Showing 399001 words to 402000 words out of 403653 words

Chapter 134 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

81

da wani sabon kukan. Ai ɗauke wuta ya yi na wasu ƴan sakanni, lokaci guda ya jisa a duniyar mercury, ƙasa motsawa ya yi bare ya rabata da jikinsa, wani irin azabbabben shock ya ji tin daga tsakiyar kansa har izuwa tafun kafarsa, uhm abin ba'a magana.

"Why? Why zaka mun haka? Wani laifi na yi da na cancanci irin wannan hukunci? Meyasa? Meyasa?". Daddaɗar muryarta ne ya daki dodan kunnensa yasa ya farfaɗo daga duniyar tinanin da ya afaka. Ta yi maganar kuma tana riko rigarsa wajen massive chest ɗinsa. Kasa magana ya yi, sai dai ya kai hannunsa ya riƙo hannunta dake a saman kirjin nasa, gam ya damke hannun nata tamkar wani ya ce zai kwace mashi ita! Shiru dai bai iya yin magana ba!!.

Lokaci guda Smart ya ji sa a duniyar samar iska, juyo da kallonsa a kan Pretty dake kwance tana kuka ya yi, shaukin soyayyar su Auta ya ɗebesa har bai san lokacin da ya janyota jikinsa ba, wai shi ma zai yi irin na Hoorain ya rarrasheta, sai ya shiga ce mata. "Ya isa haka, ki yi shiru." Daga haka bai san me zai sake cewa a gaban ba, sai ya yi shiru yana kallan face ɗinta, cigaba da kukanta ta yi tana shessheƙa. A ransa ya ce ko kukan ma take yi kara kyau take yi, tamkar ita ta yi kanta. Ya kai karshen zancen zucin nasa tare da kai hannunsa ya shafi lallausan lips ɗinsa da suka tura pink sosai saboda kukan, sai wani ɓari suke yi tamkar mai jin sanyi, hancinta ya yi jajir, kazalika kumatunta ma ya yi jajir.

Ɗan jan dogon numfashi ya yi tare da saukewa a hankali kafin yasa hannu ya ɗan shafi lallausan kumatunta!. Cigaba ta yi da kukanta tamkar bata san yanayi ba, haka ya bi ya rinƙa tattaɓara har lokacin da barci ya ɗauketa a jikinsa, ajiyar zuciya ya sauke a fili ya ce dai gobe zaki yi azumi dik rigimarki!.

Shi kuwa Hoorain yana san ya yi mata rarrashi mai kyau, amma yana jin tsoro saboda da kunnuwansa kuma da idanunsa ya gani kuma ya shaida ita matar Abdussalam ne, dan haka sai ya rabata da jikinsa ba dan ya so ba, ya rarrasheta tare da ce mata ta zauna kada ta sake fita yana zuwa. Yana fita Smart ya yi mashi sakon a kan ya shirya kayansa yau zai dawo kingdom of power, saboda Auta ta rigada ta ganesa, kada azo a samu matsala, kar su jiƙa mashi aiki ba tare da ya gama bincikensa ba, su yi abin kunya, ai kunga da kunya idan bincike ya bada cewa yaya da kanwa ce su ɗin, so dole ya rabasu.

Sosai Hoorain ya ji zafin hakan, amma bashi da zaɓi, dole ya bi maganar babban yaya idan yana son cigaba da kasancewa cikin farinciki. Dole ya haɗa kayansa a ranar ya koma kingdom of power, ita kuma Auta Smart ya sanar da ita ta yi hakuri Hoorain zai dawo gareta nan da ɗan lokaci, ta kasance cikin farinciki, kuma ya basu dama su rinƙa yin waya da juna.

Uhm lokacin da Hoorain ya dira a kingdom of power babu wanda bai girgiza ba, musamman ma King da shi ya gama saddakarwa Hoorain ya mutu, ya ji zafin cetan ransa da Smart ya yi, hakan yasa ransa ya ɓaci matuƙa da har ya fusata ya ce Smart ya wuce ya koma Paris, shi kuma Smart ya ce sai ya gama abin da ya kawosa, dama shi bai zo zama a kingdom ɗin ba, dan haka idan ya kammala dole zai koma in da ya fito, dan a can ya fi wayo.

A wannan dare dai King da uncle Abbas game da Akka suka yi zaman meeting su uku wanda babu uncle Jahiz a ciki, a nan ne Akka ta ce. "Idan muka aura mashi Sareena ina da yakinin zata iya mantar da shi dik wannan bincike da yake son yi, kuma ina da tabbacin zata iya sauya shi ta yadda zai dawo yana jin maganarmu".

Uncle Abbas ne ya karɓi zancen da cewa. "Ina fatan hakan ya kasance, in ba haka ba tabbas zamu shiga bala'in da gara mutuwa a kanta, zai zama dik abin da muka yi a baya ya tashi a banza".......... Shi dai King ya yi ƙasa da kansa bai iya sake cewa komai ba! Kun san wani irin zulumi King yake a ciki? Batu ne a kan Hoorain! Kun san da cewa su Akka basu san alaƙar dake a tsakaninsa da matar commander ba? Shi ne tashin hankalinsa na biyu bayan batu kan Ramish, yana tsoron gaskiya ta bayyana, mutumcinsa zata zube, kuma ai yanzu ya tuba.

Su Akka kuma suna cikin zulumi ne a kan batun Ramish, suna tsoron Smart ya bankaɗo gaskiya, dan dikkansu abin ya shafa!! Shi ne fa suke san aura mashi Sareena wai dan su rufe mashi baki..... KAI SMART ƊAN DUNIYA NE, YA HANA SU AKKA SAKAT YA TAFI YANA SOYAYYARSA DA PRETTY!! WATO DIK SUN SAN KOMAI DAKE FARUWA! UHM AKWAI KALLO A GABA WLH!.

Ganin King ya yi shiru yasa Akka ta ce. "Zuhair lafiya kuwa?". A hanzarce ya girgiza mata kai alamar babu komai, shiru suka zuba mashi idanun suna kallonsa, da yake sun san halin da suke a ciki sai suka ce kila shi ma fargabar abin da Smart zai iya tonowa ne yasaka shi a cikin damuwa, hakan yasa suka hau rarrashinsa suka tausansa tare da cewa kada ya damu da Smart ya auri Sareena komai zai canza, ita Sareena tana jin maganarsu, dan haka zata zama wadda Smart yake jin maganarta In Sha Allah!.... My people's kuna ganin haƙarsu zai cinwa ruwa kuwa? Anya zasu iya sanya Sareena ta zama wacce Smart yake jin maganarta kuwa? Muje dai zuwa.

Haka suka yi wannan zaman meeting suka tashi ba tare da kwakkwarar mafita ba, da alama uncle Jahiz bai san me yake faruwa bane yasa babu shi a wannan zama.

Ita kuwa Mammie tana can tana shirya yadda zata ɗauki Fanan daga gidan ba tare da kowa ya nemeta ba, wato ta rufewa ƴan gidan baki kada su nemi in da suke. A gefe guda kuwa ana can ana ta rabon kayan masarufi saboda azumin da za'a tashi da shi gobe, sarkin hatsi King ya bawa ragamar kula da wannan, talakawa sun wadatu da kayan abinci kam babu karya, ga tarin dukiya da aka raba masu dan sayan kayan abinci!!.

YANZU NE CROWN OF POWER WATO (KINGDOM OF POWER) ZATA KAMA DA WUTA, YANZU WASAN ZAI FARA. ƘAƘA KARA ƘAƘA, GA HOORAIN GA KAMAR, SANNAN GA KING AND COMMANDER A TSAKIYA, UHM MAI WARWARE WANNAN CAKWAKIYA INA GA SAI MAMMAN KAMRAN KAWAI!!.

🔥🔥🔥BLACK WORLD🔥🔥🔥

A hankali take salallaɓowa kamar wata ɓarauniya, misalin karfe 6 ne na safe, sanye take da uniform ɗinta, yau sport wears na school ɗin ta sanya, ta yi kyau a cikin kayan sosai, tin da take a cikin empeir ɗin bata taɓa shiga cikin kitchen ba sai a wannan karan, dan haka sai ta nufi kitchen ɗin cikin sanɗa.

Sai dai fa a lokacin da ta isa cikin dry kitchen ɗin nasu sai da ta waro idanu waje, duniya guda ta gani, gabaɗaya ta zama ƴar kallo, ta ko'ina Robbot ne suke ta aikin kai komo, aikin dake gabansu kawai suke yi! Ajiyar zuciya ta sauke, almost 10 mins tana tsaye tana karewa kitchen ɗin kallo kafin ta karisa ciki. Babu wanda ya kulata, nan ta fara ƴan waige waige tana neman ta ina ne wajen girki da wajen shirya abinci suke!.

Ta ɗauki a kallah good 10 mins kafin ta iya gano wajen girki a ciki. Can ta hango katafaren trys mai shake da kayan girke girke da ake kaiwa Black Tiger, sun kammala shirya mashi breakfast yadda yakamata, lokaci kawai suke jira ya cika su kai mashi, kun san shi ba'a haura lokacinsa kamar yadda ba'a nufara idan lokaci bai cika ba! Dole sai lokacin ya cika sannan ake zuwa kai mashi kome ya buƙata

Can ta nufa kirjinta na dukan uku uku, tana zuwa tana satar kallon robot ɗin, dan tana ga kamar zasu ganota. Sai karanta Hasbunallahu wani'imal wakil da kuma lailla haillah anta subhanaka inni kuntu minaz-zalimin, ta haɗa da ayar kariya. A cikin suratul yasin, aya ta 9.

وَجَعَلْنَا مِنۢ بَيْنِ أَيْدِيهِمْ سَدًّۭا وَمِنْ خَلْفِهِمْ سَدًّۭا فَأَغْشَيْنَـٰهُمْ فَهُمْ لَا يُبْصِرُونَ


Ta karanta wannan aya, tana karantawa tana nufar wajen abincin. Kuma wannan addu'a ya taimaka mata Allah ya datse ganinsu basu ganta ba har ta isa wajen, cikin gaggawa tasa hannunta ta ciro wani robar ruwa da ta ɓoyesa a wajen cikinta, a gaggauce ta ɗauke ruwan dake a saman tray ɗin da suka sanyawa Black Tiger ta sanya mashi wanda ta zo da shi, a miliyan ta bar wajen ta gudu ta koma parlourn.

Wannan aya ta cikin suratul yasin, aya ta 9.

وَجَعَلْنَا مِنۢ بَيْنِ أَيْدِيهِمْ سَدًّۭا وَمِنْ خَلْفِهِمْ سَدًّۭا فَأَغْشَيْنَـٰهُمْ فَهُمْ لَا يُبْصِرُونَ


Aya ce dake makantar da idanun abokan gaba dan cinma mutum, wannan aya Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yake karantawa a dik lokacin da mushrikai suka nufosa, a lokacin da ya bar garin Makka ya yi hijira zuwa Madinah, lokacin da suka shiga kogo da sayyidina Abubakar wannan aya Manzon Allah (SAW) ya karanta hakan yasa Allah ya datse idanun mushrikan da suka biyo bayansu, basu samu damar ganinsu ba, a lokacin da Manzon Allah ya yi tafiya da Nana A'isha ma ayar nan ya karanta suka kau daga idanun makiya, so wannan aya tana da matuƙar muhimmanci ga Musulmi ya riketa, musamman a rayuwar yanzu da tsaro ya zama abin da ya zama, so na baku shi sadaka ku mun addu'a ta alkhari da bakunanku masu albarka!.

Suratul Fatiha da Ayatul Kursiyyu ma suna daga cikin abin da Annabi (SAW) ke karantawa don neman kariya daga wajen Allah!.

-----------------------------------🔥🔥

A miliyan ta nufi waje rike da robar ruwansa da ta ɗauko a cikin tray ɗin, tsabar murna sai murmushi take saki. A parlour ta isko Ronnie yana tsaye, yana shirye cikin hoodie mai bala'in kyau, yau garin nasu akwai sanyi sosai, ga iskar dake kaɗawa kamar za'ayi ruwan sama, damuna ta kusa dawowa, a wasu yankuna ma ta dawo!.

"Good morning lovely bro". Ta faɗa tana tsananta murmushinta, ji take yi yau tamkar ta zuba ruwa a kasa ta sha...... A tinaninku me ta saka a cikin ruwan da ta bawa Black Tiger?.

Hararar ya ɗan dalla mata kafin ya ce. "Ina kika je kuma bayan kin san ina jiranki". "Sorry my bro, na je wani wajen ne, mu tafi yanzu". "Ba za'a faɗa mun in da aka je ɗin ba?". Hannu tasa ta rufe fuskarta tana ɗan murmushi mai ƙayatarwa....... "Me zaki yi da robar ruwa ke da kike azumi yau?". Ya jefa mata tambayar yana kallan robar ruwan dake hannunta.

"Mantawa na yi da ina azumi na ɗauko har zan sha sai na tina, yanzu dai please let's go". Ta kai karshen maganar tare da wucewa ta ɗauki jacket ɗinta and school bag ɗinta, ta miƙa mashi school bag ɗin kafin ta sanya jacket ɗin, tana ƙoƙarin zuge zip sama ta wuce gaba tana faɗin su je. Bayanta ta bi yana yaba irin kyan da ta yi yau, ya ce ta fi kyau a cikin sport wear ɗin nan, godiya kawai ta yi mashi suka wuce izuwa wajen motocin.

Ba tare da ɓata lokaci ba suka wuce school. Kamar kullum yana sauketa ya dawo gida. Yana dawowa bedroom ɗinsa ya nufa ya kwanta, dan dama barci bai ishe shi ba, daren jiya bai samu ishasshen barci ba, dan tin da ta farkar da shi da ihunta da ya koma bai rintsa ba.

A ɓangaren Black Tiger kuwa, dik karfin tsafinsa Allah ya datse idanunsa sakamakon addu'ar da Sweetie ta yi, so bai ga lokacin da ta canza ruwan shansa ba, saboda haka ana kawo mashi abinci kamar yadda ya saba ya ci ya ƙoshi, sannan ya zuba ruwan nata a cikin cup ya sha ba tare da tinanin wani abin ba.

Sai dai kuma yana shan wannan ruwa sai me? Take a wajen ya fara kwarara amai tamkar zai amayar da kayan cikinsa, wani irin amai bakinkirin kamar bakar leda mai bala'in yauki ya fara kwararawa tamkar ba daga cikinsa ya fito ba, gabaɗaya ilahirin jikinsa ya hau kakkarwa tamkar wanda ake jonawa kantarki, lokaci guda gabaɗaya empeir ɗin ta yi wani irin azabbabben duhu na ƴan ɗakiku kafin daga bisani ta sake yin haske, wani irin juyi yaga gabaɗaya room ɗin nasa tana yi mashi, kansa dake barazanar tarwatse mashi ya dage, lokaci guda idanunsa suka rikiɗe zuwa Jade eye mai duhu kafin su koma normal.

Wasu irin zaratan jijiyoyi ne suka bayyana sosai a gaban goshinsa, dafe cikinsa dake tsananin murɗa mashi da hannu guda ya yi, a take a wajen ya zube ƙasa a saman gwiwowinsa ya hau murkusoso a wajen. Robot dake serving ɗinsa abinci ne ya yi gaggawar ɗaukarsa cak daga wajen, sai dai kafin ya motsa da shi daga wajen Black Tiger ya daina numfashi gabaɗaya. Dik wannan abin dake faruwa Ronnie yana can yana barcinsa, ba shi ya tashi ba sai karfe 1:30 dai'dai, kai tsaye bedroom na yayan nasa ya nufa, sai dai a lokacin ya iskosa yana barci, bai san ba barci yake yi ba, tin wannan suma da ya yi Robot ya dawo da shi saman bed ɗinsa shi ne har yanzu bai farfaɗo ba!

Ronnie ya ɗauka barci ne, so sai ya wuce cikin luxury toile ɗinsa ya watsa ruwa, sannan ya ɗauro alawala ya fito. Shiryawa ya je ya yi cikin pj's dress ya zo ya tada sallah domin yin azahar sai ya je ya ɗauki Sweetie a school. First time ɗinsa da yin azumi kenan yau, amma bai ji wani wahala ba, saboda iska da sanyin da suka tashi da shi.

Ko da ya idar da sallah bai bi ta kan yayan nasa ba ya fito ya nufi wajen parking lot ɗinsu. Cikin motarsa ya shiga tare da escort ɗinsu suka wuce ɗaukota. Yau dai ita kaɗai take zauna abinta tana jiransa, dik ƴan kawayen nata ma sun janye jiki da ita, saboda sun gano daga BLACK TIGER EMPIRE take, suna bala'in tsoro sai suka ja baya, ta yi ƙoƙarin nuna masu babu komai, amma sun ki yarda da ita, sun ce ina ta wuce class ɗinsu!.

Ko da ta dawo daga school bata zame ko'ina ba sai part ɗin Big Bro, dan tasan me ta yi mashi, so burinta kawai ta zo ta gansa, ta ga abin ya yi aiki ne ko bai yi ba! Da ta zo taga yana barci sai ta ji babu daɗi, dan sai ta yi tinanin bai sha ruwan ba, dan haka jiki babu kwari ta juya ta koma bedroom ɗinta. Ronnie ya so zargan wani abin, amma kuma sai ya kawar da hakan ta hanyar korar shaiɗan.

Wanka ta yi ta shirya cikin malesian gown wanda ya kai mata har ƙasa, ya bi coca cola shape ɗinta ya zauna ɗas, hp ɗin nan nata ya fito sosai, gata ta ko'ina ta cika ɓul-ɓul. Kasancewar yau suna azumi babu batun yin dinner, sai suka zauna yin karatu kawai har zuwa bayan la'asar. Bayan sun yi sallah sai ta ce su wuce church, har lokacin Black Tiger yana nan yadda yake tin safe, bai farfaɗo ba!.

Church suka wuce ita da Ronnie, amma sai da ya ja mata kunne sosai a kan kada ya ji bakinta ta yi magana, da okey kawai ta amsa mashi. Ta so su gana da Black Tiger kafin su tafi, amma ina, bata samu wannan dama ba, dan a tinaninsu barci yake yi. Addu'a sosai ta yi a lokacin fitarta empeir ɗin, shi ma Ronnie ta ce ya yi addu'a, ba musu ya yi, dan yasan dik abin da zata ce ya yi to mai kyau ne.

Tin da suka doshi katafaren ginin church ɗin ta ji gabanta yana wani irin faɗuwa, yana bada bugu dum dum, amma ta cigaba da ambato sunan Allah har suka ƙarisa ciki. A tare suka sauko ita da Ronnie, yau sai ta saje da kiristocin ma, dan kan babu ɗankwali, kun san a irin wannan birni dama yaushe zasu samu ɗankwali? Ai babu, so haka ta fito dan sonta da zuwa church ɗin.

Hannunta Ronnie ya kama suka ƙarisa ciki. Wani irin mamaki ne ya kamata ganin yadda aka ƙawata ginin church ɗin, an zuba kayan alatu na more rayuwa, ga wasu irin luntsuma luntsuman kujerun zama mai sa mutum ya mance in da yake, ga wani sanyin Ac mai ni'ima dake dukan kowa. Can saman stage father church ne zaune saman haɗaɗɗen kujerarsa mai kama da King seat, yana sanye cikin suit while face ɗinsa da white glass, daga bayansa wani katan bookshelf mai girman gaske wanda yake shake da tulin Bibles da littafan tarihi, ga wasu kyawawan flowers decorations a kusa da bookshelf ɗin, sannan a gaban father church akwai wani katafaren table mai shake da wasu littattafai da kuma bell na bugawa dan samun attention na mutane!. Gaskiya Church ɗin ya haɗu babu karya.

A saman waɗan nan haɗaɗɗun kujerun suka zauna, mutanen birnin suna cike sosai, da alama wannan Church na manyan kai ne, dan dik waɗan da suke ciki jikinsu ya nuna alamar jin daɗi da hutu!.

Kowa ya natsu tsit sun mayar da hankali a kan Father church wanda shi ma a yanzu ya shigo, gyaran murya Father ya yi kafin ya fara jawabinsa game da buɗewa da addu'a tasu ta kiristoci, a cikin addu'ar ne ya ce sun fara da sunan UBANGIJI Jesus....... Pastor na faɗin haka ta yi gaggawar miƙewa tsaye, with harsh voice ta ce.

"Karya ne, Annabi Isa ba Allah bane, kuma shi bai taɓa ce maku shi Allah bane, infact shi ce maku ma ya yi ku bi Allah ku yarda da shi manzan Allah ne sai ku tsira, amma babu in da ya ce maku shi Allah ne, idan kuma akwai shi ka bani hujja, in dai ka kawo mun in da ya ce maku ku bini nine Allah to

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login