Showing 297001 words to 300000 words out of 403653 words

Chapter 100 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

58

lastly har ya gama rubuta littafi a rayuwata star ɗita ba zata taɓa haura 15 years ba In Sha Allah, na baku satar amsar yadda zakuna gane Stars mata na littafaina, ba zasu taɓa haura 15 years ba........😅

STORY🔥♥️


🔥🔥KINGDOM OF JUSTICE🔥🔥

Wato RAWANIN ADALCI kenan, shi ne sunan masarautar nan na Queen Zarina, wasu suna kiranta da kingdom of justice, sai dai kuma sunane saɓanin aiki, dan kuwa babu koda kwayar zarra na adalci a cikin wannan masarauta, mulki suke yi mai cike da zalinci wato mulkin kama karya, babu adalci a tafiyarsu, babu tausayawa bare jin ƙai. To meyasa kenan sunan masarautar ta kasance na adalci?. Muje zuwa zaku ji tarihi a nan zaku fahimci daga ina aka samo matsala ta sauyawar abubuwa.

Fadar Sarauniya wato Qeen Zarina, ita ce zuciyar masarautar zaluncin. Babban katafaren gini ne da ya kai girman wata gari gabaɗaya.

Ga wata katanga dake ɗauke da gicciye-gicciyen bayi da aka kashe don tsoratar da mutane birnin su yi biyayya dan dolensu, in ba haka ba su bi sahun waɗan da aka gicciye suma. Ƙofofin fadar guda uku ne kuma gabaɗayansu suna da ƙaho na zinariya, dik wanda baa bashi izinin shiga ba ya keta ƙofar, fatar jikinsa za ta ƙone nan take, tsabar karfin tsafin Queen Zarina.

Gidajen bayi a cikin kingdom ɗin suna a cikin duhu, babu haske, babu kwanciyar hankali, ana ɗaure su da sarƙoƙi, ana azabtar da su idan suka yi ba daidai ba. Ana azabtar da mutanen da suka yi laifi a wurin, wasu ana yanka su, wasu ana narkar da fatarsu da wani abin sihiri nata dan nuna barazana ga ƴan baya tare da tilasta masu dole su yi biyayya ko kuma suma su riski irin wannan tsastsauran hukuncin. Qeen Zarina tana da wani ɗakin sirri da ke ƙasa (underground) wanda ke cike da abubuwan al’ajabi, kamar wurin bautar da jini dan ƙarfafa mulkinta da sauransu.

Suna da ƙasashe da yawa da suka mamaye, ana bautar da mutanen waɗancan ƙasashe a matsayin bayi. Dik wata ƙasa da ta ƙi biyayya, suna kisan jama'arta gabaɗaya ko kuma su tilasta wa yara da matan su zama bayin fadarta masu yi mata hidima. Queen Zarina ita ce uwar zalunci, tana amfani da doka mai tsauri dan riƙe ƙarfinta. Ba wanda zai iya yi mata ƙarya, domin tana da sihirai da sirri mafi ƙarfi da zata iya gano karya suke yi mata, dan haka dole yake tilastawa mutanenta faɗa mata gaskiya koda sun san kashesu zata yi.

Tana da Jagororin mabiyan sihirinta. Wata macece mai suna bokanya Ruhgara, da ke kula da manyan bokaye da matsafa da ke fadar Queen Zarina. Su ke tabbatar da cewa dik wanda aka kama yana tunanin cin amana, sai a hallaka shi kafin ya yi wani abin.

Ana kiran shugaban warriors ɗinsu da black scorpion, wato bakin kunama mai harbi ɗaya sai lahira. Warriors ɗinta ba mutane ne na yau da kullum kamar yadda kuka sani ba, a'a ita ta ƙunshi mayaƙa marasa tausayin da aka horar tun suna yara don su zama na musamman, gabaɗa warriors ɗin renon black scorpion ne.

Mai tsaron dukiyarta. Wanda ke kula da taskar zinariya, azurfa, da kayan sihiri da aka kwace daga ƙasashe da suka mamaye, wani bakin mutum ne, mai hudun launin fata sosai, ga shi shirgege gwanin ban tsoro, mummunar gaske, fuska babu alamar annuri ko ɗigo, in ya yi maka duka ɗaya sai mutuwa, yana da faɗi sosai.
Sannan warriors ɗinta mutane ne da suka haɗa da, mayaƙan Jini wato mutanen da aka yi wa wani sihiri mai karfin gaske, suna jin karfi da lafiya ta yadda suke ganin babu wani bala'i da zai iya shafan su, kuma idan aka sare su, jinsu na iya dawowa su cigaba da yaƙi, wato saboda da tsafi suke amfani ko an saresu suna iya tashi su koma normal yadda suke su cigaba da yaƙi, waɗan nan mayaƙa ne masu haɗari wanda har yanzu tana kan sihircesu ne, bata fara amfani da su ba, sune mayaƙanta na rukunin farko a ɓangaren haɗari. Wlh ba dan kingdom of power masarauta ce ta Allah sun riki addini ba da ba zasu taɓa sha a hannun wannan azzalumar mata ba! Makircinta ya zarce yadda kuke tinani!!.

Akwai masu take masu baya, wato su kuma mutane ne da aka horar tun suna ƙanana dan su zama tamkar dawakai a fagen karfi dik dan su zama masu saurin kashe mutane babu imani babu tausayi. Maza da mata da ke ɓoye suna satar sirrin wasu ƙasashe domin tabbatar da babu wanda zai iya yin juyin mulki, shiyasa kuka ga har cikin kingdom of power suna da ƴan leken asirinsu waɗan da suke binciko masu menene ke wakana a manyan masarautu.

Magana ta gaskiya babu wanda ya isa ya yi masu tawaye. Mutane basu da ƴanci. Dik wanda aka samu da yunkurin yin tawaye, daga shi har danginsa dikka sai an hallaka su. Basa son wata daula ta yi ƙarfi ko kwatansu. Dik wata ƙasa da take kokarin girma ko samun ƴanci, warriors na masarauta suna zuwa su mamayesu su kuma kwace komai. Yadda kuka san Queen Zarina renon BLACK TIGER ce, wlh zalincinsu kusan ɗaya, sai dai Black Tiger ya fita haɗari ne da karfin tsafi.

Sannan tana sihirce mutane. Idan aka samu wani yana tunanin cin amana, mayakan sihiri suna iya hango hakan kafin ma mutum ya furta shi, sai ta sa a sihirce sa, a mayar da shi wani gunki ko kare ko dai wata ƙasƙantacciyar dabba a ajiye shi a kofar gate ɗin farko na shigowa masarautar dan ya zama ya kare a kaskance kuma ya zama izina ga masu tasowa. Wanna ba dalilin yasa ƴan birnin suke yi mata biyayyar dole!.

Masarautar tana da zinariya fiye da kowacce ƙasa except birnin BLACK WORLD. Sannan a tsarin Queen Zarina babu wata ƙasa da za ta iya yin ciniki ko kasuwanci ba tare da izinin ta ba, muna magana a kan kasashen da ta mamaye, kasuwancin dik waɗan da suke kewaye da ita a karkashin sarrafawarta suke yi. Bayin basu da wata ƙima da daraja, a haka kuma wai sun fi talakawar da ake mulka kima, idan ka zama bawa a wannan kingdom ɗin, to ka san rayuwar ka ba taka bace. Wannan kingdom da fadar Sarauniya tana da ƙarfi fiye da sauran ƙasashe. Za su iya mamaye kowace ƙasa, kuma babu mai iya taka masu birki sai KING ZUHAIR, wato KINGDOM OF POWER sune kawai suke zama babbar barazana ga ZARINA! Black Tiger kam bai ma san da wanzuwan Zarina a doran duniya ba!.

Doka mai tsauri, dik wanda yayi gaban kansa ko ya yi magana kan zalunci, ana hukunta shi da azaba mai tsanani. Masu iko sunfi kowa daraja. Dik wanda ba shi da arziki ko gata, rayuwarsa bata da kima. Ana amfani da bayi da kuyangu. Akwai kasuwannin bayi da ake siyar da su kaman dabbobi, kuma manyan gidaje sun cika da kuyangu da ke aiki ba dare ba rana kamar injuna.

Mu leƙa cikin fadar Sarauniya ZARINA mai cigiɓi cigiɓin nau'ikan azaba. Babban gini ne mai girma da ɗan duhu. An gina shi da baƙin dutse na zinariya, yana da hasken fitila ja da launin shunayya. Akwai manyan azurfa da zinariya da aka ƙawata ginin da su. Sarautar ta tara dukiya daga harajin da ake karɓa daga talakawa da ƙasashen da suka mamaye, bayin Allah su sha wahala su yi noma sai su karɓe kaso biyu cikin uku na amfanin gonar su barsu da kaso ɗaya wai haraji, hakan yasa rumbun hatsin QUEEN ZARINA ya cika har yana amai da kayan abinci, girman wannan rumbu kuwa ya kai girman gari guda daga cikin garuruwan kasar. Amma hegiyar matar nan bata sadaka bare kyauta, gara ta bar abincin ya yi ta cike koma lalacewa ne ya yi a kan ta bawa talakawa!!.

Fadar ta cike take da bayin dake hidima. Kowanne yanki na fadar akwai kuyangu da bayi masu bauta mata. Babban zaure mai girma. A nan ne take karɓar baki da shari'a, akwai dogarai masu sanye da rigunan karfe da takubba kamar warriors. Sai ɗakin sirri a cikin fadar, wani ɗaki ne da ba kowa ke da damar shiga ba, anan ne take shiryawa ko boye wasu sirrikan mulkinta.

Bari mu taɓo tahiri a kan Queen Zarina wadda kuka jima kuna jin labarinta ba tare da kun san menene ainahin tsamar dake tsakaninta da Kingdom of power ba, bama ku san wacece ita ba, shin yarinya ce, babba ce, matar aure ce, ko dai bazawara or budurwa, dik baku sani va, to yanzu labari ya juyo ta kanta, bari mu faɗa maku ya take domin yanzu story zai juyota.

Kingdom ɗin nan ba kawai mai arziki bane, yana da cikakken iko a duniya. Nasan ko a iya haka kun fahimci dalilin da yasa a koda yaushe suke cikin takun saƙa da King Zuhair, dan shi baya barin mulkin zalinci ta cigaba da tafiya.

Tabbas kujerar mulkin da Queen Zarina take zama banbancinsa da na King Zuhair kalilan ne, ita ma nata diamond seat ne, sai dai na shi ya fi nata girma sa ƙawatuwa. Ta dake saman kujerar nan tana haɗe cikin alkyabbarta launin gold mai daraja, ba karya kyakkyawar gaske ce, zubin Iceland lady, jajir da ita kamar ka latsa jini ya fita, ga gashin kanta light brow, ka zalika kwayar idanunta light brown, babbar macece ba yarinya ba, ko dai in ce uwa, sai dai yanayin zubin halittarta zaka yi zatan irin ƴan 25 to 30 years ɗin nan ne. Da ka kalli face ɗinta kaga zallar madarar rashin imani, babu annuri kuma babu dariya ko kaɗan, doguwa ce sosai dik da take a zaune, kun san matan Iceland da shegen tsawo sosai Masha Allah.

Gabaɗaya amintattunta da manya manyan bokayen cikin fadarta suna ciki, daga gefen damarta wata kyakkyawar matashiyar budurwa ce zaune a saman kujera ta mulki irin wanda Queen take kai, sai dai nata kujerar bai kai na Queen girma, kima da kuma daraja ba. A shekaru yarinyar nan ba zata wuci 17 years ba, ta tsantsara kyau cikin shiga na ƴaƴan manya manyan sarakuna da ake ji da su, ba karya kyakkyawar yarinyar ce irin uwarta sak.

Wani kamshakin dakakken namiji mai kirar lafiya da karfi ne ya danno cikin fadar, cikin tafiyar jarumta da nuna isa, yana cikin shiga irin na manya manyan sarakuna masu karfin iko, da ka gansa babu tambaya kasan basarake ne, jiga jigan warriors huɗu suna take mashi baya har ya ƙariso saman stage da Queen take, yana shigowa gabaɗaya manyan cikin fada suka miƙe tsaye except Queen and her daughter.

A saman kujerar gefen damanta ya zauna, yana zama kowa ya koma ya zauna, yana zama bai fi da minti biyu ba sai ga wani zaƙwaƙurin cikakken namiji mai zubin jarumta shi ma ya shigo, da alama family ake san haɗawa kafin ayi abin da za'ayi, dan wannan matashi ma dai falimy ne, saboda shigar dake jikinsa irin ta Prince.

Gefen wannan matashiyar budurwa saman kujera ya zauna. Gabaɗaya ko'ina tsit kake ji tamkar babu halittu a cikin fada. Queen hannunta na rike da wani ɗan karamun akwatin lu'ulu'u mai shegen kyau yana kyalli launin gold.

My people's a tinaninku a kingdom of power ake cin amana da munafurci ko? To kun yi kuskuren tinani, bana jin akwai kingdom ɗin da ya kai nan cin amana da munafurci dik wannan uban tsaro da kuka gani da izayar da Queen Zarina take yi wa masu tinanin cin amana kafin ma su aiwatar, wlh dik da haka ta ko'ina akwai makarkashiya da suka mamayeta, ku dai mu je zuwa.

ZARTAR, shi ne shugaban bokayen a ɓangaren yanke hukunci a kan abin da ya shafi bayi da sauransu. Gabaɗaya fada ta zuba mata idanu suna jiran jin mezata ce. Ita kuwa shiru ta yi na tsawo a kallah good ten minutes kafin ta ɗan kara dakewa a cikin alkyabbarta zubin Uk, cikin kakkaifar murya ta fara magana kamar haka. "Zartan har yanzu kana nufin baku iya gano in da wannan makulli yake ba? Dik karfin ganinka, dik karfi eagle eyes ɗinka, amma baku iya sanin in da yake ba?".

Kasa gabaɗaya bokayen fada suka yi da kansu, Zartan da ya kasance wani tsohon dattijo mai farar gashi kal, ga shi dogo da shi zubin Uk, idanunsa tamkar na mage gwanin ban tsoro, yana sanye da fararen kaya da wani dogon mayafi dake ja har ƙasa, gashin kansa da kayan jikinsa iri guda ne, yana da wani tabo a goshinsa kamar zanen katan maciji ya fasa kai. Zartan yana ɗaya daga cikin Kim family, Kim family kuma su ne familyn Queen Zarina kenan, kazalika yana da kafa a fada sosai.

Miƙewa tsaye ya yi cikin girmamawa ya ce mata. "Ina kara miƙa hakurina a gareki, dik iya hangen da zamu yi mun hakanga bamu ga wannan makulli ba, amma dai tabbas wannan makulli baya kingdom of power, tabbas yana ta wani wajen ne na daban".......... Tsufa ta fara yawaita a tattare da shi, domin kuwa maganarsa ma bata fita sosai. Mai da kallanta a kan wannan sarki da ya shigo ɗazun ta yi, a natse ta ce. "Baka da abin faɗe ne a kan wanna case ɗin Ude?"...... Shiru ya ɗan yi kafin ya amsa da. "For now dai babu, amma abin da zan ce shi ne zamu yi nasarar mamaye ko'ina, mu cure duniya ya zama abu guda kuma mu mulketa, ko Zuhair yana so ko baya so dole sai ya zube gwiwowinsa a ƙasa ya lashi kasan takalmarmu ya kuma goge mana saman, daga karshe ya zama bawanmu".

Wani irin shu'umin murmushi ta saki saboda Ude ya faranta mata ranta sosai, tana matuƙar yunwar ganin ta cure duniya ya zama abu guda ɗaya, babu wasu kasashe dik a zama ɗaya, sannan ta zama ita ke mulkarsu dikka, ta murza kambunta ta juya kowa, dik wanda yake san sanyaya ranta to ya yi mata kamalai irin wanda Ude ya yi mata a yanzu, koda hukuncin kisa tasa aka yankewa mutum in dai ya yi mata irin kalaman Ude tana iya yafe mashi.

"Amma ya batun Nieelarh da MUZAFFAR FAMILY fa?. Cewar Queen kenan..... Nieelarh ƴar cikin Queen Zarina ce, ita ce kuma wannan kyakkyawar matashiyar yarinya dake gefenta. MUZAFFAR FAMILY wasu jiga jigai ne daga cikin birnin waɗan da su ke da arzikin dik wani abincin da ake ci a cikin birnin, sannan sune politics family dake kasar gabaɗaya, mutane ne masu karfin iko da isa, da ace yau zasu ɗauke wa birnin Justice dik wata tallafi hakika da birnin ta cika da yunwa matuƙa. So head of the familyn wato MUZAFFAR ya kasance mutum mai girma a fada, sannan mutum mai girma a birnin, dik bala'in Zarina tana raga mashi, wasu daga cikin mutanen birnin suna cewa akwai wata alaƙa a tsakaninsu, wasu kuma suna cewa saboda karfin musuluncinsa yasa bata iya tsafacesa har ma take shakkarsa.

To dik bama wannan ba, haƙiƙa karfin musuluncinsa yasa bata iya tsafe familyn Muzaffar har ta samu damar sarrafasu san ranta kamar yadda take yi wa sauran jama'a, amma ba hakan ce tasa take shakkar Muzaffar family ba, akwai wani sirri nata da shi dattijo Muzaffar ya sani wanda kuma ga dukkan alamu tana tsoron ya fasa kwai shiyasa take shakkarsa sosai, to a halin da ake ciki yanzu ɗaya daga cikin Muzaffar family ya nuna ra'ayin yana san ƴarta Nieelarh wanda kuma dan dole ta amsa da ta yarda da batun, amma ta ƙarƙashin ƙasa tana neman ta yadda zata yi ta warware wannan batu, saboda ba zata yarda haɗa jini da musulmai ba a cewarta, ta kuduri niyar ko ta halin yaya sai ta ruguje wannan batu, sai dai kuma ba zata iya yin fito na fito da Muzaffar family ba!.

Amma me kuke tinanin zai kasance sirrinta da bata san ya fashe kowa ya sani da har take daurewa ta yi wa Muzaffar family sauki haka?.

Ɗaure fuska sosai Ude ya yi kafin ya amsa da. "Haƙiƙa Nieelarh ba zata shiga Muzaffar family ba, dan hakan ƙasƙanci ne da faɗuwa a garemu". With his full confidence ya yi maganar, haƙiƙa yana da tabbaci a kan maganarsa!. Ɗan Nieelarh fa ƴarsa ce, ba zai bari hakan ya faru ba!.

Jinjina kai ta yi cike da farincikin amsoshin Ude a ranta, sannan ta miƙe tsaye, cike da bada umarni ta ce. "Zartan ku cigaba da binciken ina Spender yake ta maduban dubanku, ku tabbatar kun yi gaggawar binciko shi, Ude ina da magana da kai, ka sameni a ciki main parlour". Tana kai karshen maganar ta yi gaggawar juyawa alkyabbarta na jan ƙasa sosai ta nufi wani katafaren diamond door da zai sadata da cikin katafaren gininsu na alfarma wanda ya kasance shi ne family part ɗinsu.
Gabaɗaya mukarraban fada suka miƙe bisa girmamawa a gareta har sai da ta bar fadar sannan suka koma suka zauna. Tana fita kofar wasu mahaukatan zaƙwaƙuran warriors suka take mata baya zuwa kofar shiga cikin part ɗin nasu!.

Cikin kakkausar murya mai amon bada umarni Ude ya kara jaddadawa bokayen royal palace ɗin abin da Queen ta faɗa, daga haka ya miƙe ya bi bayanta ya bar Nieelarh da Beer wato kanin Zarina ne shi ɗin.

Kai tsaye katafaren parlournsu na alfarma Quren ta shiga, still dai hannunta rike da wannan akwatin. Saman wani luntsumemen sofa mai zaman mutum uku ta ajiye akwaitin, sannan ta fara safa da marwa a tsakiyar parlourn tana ɗan bubbuga hannayenta cikin juna, alamar tana cikin damuwa..... A haka Ude ya shigo ya sameta, cike da kula sosai haɗe da nuna damuwar ganin halin da take ciki ya ce. "Lafiya kuwa ranki ya tsananta fiye da kowacce rana?".

A gaggauce ta juyo da kallonta a kansa, cikin kakkaifar murya ta amsa mashi da. "Ba zai taɓa kasancewa lafiya ba ka ganni a tsaye, kasan da cewa in dai bamu samu Spender ba tabbas Muzaffar family sai sun ɗauke Nieelarh daga garemu, sannan zata iya shiga wannan addini nasu, dik bama wannan ba, damuwata shi ne Zuhair ya tsugunna ya goge mun takalma, na mayar da shi bawa na dattijo mai goge goge a

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login