Showing 273001 words to 276000 words out of 403653 words
fa ta fara zagin uban Sarina, amma yanzu kun ji da Sarina ta rama shikenan abu yazama laifi an zagi bappanta ba zata bari ba, har da zubar da hakwaran Sarina zata yi, kai Mahreen duniya.
Ƙanƙameta da kyau guyson ya yi, cikin sanyin murya ya ce. "Ki natsu mun in ji me ya haɗaku faɗa".
Juyo da idanunta kansa ta yi, cike da rashin kunya ta yi mashi kallan uku saura kwata kafin ta ce. "Ji yadda yake magana kamar wani babban mutun bayan kai mai kukan ciwo ne kawai, kai da rarrashinka ake yi kamar karamin yaro ne zaka ce zaka raba faɗa? Kai fa zan iya zaneka ka yi kuka". Babbar magana!!.
Bawan Allah a maimakon ya ji zafin kalamanta sai ma ya saki cool murmushi kafin ya ce. "To na ji zaki iya zaneni, yanzu dai muje part ɗin momma sai ki zaneni a can".
Sarina kuwa hannu ta kai zata kai mata capka ya yi saurin janyeta daga tsakaninsu shi ya shiga tsakanin nasu yana rike da hannunta, a natse ya ce. "Aunty Sarina dan Allah kiyi hakuri, kada ki biye mata, baki ga yarinya bace?". ..... Ai bai gama rufe baki ba ta sake yin tsalle ta dire haɗe da cewa. "Wlh ni ba yarinya bace, kuma ma ai na fika tun da ni bana kukan ciwo".
Sarina kuwa, dama zata yi magana da ya yi magana ne, amma jin Mahreen ta capki zancen tana jajjaga mashi masifa yasa ta haɗiye maganarta tana huci. Shi dai har yanzu ko kaɗan kalamanta basu wani taɓa shi ba bare har su ɓata mashi rai, kara burgesa ma take daɗa yi, dan haka bai kulata ba ya sake duban Sarina ya ce. "Aunty Sarina dan Allah ki yi hakuri kin ji?".
Sarina na ƙoƙarin cewa ya kyaleta ta taka Mahreen yadda yakamata ko zuciyarta ya huce, sai Mahreen ɗin ta rigata da cewa. "Kada ta yi hakuri, ta zo ta lililili ta likeni ta zurani ta bakin allura ta sake fitarwa karshen kenan idan ta isah"...... Yau dai guyson yaga ta kansa, ana ƙoƙarin kashe wuta ita kuma tana kara hurata. Sake kaimata wawura Sarina ta yi ya yi saurin janyeta, ita kuma ana janyeta tana wani matsowa zata kaiwa Sarina duka har da wani dunkule hannu wai ita nan jaruma, sai wani kyafta idanu take yi.
Guyson dai da yaga wannan abin fa ba karewa zai yi ba sai ya shammaceta ya ɗauketa cak yana bawa Sarina hakuri ya nufi part ɗin Momma, rai a ɓace Sarina ta ce wlh ba zata kyaleta ba, sai dai kada su haɗu, in suka haɗu sai ta fasa mata baki, ita kuwa Mahreen ya ɗauketa ma bakin bai mutu ba, faɗi take. "Wooooo ƙatuwar banza ta sha duka, kuma na daki banza ba yadda zaki yi".
Kai Mahreen sai shirin Allah.
Bai sauketa a ko'ina ba sai a tsakiyar bedroom na momma, babu kowa a ɗakin sai Mahnoor dake kwance saman bed tana barci, momma taki yarda ta matsa ko nan da can, ta ce a gadanta zata rinƙa kwana tun da ba a nan King yake kwana idan yana ɗakinta ba, gadanta ne ita kaɗai, so Mahnoor zata iya kwana a kai, tun Mahnoor na noƙewa har ya saki jiki ta ɗauki momma matsayin uwa kawai.
Yana sauketa ta riko waist ɗinta da hannu dikka biyu tana binsa da wani irin kallo. Ɗan sunkuyar da kansa ƙasa ya yi alamar kunya da kamala kafin ya ce. "To sarkin faɗa kallan me ni kuma kike mun? Ko dai kina duba ta in da zaki ɗauki fansa a jikina ne dan na hanaki yin faɗa?"....... Kai ta ɗan girgiza mashi alamar a'a, sannan ta ce. "Ina mamaki ne". Ɗago da kallansa a kanta ya yi kafin ya ce. "Mamakin menene kuma?". Ɗan nisawa ta yi kafin ta amsa da. "Ashe kana da karfa fa? Ban yi zatan kana da karfi ba ai, kuma da kake maganar ɗaukar fansa ai ko zan ɗauki fansa a kan kowa ban da Hammana (Jaish) da mai kama da shi, kana kama da Hamma shiyasa idan ka rabamu faɗa da mutane bana komawa kanka da faɗar".
Siririn murmushi ya saki har sai da dimple ɗinsa suka lotsa, sannan ya ce. "To nagode da nike cin darajar kamannina da Yah Jaish nike tsira daga dukanki, amma in tambayeki mana?"........... Tsaresa da ido ta yi alamar tana jinsa ba tare da ta yi magana ba........ "Meyasa kike san yin faɗa ne?". Shi ne tambayar da ya jefa mata.
Kai ta ɗan ɗaga sama kamar mai tunanin wani abin, can ta sauko da kallanta a kansa, ya yi shiru yana jiran amsa..... "Idan aka taɓoni ne bana iya bari, yanzu ma ban yafewa wannan mai kama da akuyoyin Nenne ɗin ba, dik ranar da muka sake haɗuwa sai na cire mata hakwaran sama dikka".
Shi dai yarintarta da shiriritarta dik yana burgesa, ga shegen san kwalliyar nan nata yasa ya kara jinta a ransa, dan shi ma kamar yadda yake ɗan wanka haka yake san ƴan gayu, bare ita da take caras cas, ga kyau da kirar jiki mai kyau, dik kalar wankar da zata ɗauka kyau take yi sosai.
"Please ki dai'na faɗar nan haka ya isa kin ji?". Cikin sigar rarrashi ya yi maganar yana kallan janbakinta da ya ɓata mata gefe gefen baki saboda faɗar da suka gwabza.
"Ni ba zan dai'na yin faɗa ba matsawar za'a rinƙa shiga gonata". Cikin tsiwa ta yi maganar......... Girgiza kai kawai ya yi, sannan ya matsa kusa da ita dab, ya kai hannunsa saman lips ɗinta domin ya gyara mata jan bakin ba...... A miliyan ta ja baya kaɗan tana faɗin. "Kai ma na lura ɗan iska ne mai san taɓa jikin mata, yanzu ka ɗaukeni ban yi maka wata magana ba na yafe maka shi ne har ka samu damar taɓa mun baki ko?".
Nisawa ya ɗan yi kafin ya kallenta from up to down, sannan ya ce. "To ai ke ba za'a kiraki da ƴan'mata ba, baki wuce munzalin ɗaukarki da nike yi ba, ke yarinya ce"........ Ai rike waist ɗinta da hannu dikka biyu ta yi, cikin tsiwa ta ce. "Wlh ni ba yarinya bace, me banbancina da ƴanmatan?"........ Kai Mahreen akwai shegen san girma...... Shi kuwa matsawa kusa da ita kaɗan ya yi tare da kai hannunsa saman ƴan kirgan danginta da ta fara, sannan ya ce. "Wannan shi ne abu na farko da ya fara banbantaki da ƴan'mata, ke baki da breast ai, kin gansu fa yanzu suke fitowa ƴan ƙananan da su, ki bari sai sun girma sai ki fara haɗa kanki da manyan mata"....... INNALILLAHI WA INNA ILAHIR RAJIUN, KAI ANA WANI SHA'ANI A KINGDOM OF POWER, AMMA GUYSON MA ƊAN DUNIYA NE.
Tsit Mahreen ta yi ta rasa abin faɗe, ga shi yasa hannu ya taɓa mata su, yau dai bakin ya mutu. Shi kuwa cigaba ya yi da cewa. "Akwai banbancinki da ƴan'mata dayawa bayan breast ɗinki, juyo in nuna maki sauran". Ya kai karshen maganar yana ƙoƙarin riko hannunta ya juyar da ita. Ai a miliyan ta fisge hannunta tare da saka mashi kukan shagwaɓa da take yi wa bappa a kauye, ta faɗi ƙasa kamar dai yadda take yi a kauye, birgima ta fara yi tana faɗin sai ya biyata taɓa mata kirji da ya yi.
Ganin Mahnoor tana motsawa zata farka ne yasa ya yi gaggawar yin ƙasa shi ma, bakinta ya sanya hannunsa ya toshe yana faɗin ta yi hakuri zai biyata taɓawa da ya yi.... NI KAM INA FATAN ALLAH YA KAWO MAI SANYA BAKIN MAHREEH YA MUTU! MASU FATAN GANIN MAHREEN A LABOUR ROOM SU ƊAGA HANNU.
Rungumota ya yi ya hau rarrashi, nan ma ashe wani laifi ya kara ya taɓata, kwace kanta ta yi tana cigaba da kukan ta miƙe ta nufo waje, wai zata je ta faɗawa Momma ya taɓa mata breast ɗinta ya kuma rungumeta ashe ɗan iska ne shi ɗin. Bayanta ya bi da sauri dan ya bata hakuri, sai da suka zo dab da bedroom ɗinsa ya capketa, tana ƙoƙarin kwace kanta ya turata cikin bedroom ɗin, shiga ya yi ya rufo kofa har da murza key.......... To ko me zai yi mata?.
••••••••••••••••••••••••••••••••🔥🔥
Kwace Dr Raj ya isko Jaish saman sofa yana ɗan juyi a hankali hankali, cike da kauna ya tambayesa menene yake damunsa haka, miƙewa zaune ya yi yana wanu nuku nuku, kun san shi da kunya sosai, dan haka ya ƙasa iya sanar da Dr ga abin da yake damuwansa, sai kawai ya ce babu komai barci yake ji. Dr ya fahimci tabbas akwai abin da kanin nasa yake ɓoye mashi, amma tin da ya nuna baya san faɗa mashi sai kawai ya kyalesa ya ce to ya tashi ya shiga ciki mana.
Ba musu ya miƙe ya nufi ciki, a lokacin ya kai kololuwan da ba zai iya cigaba da rike kansa ba, har ya nufi bedroom ɗinsa sai kuma ya fasa ya juyo ya nufi na momma, a cewarsa zai je gaisheta ne kawai..... GAISUWA TSAKIYAR DARE KUMA? WAI BA SHI NE MA YAKE KIRANTA A WAYA DA SAFE BA? TO ME NA GAISUWAR DARE TUN DA NA SAFE MA A WAYA AKE YINTA? TO MU DAI MUNA NAN DAI'DAI DA KAI ƊAN RAININ SENSE.
A sama farkon page ɗin nan na yi magana a kan kashe rai ba bisa haqqi ba da Sweetie ta faɗawa Black Tiger, to waɗan ne rayuka ne suka kalatta a kashe su wato bisa haqqi kenan, zan kawo maku su a jere domin ku sani.
A Musulunce, an haramta kashe rai ba bisa hakki ba, amma akwai wasu nau’ikan laifuka da shari’a ta halatta a yankewa hukuncin kisa, ga sunan kamar haka, na farko, idan mutum ya kashe wani da gangan ba tare da dalili ba, shari’a ta yarda a kashe shi a matsayin ramuwar gayya. Wannan hukunci yana nan cikin Alqur’ani, suratul baqara sura ta 2 aya ta 178, Ya ku waɗanda kuka yi imani! An wajabta muku hukuncin ramuwar gayya a kan kisanku.
Duk da haka, iyalan wanda aka kashe na da damar yafiya ko karɓar diyya kuɗin fansa kenan, maimakon a kashe wanda ya aikata kisan.
Abu na biyu zinacewar mutumin da ya taɓa aure. Mutum da ya taɓa yin aure wato baligi ne, yana da hankali, idan ya aikata zina, to hukuncinsa kisa ne ta hanyar jifa da duwatsu. Wannan ya tabbata a cikin hadisai, cikin muslim lamba ta 1690 da bukhari lamba 6814, Idan namiji da mace sun aikata zina kuma sun taɓa yin aure, to a jefe kowannensu da duwatsu har su mutu. Sai dai, dole ne a samu shaidu huɗu ko kuma mai laifi ya furta da kansa.
Laifi na uku riddah ficewa daga addinin musulunci. Mutumin da ya musulunta, daga baya ya fita daga addinin Musulunci shari’a ta yarda a yi masa hukuncin kisa. Annabi (SAW) a cikin Bukhari hadisi mai lamba 6922 ya ce. Duk wanda ya canza addininsa ya fita daga Musulunci, ku kashe shi.
Sai dai, malamai sun yi bayani cewa dole a fara ba wa mutum dama ya tuba kafin a aiwatar da hukunci.
Na huɗu fasad a kasa. Fasad fil-Ardh Wato Fashi, Ta’addanci, da cin zarafi.
Mutane da suka aikata manyan laifuka irin su fashi da makami, ta’addanci, ko cin zarafin mutane a ƙasa, shari’a ta yarda a yanke musu hukuncin kisa. Allah cikin suratul ma'ida ya ce. Lalle ne sakamakon waɗanda suke yaƙi da Allah da Manzonsa kuma suke yin ɓarna a ƙasa shi ne a kashe su ko a gicciye su ko a yanke hannuwansu da ƙafafunsu, ko kuma a kore su daga ƙasarsu. Wannan wani kaskanci ne a gare su a duniya, kuma a Lahira suna da azaba mai girma da tsanani.
Wannan hukunci yana kan barayin da suka aikata fashi da makami, masu tayar da fitina, da waɗanda suka haddasa ruɗani a cikin al’umma.
Na biyar luwaɗi da maɗigo. Homosexuality. A shari’ar musulunci, idan an samu mutum yana yin luwaɗi (homosexuality), hukuncinsa kisa ne, kamar yadda wasu hadisai suka nuna, a cikin tirmidhi hadisi mai lamba 1456 da Abu Dawud lamba ta 4462. Idan kuka kama mutum yana aikata aikin mutanen Lut, to ku kashe shi da wanda ake aikata da shi. Sai dai, malamai sun yi saɓani kan yadda za a aiwatar da wannan hukunci.
Waɗannan su ne manyan laifukan da shari’ar musulunci ta halatta a yankewa hukuncin kisa. Sai dai dole ne a bi ƙa’idojin shari’a sosai kafin a aiwatar da hukunci, don kauce wa zalunci. Haka kuma, addini ya fi son yafiya da gyara fiye da ɗaukar fansa. Fatan kun gane? Ina san ku rinƙa sanin hukuncin addini ne dan shi ne hukunci na gaskiya, shiyasa ma nike kawo maku kwararan hojjoji faɗar Allah. Allah kasa mu cika da imani
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========
MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
Bakinsa a ɗauke da sallama ya shiga cikin bedroom ɗin, rashin mutane a ciki yasa ba'a amsa mashi sallamar tasa ba, kuma dama already yasan momma bata ciki, dan ɗazun ya sameta a part na King, kawai dai ya zo ne dan ya rasa in da zai je.
A saman sofa ya zauna yana tinanin me mafita a garesa? Dan shi ya rasa abin yi, ya yi shiru cikin tinanin da yake yi ba tare da ya lura da akwai mutun a cikin ɗakin ba, wayarsa dake aljihunsa ce ta fara ruri alamar shigowar kira. Shiru ya ɗan yi tamkar ba zai ɗauki kiran ba, sai da ta kusa katsewa ne ya ciro wayar.
Yah Omerish shi ne sunan da yake yawo a saman screen ɗin, jikinsa dik kasala, da kyar ya iya yin picking tare da kara wayar a kunnensa. Kamar wanda yake cikin magagin barci ya ce. "Hello, good evening Yah Omerish". Daga ɗayan ɓangaren Smart dake kwance a saman rest bed dake wajen balconynsa ya amsa mashi da. "Evening how was your day?". .........Da kyar ya amsa da Alhdulillah, idan yana magana sai ya ji kamar yana kara jefa kansa cikin wahala ne.
(Na manta na ce ba zan sake saka turanci a cikin rubutu na ba, saboda su Sumayya sun yi complain kuma na ji kukansu dama ba yarenmu bane bamu da gadonsa, shegen iyayi ne kawai irin namu,🥱 yanzu idan turanci ta mutu muna da gadonsa ne? Yen yen yen mun ishi mutane. Wai mu ba zamu tsaya mu daraja yarenmu ba, ance Hausa novel ko uban me ya kawo turanci a ciki?🤔 Hegu masu jajayen kunnuwa sun sa wasu basa kallan yaren iyaye da kakanni da daraja, sun gurɓata mana tinani, sai shegen iyayi da feleƙe muka iya😅 to ni dai mutane na ƴan Niger sun kawo korafi kuma na karɓa mun raba jaha da masu jajayen kunnuwa, Allah yasa kada na rinƙa mantawa ina rubutawa, kun san sabo da rubuta shi ne yasa ko kace ba zaka saka ba sai ka manta ka saka, amma zan yi ƙoƙarin dainawa!!.)
"Ina momma? I have been calling her number since isn't going". Ya faɗa yana miƙewa zaune. Dan ya ji alamar motsi a parlourn ƙasa, dan haka sai ya miƙe zaune dan ya saurara da kyau.
"Ka kira number dad tana tare da shi yanzu". Jaish ya faɗa yana ɗaga kansa sama. Unexpect kallansa ya sauka a kan bed ɗin momma, ɗan zaro idanunsa waje ya yi yana kallanta, sam bai yi zatan ganinta a cikin ɗakin ba.
Miƙewa tsaye ya yi a hanzarce, tun daga Smart bai sallamesa ba ya katse kiran tare da nufar in da take kwance. Like wow abin ya birgesa ya kuma bashi mamaki, ga shi momma bata nan, so the thing sweet him over. Shiru ya ɗan yi yana tinanin me yakamata ya yi kenan? Ya zuba mata idanun yana yi mata mayen kallo yadda ta kudundune a cikin bargon, kallo ɗaya ya yi wa face ɗinta ya fahimci ta sha kuka kafin ta yi wannan barci, a cikin zuciyarsa ya ji wani abin ta ɗan sokesa ganin busassun hawayen nata, kun san akwai tsohon soyayyarta a kasar zuciyarsa, so idan wani abin ya sameta baya jin daɗi, amma kuma yaki yardanwa kansa ya yi accepting ɗinta hundred.
Wani ɓangare na zuciyarsa ce ta ayyana mashi momma zata zo ta same shi, ai tuna haka yasa ya yi gaggawar sanya hannunsa ya ɗauketa cak har da bargon momma ɗin dik ya haɗa ya nufi bedroom ɗinsa da ita, buƙata ta biya, wai ita momma a nan ta ɓoyeta sai ya kawo kansa ya bada hakuri ne, to ga shi dai ya ɗauke matarsa abinsa. MAHNOOR SAI DAI MU CE ALLAH YA BAMU ƳAN TWINS IRIN UNCLES ƊINSU OMAID AND OBAID.....🥱
(Yauwa kun takurawa jikokin Akka fa my people's, kun saka masu idanu saboda suna da sha'awa sosai, ku rufe mun baki shiru, kada na kara jin wata ta takurawa jikokin Akka, dik duniyar yanzu ba haka ta zama ba? Ba haka kuke ba wai? Ko kun ɗauka bamu sani bane? Mun san komai dan haka ku dai'na takurawa jikokin Akka dik haka kuke😒 kuma ni dai bana ganin laifinku, dan dama a karshen duniya sha'awa zata yawaita sosai shiyasa za'a samu zinace zinace, da addini nike rubuta littafina ba da ka ba!! Na san me nike yi, wasu abubuwan sai gaba idan suka bayyana zaku ce mun karanta a littafin Princess Teema da jimawa)
Shi kuwa Smart Jaish yana katse kiran ya kira number King tare da miƙewa ya nufo waje domin ya duba waye