Showing 33001 words to 36000 words out of 403653 words
suna tsananin kaunarta saboda sanin yakamatanta suna kuma girmamata, bata da san kai, hukunci cikin adalci take yankewa.
Cike da tsantsar so da kaunarta ya ce. "To Raeesa me kike san na yi masu a yanzu kenan? Kin dai san babu wanda na tsana a duniya biyun King Abdul Mutallab da kuma King Al Mustapha".
Nisawa ta yi kafin ta amsa da. "Na sani daddyna, kuma kana kan dai'dai, amma idan ba damuwa ni ka bani izinin in je in yi magana da shi".
"Kina ganin hakan zai sakaki farinciki ya kuma biya buƙatarki?".
Jinjina mashi kai ta yi tare da amsawa da e. Dawo da kallonsa a kan commander Zafar ya yi tare da bashi umarnin da ya yi mata rakiya haɗe da wasu zaƙwaƙuran warriors ɗin su take mashi baya, kada su bari komai ƙanƙantar wani abin ya taɓata.
Cikin girmamawa suka risinar da kai haɗe da karɓar umarni. Miƙewa tsaye ta yi tare da karisowa gaban King, ta duka a saman gwiwowinta cikin ladabi da biyayya ta bayyana godiyarta a garesa haɗe da nuna mashi ta yi farinciki na sauraron korafinta da ya yi ya kuma yi amfani da shawarinta.
Hannunsa ya ɗaura saman kanta ya fara kwararo mata madarar albarka. Su commander sai tayata amsawa suke yi da amin ya Allah.
Tsawon 5 mins tana tsugunne a gabansa har sai da ya gama zuba mata addu'oin nasa ne ya bata umarnin ta tashi su je. Sumbata a goshi ta ɗan miƙe ta kai mashi kafin ta miƙe tsaye gabaɗaya, ta yi gaba su commander Zafar suka rufa mata baya, alkyabbarta sai jan kasa yake yi.
===========================💘
Tin daga nesa ta hango sarkin Qahtaniyawa dake a saman koshashiyar dokinsa, kai daga ganinsa kasan ya ji izza da isa malam, dukiya ta yi mubaya'a, kayan adan da aka kawata dokinsa da yake kai kawai ba karamar dukiya bace, babban sarki ne mai isa da izza, sai dai a karkashin Daular kingdom of power suke, sun taɓa bijirewa umarni da dokikin King Zuhair har ya yakesu.
Warriors sun kai 20 zaƙwaƙuran sadaukai ne suka take mata baya, tana a tsakiya, commander Zafar yana gefen damanta, sarkin Fada yana a gefen hagunta, kai daga ganin yadda take taku kasan jinin Modarawa ne yake gudana a cikin jikinta, ga jinin mulki dake ratsa jikinta, ai kunsan abin ba'a magana.
Ganinta yasa King Al-Mustapah ya buƙaci sauka daga saman dokinsa, dan ko baa gaya mashi ba yasan ita ta wakilci King Zuhair, dama yasan da wuya King Zuhair ya yarda ya basu fuskar da zasu iya shiga cikin kingdom of power ɗin ko su sami damar yin magana da shi kawai dai sun gwada ne dama, kun san ance a rashin ta yi ake barin arha.
King Al-Mustapah yana sauka daga saman dokinsa dikka sauran ƴan rakiyansa ma suka yi kasa, suka sauka.
Step biyar tsakaninta da shi ta dakata a wajen tana kallonsa from up to down.
Cikin girmamawa ya yi mata barka da zuwa. A maimakon ta amsa sai ta yi shiru na tsawon good 2 mins tana kare masu kallo.
Har sun fidda ran zata tankasu, har sun fara tunanin ko dai King Zuhair bai bata damar ta yi magana da su bane, ko kuma wani abin ake shirya masu.
Sun luluƙa duniyar tunani kamar daga sama suka tsinkayo voice ɗinta tana faɗin.
"Menene ya kawoku nan?".
A kanta King Al-Mustapah ya tsayar da kallonsa, tsohon zumar soyayyarta ce ta taso mashi, ya so Aunty MieMie kamar hauka, amma King ya hanashi ita sakamakon tsohuwar mummunar gaba dake a tsakaninsu tun iyaye da kakani, kada ku manta jinin Modarawa basa yafiya kuma basa matuwa, in baku gaji da faɗa ba ko shekara miliyoyin za'ayi ana yi ba zasu gaji ba.
Dalilin haukar san ta da yake yi ne ma yasa yake bata girma kamar yadda yake bawa mahaifinta King Zuhair.
•••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
"Dama mun zo ne muna masu miƙa wuya haɗe da mubaya'a kamar yadda muka buƙata a baya mai girma King ya ki yarda, bamu gaji ba a wannan karon ma mun sake dawowa da kokan bararmu a garesa, ki taimaka ki sanar da shi mun durkusa a kan gwiwonmu muna masu mubaya'a da kaskantar da kai, ya yi hakuri mu koma zama kamar da tsawon shekaru da suka shuɗe, wanna gaba na iyayenmu ne ba namu ba..............."
Ɗaga mashi hannu ɗaya ta yi alamar ya yi mata shiru, hakan ne ya katse maganar da yake yi.
Tin da ya fara yin magana ta fahimci akwai zallar munafurci da tuggu haɗe da sharri da zallar karya a cikin kalamansa, a yanayin karantarsa da ta yi ta fahimci shigo shigo ba zurfi yake san yi masu, so ta gane komai, shekara nawa tana tare da waɗan da suka fishi sanin duniya, zata iya cewa dik duniya bata taɓa ganin bakin bakiri irin King Abdul Mutallab ba, shi ma bai sha ta daɗi a hannunsu ba bare King Al-Mustapah ba.
Cike da isa da izza ta ce.
"Umarni nike baku ba shawara ba! Ku yi gaggawar barin nan tin kafin rai'na ya ɓaci, ka dai san ba zamu karɓi wani risinawarku ba, dan bamu da buƙata!".
Zai sake yin magana ta ɗaga mashi hannun alamar bata da buƙatar sake jin ko uppan daga gare shi, daga haka ta ce.
"Commander nan da mintuna 5 idan basu bar nan ba ku yi masu zobe ku yakesu!".
Ta yi maganar a dake ba tare da ta kalli in da commander yake ba, yana kai karshen maganar kuma ta juya cikin zafa ta bar wajen.
Har ta ɗan yi nisa a tafiyar tata sai kuma ta juyo, cikin kakkausar murya ta ce. "Babu sulhu a tsakaninmu da ku har abada, ayi ta yaki daga nan har illah Masha Allah, muddin ba zaku daina zalinci ba, mu kuma ba zamu ɗaga kafa ba, babu wani sauran azzalumi da zamu bari ya sarara!".
Tana kai karshen maganar ta wuce abinta, a hanzarce warrios goma suka rufa mata baya, warrios goma kuma suka tsaya a tare da commander Zafar dan su kori su King Al-Mustapah!.
========After some hour=========💘
King Al-Mustapah ya juya ya koma Daularsa, su commander an dawo cikin gida dan cigaba da shagalin biki, hankalin kowa a kwance, sai kaiwa da komawa ake yi, ana ta hidima, abubuwa sun kara tsananta, haɗuwa iya haɗuwa.
•••••••••••••••••••••••••••••••••••💘🔥
Waje ya yi waje, cikin katafaren hall dake cikin kingdom ɗin aka shirya wanna gagarumim taro domin dinner bikin, haɗuwa iya haɗuwa wanna waje ya yi, an zuba sabin furniture da komai da komai, zayyana maku ƙawatuwar wannan waje ma ai ba zai yi wu ba, dan ya zarce tinaninku.
An ƙawata kujerar zaman amarya da ango sosai, gabaɗaya cikin hall ɗin matasan ƴaƴan manya manyan sarakuna da shuwagabani masu ji da kansu ne a ciki, iyaye basu halarci wajen ba, saboda abu ne na yara matasa, Auntynsu Jawad ita ce a gaba wajen kawatawa gimbiya Chuchu kwalliya, har yanzu bata san cewa Jawad aka aurawa Chuchu ba Rizwan ba, King ya bar abin sai bayan komai ya lafa za'a yi maganar, iya momma ce kawai ta san a matansa ma.
Abu fa ya yi abu, sai dai ango Jawad dik a susuce yake, bashi da kuzari ko kaɗan, hankalinsa dik ya karkata a kan Rizwan yanzu, amma ba karya kwalliyarsa da ya sha ta yi kyau over, dik da akwai ɗan rama a tattare da shi, hakan bai hana haiba da kalama tasa ta bayyana ba, ya fito a jikin Akka ɗinsa, zallar madarar kyau.
Sai shirye shirye ake yi da misalin karfe 11 na dare za'a fara gudanar da dinner ɗin.
To bari mu garzaya wani part kafin lokacin yin dinner ya cika sai mu dawo dan ganin yadda komai zai gudana.
=======BLACK 🌑 WORLD🪐========
Today part in this Black world is the best part amount the previous part's!! I really like this part more than your expectations 💘 because I really like islam, am very very proud to be a Muslim💘 a kullum burina in ga ina magana a kan addinina tare da manya manyan hujoji, ina faɗar niimomin addinina da fifikonsa da kowani addini, kai ba zan iya gaya maku yadda nike kaunar musulmai da musulci ba wlh, Allah dai ka kara mana soyayyar Manzon Allah, amma muna alfahari da musulunci kam ba karya!!.
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
Karfe 7 dai'dai Ronnie suka dawo daga church, yana san zuwa ya ga Sweetie amma ya fi san ya kai ga yayansa a farko, dan haka a bakin kofar room ɗinsa suka rabu da Floris, ita ta shiga ciki shi kuma ya wuce part na Black Tiger.
Ya ɗauki a kallah 30 mins a ciki, can ya fito sanye da hoodies masu balai'n tsada a jikinsa, ya yi matuƙar kyau, da alama a part ɗin ya yi wanka, da yake yana da hasken fata sosai sai black color tana bala'in yi mashi kyau launin kayan kenan.
Dab zai shiga room ɗinsa ya tsinkayo muryar Floris da Sweetie suna magana, ɗan dakatawa ya yi dan ya ji me suke faɗa.
"Kina nufin kin san Jesus?". Cewar Floris. Ta yi maganar mamaki sosai a saman face ɗinta, dan suna dawowa daga church ta yi saurin karisawa wajen Sweetie, a shirmenta wai bari ta yi saurin fara koyawa Sweetie addininta dan ta rinjayeta, shi ne da ta fara magana a kan Annabi Isa (A.S) sai Sweetie ta ce mata ta san shi ai, abin ya bata mamaki matuƙa. Sai ta samu wajen a bakin bed ta zauna dan ta ji daga ina Sweetie ta san Jesus?!.
Jinjina kai Sweetie ta yi tare da amsa mata da. "I think mu musulmai ma mun fi ku sanin wanene shi! Kai bama i think ba, mun fi ku sanin wanene shi menene tarihinsa na hakika!".
Sanya password Ronnie ya yi a kofar ya buɗe, dan yana san ya ji hujjojin da Sweetie take da shi da har take magana with full confidence a kan addinin nan nata yana san kureta.
A tare suka dawo da kallonsu a kansa tin da ya shigo, zama ya yi saman egg-s chair dake fuskantarsu, ya harɗe hannaye a saman kirjinsa yana binsu da kallo.
"Beb ka ji Sweetie wai ta san Jesus fa!". Cewar Floris da bata yarda Sweetie ta san Annabi Isa or ta fita saninsa ba!.
Kallonsa a kan Sweetie da ita ma take kallonsa. "A ina kika san Jesus bayan ba addinin nin mu kike ba?".
Kamar baya san yin magana ya yi ta, kuma shi ma yanzu yana san kure Sweetie ne, saboda ya ga confidence ɗinta ya yi yawa, gara su kureta su gani.
"A malamullah mai tsarki wato Alqur'ani, a nan nasan shi, shi ya zo mana da tarihinsa gabaɗaya har ta dalilin da yasa kuke ce mashi Allah, wasunku su ce mashi ɗan Allah".
Ta bashi amsa cikin halin ko in kula bare har ta wani damu.
"Wanene Jesus?". Ronnie ya wurga mata tambayar dan ya kureta, su ji shin da gaske ta san shi ne ko dai cika baki ne kawai, basu yarda da ana yin karya a duniya ba, dan basa yi, amma a kan wanan magana sun fara tunanin kamar san zuciyarta kawai Sweetie take faɗa, sunga kamar tana san janyesu izuwa addininta ne ba tare da wani hujja ba!.
Miƙewa tsaye ta yi cike da jin daɗin tambayoyinsu a gareta, dan dama so take su bata dama ta yi masu bayani game da hujoji domin ta samu Allah ya taimaketa ta tsiratar da su daga duhun kafurci izuwa haske da rahma. Tambayar Ronnie ya yi mata matuƙar daɗi sosai, sai ta ji tamkar ice block ya manna mata a kirjinta.
Jingina da jikin wall ta yi tare da harɗe hannayenta a kirji, dikkansu idanunsu a kanta suna jiran bayaninta.
A nitse ta fara magana one by one with full confidence.
"Jesus wato Annabi Isa manzon Allah ne, yana ɗaya daga cikin manya manyan manzanin da Allah ya turo masu riƙe da litafi, shi ne annabin da aka turowa bani Israela wato yahudawa, shi ne ya zo da littafin injila wanda a yau kuke kiranta da Bible domin isar da saƙon Allah zuwa ga bani Isra'ila................"
Katseta Ronnie ya yi da cewa. "Ta yaya Jesus ya zo duniya? And yana da baba ko bashi da shi?".
All his though ya ɗaureta a wanna tambaya, dan da wanna suke amfani a koda yaushe su danganta annabi Isa a matsayin ɗan Allah, idan ta bashi amsar Annabi Isa bai da baba kunga ya samu damar kara karfafa cewa ɗan Allah ne shi.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Da ga kai har Floris kada wanda ya sake katse mun maganata, zan yi maku bayani a kan wanene annabi Isa (A.S) dallah dallah, dan da alama ku baku san ainahin wanene shi bama, so yakamata ku san shi da kyau ku kuma san in da kuka dosa!!"......... Tashin sense.
Ko tsoronsu bata ji ba ta gaya masu hakan, idanunta a kan Ronnie da yanayin face ɗinsa ta fara canzawa izuwa na ɓacin rai, ita kam Floris tuni dama ranta ya gama ɓaci, ta ya Sweetie zata ce masu basu san Jesus ba? Wannan ma ai rainin wayo ne!.
Ko kaɗan bata damu da ganin sun ɓata rai ba, ko a gefen takalmarta, cike da kwarin gwiwa da yakinin in ta yi masu bayani zasu fahimta ta fara magana kamar haka.
"Annabi Isa (A.S.), wanda ake kira Yesu Almasihu a Kiristanci, yana daga cikin manyan annabawan Allah da Musulmai da Kiristoci ke girmamawa, kowane yana da fahimtarsa kan tarihinsa da matsayinsa".
"Tarihin Annabi Isa (A.S.) a Musulunci". Idanunta a kan Ronnie take wannan magana ko shakkarsa babu bare tsoronsa.
"An haifi Annabi Isa ta mu’ujizar Allah ba tare da uba ba, mahaifiyarsa Nana Maryam tana cikin tsarkaka. Wannan lamari ya faru ne saboda umarnin Allah don ya zama alama ga duniya a cikin Suratul Maryam shafi na 19 aya ta 16 zuwa 34 a nan wannan bayani yake!"
"Annabi Isa ya zo da sakon tauhidi, yana kira mutane su bauta wa Allah shi kaɗai, ya kuma tabbatar da shari'ar Annabi Musa (A.S.). Ya kuma kawo mu’ujizai da suka haɗa da warkar da kurma da makafi da maido da matattu bisa iznin Allah".
"Matsayinsa a Musulunci. Musulmai ba su dauki Isa (A.S.) a matsayin Allah ba, sai dai matsayin annabi kuma manzon Allah. A Musulunci annabi Isa ba kasheshi aka yi kamar yadda kiristoci suke tunani ba! Allah ya ɗaukaka shi zuwa gareshi wato sama, cikin Suratul An-Nisa shafi na 4 aya ta 157-158 Allah ya yi magana akan hakan!"
____________________🪐💘
"Dalilin Da Yasa Wasu Suke Bauta Masa a Kiristanci. A cikin Kiristanci, Yesu ana ɗaukarsa Ɗan Allah, kuma Kiristoci suna ganin shi a matsayin cikar alkawarin Allah ga ƴan Adam don cetonsu daga zunubi ya kaisu ga rahma!. Kiristoci suna ganin nassoshi da aka rubuta a Littafinsu suna nuna cewa Yesu shi ne Ɗan Allah wanda aka aiko domin ya mutu don zunuban duniya, sannan ya tashi daga matattu, malamansu sun gaya masu irin mu'ujizozinsa hakan yasa suke ganin ya kai ya zama ɗan Allah, saboda ya tada matattu ya kuma warkar da marasa lafiya bisa umarnin Allah. Wannan shine tushen imaninsu kiristoci".
"Wasu Kiristoci suna daukar Yesu a matsayin wani bangare na Ubangiji. Wannan akidar ta samo asali daga fahimtar su game da littattafan Injila ko in ce Bible ɗinsu na yanzu!".
"Nasan zaku yi mamaki idan nace maku Bible da kuke karantawa a yanzu ba shi ne wanda Annabi Isa ya zo maku da shi ba, and canza maku shi tsawon dubbanin shekaru, amma bari in yi maku bayani yadda zasu fi fahimta da kyau, bari in banbance maku Alqur'ani mai girma da kuma injila haɗe da Bible ɗinku na yanzu, bari ku ga banbancin sai ku fidda na gaskiya".
Ta kai karshen maganar tana sauke ajiyar zuciya. Daga Ronnie har Floris babu wanda ya sake tofa ko uppan, sun tsareta da idanu, sai dai dikkansu ransu ya sosu na yadda take ƙoƙarin karyata malamansu da kuma littafinsu, amma sun kasa kunne dan su ji hujojinta.
Cigaba da yin maganar ta yi cikin tsanaki yadda komai doɗewar kwakwalwar mutum sai ya fahimci zancenta tsaɓ!.
"Bambanci Tsakanin Injila da Al-Qur'ani Mai Girma, and Bible".
"Injila wanda Annabi Isa (A.S.) ya kawo shi ne wahayi daga Allah, wanda aka yi niyya ga bani Isra'ila a lokacin. A Musulunci, an san wannan da Injil, amma ba wannan ba ne Littafin Bible da Kiristoci ke amfani da shi a yau. Littafin da Kiristoci ke kira Bible an haɗa shi ne daga rubuce-rubuce daban-daban, ciki har da Tsohon Alkawali da Sabon Alkawali, wanda yawanci ya ƙunshi tarihin Annabi Isa da wasikun manzanni, ba asalin Injila da Allah ya saukar ba, tarihin mu'ujizar Annabi Isa ne suka cika cikin Bible na yanzu, shiyasa kiristoci suka zage a kan lallai Annabi Isa Allah ne tun da zai iya raya matattu, ina da yakinin da anbawa kiristoci ainahin littafin da Annabi Isa ya kawo masu domin su san girman Allah to da tabbas yau za'a wayi gari babu Christians ko ɗaya a duniya, da zasu san girman Allah su san kuma dik abin da Annabi Isa ya aikata dan gane da mu'ujizarsa to Allah ne ya umarcesa ya kuma yassare mashi yin hakan, amma an ɓoye masu gaskiya an barsu cikin ɓata!".
Ɗan dakatawa ta yi da maganar tana jan numfashi, tabbas ta lura ran Ronnie ya kara ɓaci. Amma ko kaɗan bata damu ba!.
Kasa jurewa Ronnie ya yi har sai da ya ce. "Menene hujjarki na cewa an canza mana littafi ne ba wanda Jesus ya zo da shi muke amfani da shi ba?!". Da ɗan daga murya ya yi maganar.
"Amma ai nace kada ku saka mun baki a magana ko ku katseni ko?".
Mamakin jin furusinta