Showing 102001 words to 105000 words out of 403653 words

Chapter 35 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

40

yake ba wajen mom ɗinmu ba, domin kuwa mom ban taɓa ganin tana tsafi ba".

Katseta ya yi da cewa. "Kina nufin ke yar sarki ce?". Cike da mamaki ya yi tambayar.

"Kamar yadda mom ta faɗa mun, hakan ce, sai dai ta ce kingdom ɗinmu bashi da wata amfani a garemu, and babanmu ma bashi da wani amfani a garemu, dan haka kada ma muje in da yake, a banza zasu kashe mu".

Shiru ya ɗan yi yana tinanin, tabbas Sweetie ta ɓoye mashi wani abin, har yanzu zuciyarta yana rawa a kan faɗa mashi gaskiyar wacece ita, ba zata iya zayyane mashi gaskiya gabaɗaya ba, sai dai ta tsakura mashi wani abin kaɗan.

Fahimtar bata san buɗe mashi komai da ya shafeta ne yasa ya kawar da zancen da cewa. "Jeki kwanta dare ya yi, bari in je wajen yaya tinda magic ɗinki ya bude mana kofa".

Make kafaɗa ta yi. "Ni dai sai dai mu tafi tare".

Haka kawai ya ji tongue ɗinsa ya yi mashi nauyin ya musa mata, sai kawai ya amince mata suka nufi side na Black Tiger a tare.

Yana rike da hannunta suka nufi master room na Black Tiger. Ko tsoro bata ji ba, dan ta kuduri niyar ba gudu ba ja da baya.

Ronnie ne ya sanya password a jikin kofar. Nan take ta wangale. Ciki suka shiga, tin da ta sako kafarta ciki take ta faman rarraba idanu tana neman ta ina zata gansa. Da yake ɗakin yana girma sosai, shi kaɗai ya kai girman gidan wani, tsakanin in da King bed ɗinsa da mirror yake ba ƙaramar tazara bace ba.

Kai tsaye bakin bed suka nufa, suna isa Ronnie ya sake hannunta ya haye saman bed ɗin ya kwanta, a hankali ya janyo pillow ya rungume yana jin wani irin nishaɗi da bai iya tantace na menene?.

Ita kuwa cigaba da rarraba idanu ta yi tana neman ta ina zata ga Black Tiger a cikin ɗakin. Can har ta cire tsammani da ganinsa kamar daga sama taga mutun a bagan mirror yana gyara gashin kansa.

S-p dress ce a jikinsa launin up white, rigar tana da dogon hannu kazalika wandan ma doguwa ce har ƙasa, yana tsaye kan kafafunsa ya basu baya.

Ajiyar zuciya ya sauke with her full confidence, with a cool voice ta ce. "Big bro good evening".

Zaro idanu Ronnie dake kwance a saman bed ya yi, bai yi expecting hakan ba, shi da ya ce su bi komai a hankali tana neman jawo masu bala'i.

Kamar bai san da su a cikin ɗakin ba, cigaba da abin da yake yi ya yi....... Hannunta dikka biyu ta riko waist ɗinta da shi, like she didn't care a kan shareta da ya yi, cike da tsiya da neman tsokana ta ce. "Big bro sam kayan nan basu yi maka kyau ba, ka canza wasu dan bana sansu a jijinka".

Ai a miliyan Ronnie ya tashi zaune a tsakiyar bed ɗin tamkar wanda aljanu suka fasa jikunsa suka shigesa a lokaci, a razane ya zaro ido yana kallonta, lallai Sweetie ta cika yar neman bala'i, ko ina ruwanta da kayansa? Ronnie ya jefawa kansa tambayar.

Ita kuwa, ɗan tawa one step ta yi gaba kaɗan, sannan ta ɗan ɗaga kanta sama kallonta a kansa, cikin salon jan magana da neman tsokana ta sake cewa. "Ni fa ko baka amsa mun ba ban wani damu ba, nasan kana jina, handsome guy kawai, amma ba wai kana da............."

Haɗiye sauran maganar ta yi sakamakon wani haske da ya fito daga cikin idanunsa ya daki mirror dake gabansa sai ya juya ya nufota, tafin hannunta tasa cikin zafa ta tari hasken, hakan yasa ya tsaya bai tarwatsata ba.

Yadda kuka san wani walkiya haka Ronnie ya diro ƙasa daga saman bed ɗinsa, da gudu ya iso gabanta, cikin zafa ya fisgo hannunta, da gudu ya jata domin su nufi waje.

Sai dai kash, suna isa kofar ɗakin sai suka kasa iya buɗeta, ta datse gam.. babbar magana, dama shi Ronnie yasan tin da Sweetie ta ji Black Tiger ba zai kasheta ba ya shiga uku, ba ita kaɗai zata sha azaba har da shi, wayyo Allahnsa.

Me kuke tinanin Black Tiger zai yi masu?.

••••••••••••••••FOREST•••••••••••••••🔥

A hankali ta fara yunƙurin buɗe idanuna da suka yi mata balai'n nauyin gaske. Jikinta dik ji take yi kamar ba nata ba, da kyar ta iya buɗe idanun nata, kyakkyawan ganye kore shar ta fara cin karo da shi a ganinta, hasken rana ne yake haskowa ta tsakanin ganyayyakin, sai hakan ya bada wani kala na musamman.

Mamaki ne ya kamata ganin an yi mata rumfa da ganyayyaki. A hankali ta yunkura ta miƙe zaune, jujjuya idanunta ta fara yi tana neman ta ina zata hango mutane. Sai dai bata ga alamar kowa a wajen ba.

Hannu ta ɗaura a kan cikinta domin ta taɓa ciwonta ta ji, sai ta ji kaya mai kauri a jikinta. Da sauri ta kai kallonta jikin nata. A wani irin zabure ta miƙe tsaye lokacin da ta ga irin rigar dake jikinta.

Zaro idanu waje ta yi, nan take ta haɗiyi wani irin yawu mai sauti, fitowa ta yi daga cikin rumfar, hannunta ne ya fara kerma alamar tsorata, kafafunta ne suka fara raunata suna ƙoƙarin kasa iya ɗaukarta, amma haka ta dake ta fara taka ƙasa tana waige waige, tamkar mai neman wani abin.

Jacket mai bala'in kyau launin black color ne a jikin nata, jacket ɗin yana da hula, da ta miƙe tsaye tsawonsa ya kai mata har gwiwanta, to jacket ɗin wanenen kenan?. Harda hular aka sanya mata a kanta.

Tafiya take kamar zata kifa kasa, tana yi tana waige waige kamar wata maras gaskiya. Cak ta tsaya lokacin da idanunta suka sauka a kan wasu irin furanni farare da yellows masu bala'in kyau da ɗaukar hankali, sai a lokacin ta mayar da hankalinta a yanayin wajen, fillin ya yi matukar ƙawatuwa sosai, korayen gayyayakin dake wajen sun kara haska ko'ina, ga furannin sai tashin wani irin kamshi mai kwantar da hankula suke yi, furannin suna da yawa sosai, sun kewaye arear wajen. Ga tsuntsaye masu launika daban daban.

Wani irin kara ta ji a gaba kaɗan kamar karar zubar ruwa kamar kuma na sahun mutane. Take ta ji jikinta ya mutu na ganin wajen, ga yanayin weather wajen iska mai ni'ima da ratsa jiki.

A hankali ta ja kafafunta ta nufi wajen da take jiyo wannan kara. Like wow, tin daga nesa ta hango wasu irin koramu dake aman ruwa mai hasken gaske, wasu irin flowers manya manyan launin white kewaye da kusa da koramar, ga duwatsu masu kyau da ɗaukar hankali, wajen ya kawatu matuƙa.

Ai Auta bata san time da ta wani irin sauke sayayyar ajiyar zuciya ba, tin ainahinta tana san irin wannan waje, kun manta nace maku ita da Chuchu suna yawan kallan films masu irin wannan dajin a nan suka sakawa soyayyarsu sunan shuka flowers ɗin kauna?.

Wani irin nishaɗi na musamman ne ta ji yana ratsa zuciyarta, har ta saki cool murmushi ba tare da ta sani ba, ji ta yi tamkar ta je ta shiga cikin wannan koramar ruwa ya yi ta zuba a kanta, ciwonta ne kawai ya hanata zuwa, da ba abin zai hanata shiga.

A hankali ta ƙarisa tinkarar wajen koramar. Can ta hango kamar an kunna wuta ta gefen koramar ɗan baya kaɗan yana ci, hayaki ta fara hangowa. Ɗan kara ɗaga kafafunta ta yi ta nufi wajen.

Wani irin birki ta ja lokacin da ta matsa kusa da hayaki, ta hango Pretty zaune a kusa da wutar tana kara jefa wasu kananan itace dake hannunta a cikin wutar yana kara kamawa, zaro idanunta waje sosai ta yi tamkar kwayar idanunta zasu faɗi ƙasa.

A zahiri zakuga kamar Pretty take kallo, amma sam ba ita take kallah ba, namijin gaske take kallah, yana tsaye a saman wata dutse dake kusa da koramar, ya sanya takobinsa a cikin ruwan dake kwarara yana wankewa, ita kuma Pretty tana jin ɗumi kusa da wuta.

A fili da karfi Auta ta furta. "HOORAIN!!!!".

A tare shi da Pretty suka dawo da kallonsu a kanta. Kafin dikkansu su yi wani motsi cikin ɗaga murya ta sake cewa. "Pretty ki gudu daga kusa da shi, mugu ne! Kasheki zai yi!".

Miƙewa tsaye Pretty ta yi, cike da yarinta a muryarta ta ce. "A'a Zunaira ba mugu bane, shi ne ya taimakemu ya kuma saka maki magani a ciwonki, ya canza........."

Tsawar da Auta ta daka mata a kan ta tashi daga kusa da shi a karo na biyu ne yasa ta yi saurin haɗiye sauran maganar, tsawa Auta ta sake daka mata. "Kizo mu gudu Pretty, kasheni ya zo sake yi".

Hoorain dake tsaye kamar an dasashe mamakin Auta ya gama kashe shi ne ya juyo da jikinsa gareta gabaɗaya ya fuskanceta.

Da yar gudunta Pretty ta baro wajen wutar ta nufo Auta, rike hannun juna suka yi da sauri suka juya da nufin su bar wajen, Pretty tana ta faɗin. "Zunaira kin san shi ne? Zunaira kin san shi ne?".

Shiru Auta bata amsa mata ba. Cikin Zafa Hoorain ya diro cikin ruwa daga saman dutsen, a gaggauce ya mayar da takobinsa mazauninsa, yaga da gaske zasu tafi, with his full power ya bi bayansu.

Gaban Zunaira ya tare, cikin sanyin murya ya ce. "Ranki ya daɗe lafiya kuwa?".

A tsawace ta ce. "Ka bani hanya na wuce, idan kuma ka biyoni nan ɗin ka ƙarisa kasheni tun da Allah ya kuɓutar dani a farko ne kuma sai in ji?".

Shiru ya ɗan yi kamar mai tinanin wani abin, sai can kuma ya ce. "Ban gane me kike nufi ba ranki ya daɗe"........... Ranta ne ya kara ɓaci, ko kaɗan babu tsoronsa a ranta, dan su ba jinin tsoro bane, a fusace ta ce. "Ba zaka gane ba ai dama, ka bani hanya!!"..

Pretty ce ta katsesu da cewa. "Zunaira wai me yake faruwa ne? Kin san shi ne?".

Rai a matuƙar ɓace, zafafan hawaye har sun fara tsere a saman face ɗinta, da kyar voice ɗinta yake fita ta kalli Pretty kafin ta bata amsa da.
"Ya wuce sani na yi mashi Pretty, kuma shi ne sanadiyar zuwana wannan dajin, shi ya ji mun wannan ciwo dake cikina! Kasheni ya so yi Allah ya yi ina da rabon cigaba da rayuwa, yanzu nasan ya jefa mun ƴan uwana cikin tashin hankali, ya cutar da zuƙata dayawa, ya zaluncemu, daddyna ya yarda da shi sosai amma ya ci amanar yarda, ba zan taɓa yafe mashi ba, na tsanesa fiye da tinanin mai tinani".

Tin da ta fara magana ya shiga ruɗani da tantanmar anya Zunairarsa ce kuwa? Dan dai shi yasan Zunairarsa ba haka take ba, bata da faɗa ko kaɗan.

Yana can yana tunani ta figi hannun Pretty suka raɓa gefensa zasu wuce. Cikin zafa ya sake tare gabanta, a dai'dai lokacin ta dafe saitin cikinta, saboda figar hannun Pretty da karfi da ta yi ɗin nan ya ja cikinta ya amsa.

Tana dafe cikin bai san lokacin da ya matsa kusa da ita ya tallapota a jikinsa ba, shi dai komai zai faru voice nasa a sanyaye cikin nitsuwa, sam baya da hayaniya komai tashin hankalin da zai shiga.

"Kin gani ko ranki ya daɗe? Dan Allah ki nitsu sai ki fahimtar dani a kan me kike magana? Ban gane me kike faɗe ba, ni ban sanki da hayaniya da faɗa ba, dan Allah kada ki sauya mun, ki yi hakuri ki fahimtar dani komai, ki faɗa mun meya kawoki nan kika jefani cikin tashin hankali tsawon wata da kwanaki ina nemanki?".

Tin da ya fara magana idanunta suke a saman face ɗinsa dik da a rufe take, wani irin kara ɗaure fuska sosai ta yi, cikin zafa ta ce. "Ka sake Ni!!".

"Idan na sakeki zaki iya fama ciwonki ne". A sanyaye ya faɗa............."To idan na fama ina ruwanka? Kai da kaso kasheni me zai dameka dan na fama ciwona a gabanka? Jikinka ne ko nawa?".

Idan hankalinsa ya kai miliyan to a yanzu ya tashi, dan yaga bil hakki da gaske take yi, bai san meyasa take cewa shi da ya so kasheta ba, shi bai san komai a kan abin da take faɗe ba, tana ta jefashi cikin ruɗani... TO FAH, ME KUKE TINANI MY PEOPLE'S? TO IDAN BA SHI YA KASHETA BA WAYE YA YI HAKAN? MUJE DAI ZUWA.

"Nace ka sake ni ko?!". Cikin ɗaga murya ta yi maganar, hakan yasa ya yi saurin saketa, saboda bai taɓa jin ta ɗauki zafi haka ba.

Da kyar ta iya tsayawa a kan kafafunta, sannan ta raɓa gefena zata wuce. Da sauri ya zube gwiwowinsa a ƙasa a gabanta, cikin nitsuwa ya fara jero maganganu masu zafi kamar haka.
"Ban san laifin me nayi maki da har na cancanci irin wannan hukunci daga gareki ba, amma dai koma menene ina mai neman afuwa da ki yafe mun, kuma ina neman alfarma, ko da ba zaki sake yi mun magana ba, kai ko da ba zaki sake buƙatar ganin face ɗina a rayuwarki ba, dan Allah ki bani damar na mayar dake gida, dan hankalin kowa a tashe yake, kowa kukan rashinki yake yi, dan Allah ki saurareni, ni ban ma buƙaci jin laifin me nayi maki ba, ni dai kawai na karɓi laifin koma menene, ina neman afuwa".

Kin saurarensa ta yi, ta raɓa gefensa ta wuce tana rike da hannun Pretty, a fili ta furta......... "Sai dai na mutu a wannan dajin da na yarda da kai, gara yunwa da kishin ruwa su kasheni da na bika da sunan ka mayar da ni gida". Kun san modarawa da balai'n zuciya, to ita ma Auta ta gado, ta fusata ba sassauci.

Dafe kansa dake yi mashi tsananin ciwo ya yi, ya sha bakar wahala tsawon kwanaki 35 yana nemanta, daga gari har daji, wani maharbi ne ma da suka haɗu a cikin gari sai ya nuna mashi hotonta ya tambaye shi, shi ne ya ce tabbas ya taɓa ganin kamar ita a bakin ruwa cikin wannan dajin, dalilin da yasa ya shigo nemanta kenan, ya shafi kwanaki 20 ciff a cikin wannan dajin yana nemanta, sai yau Allah ya yi ya ganta, amma taki ta bashi dama ta saurare shi.

Miƙewa tsaye ya yi, dik jikinsa ta mutu, ba abin da yake damunsa a zuciyarsa ma kamar yadda take ta ikirarin shi ya kasheta, to shi a yaushe ya kasheta? Wata ɓangare na zuciyarsa ce ta amsa mashi da. "Ko dai kin bayyana mata soyayyarta da ka yi ne yasa take ikirarin ka kasheta, kila hakance ta cutar da zuciyarta har take gaba da kai".

Tuna hakan yasa ya yi saurin bin bayansu. Can ya iskosu suna san tsallaka wani ruwan dake gudu mai ɗan girma, ba zasu iya tsallakawa ba sai sun shiga su wuce, to suna tsoron shiga kada ace wajen yana da zurfi, Auta tana dafe da cikinta, ita kuma Pretty tana ƙoƙarin samo itace su sanya a cikin ruwan dan su gwada zurfin ruwan.

Gabanta ya kariso ya tsaya, cikin girmamawa ya ce. "Dan Allah ranki ya daɗe ki bani dama, dan Allah ki tsaya ki saurareni, kada ki yanke hukunci cikin fushi, tuba nike yi, nasanki da hakuri da juriya game da yafiya, dan Allah ki yi hakuri kin ji?".

"Okey kasanni da hakuri shiyasa ka kasheni dan kana ganin zan yafe maka ko?". Ta gefa mashi tambayar tana kawar da kallanta daga kansa, bata san sake ganin face ɗinsa.

"Wlh ranki ya daɗe ni ban kasheni ba, ban taɓa tinanin dede da second ɗaya na cutar dake ba, bani da burin da ya wuce in ganki a cikin farinciki, please ki saurareni".

"Amma kuma dik da san farincikina da kake yi hakan bai hanaka caka mun wuƙa a ciki ba ko?". A fusace ta yi maganar!.

Wani irin zaro idanu ya yi, sai a yanzu ya yi magana cikin ɗaga murya.

"What!!!! Wuƙa a ciki kuma? Ni na caka maki wuka?". Cike da tashin hankali ya yi tambayar......... Ɗan siririn tsaki ta ja tare da juya mashi baya dan bata bukatar sake yin magana da shi.

To fa!! Wannan lamari akwai sarkakiya sosai wlh.

"Ban gane ni na caka maki wuka a ciki ba? Ki mun bayani".......... Yadda ya yi maganar sai da yasa ta yi saurin juyowa garesa, ko da wasa bata taɓa jin sautin muryar a haka ba, Allah sarki wato koma dai menene akwai tsantsar sansa a ranta har yanzu, tabbas ba bawa yake sanya kansa son wani a ransa ba, dan kuwa da mutum yake sanyawa kansa da Auta ta cire son Hoorain daga cikin zuciyarta.

Ganin yadda tashin hankali ya bayyana a tattare da shi ne yasa ta ji yana da kyau ta sauraresa, dan kuwa alamu sun nuna kamar akwai wani abin........... Cikin nitsuwa ta bashi labarin yadda aka yi ya kasheta tsab, yadda suka haɗu a bayan part ɗin uncle Abbas da komai da komai har yadda ya caka mata wuka a ciki tana kallon kwayar idanunsa.

Ita dai Pretty ta yi tsaye hannunta rike da sanda tana kallansu....... Innalilahi wa inna ilahir rajiun, Hoorain bai san lokacin da ya zube gwiwowinsa a ƙasa ba, wani irin sara mashi ya ji kansa ta yi, da kyar ya fara maimaita kalmar innalilahi wa inna ilahir rajiun, Hasbunallahu wani'imal wakil. Sai da ya maimaita sama da sau hamsin durkushe a wajen, ya kasa ɗago kai ya kalleta ma, idanunsa sun rikiɗe sun yi jakir gwanin ban tsoro, alamar ran maza ya ɓaci.

Ganin ya durkushe ƙasa ya sunkuyar da kai yasa Auta ta juya zata bar wajen. Cikin Zafa ya kai hannu ya riko hannunta. Da sauri ta juyo da kallanta a kansa.

Can ƙasa ƙasa ta tsinkayo muryarsa yana faɗin. "Bani bane, bani bane ranki ya daɗe, wlh bani bane, tabbas nayi waya dake, kuma tabbas kin ce mu haɗu a bayan part ɗin uncle Abbas a wancan ranar, kuma tabbas na je wajen, amma

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login