Showing 291001 words to 294000 words out of 403653 words
yaushe zaki bani haɗin kai wajen bincikena? Ki bani cikakken bayani dan kama mutanen can". Ya jefa mata tambayar tare da dawo da kallansa a kanta........ "Anytime". Ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya. "Are you sure and are you serious?"........ Kai ta jinjina mashi alamar e ta tabbatar. Sosai ya ji daɗin amsarta, dan yana san cigaba da abin da yake yi, yana burin kama masu nikaf, and yana san tambayarta wasu tambayoyi a kan abin da ya faru a tsakaninsu a wancan ranar, amma yana shakkar tambayarta saboda har yanzu bata yarda ba da gangan ya yi mata ba, da ta aminta da shi ne he has a lot of question for her, amma babu dama, dan haka sai ya shanye wannan tambayoyi a ransa zuwa time da zai samu dama.
Shiru motar ta kasance na ɗan wani lokaci, yana tuki yana tunanin abin da yakamata ya fara yi. Da yake yana sharara gudu sai cikin ƙanƙani lokaci suka isa wani haɗaɗɗen wajen cin abinci na masoya mai bala'in tsari, tsada da kuma haɗuwa, gabaɗaya yankin wajen ice ne kewaye. Ya lura in dai a gida ne Leesharh ba zata taɓa cin abinci ba, amma in suka fito waje ko dan idanun jama'a ba zata kunyata shi ba, komai ya ce ta yi a waje yana da yakinin zata yi dan kada ta bashi kunya, shiyasa dik da baya cin abincin waje yau ya daure zai jarraba saboda ita ta ci ta ƙoshi. A katafaren parking space ɗinsu ya tsaida motar tasa, cike da kulawa ya ce. "Muje ko?".
Ai ta shagala da kallan kyau da tsaruwar wajen, kai Dubai ba dai kyau ba wlh, ga komai nasu cikin tsari, bata taɓa kallan irin wannan gidan cin abincin ba ko a mafarki, ba abin da ya fi ɗaukar hankali ma irin abubuwa sky blue da suka yi amfani da shi a wajen, ga golden da ya ji light mai haske, gaskiya ne wannan gidan cin abincin ya ci sunansa paradise ɗin kamar yadda yake a rubuce da manyan baki. Buɗe motar ya yi ya fito, ganin ya fita yasa ta yi gaggawar bin bayansa, dakatawa ya yi yana jiranta, tana ƙarisowa in da yake yasa hannu ya riƙo hannunta, ai a miliyan ta ɗago da kallanta a kansa, sai taga sam ba ita yake kallo ba, da gangan kuma yaki kallan nata, dan baya san ta hana shi yin abin da ya fito da shi, ya fito da ita ne domin ya samu ta rage damuwar da yake a ranta, yau dai ɗaya ta yi farinciki sosai.
Cikin natsuwa ya fara takawa ya nufi cikin wajen, ga mamakinta sai gani ta yi ƴan'mata da samari masu class da ji da kansu sun tsaya sai ɗaukarsa hoto a wayoyinsu suke yi, saboda kyan da Allah ya yi mashi, kun san su kyawawa dik in da suka shiga ko sun shirya ko basu shirya ba sai mutane sun yi ta ɗaukarsu hoto, wai a hakan ma ya sanya p-cap a kansa fa, basu wani ga face ɗinsa da kyau ba, amma haka suka rinƙa kashe mashi hotuna ta ko'ina babu kakkautawa. A nan ne wasu suka ɗauketa ita da shi a tare, and a media suka ɗaura hotunan, shi ko a jikinsa, in da yasa kai kawai yake tafiya cikin natsuwa, ita kuma ta damu sosai, dan tana tsoron abin da zai iya faruwa, tana tsoron masu nikaf su gani saboda suna bibiyarsa ta kowacce hanya.
My people's me kuke tinanin waɗan nan hotuna zasu haifar?.
Sosai ta waro idanu tana kallan yadda cikin wajen ya yi bala'in haɗuwa, sofas masu bala'in kyau, laushi da kuma tsada, waje ne na manyan kai. Zama suka yi saman sofar da ya zaɓa masu, sannan ya saka oder abin da yake ganin zasu iya ci, online oder ake yi, sannan sai ka biya ta online ɗin ka yi komai za'a kawo maka, sp kana ci zaka tashi ka tafi babu wani tsayawa yin payment, haka tsarinsu yake. Yana oder bai fi da mintuna uku ba sai ga shi an fara shirga masu abin da ya buƙata a gabansu saman table, dik a takure take saboda kallansu da jama'a suke yi, dik ta in da ta juya idanun jama'a a kansu, ga uban hotuna da ake kashe masu light ta ko'ina. Zuba mata idanu na ƴan sakanni ya yi kafin ya ce. "Ɗauki chopping stick or spoon mu ci abinci".
Ɗago kai ta yi ta kallesa da nufin ta yi mashi gardama, amma sai ta gagara yin hakan saboda idanun jama'a dake a kansu, kuma ya yi mata wani irin kwarjini, yau idanunsa a kaifafe suke sosai, dan dole ta ɗauki spoon dan da shi ta saba, shi kuwa sai ya ciro wayarsa ya fara latse latse dan baya jin kamar zai iya cin wannan abinci, bai saba da waje ba. Tana jin yunwa over to over, dan haka sai ta fara cin abincin a natse, sai dai kaɗan kaɗan take ci. Dik abin da take yi attention ɗinsa yana a kanta, bcoz ta ci ta koshi ya zo da ita tun da taki ci a gida.
Ya lura ɓata masu lokaci zata yi, dan sai su wuni a wannan waje bata gama cin wannan ɗan abinci ba, ɗan kaɗan kaɗan take ɗebowa kamar bakinta na ciwo, sai ya ajiye wayarsa a saman table ɗin ya kai hannu ya karɓi spoon ɗin nata, cikin natsuwa ya ɗebo abincin mai ɗan yawa ya kai mata saitin bakinta. Ɗago kai ta yi ta kallesa, while shi ma ita yake kallah ta cikin glass ɗin nasa, bata san disga shi a cikin mutane sai ta buɗe baki ya fara bata dai'dai san ransa, har lokacin hotuna ake ɗaukarsu.
Yana tsaka da bata abincin ne gabaɗaya yankin gidan cin abincin nan ya karaɗe da jiniya ta ko'ina, tamkar za'a tashi garin. Yana zaune bai motsa ba, ita kuwa hankalinta ya tashi sosai, dan idan ba a gidan Abu Abdussalam ba bata taɓa jin jiniya irin haka ba, a gidan Abbie kawai tasan idan za'a fita ko za'a shiga wannan jiniya yake tashi, to waye ne kuma ya zo a yanzu?. Bata kammala tambayar kanta ba sai ganin wasu jiga jigan jami'ai sun danno cikin restaurant ɗin a guje ta yi, ba dan tana tare da shi kuma taga bai motsa ba da ba abin da zai hanata tashi ta gudu. Gabaɗaya big girls and big boys dake wajen babu wanda hankalinsa bai tashi ba, babu wanda bai ji tamkar ya tashi ta gudu ba, bare ma yanda jami'an nan suke muzurai tamkar zasu ɗauki rayuka nan take.
Ko'ina tsit kake ji, jami'an gabaɗaya sun yi tsayuwa jarumta sun kewaye wajen gabaɗaya, shi dai Ramish tamkar bai san da zuwansu ba, yana cigaba da bata abinci a baki, ya lura ta tsorata sosai, dan haka sai ya yi ƙoƙarin ɗauke mata hankali daga kansu ta hanyar tambayarta a ina ta haɗu da masu nikaf har suka bata contacts na kashe shi?.
Tana ƙoƙarin bashi amsa wani very handsome jami'i ya danno kai ciki, he was so cute, handsome and gorgeous, sai dai shi chocolate color ne ba balarabe bane, and zubin Nigerians ke garesa, cikakken namiji ne mai rai da lafiya, kyakkyawa ajin farko, very hot guy, yana da tsawo dai'dai misali, Ramish ya fisa tsawo da kaɗan. Sanye yake cikin kakinsa, wasu zaratan jami'ai guda huɗu suna take mashi baya, kai tsaye in da su Ramish suke ya nufo. Yana isa wajen waɗan nan jami'an da suka rakosa suka yi gaggawar kewaye kowani angle na table ɗin da su Ramish ke kai, shi kuwa guy ɗin haɗe kafafunsa ya yi cike da jarumta ya ɗaga hannu ya sarawa Ramish. Ajiye spoon na hannunsa Ramish ɗin ya yi tare da miƙewa tsaye, hannu ya bashi suka yi musaba cike da kulawa yana faɗin. "Saukar yaushe my guy?".
Sai a lokacin Leesharh ta ɗago kai cike da tsoro dan taga wanenne?. Ai bata san lokacin da ta zabura ta zaro idanunta tana kallansa ba, kamannin dake kan face ɗinsu har ya ɓaci, sun yi kama sosai tamkar ƴan uwa na jini, sai dai kowa da yadda yake kallan mutum, shi ma Ramish yaga kamanninta da friend ɗin nasa, sai dai ba can sosai ba, shi kuma friend ɗin nasa bai ma bi ta kanta ba bare har yaga ko suna kama or akasin hakan.
Izini Ramish ya bashi a kan ya zauna mana, kun san sofas na table ɗin irin two seater ɗin nan, ɗaya ta side ɗin nan ɗaya ta side ɗin can, table yana tsakiya, so shi da Leesharh suna saman sofa guda, abokin nasa sai ya zauna a ɗayan shi kaɗai. ...... Cike da mamaki guy ɗin ya ce. "My Man yaushe ka fara cin abinci a restaurans kuma?". Cewar jami'in kenan ba.
Zama Ramish ya koma ya yi kafin ya amsa mashi da. "Ba ni zanci ba, ga wadda na kawo ta ci nan". Ya kai karshen maganar yana nuna Leesharh da hannunsa. Sai a lokacin guy ɗin ya lura da ita a wajen, cike da mamaki ya yi mata kallo ɗaya kafin ya mayar da kallansa a kan Ramish, sannan ya ce. "My man wacece wannan ɗin? And I was so surprised ganinka tare da mace, the thing looks some how to me, i never expect that for now, amma dai nasan gaba kila in yi expecting ganinka da mace, but now kai I was so surprised". Ya kai karshen maganar yana sake dawo da kallansa a kan Leesharh, dan shi kansa yaga kamannin dake tsakanin fuskokinsu. Ita kam ba iya kamanni kawai ba, gabanta ne yake faɗuwa idan ta gansa, ji take yi kamar ta san shi? Sai dai a ina? Ita da bata san kowa ba bayan iyayenta da suka tsinceta sai mutanen gidan AAJ, gidan aikinta ita da mamarta yanzu kuma ƴan gidan Abu Abdussalam, su kawai ta sani.
Kai tsaye Ramish ya amsa mashi da. "She's my wife to be In Sha Allah"...... Dum!!! Dum!!! Zaro idanu guy ɗin ya yi yana kallan Ramish, sai kuma ya ɗan saki murmushi kaɗan kafin ya ce. "Amma baka taɓa yi mun wasa ba, meyasa yau kake san yi mun? Ka manta ka ce kai babu abin da zaka yi da mace a rayuwarka ne?". ....... Harara Ramish ya bisa da shi kafin ya ɗan saci kallan Leesharh ta wutsiyar ido, take ya ga face ɗinta ya sauya saboda ta ji ya ce babu abin da zai yi da mace a rayuwarsa, wato kenan dama abin banza suka ɗauki mata kenan?. Shi kuma wannan guy ɗin bin Ramish da kallo yake yi yana jiran amsa, bai san da cewa Ramish neman amincewanta ma yake yi taki ba, yanzu ba batu ake yi na me zai yi da mace ba tukun nan, batu ake yi na yana neman hanyar da Leesharh zata aminta da shi.
Spoon ya ɗauka tare da fara ɗebo abincin yana kai mata ɗan bakinta ba tare da ya sake bi ta kan abokin nasa ba, dan ya lura idan ya biye mashi zai cigaba da faɗar maganganunsa da ya rinƙa faɗa a baya wanda kuma zai sa Leesharh ta ƙara arzuƙa ta ki yafe mashi, zata ce dama a banza ya ɗauki mata shiyasa ya yi mata abin da ya yi mata kenan, dan haka gara ya fiske kawai. Abokin nasa ya lura da baya san maganganun da suka wuce, dan haka sai ya yi mashi fatan alkhairi tare da juyowa ga Leesharh ya hau tsokanarta da sunan amaryarsu.
Ƙasa da kai ta yi tana jin gabanta na faɗuwa, har ga Allah tana jin kamar jini na fusgarta idan ta ga face na guy ɗin.
Lokaci guda Ramish ya ji kishi sosai a kan maganan da guy yake yi mata tana amsawa, ransa ta sosu, sai ya ce ta tashi su tafi cin abincin ya isa haka, kun san mutanen da kishin bala'i, ya ce wa guy ɗin kuma ya wuce gida zasu haɗu zuwa dare........... TO WANENEN WANNAN GUY ƊIN KUMA?.
Yana kai karshen maganarsa ya miƙe tsaye tare da riko hannunta, kamar zata kwace kanta sai kuma ta daure ganin jami'ai a wajen, ta san kuma shi ba ƙaramin jami'i bane, kada ta ja mashi raini, dan haka sai ta hakura ta biye mashi har suka fice daga wajen, haƙiƙa ya jinjinawa halaccin da ta yi mashi, ta daure ko sau ɗaya bata kunyata shi a idanun mutane ba, abin ya yi mashi daɗi sosai!.
Suna fita cikin wajen ta kwace hannunta, bai ce mata ko uppan ba ya shiga gaban mota, kafin ma guy ɗin ya fito sun bar gidan cin abincin da gudu gaske.
A maimakon ya zame da ita gida, sai ya wuce da ita wajen shakatawa da wasanni dik dan ya samu ta sauko ta yafe mashi, ranar yau gabaɗaya ya sadaukar mata, ya sanya a ransa ba zai mayar da ita gida ba sai can tsakiyar dare, watakila zata ji sanyi a ranta. Amma fa yasa a ransa tana yafe mashi zai mayar da ita gidan Abbie ya cigaba da aikinsa.
To bari mu je Paris mu dawo mu bisu wajen shakatawar mu ga me zai faru a can kuma, amma kuma tinanin Leesharh zata yafe mashi kuwa? Zai kama masu nikaf? Wani irin hukunci zai yi wa Ummie a lokacin da zai gane ita ta cutar da rayuwarsu?.
🔥🔥🔥🔥🔥PARIS🔥🔥🔥🔥🔥
Washegari da safe babu yadda Auta bata yi da Pretty a kan ta zo su sauka kasa ba, amma taki, ta ce wlh babu ita babu batun sauka kasa akwai damisa a wajen. Dan dole Auta ta rabu da ita a saman ta sauka, wunin ranar dai a ɗaki Pretty ta wuni har dare, ko abinci a ɗaki Auta ta kawo mata. Sai can dare bayan sun yi sallar mangariba da isha'i ne Auta ta shiga toilet dan ta yi wanka, a lokacin ita kuma Pretty ta yi wankarta, ta shirya cikin wani sleeping dress mai shegen kyau, launin purple color, ta yi kyau matiƙa.
Yunwar dare take ji yana addabawa cikinta, ga Auta tana cikin toilet, tinai ta fara yi a kan mafitarta, dai'dai da second ɗaya ba zata iya jurar yunwa ba. Saukowa kasan bed ɗinsu ta yi, cike da tsoro ta nufo parlourn sama. Sai wani lallaɓawa take yi kamar wata ɓarauniya, wai dik dan kada damisan nan ya ji sautin takunta, a hankali ta turo kofar bedroom ɗinsu, kanta ta sako waje ta leƙo dan ta duba. Watam parlourn babu kowa, ƙarisa buɗe kofar ta yi ta kara fito da jikinta waje da kyau ta leƙa. Da gaske dai babu kowa babu komai, ai a miliyan ta yanka da gudu sai ɗakin Smart.
Babu ko excuse ta afka mashi cikin ɗaki. Yana tsaye a tsakiyar bedroom ɗin rike da wayarsa, sanye yake da haɗaɗɗen bathrobe launin up white a jikinsa, kamar sako yake typing a cikin wayar. Da gudu ta tafi ta faɗa jikinsa tana sauke ajiyar zuciya, kun san ta saba yi wa Kamran haka, so bata wani damu da waye shi ba. Har sai da ta buge mashi waya ya faɗi ƙasa, dan bai yi tsammanin wani zai shigo ba, sao gata ta shigo har da faɗawa jikinsa. Cak ya tsaya, slowly ya dawo da kallansa a kanta.
Kun san halinta da shegen shagwaɓa, tamkar zata yi kuka ta ce. "Yah Omerish yunwa nike ji, kuma ina tsoron wannan damisan naka, ka je ka kawo mun abin da zanci dan Auta tana toilet"....... Ai rasa abin faɗe Smart ya yi, wai shi ne zai je ya kawo mata abin da zata ci, kai sai kace a mafarki, tab lallai wannan yarinya ta zo da sububa a lamuranta, tana da buƙatar gyara.
Ya luluƙa duniyar tinanin me zai yi mata sai ji ya yi ya fashe mashi da kuka, kun san halin mutuniyar, yo ita ina ruwanta da yana da izza? Ai shi ya jiyo shi da sarautar tasu, ita dai abinci ta sani sai shagwaɓa, dan haka yunwa take ji dole a bata abinci in ba haka ba ta yi ta kuka daga nan har wayewan gari.
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
========🔥🔥🔥=========
MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
49
🔥🔥🔥🔥PARIS🔥🔥🔥🔥
Wani irin ratsa mashi zuciya kukanta ya yi, amma sai ya yi ƙoƙarin dannewa haɗe da ƙoƙarin daka mata tsawa, sai dai kash, ya gagara iya rabata da jikinsa, dan ta ƙanƙame shi gam tana kukan ita dai lallai ya samo mata abin da zata ci tin da shi ya ajiye Tiger and Lion a gidan.
Dan dole ta tilasta mashi ya sassauta muryarsa tare da sanya hannu ya ɗan rungumeta kaɗan, already ya iya rarrashi tun da yana rarrashin Auta, sai dai Autar kawai yake yi wa ban da kowa, gara ma guyson idan yana ciwo yana bi ta kansa. Matsawa ya yi da ita ya zauna a saman side bed, sannan ya rabata da jikinsa ya zaunar da ita a gefen, in a low voice sosai ya ce. "Wait for me here bari in je in kawo maki abincin". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye.
A miliyan ta riko hannunsa cikin nata, tana kuka sosai, cikin shessheƙa ta ce. "Ni dai sai dai mu tafi a tare, ba zan iya zama ba, dan ina tsoron waɗan nan Tiger ɗin naka".
Wai my people's bakwa tinanin meyasa Pretty bata maganar su Sweetie? Ko sau ɗaya bata yi maganarsu ba, tamkar babu su a babin rayuwarta fa, kada ku manta kuma ita da