Showing 135001 words to 138000 words out of 403653 words
dariya.
Sai da ta yi mai isarta sannan ta dakata haɗe da ɗaure fuska lokaci guda, sannan ta sauko ƙasa daga saman bed ɗin, gaban mirror ta nufa wayar na manne a kumnenta, har ta kusa isa wajen kuma sai ta koma ta kunna wutar ɗakin yadda zata ji daɗin ganin kanta da kyau, sanye take da wando da riga na barci masu kyau launin ash colar.
Tsayuwa ta yi a gaban mirror, cike da kwarin gwiwa take bin kanta da kallo, dik sun yi shiru suna jinta, amsarta kawai suke san ji.
Raunartar da muryarta ta yi, kamar wata marainiya haɗe da fuskar tausayi, cikin nuna damuwa ta fara magana kamar haka.
"Dan Allah kada ku cutar mun da babana, zan yi dik abin da kuke so, ku yi hakuri kun ji?..................." Tana gama faɗar haka ta wani irin ɗaure fuskarta sosai, cikin kakkausar murya ta cigaba da cewa. "Haka kuke son jin na faɗa ko? To baku isa ba, wlh ba zan sake yin abin da kuka ce ba, mahaifina kuma Allah ne ya haliccesa ba ni ba, dan haka shi zai karesa ta in da baku taɓa zata ba, ba zan sake cutar da wani a dalilinku ba, na saka mashi guba na cutar da shi a farko, na sake zama sanadiyar da aka harbesa da bullet, na sake zama sanadiyar da aka shirya bomb da zai kashe mutane dayawa, na cutar da Ramish sosai wanda dole a yanzu na gyara kuskure kada Allah ya kamani, shi kuma babana ku je ku da Allahn da ya haliccesa, sannan kada ku manta idan kun kashe babana ku kuma ku tabbata a duniya kada ku mutu, daga karshe ina yi maku mummunar albishir da cewa wlh tallahi dik da ban taɓa ganin fuskokinku a zahiri ba, to ku sani zan iya gane ne ku, sannan ku sani nasan gidan wannan mata mai kibar, bugu da kari kuma ku sani dik maganganun da muke yi da ku tun daga ranar farko har zuwa yanzu ina da recording ɗinsa in audio a cikin memoryna da na yi mashi ajiya mai kyau, dik time da muka yi waya ina recoding in saka memoryna in yi copy in cire in ajiye dan samun shaida, ku jirani yanzu lokacina ne, dik sai na ɗauki fansan abin da kuka yi mun, kuma Ramish da izinin Allah ya fi karfinku, daga yau ni zan zame mashi garkuwa mai taimaka mashi ta hanyar da bai zata ba, sai asirinku ya tonu azzalumai, kuma ku kwana da sanin cewa nasan wanenen Bilal a cikinku, kuma tabbas dan na taya Ramish aiki zan shiga jikin Bilal, zaku sha mamaki". Babu tsoro ko miskala zarratin a ranta ta zayyano maganganun nan. Tana gama faɗar hakan ta katse wayar tare da kashe shi mai gabaɗaya.
Idan hankalinsu ya kai muliyan to fa a yau ya tashi. Ita kuwa kallan kanta a cikin mirror ta yi, a fili ta furta. "Lokacin ku ya fara daga yanzu, wlh ba zan dai'na zargin Bilal ba, kuma zai gane bashi da wayo a lokacin da zan kama shi cike da hujojin da ba zai iya kubcewa ba, zai sha mamakina, sun ɗauka bani da ilimi bani da wayo ko? To su shirya, Bilal kai ma lokacinka ya fara, zaka sha game na karya, zaka gane baka iya cin amana ba, am sorry Yah Ramish, kila idan na tayaka wannan yakin ka iya yafe mun laifukan da na yi maka, is time now!". Ta kai karshen surutan nata tare da juyawa ta isa ga switch, kashe wutar ɗakin ta yi ta wuce izuwa saman bed abinta.
Jama'a na ce ku tafawa Leesharh, ana ganinta kamar wawiya ashe tana da wayo, kenan harda recoding na maganganunsu ta rinƙa yi? Lallai ta cika jajirtatciya, kenan saboda ta gane wanenen Bilal ta aminta da soyayyarsa ko dai ya abin yake? Akwai cakwakiya kuwa! Muje dai zuwa dan muga ya wannan wasa zata kaya. Amma kuna tunanin masu nikaf zasu barta da ranta? Kada ku manta ta yi masu barazana da hujoji masu karfi kamar recoding nasu, sanin gidan Hajiya two seater, sanin Bilal da dai sauransu, kuna tunanin zasu barta ta tona masu asiri?. To sai dai muce Allah yasa ta kai wayewar garin gobe, dan gaskiya akwai matsala, suna fa da mutane a cikin gidan, ga shi Sharifat bata ɗakin yau, fatana kada su saka mutanensu su biyo dare su kasheta fa.........😥💔
••••••••••••••• FOREST•••••••••••••••🔥🔥🔥
Kwance suka isko Pretty a cikin runfar da ya yi wa Auta a lokacin da suka ƙarisa wajen. Ta yi barci baiwar Allah, ta cinye kifinta tas har da haɗawa da na Auta abinta, dik ta yi masu tas.
Kallon Hoorain Auta ta yi, a ɗan shagwaɓe ta ce. "My Hero yunwa fa nike ji". Cike da mamaki ya amsa da. "Ba na kawo maku abinci ba".
Taku step biyu ta yi ta matsa kusa da shi. "Ai ɗaukin ganinka yasa na tafi na bar abincin, kaga kuma Pretty ta cinye".
Jinjina kai ya yi, cikin sanyin murya ya ce. "Bari in je in kama maki wata in gasa sai in kawo maki, je ki zauna kusa da Pretty".
Make mashi kafada ta yi ba tare da ta yi magana ba. Kawar da kallansa a kanta ya yi yana tambayar menene kuma. "Ni dai sai dai mu tafi tare". Kamar zata yi kuka ta yi maganar.
"A'a bana san ki wahala, wajen da ɗan nisa, zauna bari in dawo". Kara make mashi kafaɗa ta yi. "A'a ni ban yarda ba sai dai mu tafi tare".
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥===========
MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
"A'a bana san ki wahala, wajen da ɗan nisa, zauna bari in dawo". Kara make mashi kafaɗa ta yi. "A'a ni ban yarda ba sai dai mu tafi tare".
"Haka kike so?".
Kai ta gyaɗa mashi da sauri alamar e. Da hannunsa ya nuna mata hanya a kan ta wuce su tafi.
Sake make mashi kafaɗa ta yi. "Ni dai ko ka wuce gaba ko kuma mu jera a tare". Ta faɗa tana ɗan karkata kanta.
"Meyasa to?". Cike da mamaki ya yi tambayar............... Ɗan ɗaure fuska kaɗan ta yi, cike da zolaya ta ce. "Saboda bana san in wuce gaba ka yi ta kallona, ina tafiya kana kirga mun taku na one by one kana kalle mun shape na bayana kaga ba alkyabba na..........."
Ƙasa ƙarisa maganar ta yi sakamakon ɗagowa da ya yi a miliyan ya sauke kallansa a kanta, kwata kwata abin da bai taɓa kawowa a ransa ba kenan, mamakinta ne ya kama shi, ko a ina ta koyi magana har haka........ Ni kuwa na ce tana matsayin masoyiya kuma aminiyar Chuchu ƴar wanka ai fin haka ma zaka ji, su da suka kware wajen bawa flowers ruwa, ai a banza uncle Jahiz yake cewa basu girma ba, ya zo ya gansu tare da flowers ɗinsu a nan ne zai tantace sun girma ko basu girma ba, yaran yanzu ai da wayonsu ake haifarsu.
Ganin ya yi shiru kamar wanda ya yi suman tsaye ne yasa ta ɗaga mashi gera guda alamar yane?. Shi kuwa shirun da ya yi tinanin time da take ƴar yarinya da bata wuce 5 years ba yake ɗaukarta idan sun fito ita da su Chuchu yake yi, dan a lokacin an bashi ragamar kula da ita.
Ganin ta ɗaga mashi gera guda yasa ya nisa tare da kawar da kallonsa daga kanta, kamar ba zai yi magana ba, sai kuma dan ya cire mata tinanin nan na banza na cewa yana kallan shape ɗin jikinta yasa ya ce. "Ai na rigada na gama kalle shape ɗin tin bai fito ya zama cikakken shape ba, dan a shekarunki biyar kam ai bai fito ba, kuma a hannunna shape ɗin ya bayyana, dan haka na san..........."
Bai ƙarisa maganar ba ta rufe mashi baki ta hanyar harara da ta dallah mashi. Kawar da kansa ya yi tare da juyawa yana jin kamar ya saki murmushi, sai dai bai iya murmushin ba, zuciyarsa ta ji daɗi ganin yadda ta ɗaure fuska tana harararsa.
A kule ta ce. "Wannan shi ne babban kuskuren da mace zata yi ta so wanda ya san yarintarta, kullum sai ya yi mata gori, koma dai me zaka ce ka ce, ai a da lokacin da shape ɗin ya bayyana a hannunka kana kallona a matsayin kanwarka ce, yanzu kuma kallon masoyiya kake mun, dan haka manufarka a kallona yanzu ya sauya!".
Ya fahimci maganganunsa sun ɗan sosa ranta, dan haka sai ya juyo da nufin ya bata hakuri. Ganin ya juyo kuma taga alamar hakuri zai bata yasa ta juya mashi baya irin ta yi fushin nan.
Yana ƙoƙarin fara yin magana ta yi saurin barin wajen ta nufi wata hanya daban tana ɓata rai. Ɗan girgiza kai kawai ya yi, dama yasan fin haka ma zata yi, dama renonsa ce ita, mata, mata, mata sai dai shirin Allah wlh, dik yadda mace take sonka hakan ba zai hanata yin abin da ta yi niyya a kanka ba, kai idan mace bata wahalar da kai ma wlh ba son gaskiya take yi maka ba, wata haka kawai zata kirkiro faɗa, ku yi ta yi har sai ta kureka, sai kuma ta ce wai tana gwadawa ta ga irin karfin son da kake yi mata ne, ta azabtar da kai, idan ka yi complain ta ce baka sonta, mu dai sai shirin Allah wlh.
Ganin ta ɗan yi mashi nisa yasa ya yi saurin rufa mata baya. Fahimtar yana biyota yasa ta watsa a guje ta shige cikin wasu dogayen ciyayi dake kusa da korama.
Ba shiri ya bita da gudu dan kada ta ci karo da wani abin ya cutar da ita.
Yana sanya kansa a wajen ciyayin zai bi bayanta ita kuma tana fitowa da gudun gaske. Karo suka unexpext. Baya baya ta yi zata faɗi ya yi saurin riƙo hannunta.
A miliyan ta faɗa jikinsa haɗe da datse idanunta gam, a tsananin tsorace murya na kerma ta ce. "Tamisa, wlh akwai tiger a wajen ruwan nan". A rikice take maganar tana haɗe word, jikinta har kerma yake yi.
Shiru ya ɗan yi yana jin yadda kirjinta yake bugawa da karfi karfi alamar ta tsorata sosai.
(Anya Hoorain ba shiru ya yi yana jin daɗin tula tulanta da suka taɓa chest ɗinsa ba kuwa🤔 shi ma yanzu ban yarda da shi ba 🥱 team Hoorain kada ku ce na ce, na ce ɗin a zo a saka mun gas🥱😅)
Kamar saukar aradu haka ya tsinkayo gurnanin damisam a kunnensa. Kafin ya tabbatar da gaskiyar abin da yake ji tuni ihunta ya fasa dodan kunnnesa, da karfi ta zunduma ihun haɗe da cewa. "Hoorain ba ka jishi ba, wayyo daddyna". Yau ta manta da my hero, Hoorain kai tsaye aka ce, ƴar ƙaniya ta hango mutuwa!.
A tsananin rikice ta yi maganar tare da sakesa zata gudu ba tare da tasan in da zata nufa ba. Ya fahimci ta rikice sosai, idan ya barta ta tafi ma zata iya afkawa wani wajen ta cutu, idan kuma ya tsayar da ita ba zata taɓa barinsa ya kwaci kansu daga hannun wannan damisa ba, to yanzu me abin yi kenan?.
Ya jefawa kansa tambaya, a hankali ya sanya hannunsa a waist ɗinsa dan ya ji ya mayar da takobinsa mazauninsa ɗazun ne ko bai mai da ba.
Kankameta ya yi da hannu ɗaya ya hanata tafiya. Ajiyar zuciya ya sauke jin takobin yana nan. Da karfi ta riƙesa tana ihu taki ta yi shiru. Yana tinanin yadda zai yi da ita sai ganin damisan ya yi a gabansu ta fito ta wajen koramar da gudun bajinta.
Wani jibgege da shi, ya ci ya ƙoshi, ruwa ya zo sha a wajen koramar ta je ya ganta, kun san kuwa dole ya biyota dama shi ne kuma ya biyota ɗin.
Ko kaɗan Hoorain bai ji tsoro ba, ita kuwa jin gurnanin dab da su yasa ta kara ƙanƙamesa tana faɗin shikenan ta mutu yau. Ido cikin ido Hoorain ya kurawa damisan nan kallo babu ko tsoro.
Wani irin uban tsalle wannan damisan ya daka sai kansu da gudun gaske. A miliyan Hoorain ya ture Auta gefe da karfi, cikin zafa shi kuma ya durkushe gwiwowinsa a ƙasa, hakan yasa damisan ya wucesu ya dira a bayansu.
Cikin zafa Hoorain ya juyo ga damusan tare da miƙewa tsaye, ita ma da ya tureta ta faɗa cikin ciyayi a haukace ta miƙe tsaye, kuka take yi sosai kamar ranta zai fita. Hakan yasa suka rabawa damisan hankali gida biyu, ya ganta ya ga Hoorain, ya rasa wazai fara kaiwa farmaki.
Tsayuwa cikin jarumta Hoorain ya yi tare da ƙara ɗaure fuska sosai, irin babu wasa a tattare da shi ɗin nan. Yasan halin dabobi sosai, yasan da cewa komai ƙanƙantar motsin da suka yi yanzu damisan nan zai sake daka tsalle ya yi kansu ne dan zai yi tunanin hari zasu kawo mashi. Hoorain yana san zaro takobinsa yana tsoron motsawa, shi ba damuwarsa ya motsa damisan ya yi kansu ba, da kansa shi kaɗai zai yi da da sauki, idan ya yi kan Auta ai damka ɗaya zai yi mata sai gawa.
Yana ƙoƙarin zare takobinsa cikin dabara Auta da ta miƙe tsaye a yanzu ne ta kurma ihu tare da nufarsa da gudu. Motsin da ta yi ya yi dai'dai da damisan ya sake daka tsalle ya yi kansu. Hakan ya bawa Hoorain damar zare takobinsa, da karfi yasa hannunsa ɗaya ya sake ture Auta baya ta koma in da ta taso, da karfi shi ma ya yi gefe, a karo na biyu damisan ya sake dira a bayansu, Auta ta sake tafiya ta faɗi cikin ciyayin dake wajen again.
"Kada ki tashi". Shi ne abin da Hoorain ya faɗa mata da karfi, amma ina bata jinsa saboda tashin hankalin da take ciki.
A lokacin kuma ran damisan nan ya gama ɓaci, ya fusata sai ya nufi Hoorain da karfin gaske yana wani irin buɗe baki. Ko kaɗan Hoorain bai tsorata ba, yana tsaye damisan ya isa garesa, cikin zafa suka fara kokawa yana ƙoƙarin zana mashi fata da takobinsa, daga karshe ma takobin faɗuwa katsa ta yi damusan ya haike mashi, da waɗan nan shegun faratunan hannun nasa ya fara kai mashi gafsa ta ko'ina Hoorain yana ƙoƙarin kaucewa.
Tsorata na ganin damisan ya kayar da Hoorain a ƙasa ya haiƙe mashi yasa numfashinta ɗaukewa diff ta zube ƙasa. Shikuwa kokawa suka cigaba da gwabzawa da damisan, ƙoƙarin kama agarar damisan ya fara yi tun da takobinsa ta faɗi ƙasa, in ya kama agaransa dolen dolensa ya risina mashi.
Gabaɗaya damisan ya yagushe mashi face ɗinsa, gwabzawa suke yi sosai, daga shi har damisan kowanne daga cikinsu burinsa ya cinma abin da yake muradi, damisan yana haran wuyar Hoorain, shi ma yana haran agarar damusan.
Ya sha wahala sosai kafin ya samu ya ture damisan daga kansa, sannan ya miƙe cike da jarumta, da gudun gaske damusan ya yi kansa dan ma kada ya bashi wata damar kara karfafa kansa kenan. Juyawa ya yi da gudu damisan ya rufa mashi baya. Tsalle ya yi ya taka wata bishiyar ɓaure dake kusa da su sannan ya juyo da karfi haɗe da haɗa hannayensa dikka biyu da karfi sosai ya dakawa damisan duka a tsakiyar kai, nan take damisan ya durkushen kafafunsa a kasa yana sakin wani irin kurnani mai ban tsoro da kuma ban tausayi, alamar Hoorain ya ji mashi ciwo a kai.
Ko kaɗan Hoorain bai yi niyar kashe shi ba, ganin ya yi ƙasa ya yi mubaya'a yasa ya rabu da shi, a hanzarce ya wuce ya nufi in da take yana sauke numfashi a hankali hankali.
Da hannu ɗaya ya ɗagota bayan ta duƙa. Kai tsaye wajen koramar ya nufa da ita. Cikin nitsuwa ya kwnatar da ita a saman dutse, ƙarisawa gaban koramar ya yi haɗe da tarar ruwa ya fara wanke jininsa da damusan ya fidda mashi, har lokacin sai jan numfashi kamar haki yake yi alamar wanda ya gaji.
Sai da ya wanke jikinsa tsab kafin ya dawo kusa da ita, cak ya sake ɗaukarta suka ƙarisa gaban koramar. Gabaɗayanta ya sanyata cikin ruwan.
Da ihu ta farka tana sambatun damusa zai cinyeta. Shi ma ruwan na jiƙasa, dan kusan a tare suka shiga cikin koramar, sai dai shi ta ɗan baki baki ne, da kyar ya iya ambatar sunanta da ranki ya daɗe.
Ina ai bata ma san yana yi ba, ihu ta cigaba da yi tana ƙoƙarin kwatar kanta, da alama bata cikin hayyacinta. Ƙanƙameta sosai ya yi, cike da tausayinta ya matsar da face ɗinsa ɗan dab da ita, sannan ya ce ta nitsuwa damusan ya gudu.
Jin hakan yasa ta yi saurin waro idanunta, ganinta a hannunsa kuma cikin indoron ruwan dake kwaranya yasa ta yi saurin juyar da kanta izuwa gefe da gefe tana neman ina damusan yake.
"Ki kwantar da hankalinki baya nan, ya tafi". Cike da so da kauna ya faɗa.
A tsorace sosai ta ce. "Ina ya tafi Hoorain?". Ta yi maganar tana kai hannunta saman face ɗinsa.
"Bai yi maka komai ba ko?" Ta sake tambaya tana shafa kumatunsa".
Jinjina mata kai ya yi haɗe da cewa. "Babu wata barazana ranki ya daɗe". Ɗan daure fuska ta yi haɗe da turo baki, a shagwaɓe ta ce. "Hoorain wai kai baka iya soyayya bane sai wani ranki ya