kuka, shi guyson King bai dakesa ba, taya Auta kuka kawai yake yi, ita kuwa nan take shatin yatsun king ruɗu ruɗu suka fito a face ɗinta, ta masu ne matiƙa.
Mummyn Chuchu ce ta yi ta mazan buɗe baki, cikin girmamawa ta ce. "Allah ya huci zuciyarka, dan Allah ka yi hakuri, ka kyale Zunaira haka, kada ka hukuntata a bisa laifin da ba yin kanta bane".
Aunty