Showing 279001 words to 282000 words out of 403653 words

Chapter 94 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

87

To idan aka jefa uwar cikin wuta sai a jefa ƴaƴan ma su da ba su san komai ba uwarsu kawai suke bi. Gabaɗaya birnin ya rikice da ihu da magiya na ban hakuri, amma Black Tiger yana tsaye yana ganinsu tamkar wani dutse ko karfe bai sarara masu ba, tamkar babu zuciya a kirjinsa, babu alamar ma sun bashi tausayi ko ɗigo a ransa.

Ihu Sweetie ta kurma, da karfi ta fara kai mashi duka a kirjinsa da hannunta dikka biyu tana jijigasa da karfi tana faɗin ya rabu da mutanen nan ya kyalesu, ya rabu da yaran da ba su ji ba basu gani ba, ya dubi girman Allah ya sauke RAWANIN ZALINCIN dake kansa ya ɗaura na adalci, sambatu take cikin fitar hayyaci tana kai mashi duka babu kakkautawa. Yana tsaye tamkar gunki, ko kaɗan babu alamar zai tausaya. A cikin kwakwalwarta Sweetie take jiyo ihun mutanen nan ta cikin mirrorsa, sai dai ba zata iya taɓuka masu komai ba. Tashin hankali da firgici ne suka yi mata yawan da ba zata iya ɗauka ba, hakan yasa tana cikin sambatu tana kai mashi duka kawai numfashinta ya ɗauke diff ta zuba ƙasa a gabansa... BA SHAKKA YAU BLACK TIGER YA FITO A AINAHIN BLACK TIGER ƊIN NASA, BABU SASSAUCI.

A miliyan Ronnie ya yi kanta yana ambatar sunanta, shi ma hawaye yake yi bibbiyu, zuciyarsa ta gaza iya ɗaukar wannan masifa da tashin hankalin, tun yana ambatar sunan Sweetie cikin ɗaga murya da kaushi, har voice ɗinsa ta dai'na fita, kan kace me shi ma ya sulale ƙasa a wajen ya sume... Innalillahi wa inna ilahir rajiun. BLACK TIGER dai ko a jikinsa, sai ma cigaba ya yi da yin aikinsa yana latsa laptop ɗinsa.

My people's kuna tinanin Black Tiger zai iya canzawa kamar yadda Sweetie da Ronnie suke so kuwa? Zai iya sauke RAWANIN ZALINCIN dake kansa kuwa? Kuna ganin team Ronnie and Sweetie zasu yi nasara kuwa? Sweetie tana yawan cewa zuciyar Black Tiger mai kyau ne akwai dalilin rikiɗewarsa izuwa bakin mugu, shin menene wannan dalilin? Ya Ronnie zai ji idan ya ji Floris ta mutu? Har da iyayenta suka bijirewa Black Tiger,.shin suma har da su aka kona? Wani irin hukunci master Devil zai karɓa a hannun Ronnie and big bro?.

🔥🔥🔥🔥DUBAI🔥🔥🔥🔥

Zaune ya isko Ramish a saman bedside drawer yana ƙoƙarin treating na hannunsa. Cikin zafa ya ƙariso wajen yana tambayarsa meya same shi a hannun nasa? Ina ya je daren jiya?, meyasa yana ta kiran wayarsa baya ɗagawa?. Cikin tashin hankali ya yi maganar.

"Get out from here!". Shi ne abin da Ramish ya faɗa cikin kakkausar murya. Gadan gadan Bilal ya nufosa. "Babu in da zanje har sai ka faɗa mun abin da ya sameka". Tsawa ya daka mashi a kan ya fita mashi a ɗaki kuma ya tabbatar kafin nan da 30 mins ya gyara mashi kofar da ya ɓallah. Da ya fahimci Ramish yana kan tsini sosai sai ya juya ya fita gudun a samu matsala, kai tsaye ya nufi wajen Abbie.

Yana fita shi kuma Ramish ya miƙe ya nufi in da Leesharh take kwance a balconynsa saman kujera, rufe kofar balconyn ya yi ya ƙarisa wajen a gaggauce, dan bai gama yi mata abin da ya dace ba.




P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️


For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========




MALLAKIN🔥

P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️






🔥🔥🔥🔥DUBAI.🔥🔥🔥🔥

Bayan wasu kwanaki da basu haura one month ba, akwai dalilin da yasa na yi maku wannan tsallake, idan mun yi gaba zan dawo baya domin yi maku bayanin abin da ya faru a waɗan nan kwanaki, muje dai zuwa.

Ramish da kansa ya yi jijyar Leesharh ba tare da sanin kowa ba, bai bari kowa yasan da abin da ya faru ba sai babban yayansu wato Smart, dan ya gane mai taya shi aiki shi ne babban yayansu da mama ta takura mashi a kan ya yi mata bincike ba ɗan King bane, yana ganin hoton Smart ya gane yayansu ne saboda kamanninsa da su Zunaira, to yarasa wani irin shaida kuma mama take so bayan kamanninsa da kannensa.

Amma fa ko da ya faɗawa Smart ga abin da ya faru bai sanar da shi ya yi mata fyaɗe ba, ya dai faɗa mashi yana zargin Ummie and Bilal, da Smart ya tambayesa dalilinsa na zarginsu sai ya sanar da shi cewa akwai wata rana da ya fita cikin hayyacinsa har ya kusa yi wa mai aikinsu fyaɗe, lokacin da ya dawo cikin hankalinsa ya zauna yana tinanin meyasa ya birkice har haka, meyasame shi? A lokacin ya ce bari ya gwada jinin jikinsa ya gani, a nan ne ya gane wasu kwayoyi sun ratsa jininsa wanda kuma yana da tabbacin ba alluransu aka yi mashi ba, da bakinsa ya sha, in kuwa haka ne to dole ko Ummie ko Sharrifat ɗaya cikinsu akwai wanda ya sanya mashi waɗan nan kwayoyi cikin abin shansa, dan baya cin abinci a waje, dik in da ya je sai ya dawo gida yake ci, kuma Sharifat ce kawai mai kawo mashi abu ya ci, to kun ji yadda aka yi Smart yasan abin da ya faru.

Batun fyaɗe ya rufesa iya shi da ita kawai, ita ɗin ma da farko ya so yi mata allura ya mantar da ita komai, amma daga baya da ya yi dogon tunani sai ya ce kila tana da ƴan uwa bayan iyaye, idan ya yi hakan ya yi mata zalincin da ba zata iya yafe mashi ba, gara ma fyaɗen da ya yi mata a kan wannan alluran, da ya kwantata hakan da kansa, ya ce yanzu shi ayi mashi allura ya manta su Smart gabaɗaya a rayuwarsa, sai ya ji ina ba zai iya yi mata ba, dama kullum a rayuwar nan idan zaka yi hukunci ka kwatanta da kanka ka gani, hakan ce zata sanyaka yin adalci, yana ɗaya daga cikin abin da yasa kuka ga ni Princess Teema bana san kashe mutane a cikin littafina, saboda kwatanta abu da kai'na ya zame mini jiki, so idan na kwantanta irin raɗaɗin da zasu ji a kai'na sai in ji kai ba zan iya jurewa ba, wlh shawara nike baku domin tsira, kasance mai kwatanta abu da kanki tabbas zaki zama adila mai yiwa mutane adalci cikin sauki, Allah dai ya shige mana gaba ya dafa mana.

Ba zan baku labarin abin da ya faru bayan farfaɗowar Leesharh tsakaninta da Ramish ba, saboda ina da dalilin ɓoye hakan, sai gaba zaku ji komai, iya abin da zan faɗa maku a nan shi ne Leesharh dai ta shafe complete sati yana wahalar jinyarta kafin ya iya shawo kan matsalar, a jinyar tata ma abubuwa da dama sun faru, jinyarta yasa bai bi ta kan bincikar dalilin da ya kawo kwayoyi a cikin jininsa ba, yana busy sosai, ga shi jinyar tata cikin sirri yake yinsa, abin ku da rashin gaskiya yana cikin tashin hankali a koda yaushe, bashi da wata natsuwa, sannan ya jefa kansa a cikin damuwa da rashin walwala dik dan abin da ya aikata wanda bai taɓa zatan ko a mafarki zai aikata ba, ya shiga zulumin kullum cikin fargabar asirinsa zata iya tonuwa, ya zama wani irin sukuku haka.

A haka ya shafe makonni uku yana fama, sai a cikin mako na huɗun nan ne ya sami natsuwa da kwanciyar hankali dalilin komawarta dai'dai, sai dai fa idan zai kwana yana yi mata magana bata amsa mashi, har yau ta gagara ɗaga idanu ta kallesa, wani irin tsananin bakinciki ne a ranta wanda take jin tamkar ta kashe kanta, abin takaici, shi kuwa Allah ya jarrabesa da tausaya mata matuƙa, ya gagara watsar da alamarinta ya kama aikin gabansa, yana ganin koma me ta yi mashi ya cancaci hakan, saboda shi ne silar kuncinta a rayuwa, dan haka baya jin komai idan ya yi magana bata kula shi ba.

Sharifat ta yi haukar nemanta har ta gaji ta fawwalawa Allah komai, ta sanar da Ramish and Bilal sai dai da ta cika matsawa Ramish ya ce mata kada ta sake yi mashi maganar Leesharh idan ba haka ba zai saɓa mata. Shi ma Bilal ya yi haukar nemanta kamar menene, ya shiga damuwa matuƙa. Amma shi Abbie bai damu da rashin ganinta ba, dan ya tambayi Ramish ya ce mashi tana nan suna tsaka da aiki ne ta bashi haɗin kai tana gabatar mashi da wasu hujoji, sai ya yi amfani da abin da ya faru da ita a ranar na kasheta da aka shiga za'ayi a ɗakinta, sai ya ce wa Abbie ai ya ɗauketa daga gidan nan ne dan kada a sake yunkurin kasheta, ya kaita waje mai tsaro sai sun gama aiki zata dawo, Abbie ya yarda da maganarsa, yasan baya yi mashi karya.

A zahirin gaskiya ya ɗauketa daga gidan Abbie tun washe garin ranar da abin ya faru, tun time da Bilal ya ruguje mashi kofa, a wannan rana da daddare ya fita da ita daga gidan ya mai da ita gidansa, a nan ya yi jinyarta, shiyasa su Bilal basu san in da take ba, sun yi neman duniyar nan babu ita babu labarinta.

•••••••••••••••••••••••••••🔥🔥🔥🔥

Zaune take a saman sofa mai zaman mutum uku a cikin parlonsa, ta yi shiru tare da buga uban tagumi tana tunanin irin rayuwar da ta sha, ta fuskanci challenges dayawa baiwar Allah nan, yanzu kuma ɗan mutumcin da take ji da shi ɗin ma babu, tinaninta ɗaya shi ne waye zai aureta a haka? Shikenan ita ta zo duniya a wahalce kuma zata koma a wahalce babu wani gata?. Kanta a kasa tana kallan yatsun kafafunta da suka ɗan ya fayau, dik ta yi rama sosai saboda bata cin abinci, kullum tana cikin tinani. Size ɗin kayan da take sakawa a da yanzu sun yi mata yawa, sai dai ƙasa da su, saboda rama, sai idanu kawai zaka gani.

Sleeping dress doguwar riga ce a jikinta launin maroon color, ta sanya ɗan ƙaramin hijabi a kanta, rabonta da abinci tin daren jiya da ta sha tea, bakinta sam babu ɗanɗanon komai, bata sha'awar cin komai kamar wata mai ƙaramin ciki.

Ko kaɗan bata ji motsin shigowarsa cikin parlourn ba, dan ta yi nisa a cikin tunanin da take yi, har ya shigo ya wuceta ya nufi kitchen, ta luluƙa duniyar tinani. Haka zalika bata ji dawowarsa ba sai ganinsa ta yi ya zauna a saman sofar da take zaune hannunsa ɗauke da cup and small chop a cikin plate, yana sanye cikin sleeping dress riga da wando launin milk color, ya yi kyau sosai, sai dai shi ma ya rame sosai alamar yana cikin damuwa, dik wanda ya yi complain a kan ramansa sai ya ce aiki ne ta yi mashi yawa. Har Smart ya yi complain a kan ramansa, amma sai ya ce zai rinƙa kulawa yana ragewa kansa pressure dan ya maida jikinsa.

Yana zama ta zabura ta miƙe zata bar wajen. A hanzarce ya ɗaura plate na small chop a saman table dake kusa da su ya kai hannunsa ya riƙo nata hannun, in a low voice sosai ya ce. "Please Aesh, ya isa haka gudun nawa da kike yi, dan Allah ki ji tausayina, ko iya haka ya kamata ki fahimci ba da gangan na yi maki hakan ba, idan da da gangan ne ba zan kwashi up to one month ina kula dake ina kuma yi maki magiyar da ki yafe mun ba, ki mun magana ba, dan Allah".

Jikinta ne ya hau kerma, dan a duniya tsoronsa take ji matuƙa, murya na rawa ta ce mashi. "Tabbas da gangan ka ci mun mutumci, ka mun tabon da ba zai taɓa gogewa a cikin zuciyata ba, ka zalinceni, dama a lokacin da ka kamani ka sakeni ka ce mun in ka yi bincike ka ga da sa hannuna a abubuwan da suke faruwa zaka mun abin da ba zan taɓa mantawa da kai ba a rayuwata, ga shi kuma ka mun ɗin kamar yadda ka faɗa, tabbas ba zan taɓa mantawa da kai ba a rayuwata! Ka cuceni ka zalinceni! Dan Allah ka kashe ni in huta da wannan rayuwa". Ta kai karshen maganar zafafan hawaye suna zubowa a saman kumatunta.

Shiyasa aka ce ka rinƙa tauna magana kafin ka faɗeta, baka san me gobe zata haifar ba, ga shi maganar da ya taɓa faɗa mata na in ya kamata da laifi zai yi mata abin da ba zata manta da shi ba ta riki maganar a ranta wanda kuma shi ba hakan yake nufi ba, jama'a ku tauna magana kafin faɗinta dan gudun abin da gobe zata haifar, shawara ce daga alkalamina!!.

Kalamanta sun kara narkar mashi da zuciya, shi dai burinsa ɗaya shi ne ta yafe mashi, amma taki sauraronsa ma. Miƙewa tsaye ya yi ba tare da ya saki hannunta ba, cike da tausayawa da kulawa ya ce. "Dik abin da zaki faɗa a kai'na na yarda na kuma ɗauka, yanzu dai dan Allah zauna ki sha tea, ni dai ki rinƙa cin abinci koma me zaki ce a kai'na ki faɗa, lafiyarki shi ne fata na kawai". Ya kai karshen maganar yana miƙo mata cup dake hannunsa, tea ne mai zafi sai tiriri yake yi.

Allah sarki, a jikinta tana jin ba da gangan ya yi mata hakan ba, sai dai zuciyarta taki yarda da hakan, wani lokaci har tausayi yake bata yadda yake neman ta yafe mashi, amma ta gaza yarda da shi, ta kuma rasa dalilin kin yarda da shi da zuciyartata ta yi.

"Ba zan iya cin komai ba, saboda ban san yanzu ina rayuwata ta fuskanta ba, dan Allah ka kyaleni ko yunwa zata kasheni in huta tun da kai ba zaka kasheni ba". Kanta a ƙasa ta yi maganar....... Nisawa ya yi kafin ya ce. "Babu abin da zai samu rayuwarki, zaki yi rayuwa kamar kowacce mace mai ƴanci, dan Allah zauna ki sha tea kin ji?". Cikin sigar rarrashin da ya koya dan dolensa ya yi maganar.

"Har abada ba zan taɓa yin rayuwa mai ƴanci ba, a rayuwar yanzu ka kai budurcinka gidan miji ma ya ka kare da walaƙanci da tozarci in baka samu miji na gari mai tsoron Allah ba bare ace ka zubar da mutuncin naka a titi ka shiga gidansa empty, me kake tinanin zai faru? Kana tinanin zan yi rayuwa mai ƴanci ne? Kana tinanin akwai wata daraja da ta rage mun wanda zai kalleni da ita ne?........."...

Katseta ya yi ya hanyar ɗaga mata hannu kafin ya ce. "Baki zubar da mutuncinki a titi ba, tabbas babu wanda zai ganki a matsayin mara daraja kin ji ko? Dan Allah Aesh ki yafe mun, ki yafe mun kin ji? Nasan na cutar dake, amma kin ki yarda ba da gangan na yi ba, kin ki yarda ba halina bane, da kin san yadda na tsani zina da baki yi ƙoƙarin danganta ta dani bama, kin san irin hukuncin da nike yi wa mazinaci wanda ya yi wa mace fyaɗe kuwa?". Cike damuwa a ransa ya kai karshen maganar............ Sai a lokacin ta ɗago da kanta ta kallesa, hawaye suna cigaba da gangaro mata masu ɗumin gaske, da kyar ta iya cewa.
"Babu ma wanda zai aureni da har zai ganni da daraja, ka kwantanta a kanka, shin zaka iya auren macen da wani ya lalata ya yi mata fyaɗe? Ko ka ɗaukeni a matsayin kanwarka na jini, ya zaka ji idan aka ce anyiwa kanwarka fyaɗe?"...... Dum!! Dum!!!! Shiru ya yi bashi da bakin bata amsa, dan yasan ko kusa ko alama ba zai iya ba, ba zai iya auren wanda wani ya lalata ba, haka zalika ba zai iya barin wanda ya yi wa kanwarsa fyaɗe ya cigaba da numfashi a duniya ba, ba zai kyalesa ba har sai ya yi mashi mummunar kisa, batun aure kuma, shi yaushe ma ya taɓa yin tinanin auren bare har ya yi tinanin irin macen da ta dace da shi, iya abin da ya sani dai shi ne ko soyayya da wani mace ta taɓa yi ba zai kulata ba bare har a kai ga aure.

Cikin matsanancin kuka ta ce. "Ka gani ko? Kai kanka ba zaka iya auran ragowar wani ba, to taya kake tinanin ni zan samu wanda zai iya karɓar ragowarka?". Cikin zafin zuciya ta yi maganar, tana kai karshen ta kwace hannunta daga riƙon da ya yi mata ta juya da nufin ta bar wajen da sauri....... Cikin zafa ya riko hannunta, kin juyowa su kalli juna ta yi, sai wani irin huci take fitarwa mai ɗimin gaske, kai ka zaci zata iya haɗiye zuciyarta a lokacin ko kuma ta kone saboda zafin da zuciyarta ya ɗauka, yana yi mata wani irin suya mai azaba, abin da ciwo matiƙa gaskiya.

"Idan na aureki shikenan zaki yafe mun?" Ya faɗa yana kallanta. Ai a miliyan ta juyo da kallanta a kansa, ido cikin ido suka kalli juna, wani irin faɗuwar gaba ta ji ya risketa, ta kasa iya magana, dan bata da abin faɗe....... "Ni zan iya ɗaukar ragowata ai ko? Budurcin mace shi ne mutuncinta right?". Ya faɗa kamar ya jefa mata tambaya wanda yasan ba amsa mashi zata yi ba. Dan haka sai ya ɗaura da cewa.
"Tabbas budrucin mace shi ne martaba da kimarta a idanun mijinta, dan haka ni zan aureki, dama ni na karɓi budurcin naki, dan haka zan kalleki da kima da daraja, kuma zaki yi rayuwa mai ƴanci kamar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login