Showing 321001 words to 324000 words out of 403653 words
sosai a cikin masarautar da kewaye, sannan a shirya gagarumin bikin da ba'a taɓa yin irinsa ba, muna tashi wannan taro a turawa manya manya sarakunan nan gabaɗaya gayyata, wannan nauyi ya ta'allaka ne a wuyarka aminta". Ya kai karshen maganar yana bin amintan da kallo. Cikin girmamawa ya risinar da kai haɗe da cewa ya karɓi umarni. Dawo da kallonsa a kan commander King ya yi. "A tsananta tsaro sosai, sannan ka shirya dakaru yadda yakamaya domin ana gama bikin nan da kwana biyu zaku shafe Zarina daga doran duniya, zalincinta ya kai matakin da babu gargaɗi ko ɗaga kafa, mun daka mata warning har ya fi sau uku, dan haka mun cike ƙaida, a rufe babinta kawai!!".
Jinjina kai commander ya yi, cikin girmamawa ya karɓi umarni, sai dai fa kowa a cikin wajen yasan commander ya canza, ya shiga cikin yanayi lokaci guda. Sarai King ma ya lura da canzawar, amma sai ya yi tamkar bai gani ba, ya cigaba da jawabinsa da irin tsare tsaren da yake da ɓuƙata a gidan, gagarumin biki za'a gudanar, bikin ƴar Auta guda! Dole sai an shirya, za'ayi taran da ba'a taɓa yi ba.
Har aka tashi wannan zama commander bai sake cewa uppan ba, ya risinar da kansa ƙasa yana sauke numfashi a hankali hankali, a ransa yake faɗin ba zai iya sanar da Hoorain ga abin da yake wakana ba, dan za'ayi babban tashin hankali sosai.
Ko da ya koma ɗaki ya samu Hoorain bayan an tashi zaman, mannne da waya ya iskosa, hakan yasa jikinsa ta kara mutuwa, cikin gaggawa ya juya zai fice daga ɗakin. Hoorain ɗin ne ya dakatar da shi ta hanyar cewa. "Abbo Gimbiya tana gaidaka". Jinjina kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, cikin sauri ya nufi kofar fita. "Abbo Gimbiya zata yi magana da kai". Hoorain ya sake dakatar da shi.
Zuciyarsa tamkar zata fashe, hankalisa a tsananin tashi, ba dan ya so ba ya juyo ya dawo, wayar ya karɓa tare da mannata a kunnensa. Tsaresa da kallo Hoorain ya yi yana nazarin fuskar mahaifin nasa, take ya fahimci akwai wani abin dake damun baban nasa.
"Abbo barka da safiya". Daga can Auta ta faɗa, sai sakin murmushi take yi, tana zaune daga ita sai wani simple gown mara nauyi da ya tsaya mata a iya gwiwa, hannun rigar ɗan siriri kamar na vest, ta ɗaure throw pillows guda biyu a saman laps ɗinta, tana zaune bakin ruwan da dolphins ɗinta suke ciki, sai janta da wasanni suke yi, amma taki kulasu. Ita kuwa Pretty sarkin sakalci da shiririta tana sama tare da Smart, taki yarda ta rabu da shi, dan tsoro, dik in da zai je kafarta ƙafarsa, yanzu haka yana sama gabaɗaya yana gym, ita kuwa tana zaune saman chair tana kallansa, dan dole Smart ya fara yin sabo da ita, yanzu har yana jinta a cikin ransa, kun san idan mutum yana yawan zama a tare da kai, dole yau da gobe ka fara jinsa a cikin ranka.
"Barkanki dai Gimbiya, fatan kina lafiya ya shirye shiryen azumi?". Commander ya tambaya yana ɗan juyawa, dan baya san kallan da Hoorain yake yi mashi, yana tsoron ya fahimci wani abin, bai san tini ya harbo jirginsa ba. "Abbo ina nan lafiya, na yi kewarku sosai, ina san dawowa ko dan na ganku". Ta faɗa cike da zumuɗi. Rasa abin faɗe commander ya yi, dan gabaɗaya hankalinsa baya jikinsa, to kawai ya iya ce mata, nan ma sai da ta kara maimaita maganarta a zuwan bai ji me ta ce da farko ba. Tin bata yi sallama da shi ba ya miƙewa Hoorain wayar ya yi gaggawar ficewa daga ɗakin.
Manna wayar a kunne Hoorain ya yi kallansa a kan Abbon nasa, a hanzarce ya ce. "My princess zan sake kiranki anjuma, yanzu bari in ɗan yi wani abin". Cike da muradin san bin bayan Abbonsa ya ji meke damunsa ya yi maganar....... Kai ta fara girgiza mashi tamkar tana a gabansa. "No my Hero, ni ban yarda ba, kwata kwata fa ko two hours muna waya bamu yi ba, ni dai Allah a'a, ka bar dik abin da zaka yi ɗin sai anjuma, now is my time". Nisawa ya ɗan yi. "Ai ko iya wannan shagwaɓar ta isa tasa dole na in ƙasa iya katse kiran, Hoonairata kina narkar mun da zuciyata da shagwaɓarki".
"Uhm uhm ba na ce kai ma ka mun kaki ba, naku sa yin fushi da kai, haka jiya na ce ka mun murmushi ka ce baka iya ba ko?". A shagwaɓe sosai ta yi maganar. Komawa ya yi ya kwanta, salanta yasa ya manta da yana san bin bayan Abbonsa, ɗan mirginawa ya yi ya kwanta ruf da ciki, cike da tsantsar madarar kaunarta ya ce. "Ban iya bane ne, amma kema kin san da na iya dole zan yi maki, but ki koya mun yadda ake yi zan yi maki". In a low voice sosai ya yi maganar, kamar wani yana yi mashi laɓe..... "My Hero ni nasan ba zaka taɓa iya yi ba, ɗan garama shagwaɓar kila zaka iya kwatantawa"......... Murya kamar yana cikin mayen madarar kauna ya ce. "To mu yi video call sai ki koya mun shagwaɓar, zan yi maki, kece fa, ai dolena in yi". Bin kayan jikinta da kallo ta ɗan yi kafin ta ɗan turo baki kaɗan. "My Hero ka bari zuwa dare ko anjuma sai mu yi video call ɗin, yanzu babu k........". Ƙasa ƙarisa maganar ta yi, saboda ta ji nauyin ce mashi babu kayan arziki a jikinta, kuma tasan idan ta faɗi hakan ma kishinsa ne zai motsa ya yi fushi, dan shekaran jiya da suna waya ya jita tana magana da Robbot mai kawo abinci a take a wajen ya ce mata wanene, da buɗar bakinta sai ta ce mai girki ne, aikuwa taga kishi, dan cikin ɓacin rai har mantawa ya yi ya daka mata tsawar a kan me zata yi magana da mai girki namiji? And babu masu girki mata ne sai maza? Take ya hau ya fara masifar da bai san ya iya ba, ya kuma ya manta cewa princess ɗinsa ce, kishi ta rufe mashi idanu. Da kyar ta shawo kansa, da kyar ta samu ya ɗan sassauto har ta sanar da shi Robbot ne ba mutum ba, dik da haka ya ce baya san ta rinƙa magana da shi, ai namiji ne koma Robbot ɗin ne, dole ta yi alkawarin ba zata sake ba, ta kuma bishi da love word masu zafi, a takaice dai a wannan lokaci bai iya yin soyayyar ba, dik da kalaman da ta zuba mashi, ransa ya rigada ya ɓaci sai kawai ya ce mata sai anjuma, ya katse kira ya zauna yana huci shi kaɗa.
Wannan dalilin yasa bata ce mashi babu kayan arziki a jikinta ba, dan kishin zata motsa, zai ce akwai maza a gidan, tasan rigimarsa bata karewa a kan kishi, har yau idan ya kirata sai ya ce ina wannan Robbot ɗin, kuma yana tambaye fa kawai dan ya ji shin tana kusa da shi ne ko dai ta yi nesa da shi kamar yadda ya ce mata, kai Hoorain ba dai kishi ba, ko da yake jinin Modarawa haka suke dikkansu! Balai'n kishin tsiya daga mazan har matan!.
Kamar zai tambayeta meyasa bata san su yi video call a yanzu, sai kuma ya basar da cewa. "To shikenan Allah ya kaimu, ki gaida mun da Pretty and Yah Omerish". Da okey ta amsa mashi kafin ta ce. "To ka bani na barci". Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke har sai da ta jiyo shi kafin ya manna wayar da ɗan bakinsa ya bata sumbata. Ɗan lumshe idanunta ta yi tamkar da gaske ya yi wa kumatunta, a hankali ita ma ta bawa wayarta sumbatar, wani irin dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, har a ransa ya ji kamar da gaske ta yi mashi, ya ji daɗi sosai. Da kyar ya iya katse kiran, ya jima a kwance kafin ya tashi da kyar ya bi bayan Abbonsa.
A ɓangaren King kuwa, shirye shirye suka fara yi babu kama hannun yaro, suna gama zama yasa Momma ta kira Smart ta bashi umarnin a kan ya dawo da Auta, nan da gobe su dira a kingdom of power, sai dai King ya ce kada su kuskura su sanar da Smart ɗin auren Auta za'ayi, a ɓoye mashi sai ranar ɗaurin aure ya ji a masallaci, ita ma Auta a ɓoye mata sai an ɗaura auren sannan a bayyana mata, a dawo da ita ta shiga dilka da halawa game da kunshi da sauran gyare-gyare.... Kam bala'i, lallai King ya shirya da zafansa, wato sai an ɗaura aure zasu sani, tab akwai cakwakiya.
Momma ta ji zafin hakan, amma yazamar mata dole ta bi umarnin King, dole su hakura.
-------------------------------------------------🔥
Rasa mafita yasa shi nufar kofar da nufin ya buɗe kawai. Sai addu'a yake yi Allah yasa ba shigowa ciki Omaid zai yi ba, ga shi ya cire kayan jikinsa, ga mace kwance a saman bed ɗinsa, me za'a zarga kenan? Ya gefawa kansa tambayar. Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki haka yasa hannu ya buɗe door ɗin. Suna haɗa ido Omaid ya ce. "Yah Omar barci zaka yi ne?". Ai bai san time da ya gyaɗa mashi kai ba, alamar e barci zai yi. "Dama na zo mu yi hira ne fa, yau na ɓata da Obaid, amma tin da barci kake ji no need, bari in je wajen Momma kawai". Kara langwaɓar da kai guyson ya yi, ya ƙara shagwaɓe fuska alamar da gaske barcin yake ji. A hankali ya jinjina kai yana ƙaƙalo hammar dole. Juyawa Omaid ya yi yana yiashi good night. Ai yana barin wajen ya mai da kofa ya garƙame tare da juyawa da gudu ya koma cikin ɗakin, saman gadan ya haye ya zauna tare da buga uban tagumi tana tinanin meyakamata ya yi ne?. Nan fa ƙwaƙwalwarsa ta bashi amsar ya bari sai dare ya yi sosai, kowa ya yi barci sai ya mayar da ita bedroom ɗinta. Na'am ya yi da wannan shawara, sannan ya fara binta da kallo, gabaɗaya ta tafi da tinaninsa, bare ma ɗan bakin tsiwar nan tata, ga shi ɗan ƙaramin amma sai iya fito da magana. Hannu ya kai saman ɗan bakin nata ya ɗan ja da ɗan karfi kafin ya ce. "Masifaffa kawai!". Ya yi maganar idanunsa a kan yatsun hannunta dake zara zara ƴan sirara. Haka ya yi ta bi yana karewa surar jikinta kallo har dare ta tsala, sannan ya miƙe ya zura jallabi a jikinsa. Ya nufo waje, sai da ya gama leƙe leƙensa ya tabbatar babu kowa, sannan ya zo ya ɗauketa ya mayar da ita bedroom ɗinta. Wani irin ajiyar zuciya ya rinƙa saukewa time da ya dawo bedroom ɗinsa, saman bed ya haye da nufin ya yi barci, yau ko sleeping dress ba za'a saka ba, sai dai kuma barcin sam sam taki zuwa, tinaninta ne kawai fal a cikin ransa har kusan asuba, yarasa dalilin dayasa yake tinaninta sosai haka. Daga karshe dai ya miƙe ya ɗauro alwala tare da hayewa saman dadduma ya fara nafilfili tin da kyan Mahreen ya azalzali zuciyarsa ya hanasa rintsawa.
-----------------------------------------------🔥🔥🔥
Ko daga ina ya koyi yiwa mata wanka? To dai yau ya yi wa Mahnoor wanka, kuma da kansa ya bata kayan da yake so ta saka, sannan ya rungumeta suka kwanta a tare. Zuciyarsa fara tas yau, ya yi barci mai shegen daɗi, ita ma ta yi barci mai shegen daɗi, yau gata ga Hammanta. Washegari da safe, bayan sun yi sallar asuba dama sun koma barci, karfe 7 ta farka, cikin sanɗo ta kwaci kanta daga garesa, a hankali ta sauko kasan bed ɗin, kai tsaye ta nufi waje, bedroom ɗinta ta koma, alkyabbarta ta ɗauko ta ɗaura a saman kayan jikinta, cikin sauri ta fita ta nufi bedroom na momma, wai dan ma kada momma ta gane a tare da mijinta ta kwana, irin ta nuna a part ɗin momma ta kwana, dan sun yi da momma ɗin a kan ba zata koma wajen Jaish ba sai ya zo ya bada hakuri, shi ne wai zata yi wayau.
Zaune ta isko momma a saman King sofas set masu bala'in kyau na cikin bedroom ɗinta, hannunta rike cup na cappuccinon tana sha. Binta da kallo ta yi, sosai Mahnoor ta shiga shakku da kame kame ganin irin kallon da momma take binta da shi. Daurewa ta yi ta kariso gabanta ta tsugunna dan ta kwashi gaisuwa. Still binta da kallon mamaki Momma take ta yi. "Ina kwana Momma?".
Shiru momma bata amsa gaisuwar ba, wani irin faɗuwar gaba Mahnoor ta ji, addu'a ta shiga yi Allah yasa ba fushi Momma take yi da ita ba. A dai'dai wannan lokacin Omaid ya shigo, a kusa da Momma ya ƙariso ya zauna. Yana sauke kallansa a kan Mahnoor ɗin ya ce. "Momma wannan mahaukaciyar fa?". Shiru dai Momma bata tankasu ba, kallanta a kan Mahnoor babu ko kyaftawa, kuma ba kallan tuhuma take binta da shi ba face kallan mamaki, abin abin dubawa ne!.
Zama Mahnoor ta yi a kan kafafunta, ta rasa abin yi, sai kawai ta yi ƙasa da kai tana jiran hukuncin da za'a yanke mata....... Cikin natsuwa ya yi sallama ya shigo, yana sanye da white arabs jallabiya, a kusa da momma shi ma ya je ya zauna, ya wani ɗaure fuska kamar ba Jaish da ya gama holewarsa daren jiya ba, har mamakinsa Mahnoor ta yi, ya wani basar kamar bai ganta a wajen ba, cikin ladabi da biyayya ya ɗagawa Momma gaisuwa.
Nisawa ta yi tare da maido da kallanta a kansa, a hanzarce ya yi ƙasa da kai yana ɗan shafa kansa. Amsa mashi gaisuwar Momma ta yi tana kare mashi kallo tamkar mai san gane wani abin. "Momma dama zan je office ne na ce bari mu gaisa first". Ya faɗa yana satar kallan Mahnoor dake kallan ƙasa. Tini Omaid ya natsu tsit kamar babu shi a wajen, da zai yi wa Mahnoor walaƙanci, da ganin Jaish yasa ya janye kalamansa ya bita da ido kawai........ "To shikenan, idan ka je office ɗin ka gyara shirin dake office ɗin naka, dan jeren da ka yi a wajen bai yi ba sam sam". Cewar Momma. A hanzarce ya ɗago ya kalleta jin abin da ta faɗa. Hararar wasa ta wurga mashi kafin ta yi mashi alama da Mahnoor da ido. Da sauri ya yi ƙasa da kai, kunyar rashin kunyar tasa ta motsa!..
Sallamar guyson ne tasasu kai kallansu a bakin kofa dikka har da Mahnoor ɗin. Ai yana sauke idanu a kanta bai san time ɗin da ya kwashe da dariya ba, har da rike ciki yana duƙawa ƙasa. Kallan mamaki ta bisa da shi, ta rasa gane me yake yi wa dariya. Ai Momma ma bata san time da murmushi irin nasu na manya ya kubce mata ba ganin yadda guyson yake dariya, dama tun ɗazun dariya kamar zai haukatata, da kyar ta iya dannewa ta ɓoye, sai ga shi guyson ya zo ya sanyata murmusawa.
Ɗan tsuke fuska Mahnoor ta yi tana bin guyson da kallo. Cikin dariya ya ce. "Aunty Mahnoor wace mahaukaciyar ce ta yi maki wannan make up ɗin? Kin ganki kuwa? Ko aljana Bilkisu sarkin kwalliya bata gwada maki hauka ba yau". Ya kai karshen maganar tare da kara kwashewa da dariya mai sautin gaske.
A hanzarce Mahnoor ta kai hannu ta shafi face ɗinta, jin alamar kwalliya yasa ta yi gaggawar ɗago ido ta kalli Jaish. A hanzarce ya kawar da kallonsa daga kanta kamar ba shi ba.
"Yah Omar kana nufin kwalliya aka mun?". Ta faɗa tamkar zata yi kuka. "Aww dama baki san da kwalliyar ba?". Cikin dariya ya yi maganar!. Takaici kamar Omaid ya kifa mata mari, shi kallan wawuya yake yi mata, ya tsani wawta a rayuwarsa. Miƙewa tsaye ta yi, jiki ma ɓari ta isa wajen guyson. "Yah Omar wlh ban san anmun kwalliya ba, faɗa mun ya na yi?!". A rikice take maganar.
Har lokacin dariya taki sake shi. Hannunta ya riƙo tare da janta suka nufi gaban tampatsetsan mirror Momma. A wajen ya tsayar da ita tare da nunata ta cikin mirror da hannu yana cigaba da dariya ya ce. "Look at you". A hanzarce ta kai kallanta kan mirror. Ai a miliyan ta wani irin zaro idanu waje, take kuma ta ji wani irin kunya ya kamata, gabaɗaya face ɗinta uban kwalliya na mahaukata. Kunya tamkar ta natse ƙasa, ta gagara juyowa ta kalli su Momma, sai dariya guyson yake cigaba da yi, ta tsaya a wajen tsit kamar daskararren man shanu.
Kallan Jaish Momma ta yi tare da cewa. "Me ta yi maka da ka yi mata irin wannan kwalliya haka?". Ƙasa ƙasa ta yi maganar ta yadda babu wanda ya ji sai ita da shi ɗin. Nan fa shi ma kunyar rashin kunyar tasa ta motsa, ƙasa ya yi da kai, kamar yana tsoron yin magana ya amsa da. "Babu kawai na tina abin da ta taɓa yi mun ne a garinsu". Cike da mamaki Momma ta bishi da kallo. "Kenan yanzu ka tina wacece ita a gareka?". Kai ya ɗan jinjina alamar e ya tina, kuma ba tin yau ma ya tina ba, tin ran zuwan Smart, akwai wani rana da ta shiga ɗakinsa a lokacin yana rike da wayarsa, idan baku manta ba har ya miƙe tsaye yana kallan wayar kuma yana kallanta, tin a wannan rana ya tina rayuwarsu na kauye, ba komai yasa ya tina ba face kallan video bikingsu da ya yi a media, ranar da aka yi bikin in baku manta ba na ce maku akwai masu vivo wato ƴan gayun kauyen da suka rinƙa ɗaukarsu a video, to a wannan rana ya tina wacece ita a garesa ta sanadiyyar wannan video, amma ya yi shiru bai nuna mata kamar ya tina