Showing 282001 words to 285000 words out of 403653 words

Chapter 95 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

94

kowace mace ko ma in ce fin kowace mace tun da kema kin kawo mun budurcinki, kin aminta da hakan?". Idanunsa a cikin nata ya yi maganar, tabbas saboda tausayinta da kalamanta na ta rasa gata yasa ya yarda zai aureta, domin kuma ta yafe mashi, ba zai so ya yi sanadiyar shigarta kunci na har karshen rayuwarta ba, gara ya aureta ko ba komai dama shi ya buɗeta, tabbas ba zai yi mata gori a kan komai ba.

Kai ta fara girgiza mashi alamar bata yarda ba, tsananta kukan ta yi, har wani shessheƙa take yi, tamkar zata haɗiyi zuciya, cikin kuka mai tsuma zuciya ta ce. "Ba zan iya aurenka ba saboda ƴar uwata, Sharifat ta mun komai a rayuwata, dan haka ba zan taɓa bakanta mata ba, da ta shiga cikin ƙunci gara ni na tabbata a cikin bakinciki, a lokacin da na rasa gata, nike matsayin mara galihu, nike cikin tsakiyar rana a dokar sahara, a lokacin da duniya ta juya mun baya, farinciki ya kaurace daga rayuwata, na cire tsammanin yin farinciki har abada, a lokacin Sharifat ta tsaya tsayin daka wajen ganin sai da ta sakani dariya a rayuwata, ta sakani na ji cewa ni mutum ce, ta sakani na ji cewa ashe ina da sauran farinciki a rayuwarta, ta zame mun uwa, uba ƴar uwa, ɗan uwa, bata kyamaceni ba, ta jani a jiki tamkar ƴar uwarta na jini, ta kyautatawa rayuwata, dalilinta nasan kai'na har nasan darajar mutuncin da yau nike kuka a kansa dan ka keta mun shi, ba dan ita ba da ban san darajar mutuncin nawa ba, Sharifat ta wuci tinanin mai tinani a rai'na, dan Allah kada ka sake yin magana a kan aure tsakanina da kai, dan kai ne burin ƴar uwata!!". Tana kai karshen maganar ta kwace hannunta da sauri ta haye sama tana kara rushewa da kuma mai taɓa zuciya.

Gum ya tsaya tamkar wanda aka sassaƙa, yau ya ji sabon labari wai Sharifat na san shi, abin da bai taɓa ji ba bai taɓa tinani ba ko a mafarki, a cikin ransa ya ce ko mata sun kare a duniya shi me zai yi da Sharifat? A yadda ya tsani uwarta ina zai kaita? Tab lallai akwai cakwakiya kuwa.

Ya jima tsaye a wajen ya rasa madafa, daga karshe ya yanke shawarar bin bayanta, dan ba zai iya jurar ganinta da yunwa ba. Sama ya haye yana tinanin mafita a garesu gabaɗaya, dan a gaskiya ba zai iya jurar ganinta a halin da take ciki ba, yana da ilimin addini yasan cewa mutum ya shiga damuwa a dalilinka na wuni ɗaya ma babban musifa ce a gareka bare ace tsawon wata kuma yana neman zarcewa har abada idan bai ɗauki mataki ba? Ina zai kai wannan zunubi haka? Gaskiya da sake.
Kwace ya iskota a saman bed ta kifa kanta a saman pillow tana kuka tamkar ranta zai fita. Wani irin tausayinta ne ya kara kama shi, tabbas yasan da ciwo abin, amma ya zai yi to? Kaddararsu ce ta zo a haka. Gaban bed ɗin ya karisa, a saman bedside drawer ya ɗauka cup ɗin hannunsa kafin ya zauna a gefenta, hannunsa dikka biyu yasa ya ɗagota tare da juyo da ita suna fuskantar juna, Allah sarki ta datse idanunta gam tamkar zata fashesu. Slowly santa ya fara shigarsa ba tare da ya sani ba, a da iya tausayi ne kawai, amma yanzu gangar jikinsa ta fara karɓan wani sabon saƙon na daban!.

"Aesh nasan na yi abin da baki ba zai iya zayyana kuncin da kike ciki ba, yanzu da bakinki ina san ki faɗa mun me kike san na yi dan ki shiga cikin farinciki kamar a baya?". Cikin sigar rarrashi ya yi maganar...... Tana san kwace kanta daga garesa amma ta rasa kuzarin yin hakan, sai ta hakura kawai ta natsu tana cigaba da kukanta. Ganin bata da niyar bashi amsa ne yasa ya kai hannunsa ɗaya saman ƙuncinta ya fara goge mata hawayen da basu da niyar dakatawa daga zuba, hannunsa ɗaya kuma ya tallabota........ "Please talk to me Aesh". Cikin wani irin slow ya yi maganar, ga murya ƙasa ƙasa.

Ganin waɗan nan hawaye basu da niyar dakatawa ne yasa ya mannata da kirjinsa dan ya rarrasheta, hankalinsa yana tashi sosai idan ya ji kukanta, sai ma idan ya tuna da cewa marainiya ce ita, sai ya kara jin hankalinsa ya tashi...... "Aesh ki faɗa mun abin da kike so in yi maki ki dai'na wannan kuka ki fita a halin da kike ciki". Da ga ji voice ɗinsa kasan yana cikin damuwa matuƙa. Kai ta hau girgiza mashi alamar babu komai, ƙanƙameta a kirjinsa ya yi yana jin wani irin abu da ba zai iya gane ko menene mane yana ratsa kashi da ɓargo har zuwa ƙwaƙwalwa da zuciyarsa.

Tun tana iya kuka mai ɗan sauti har sautin ya dai'na fita, daga karshe ta yi diff alamar barci ya ɗauketa a jikinsa babu shiri, kun san idan mutum ya yi kuka sosai yana saurin yin barci, to ita ma dai ta yi ba tare da ta shirya ba, kuma bata sanya komai a cikinta ba, da yunwa ta yi barci, hanjinta dik a tattare sun naɗe. Jin numfashinta ya sauya zuwa irin na mai barci ne yasa ya dawo da kallonsa a kanta, a nan ya tabbatar da ta yi barci. Kwantar da ita ya yi a hankali cike da kulawa, sannan ya zubawa face ɗinta da ya yi jaga jaga da hawaye kallo na ƴan mintunan da basu gaza biyar ba. Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗan matsar da bakinsa kusa da ita kaɗa, a fili ya furta. "Isn't all my fault Aesh, am so so sorry, by the grace of god I will make you happy irin wanda haki taɓa samu ba a rayuwarki, ba zan bari ki sake yin kuka a kan wani abin ba, zan gyara abin da na ɓata da kai'na". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye. Bargo ya ja ya lulluɓa mata kafin ya nufi switch. Wutar ɗakin ya kashe sannan ya nufi waje, zuciyarsa cike da tinanin bata sanya komai a cikinta ba, tabbas kuma yasan tana jin yunwa, amma haka ya nufi nasa bedroom ɗin.

Saman bed ɗinsa ya kwanta, tunaninta ne kawai a cikin kwakwalwarsa, tin da wannan abin ya faru a tsakaninsu bai sami barci mai natsuwa da daɗi ba, kullum a daddafe yake yi kamar dai yau ɗin dai, da kyar ma barcin ta yi awon gaba da shi. Ransa cike da tinaninta

(Oh ni Princess Teema, kowa da kalar nasa cakwakiya da kaddarar a cikin RAWANIN ZALINCI, ita kuma Sweetie tana can tana fama da mai black heart ɗinta, shi ne kaddararta kuma ita ma ita ce kaddararsa, Auta da nata kaddarar, kai kowa ma da na shi bala'in da yake ciki, to ni kuma ina da Maltina mai sanyi, ba abin da ya fi rai'na, idan komai ya ɗauki zafi sai na kora kayana.)

••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥

🔥🔥🔥🔥PARIS🔥🔥🔥🔥

Kai tsaye bedroom ɗinsu Smart ya nufa da ita, kwance ya isko Auta idanunta a rufe, ya yi zatan barci take yi, dan haka sai ya shinfiɗe Pretty a gefenta, ya zauna saman bedside drawer ya hau tofa masu addu'oi. Dik abin da yake yi Auta na jinsa, sai da ya kammala ya rufesu da bargo ya fito ne ta miƙe zaune, ta gagara yin barci saboda tinanin Hoorain ɗinta, ta gaza samunsa a waya. Uban ta gumi ya buga a tsakiyar bed ɗin tana tinanina mafitarsu ita da shi.

Wayar ta ne ya fara kara alamar shigowar kira, jikinta har yana kerma wajen miƙa hannu a gaggauce ta ɗauko wayar. Wani irin zabura ta yi har ta miƙe tsayea tsakiyar bed ɗin ba tare da ta san ta yi hakan ba, dik kawai saboda murnar number Hoorain ne ya kirata. Jiki na tsuma hannu na kerma ta yi picking tare da kara wayar a kunnenta.

Kasancewar bai san number ba saboda number waje ce ba ta ƙasarsu ba sai ya yi sallama haɗe da tambayar wanene?. Da ka ji yadda yake yin magana zaka fahimci yana cikin tsananin ciwo da rashin kwanciyar hankali...... Idanunta ne suka cicciko da kwallah, a raunace ta ce. "My Hero Hoonairar kace, ni ce". Ta yi maganar tana zube gwiwowinta a saman mattress ɗin.

Shi kuwa yana jin haka yana daga kwance a gadan asibitin ya zabura ya miƙe zaune, tamkar zai ganta a gabansa ya ce. "Hoonaira, Hoonaira dama........dama......". Ƙasa yin maganar ya yi saboda sarkafewa da voice ɗinsa yake yi. Commander dake kwance a gefensa saman bed na masu jinyar majinyata ya fara yin barci ne ya tsinkayo muryan ɗan nasa cikin kuka kaman yana sambatu, hakan ya sa ya tashi zaune, dama wutan room ɗin a kunne. Ganinsa manne da waya a kunne ne yasa ya fahimci waya yake yi da Auta, dan ita kaɗai zai yi wa wannan rikicewar. Binsa da kallan tausayi commander ya yi yana jin zuciyarsa na kara raunata.

•••••••••••••••••••••🔥

"Calm down my hero, na dawo gareka ai a yanzu, kuma ba zamu taɓa rabuwa ba, please ka kwantar mun da hankali ka ji?". Cewar Auta...... Allah sarki soyayya, jinjina mata kai ya yi tamkar yana a gabanta tamkar kuma wani ƙaramin yaro wanda ake san yi wa dabara da alawa, dik ya susuce kamar ba jarumin assistant commander namu ba...... Abbo dai kallan tausayi kawai yake binsa da shi.

"Promise me that zaka dai'na damuwa ka ji?". Ta faɗa tana goge hawayen da suka zubo mata....... "Na yi alkawarin zan dai'na damuwa, ni ma ki mun alkawarin zaki dai'na kuka, kuma ki share hawayenki na yanzu da suke zubowa, kada ki bari su sake zuba kin ji my life?". Kai ta gyaɗa mashi alamar to ba tare da ta iya amsawa ba........ "Kece rayuwata Hoonaira ta, kece farincikina, ina san ganinki, na yi kewarki, please kizo in ganki kin ji?"....... Da kyar ta iya faɗin. "Bana nan my hero, ina wajen Yah Omerish, amma zan zo muga juna ka ji?".

A dai'dai lokacin da suke yin wannan magana shi kuma King suna yin meeting shi da uncle Jahiz, uncle Abbas and Akka, suna ƙoƙarin tsayar da magana a kan aurenta da Abdussalam and dawowar Smart kingdom of power saboda ya zo ya riki mulkinsa, dama nasa ne, tashin hankali kenan, akwai cakwakiya.

Sake jiki suka yi suka zubawa juna kalaman soyayya masu narka zuciya, tin Auta tana kuka har sai da ya sanyata dariya kai ɗan sauti, tini yasa ta mance da ta taɓa shiga kunci a rayuwarta, haka ta koma ta kwanta ta rungumo pillow, har da ce mashi. "My Hero da na rungumi pillown nan sai na ji kamar kai a ruguma, ka tuna mun forest".

Shi ma komawa ya yi ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya, cike da kauna da kulawa ya ce. "Soon watarana zaki rungume ɗin ba pillow ba" ....... Hoorain fa bai lura da Abbonsa ya tashi ba, kawai ya hau zuba love word abinsa. Ai taɓe baki commander ya yi yana mamakin ɗan nasa, tinani yake yi wai yaushe Hoorain ya iya magana haka? Shi dai yasan ko magana ta minti guda ɗansa baya yi, mutum kamar kurma, amma ji yanzu yadda yake zuba wasu zafafan kalamai kamar ba shi ba, har tantama commander ya yi a kan anya jarumin zakin ɗan nasa ne kuwa?.

Shi kuwa Hoorain lumshe idanu ma ya yi yana cigaba da bawa flower ɗinsa ruwa, daga karshe ma ya juyawa Abbo baya yana faɗin. "Kin tabbatar?". Tana daga kwance ta kara matse pillow a kirjinta kafin ta ce. "Tabbas da safe zamu yi video call, na tabbatar"....... Ajiyar zuciya ya sauke, wani bargo mai sanyi ne ya lulluɓe zuciyarsa, ya yi kewarta over.

"I really love you my Hoonaira, i promised to be with you with happy or not, kece farincikina kuma kwarin gwiwata". Da kyar ya iya kai karshen maganar, saboda bai saba dogon magana ba. Yau dai Auta baki har kunne, sai murmushi take saki. Ba su suka rabu da juna ba sai karfe 3, nan ma shi ya ce ta kwanta ta yi barci kada ta makara tashi sallah, da safe zai kirata. Bata yi mashi musu ba ya amsa da to, cike da kwarewa a iya bawa flower ruwa ta sumbaci wayar tata tare da ce mashi ya sanya a ransa kumatunsa ta sumbata, ƙara lumshe idanunsa ya yi yana jin wani irin yanayi mai daɗi, sai ya ji dama da gaske ne mana kumatun nasa ta sumbata, ai da ba zai iya yin barci ba yau.

Jin ya yi shiru bai yi magana bane yasa ta ce. "My Hero ni ba zaka bani na barcin bane?". A shagwaɓe sosai ta yi maganar. Sumbatar take nufin shi ma ya yi mata tamkar yadda ta yi mashi. Haba ji tamkar an yi mashi bushara da aljanna, juyowa ya yi tare da kai wayar ɗan bakinsa ya manna mata sumbatar kenan idanunsa suka sauka a kan Abbonsa da ya buka tagumi yana kallansa, commander ya bushe a zaune kamar wanda aka sankarar, a ransa yake faɗi ashe har da sumbata ɗansa ya iya bai da labari? Kai wannan abin mamaki ne a wajensa.

Wani irin kunya ne ta lulluɓe Hoorain, ga shi ya rigada ya kai sumbatar, sai ya rasa ya zai yi kawai ya yi gaggawar cire wayar daga bakinsa tare da fara kame kame kaman maras gaskiya, yana jiyo sanyayyar muryarta tana faɗin. "My Hero wannan sumbata ta isa ya rikeni daga nan har zuwa safiya in kwana cikin farinciki haɗe da mafarkinka". ...... Amma ya ƙasa iya bata amsa, sai ma ya yi gaggawar katse kiran kawai yana kallan Abbo...... Ajiyar zuciya commander ya sauke, can ƙasa ƙasa ya furta. "Dole in yi maka aure my lion". Ya yi maganar ne ta yadda Hoorain ɗin bai ji me ya faɗa ba. A hankali ya koma ya kwanta tare da juyawa Hoorain ɗin baya irin alamar bai ji komai ba.

Ajiyar zuciya Hoorain ya sauke, kunya ta gama rufesa, tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki ya juya ya bawa Abbon nasa baya yana lumshe idanunsa. A maimakon ya yi barci sai ya hau tinanin Hoonairansa yana nishaɗi. Ita kuwa yana katse kiran ta kara rungume pillow tana sakin murmushi har barci ya yi awon gaba da ita.

🔥🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥🔥

After one day. A hankali ta fara motsa idanunta tana san farkawa, Ronnie dake kusa da ita ne ya yi gaggawar matsawa ya riko hannunta, cikin sanyin murya ta fara ambatar sunanta a natse, shi tun daren jiya ya farfaɗo bawan Allah, ita kuwa da yake ta fisa tausayi sai yau ta farfaɗo, dan zuciyarta ya raunata sosai.

Waro idanunta da suka kumbura luhu luhu suka yi jajir waje ta yi, saman celling ta kafe da kallo kamar wadda bata a dai'dai, kamar taga bakon abu, sai ambatar sunanta Ronnie yake yi amma ina kamar bata a wajen, sai da ya sa hannu ya shari kumatunta ne ta juyo da kallonta a kansa. Suna haɗa idanu ta zabura ta miƙe zaune, cikin fitar hayyaci ta fara sambatu kamar haka. "Lovely bro yanzu big bro ya kashe mutanen nan dikka har da yaran da basu ji ba basu gani ba? Ko kuma ya hakura ya kyalesu?". A ruɗe take maganar tana jan numfashi da karfi karfi tamkar zata sume.

Ya lura bata a daidai, dan haka sai ya ce mata. "A'a ba dikka ya kashesu ba, ya yi wa wasu afuwa". Tabbas karya ya yi mata, kuma wannan shi ne karyarsa ta farko a duniya, shi baya karya wlh, amma saboda kwanciyar hankalinta ya yi.
Wani irin ajiyar zuciya ta sauke, a fili ta furta. "Alhamdulillah, ko ba komai mun yi nasara tun da muka iya sanya shi ya yafewa dubban al'umma"...... Ronnie dai jinta kawai yake yi, a cikin zuciyarsa yana cewa, lallai yarinya baki san waye big bro ba, bai taɓa yafiya ba a rayuwarsa, idan ya zartar da hukunci to fa dik abin da zai faru sai dai ya faru amma babu mai canza wannan hukunci, a haka suke rayuwa tun daga kan mulkin mahaifinsa har shi ɗin, babu wanda aka taɓa yi wa afuwa daga hukuncin da ya yanke a wannan birni, harta iyayen Floris Black Tiger ya kashe, an konasu a cikin wannan wuta, bai ragawa kowa ba, master Devil kawai ya bari a cikin maciya amanar nasa, shi ma akwai dalilin da yasa ya barshi, nasa hukuncin ta musamman ya tanada mashi.

Zuro kyawawan kafafunta kasan bed ɗin ta yi, jikinta na rawa saboda murna ta ce. "Lovely bro bari in je in ga big bro, dole na yi mashi godiya bisa wannan abin da ya yi, ya yi namijin ƙoƙari wajen yi masu afuwa". Ta kai karshen maganar tare da yunkurawa zata miƙe. A nan ne ta fahimci akwai drip a manne a hannunta, saboda zafin da ta ji, ta lankwatsa hannun ne ta dafa jikin mattress zata miƙe, shiyasa ya yi mata zafi. Shi kuwa tana wannan magana ya yi gaggawar kai hannu zai dakatar da ita saboda bai san a wani irin hali Black Tiger yake a yanzu ba, kada ta je yana kan tsini ya yi mata illah, dan ba imani ne da shi ba kuma ba gane kansa ake yi ba.

"Ronnie yaushe aka saka mun wannan abin kuma?". Ta faɗa tana kallan drip da ya kusa karewa, ɗan kaɗan ya rage. Sake hannun nata ya yi kafin ya amsa mata da tin wuraren la'asar, yanzu kuma mangariba ta kawo kai. Zaro idanu ta yi tana tambayarsa wai yau yaushe ne ma? Nan ya sanar da ita ai kwana ɗaya ta wuce, tun jiya take sume ai. Kara zaro idanu waje ta yi, jikinta har kerma ya fara yi, a natse ta furta Hasbunallahu wani'imal wakil.

Rarrashinta Ronnie ya shiga yi yana bata baki har ta hakura ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login