Showing 348001 words to 351000 words out of 403653 words
ta yi tin daga kan lokacin da matar commander take raye, ita dai tasan ma tin kafin commander ya aureta kamar ita ce kuyangarsu ba kuyanga Zubaida ba, wato ita ce wacce King ya amincewa da ta rinƙa zuba mashi abinci tana kuma girkawa kamar yadda ya aminta da kuyanga Zubaida a yanzu!
Take ƙwaƙwalwar momma ya fara shiga ruɗani, sai a lokacin kuma ta tina ita fa bata taɓa kallan face ɗin Hoorain ba a tsawon rayuwarta! Wani irin mummunar faɗuwar gaba ta ji a lokacin da ta tina bata san face ɗinsa ba! Saura kaɗan kwakwalwarta ya kama da wuta a lokacin da tinanin dalilin mutuwar mahaifiyar Hoorain ya ratso cikin kwakwalwarta, yanzu ta fara tantama a kan mutuwarta, anya kuwa ba kasheta kawai aka yi da gangan ba? Meyasa da ta ɓace babu wanda ya sake yin maganarta bare ma har ya nemota? Meyasa King bai tsaya tsayin daka sun nemota ba tin da amintacciyarsa ce a lokacin?.
Kai ganin ƙwaƙwalwarta yana ƙoƙarin tarwatsewa ne yasa ta miƙe ta nufi wajen Smart, dan wannan tinani ya fi karfin kwakwalwarta. A ɓangaren su mummyn Chuchu dik tinanin da suke yi kenan, wato meyasa King zai tsani Hoorain har haka ne wai?.
Gida ya rikice da koke koke, gidan biki ya koma gidan mutuwa!.
Kwance momma ta isko Smart, ya ja bargo har zuwa saman chest ɗinsa, hannunsa rike da phone ɗinsa yana latsawa. Ya yi nisa cikin abin da yake yi, har momma ta shigo bai ji shigowarta ba, a kusa da shi ta zauna, ganin hankalinsa ya yi nisa a taɓa waya yasa ta kai hannu ya karɓi wayar. Sosai ta ji mamakin ganin yadda ya zabura zai kwace wayar, sam bai yi tunanin ita bace. Yana ganinta sai ya kara ɗaure fuska tare da komawa ya kwanta yana ɗan kawar da kansa gefe.
Bata yi magana ba, amma ta sha jinin jikinta ganin yadda ya ɗaure fuska, alamar ransa a ɓace har yanzu kenan. Juyo da screen ɗin wayarsa ta yi dan taga me yake gani da ya zabura dan an kwace wayar haka. Ɗan zaro idanu ta yi tana kallan screen ɗin, sai kuma ta dawo da kallonta a kansa, lokaci guda ta ji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta, cike da zolaya ta ce. "Wannan ita ce sirikar tawa ne?".
Shiru ya yi bai amsa mata ba, sai ma gyara kwanciyarsa da ya yi zai ja bargo ya rufe har face ɗinsa. Rike bargon ta yi, cikin sigar tausasawa ta ce. "Ɓacin rai ne ya sanya ni yin wancan furicin, ba wai dan wani abin ba".
A ɗan takaice ya ce. "Amma dai ke kanki kinsa daddy ba'a a kan dai'dai yake ba ko? Meyasa ba zaki yi ƙoƙarin mai da shi hanyar dai'dai ba!"........ "Omerish wannan sarauta ce ba siyasa ba, sarauta da siyasa akwai banbanci matuƙa, kai siyasa ka sani baka san sarauta ba, karfin izza da isa a sarauta yake ba'a siyasa ba, ba komai ake juyawa da karfi a sarauta ba, dik abin da ka gani sai dai ka bishi a haka yadda yake a dokance.........".
Shiru ya ɗan yi na ƴan sakanni kafin ya ce. "Babu wata dalili da zata sanya in yi shiru in bar iyayena a kan hanyar halaka, and babu wata dalilin da zai sa in yi shiru a kan saɓon Allah ana aikata ɓarna ba dai'dai ba!!". Ya kai karshen maganar yana sake mata bargon. Ɗan matsawa kusa da shi ta yi. "Zaka iya dawowa nan?". Ta yi maganar tana nuna mashi saman laps ɗinta da hannu. Shiru ya yi mata kamar bai ji ta ba. "Zan faɗa maka wata magana ne"......... "Momma zaki fara ko? Please ki barni in more ɓacin rai'na".
Kai ta ɗan girgiza. "Naki gaskiya, zo ka ji wani magana". Ta yi maganar tana jan dogon hancinsa............. Ajiyar zuciya ya sauke... "Momma dayawan mata sun iya kalaman yaudara, shiyasa bana haɗa hanyata da mace, haka mom take mun irin wannan abin, idan dad ya ɓata mun rai bata barina in more ɓacin rai'na bare in yi fushi in ki kula dad, sai ta zo ta mun kalaman yaudara tasa na manta, shi ne kema zaki mun abin da take mun ko?".
(Malam Smart mu dai mata ba kalaman yaudara muka iya ba, tausasawa da tausayi muka iya, ko ya kuka ce my people's?🤨🤓😇)
Da hannu ta kara nuna mashi saman laps ɗinta ba tare da ta yi magana ba, dan dole ya dawo da kansa samansu ya kwanta yana kallanta. Kyakkyawar dark black curly hairnsa ta fara shafawa, ta lura ransa ya ɓaci sosai, sai ta nemi kawar da zancen da suke yi ta hanyar cewa. "Wannan ce sirikar tawa?".
Ɗayan hannunta ya riko cikin nasa, yana ɗan rarrabe yatsun hannun nata ta amsa da. "A'a kawai dai na ajiye hotonta ne, amma bamu da wata alƙa".
Hararar wasa ta wurga mashi kafin ta ce. "Ka tabbata kawai ka ajiye hoton ne?". Kai ya gyaɗa mata alamar e. "To meyasa ka ajiye shi kuma meyasa kake ta kallanta?"...... "Kai momma zaki fara ko? Ni kam ma dake da mom ban san wace ta fi wani ba, ni fa ba kallanta nike yi ba"......... Kallan gefen ido ta wurga mashi, da sauri ya sake cewa. "Da gaske momma ba kallanta nike yi ba".................. "Omerish har na shigo ɗakin nan fa baka san na shigo ba saboda ka shagala da kallonta, in baka faɗa mun gaskiyar wacece ita ba wace zaka faɗawa?". Cikin sigar tausasawa ta yi maganar.
Yatsanta na tsakiya ya riko, ring da Jaish ya sanya mata ranar ya fara ƙoƙarin zaresa daga hannun nata, sannan ya ce. "Momma kawai kyau take mun, and ina san wasu ɗabi'u nata, that's all". Ya kai karshen maganar tare da cire ring ɗin. "Kana sonta ne?". Ta jefa mashi tambayar. Da sauri ya girgiza mata kai kamar wani baby. "Momma ni fa ki rabani da sharrin mata, kina ganinsu ƴan yaudara ne, ya na kare dake da mom ma, bare in karawa kai'na wata".
Ita momma sam bata damuwa da yanayin maganarsa without a respect, saboda tasan ya yake tin yana karami, a koda yaushe tana bibiyarsa, to tasan ba wai raini bane, haka ya iya magana.
"To shikenan na ji baka sonta, yanzu dai ta shi ka yi lunch ka ji? Zuwa dare zan zo mu yi magana, ina da magana mai mahimmanci da kai". Ta faɗa tana bin hoton dake saman screen ɗin nasa da kallo, saboda ita kanta ta yi matuƙar burgeta, ta fita sosai a hoton, sai murmushi take yi dimples ɗinta sun lotsa, ga eyesball ɗinta su tura olive sosa, kamar ka saceta ka gudu!.
Jinjina mata kai ya yi haɗe da sakin hannunta ya karɓi wayarsa. "Ki sa Jaish ya kawo mun lunch ɗin a yanzu". Ya faɗa yana miƙewa daga saman laps ɗin nata, dama yunwa yake ji, kawai baya san kulasu ne yasa bai bi ta kan lunch ɗin ba. Ya kuma cire mata ring ɗinta, dan ya ɗan kama hannunta har ya yi mata shaida, shiyasa ya cire kamar yadda a baya Jaish ya cire ya canza mata.
"Allah ya yi maka albarka". Shi ne abin da ta faɗa kafin ta miƙe ta nufi waje. Da kallo ya bita yana jin wani irin kaunarta tana kara narka zuciyarsa, yana san mahaifiyar nan tasa over!.
Komawa ya yi ya kwanta shiru yana cigaba da kallon hotonta. Kamar daga sama ta witsiyar ido ya ga alamar mutum a tsaye a tsakiyar ɗakin. A hanzarce ya juyo da kallansa. Ɗan binta da kallo ya yi kafin gently ya ce. "Wai ke baki iya sallama bane?". Ya yi maganar kallansa a kanta cak. Turo mashi baki ta yi. "A ina zan ajiye maka abinci ya yi mun nauyi sosai a hannu". A maimakon ta bashi amsa sai ta faɗi abin da take da buƙata.
"Ina Jaish da nace ya kawo mun abincin?". Ya tambaya yana wurga mata harara...... Shiru bata amsa mashi ba, dan tana ganin bata da alaƙa da wannan tambayar tin da ita bata ma san wanene Jaish ɗin ba, kawai momma ta shiryata ta ce ta kawo mashi abinci.... Ganin ta yi shiru yasa ya fahimci nufinta, yanzu yana iya karantar shirunta sosai. Kai Pretty duniya, wato tana bawa Smart sabon karatu. Bin kayan jikinta da kallo ya yi, a ransa ya ce dik yadda aka yi momma ta sanyata saka wannan kaya, arabian abaya ce mai shegen kyau launin dark purple, ta yi masifar kyau sosai, sai dai kan nan dai babu ɗankwali, ta saki gashi har baya. A ransa ya ce shegen kyan bala'i ne da ita, kowani irin dressing ta yi kyau yake yi mata tamkar dan ita aka yi kayan! Ya zauna a jijinta zam zama har sai ka ji sha'awar irin dressing ɗin a ranka.
Ganin ya yi shiru yana bin jikinta da kallo ne yasa ta dongwarar mashi da try ɗin abincin a tsakiyar bedroom ɗin, a cewarta tin da ba zai faɗi in da za'a ajiye mashi ba ai tana da damar ajiyewa a ko'ina tin da ba shi ya bata hannun nata ba da zata tsaya tana rike da abincinsa tsawon lokaci, ga shegen nauyin tsiya, dama da kyar ta ɗauko shi, ba dan Momma da Allah ba zata ɗauko ba!.
"Ke zonan!". Ya faɗa with harsh voice, wai irin ta san ba da wasa yake yi ba, ta tsorata ta zo. Banza da shi ta yi tana cigaba da tafiyarta zata fita. Dab zata fita sai ji ta yi an damko gashin kanta ta baya. Wani irin kara ta saka mashi saboda zafi tare da juyowa da sauri. Angry face ɗinsa a ɗaure tamau, in a harsh voice ya ce. "Ina kiranki kina tafiya ni sha'anki ne?". Ya yi maganar ba tare da ya saki gashin nata ba.
Tana turo baki tana yamutse fuska saboda zafin damkar gashin nata da ya yi ta ce. "Ai ke na ji ka ce ta zo ba ni ba, ni sunana Pretty, da Pretty ka ce da na tsaya ko ban zo ba". Kam bala'i, lallai Pretty ƴar duniya ce......... 😅
Rasa abin faɗe ya yi, dan wlh idan ya biyewa yarinyar nan mari ɗaya zai yi mata ta mutu........... "Ni ka sake mun gashi kada ka cire mun su, zafi yake mun". Shagwaɓaɓɓiyar voice ɗinta ta daki dodan kunnensa. Ɗan sauko da kallonsa a kanta ya yi, da karfi ya sake jan gashin nata baya dan mugunta. Hakan yasa ta ɗaga kanta sama dan dole. Ɗago kanta yasa ya kalli face ɗinta a kurkusa, har cikin zuciyarsa ya ji wani iri na ganin kwayar idanunta, ga idanun fari tas tamkar audiga, kwayar olive ɗin kuma ya tura kala sosai, pink lips ɗinta ya tura sosai shi ma, dik yadda aka yi bata jima da yin wanka ba, soft skin ɗinta sai sheki yake yi yana wani glowing. Yaran nan Sweetie and Pretty sun mori jiki sosai, shape ɗinsu tamkar su suka yi wa kansu!
Ya shagala da kallanta sai ji ya yi ta gabza mashi cizo a hannu, wai dan ya ja mata gashi ta ji azaba sai ta kama ɗayan hannunsa ta gabza mashi cizo da karfi kuma taki sake fatar, sai kara datsewa take yi da hakwaranta. Zuba mata idanu ya yi yana kallanta ba tare da ya saketa ba, tinanin abin da zai yi mata yake yi, dan dole ya hukuntata!.
Da taga cizon kamar bai wadatar ba, bai saka shi ya sakin mata gashi ba, sai ta sake shi haɗe da dunkule ƴan hannayenta da basu wuce ya kama ya karya ba ta fara kai mashi duka a damatsan hannunsa. Abin ma gwanin ban dariya, wai ita nan dukansa take yi dan ya ji zafi ya saketa, bayan hannun nata ba auki kamar sandan snooker. Siririn tsaki ya ja kafin ya sa hannu ɗaya ya ɗagata cancak kamar ƴar tsana ya wurga a saman bed ɗinsa kamar wata kayan wanki. Tana ƙoƙarin miƙewa ya daka mata tsawa a kan ta zauna. Ai ina bata tsoron tsawar tasa, dan haka ta yi tashinta, yana tsaye ta zo ta wucesa zata fita.
Juyowa ya yi yana kallan yadda take tafiya ko a jikinta, yau ta goge mashi hadda, wai me zai yi wa yarinyar nan ne ta fara jin tsoronsa? Shi kowa a gidan nan yana tsoronsa amma ban da yarinyar nan, ita dik wasu tsawa da hargagi game da jan ido dik bata tsoransu. Ganin zata fice daga ɗakin ba tare da ya hukuntata bane yasa ya ce. "Yauwa my tiger come in.......".
Ai bai gama rufe baki ba ta watso a miliyan ta juyo, ihu ta zunduma tare da ɗale jikinsa, ta ƙanƙame shi gam tana faɗin. "Dan Allah Yah Omerish ka ce kada ya shigo, wlh cinyeni zai yi"...... Mamaki ne ya kama shi, ashe tasan sunansa Yah Omerish kenan, wato dama iskanci ne ya yi mata yawa a kai kenan? Wannan yarinya wlh sai shirin Allah, shi ya rasa ma me zai ce mata, ta wani ƙanƙame shi, wato dai bata tsoron mutane sai dabbobi, yanzu ya gane me zai rinƙa yi mata, dole ya ɗauko abubuwan tsoro ya kawo nan dan ta rinƙa respecting ɗinsa idan tana san zaman lafiya.
Ihun da take ta zundumawa ne ya farkar da shi daga duniyar tinanin da ya afka. A ɗan tsawace ya ce. "Sauka mun daga jiki ki je Tiger na jiranki a bakin kofar shigowa, ba ke bakyaji ba?". Kara ƙanƙame shi ta yi tana cusa kanta a kirjinsa ta ce. "Yah Omerish wlh ina jin magana, dan Allah ka ce ya tafi, wlh ba zan sake ba". Bilhakki da gaskiya take ihun nata!!.
"Kin yi alkawarin zaki rinƙa jin magana idan aka yi?". Kai ta shiga gyaɗa mashi da sauri sauri, tana faɗin ta yi. Hannu yasa ya rungumota a jikinsa sosai ya fara faɗin. "To ki yi shiru ihun ya isa haka kada ki tara mana jama'a, zo ki zauna mu ci abincin a tare". Kin sake shi ta yi, sai dai ta dakata da zunduma ihun, cikin shesshekar kuka ta ce. "To ka ce kada Tigern ya shigo ka ji?". Yadda ta yi maganar har cikin zuciyarsa ta ratsa shi, ga shagwaɓa ga muryar kuka, abin sai ya haɗe. Nisawa ya ɗan yi kafin ya ce. "To ba zai shigo ba, amma idan kina ihu zai shigo ne, sakeni mu je ki ci abinci". Wato shi ma yasan ita sarkin son abinci ne fa!.
Ba musu ta sakesa tana shessheƙa. In short a tare suka ci abincin, kuma wunin ranar a bedroom ɗinsa ta wuni har dare, taki fitowa wai kada Tiger ya kamata, shi kuma yaki zuwa ya je ya rakata, dan bashi da matsala na zamanta a bedroom ɗin, tana ma ɗebe mashi kewa ne, da rana ta yi sanyi ma hayewa saman bed ɗinsa ta yi a kusa da shi ta kwanta, ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita.
--------------------------------------🔥
A takaice tsawon sati biyu Auta tana jinya, ban da uhm da mmm babu abin da take cewa, tana kwance shiru a wannan part ɗin, Abdussalam sai ƙoƙarin shiga ziciyarta yake yi ta hanyar zuba mata kalamai masu sanyi da tausasawa game da kulawa, amma dik taki kula shi, sai ma layi da ya shata mashi a kan kada ya kuskura ya matso kusa da bed ɗinta, bai yi mamaki ba, dan yana tinanin zafin ciwo ne, shi kwata kwata bai san da batun soyayyarta ba, wlh da ya sani ko kaɗan ba zai taɓa yarda su yi aure ba, yana san farincikinta sosai, so bai sani ba, ya zaci kawai bata son ayi mata aure a yanzu ne, shiyasa idan ya zo wajenta yake yawan ce mata kada ta damu shi zai iya barinta har ta kammala karatunta kafin su yi zaman aure, dan hankalinta ya kwnata har ce mata yake yi zai iya barinta a kingdom of power cikin ƴan uwanta ya koma Dubai, dik dan ta samu farinciki, amma ina, ita dik ba wannan ne a gabanta ba, hankalinta ya yi nisa, wai a haka ma bata san Hoorain ya mutu ba, ta yi alkawarin babu wani namijin da zata mallakawa jikinta, a cewarta zata yi ta avoiding ɗin Yah Abdussalam har ya gaji ya sawwaƙe mata ta kawo kanta ga Hoorain ɗinta, ta ci alwashin in dai Hoorain bai sameta ba, to tabbas kashe kanta zata yi, dan jikinta mallakinsa ne, ta yi mashi wannan alkawarin tin tana France. Ya kuke tinanin zata ji idan ta san ya mutu? Anya ita ma zata rayu kuwa?!.
A ɓangaren Smart kuwa, wlh yadda kuka san baya gidan, kuma dik abin da yake faruwa yana sane, amma bai shiga harkarsu ba, ya zuba ido, sai dai kuma kamar akwai abin da yake shiryawa daddyn nasu, dan ya ɗaukarwa kansa alkawari idan King ya yi sanadiyar mutuwar Zunaira to tabbas wlh ba zai rabu da shi ba, kuma ya san in dai tasan Hoorain ya mutu da wuya ta tsallake ita ma. Uhm akwai cakwakiya fa!!.
Cigaba da rayuwarsa Smart ya yi, sai kiransa daddynsa yake yi yana cewa ya dawo, amma sam babu alamar komawa, dan ya ce ba zai bar kingdom of power ba har sai ya gyara masu zama, azumi ta iso, Momma zata je Dubai gaisuwar azumi, sai ana gobe za'a ɗauki azumi zata dawo, to shi ne abin da Smart yake jira, so yake yi momma ta tafi, sannan su yi uwar watsin da za'ayi, kunga bata nan bare ranta ya ɓaci ya ji babu daɗi!!.
Uhm Zunaira ta shafe two weeks a saman gadan jinya ba tare da sanin Hoorain baya raye ba, tana nan tana tattalin soyayyarsa a cikin zuciyarta, ta yi mashi ginin da babu mai iya rusa mata!! Kullum tana kan ƙoƙari kara yawan son nasa a ranta!! Ba ci ba sha, dik ya rame ta lalace fiye da tinanin kai tinani, bata da wani walwala, wannan ma wai dan su Chuchu sun ta ƙoƙarin kwantar mata da hankali, wlh shi kansa King tsoron zuwa dubata yake yi, saboda yadda ta rame bata a cikin hayyacinta,