Showing 27001 words to 30000 words out of 403653 words

Chapter 10 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

113

kinga in abin da ya kawo ki nan kenan tashi ki bamu waje".

Ɗan zaro idanu Fanan ta yi like surprise haka. "Aunty Sarina su Yah Jawad ne fa!".

"To sai aka yi yaya idan su ne? Nace su mutu idan suka ga dama! Ni ki rabu dani da abin da nima yake rai'na".

Da sauri ta dawo da kallonta a kan Mammie. "Mammie kin ji abin da Aunty Sarina take faɗe ko? Su Yah Jawad take cewa su mutu fa".

Ta yi maganar cike da yakini da sa ran Mammie zata yi wa Sarina faɗa kuma ita ma ta ji babu daɗi a kan maganar, ina ai sai ta ga saɓanin tunaninta, dan kuwa ɗaure fuska sosai mammie ta yi kafin ta ce.

"To sai me dan ta ce hakan?".

Zaro idanun sosai Fanan ta yi, she was so surprised jin amsar Mammie tasu.

"Mammie ban gane ba!". Tana kara zaro idanu ta yi maganar.

"Ba zaki gane ba ai, mu kingan mun nan ba su Jawad bane a gabanmu, kowa ma a cikin Kingdom ɗin nan in ya ga dama ya mutu!!". Cewar Sarina uwar rashin kunya.

Kasa yin magana Fanan ta yi, ta zuba masu ido tana mamakin jin furucinsu.

"Ke wai baki ma san dik abin da yake faruwa da su Mammie ɗin ce ta haɗa ba ko?". Cewar Sarina.

A miliyan Fanan ta kara zaro ido waje tamkar kwayar idanunta zasu faɗi ƙasa haɗe da furta kalmar what!! Ba tare da ta san kalmar ta fita daga bakinta ba.

"Kwarai kuwa, mammie ce ta haɗa dik wanna cakwakiya, dan haka ki wuce ki bamu waje uwar ƴan tausayi!". Cewar Sarina again.

Yadda kuka san ruwa ya cinye Fanan, tamkar babu ita a wajen ta yi shiru, al'ajabi ya kusa kasheta.

"Tashi ki fita ki bamu waje tattaunawa muke yi uwar masu tausayi". Cewar Mammie.

Tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki ta mike, sumumui sumumui ta nufi kofar fita.

"Sakarya kawai wadda bata san ina yake yi mata ciwo a jikinta ba, shashasha wai ke uwar tausayi! Zaki mutu babu wanda ya ji sautin kukanki in dai kika ce tausayi zaki yi a rayuwarki!!" Cewar Sarina dake binta da wani matsiyacin kallo.

Sarai ta ji abin da Sarina ɗin ta faɗa, amma bata juyo ta tanka mata ba ta nufi waje kawai tana yi masu addu'ar shiriya.

"Ya isa haka my daughter". Cewar mammie ga Sarina.

"Allah Mammie Fanan wawiya ce wacce bata san ciwon kanta ba, ni bakanta mun rai take yi wlh".
Tana magana tana hararar kuyangar dake gabanta tana wanke mata kafa, kamar kuyangar ce ta yi mata laifi.

Kunsan Fanan a part ɗin Momma take yawan zama dan ta sami soyayyar Jaish, da farko ita ma zuciyarta ya fi karkata a irin halin mammiensu, amma zamanta da momma ya canzata izuwa mutumiyar kirki, kunga kuwa ko bata auri Jaish ba ai ta sami babban abu da zai iya zame mata makamin tsira duniya da lahira, wato halayyar kirki haɗe da ilimin addini kenan, ai kunga ta tsira ta kuma ci ribar zamanta da Momma ko?!.

Tana barin part ɗin nasu ta wuce King part, kai tsaye ɗakin gyaran jikin su Aneesa da su Mama Haulat suke girka su a can ta nufa, jikinta dik a sake baiwar Allah.

Ta sha madarar mamakin rashin samun Chuchu a ɗakin, Aneesa kawai ta samu, ta so tambayarta ina Chuchu and Auta sai kuma ta sami Aneesa tana murzar kuka, shanye tambayar ta yi a ranta tare da hayewa saman bed ɗin, cikin sanyin murya ta fara rarrashin Aneesa tana bata baki har da gaya mata wata bata auran mijin wata.

Sam Aneesa taki kulata, dan ita kaɗai tasan me take ji a cikin zuciyar nan tata, tana san Rizwan za'a aura mata Jawad haba dole ta ji zafi.

==========Luv Bird💘🕊️==========


A tsorace ta sake shi tare da komawa jefe ta tsaya haɗe da dawo da kallonta a kansa. Dik jikinta kerma yake yi alamar tsoro, a hankali take ta satar kallon su uncle Abbas da suka shigo cikin ɗakin.

Allah sarki shi kuwa kasa iya riƙe kansa ya yi, wani irin jiri da ta ɗebesa ne sai da ya yi baya baya ya koma saman mattress ɗinsa ya zauna yana sauke numfashi a hankali hankali mai zafin zazzaɓi, dama saboda ganinta yasa ya samu kwarin gwiwar iya miƙewa.

Dikkansu idanunsu a kan King da yake ta aikin binsu da dara daran idanun gadon nan nasu.

Momma dake tsaye kusa da uncle Taheer ne ta ce.
"Jannat me kike yi a nan kuma? Ya aka yi su Haulat suka barki kika fito daga wancan part ɗin?".

Ai tana jin maganar momma tamkar wadda aka kwaɗawa guduma a tsakiyar kai, da karfi ta wage murya ta rushe masu da kuka babu kama hannun yaro.

Kasa da kai Jawad ya yi yana tunanin abin da yakamata su yi, dan dai shi wlh ba zai iya hakura da ita ba!.

Uncle Taheer ne ya ce. "Haba momma, wai ni ku meyasa kuke son saka yarana kuka ne? Yanzu dai ga shi kin sakata kuka".

Harararsa ta yi tare da cewa. "Daga tambayarta zata rushe da kuka ka ce na sakata? To me na yi mata?".

Uncle Taheer zai sake yin magana King ya ɗaga mashi hannu hakan ya haifar da nutsuwa tsit na gabaɗaya familyn dake biye da shi, sannan suka kara gyara tsayuwansu tsit alamar sun bi umarni.

Uncle Abbas ne ya fara takawa ya ƙarisa cikin ɗakin kusa da Chuchu, hannunta ya riƙo a cikin nasa, cikin sigar rarrashi haɗe da zolaya kaɗan ya furta.

"Menene kuma Jannat? Meyasameki kike kuka?".
Kamar bai san kukan me take yi ba!.

Faɗowa jikinsa ta yi tana kara sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, irin kukan nan ne wanda zuciyan mutum yana kusa, zaku ji har wani shessheƙa take yi kamar zata haɗiyi zuciyarta.

Cikin kuka haɗe da ɗaga murya, da kyar ta iya fara faɗin.

"Daddy wlh ni Yah Jawad nike so, shi ma ni yake so, dan Allah ka cewa dad kada ya rabamu, ni bana son Yah Rizwan".

Yadda take magana sai ta baka tausayi, har wani shakewa voice ɗinta yake yi.

King ne ya amsa mata da cewa. "Amma ba ke kika ce mana Rizwan kike so ba?".

Sautin kukanta ta kara haɗe da faɗin. "Allah dad ni ban ce ba, ni Yah Jawad nike so".

Momma ce ta murje idanu haɗe da shafa toka kamar bata san komai ba ta ce.

"Da bakinki kika ce Rizwan kike so ba Jawad ba, dan haka zo ki wuce ki koma wajen su Haulat su cigaba da shiryaki anjima akwai taron dinner na musamman".

Ƙanƙame uncle Abbas da karfi ta yi tana mai cigaba da kuka tana faɗin.
"Daddy ni nasan zaka yarda da ni, tun da dad da momma basu yarda da ni ba shikenan, nasan kai zaka fahimceni, wlh ni ban ce ina son Yah Rizwan ba, dan Allah daddy kada ka bari dad ya kai ni wajen Yah Rizwan........"

Bai bari ta ƙarisar da maganar ba ya ɗaura manuniyar yatsarsa a saman lips ɗinta alamar ta yi shiru, dan yadda take maganar nan tsab zata iya haɗiyar zuciya ta mutu.

"Ya isa haka Jannat, ina nan ai babu wanda zai rabaki da Jawad ɗinki, ba wanda zai kai ki wajen Rizwan, ki kwantar da hankalinki".

Cewar uncle Abbas da yake aikin goge mata hawayen, sai dai yana gogesu wasu suna kara zubowa kamar ruwa ya buɗewa kansa hanya.

Cikin zolaya momma ta ce. "A'a fa matar Rizwan ce kada ka kawo mana shubuha a cikin lamura".

Kara ƙanƙame uncle Abbas ta yi tare da cewa. "Wlh ni daddy bana son shi, Yah Jawad nike so".
Yadda ta yi maganar a ruɗe ne yasa uncle Abbas ya yi saurin katseta, dan ya lura su momma zasu ruɗar mashi da ita, sai ya yi maza ya ce.

"Babu wanda zai kai ki wajen Rizwan, Jawad shi ne mijinki ba Rizwan ba".

Jawad da tun da suka shigo kansa na'a kasa ne ya ɗago a miliyan yanzu, idanu ya zaro waje sosai, da kyar ya iya cewa.

"Daddy me kake nufi?".

Jinjina kai uncle Abbas ya yi kafin ya ce. "Kwarai kuwa abin da ka ji shi ne gaskiya, kai ne mijin Jannat ba Rizwan ba".

A hanzarce ya miƙe tsaye, lokaci guda ya ji karfi ta zo mashi, ita ma Chuchu bata san lokacin da ta saki uncle Abbas ta dawo da kallonta a kan flowern nata ba.

"Please dad don't play with my heart, ba wai na faɗi hakan dan raini bane, a'a, nasan ka saba yi mun wasanni kala kala, please don't make this as a part of joke to me, zan iya mutuwa idan ka yi hakan".

Siririn murmushi uncle Abbas ya saki, a hankali ya kamo hannun Chuchu, ya matso ya riƙo hannun Jawad ɗaya. Ya buɗe tafin hannun Jawad ya ɗaura tafin hannun Chuchu a saman, cike da so da kauna ya fara magana kamar haka.

"I knew that koda yaushe muna cikin wasa da kai, but this isn't a joke, Jannat is ur wife, gata nan kuma na miƙa maka ita amana, don't let her tears to come out dik da nasan ba zaka yi hakan ba".

Ai mutuwar tsaye ya yi, ya kasa iya sake yin magana, wasu irin zafafan hawayen farinciki ne suka fara wanke fuskarsa, ya kasa fahimtar a wace iriyar duniya yake, gabaɗaya ya rasa me zai sake yi.

King ne ya ce. "Eyeee my son ya girma ya yi aure, to me zaka yi mana kuka kuma?".

Uncle Taheer ya karɓa ta cewa. "Ni yaya kada ku takurawa ɗana, ku je bari mu yi sirri da shi".

Yana magana yana nufar Jawad.

Mom ce ta ce. "To mu dai a bamu ɗiyarmu mu tafi da ita, sai ku yi ta sirrinku ɗin".

Ta yi maganar tana miƙawa Chuchu hannu a kan ta zo. Kara ƙanƙameta Jawad ya yi, da kyar ya iya furta.

"Please Momma ki ɗan bar mun ita a nan ko da na 10 mins ne kin ji? Long time bana tare da ita, and...........".

Uncle Abbas ne ya katse shi da cewa. "Babu wanda zai ɗauke maka ita, ba 10 mins ba, even one hour take is your time today".

Juyawa momma ta yi ta nufi waje tana faɗin. "Kuzo mu je kada Abbas ya koremu".

King ne ya rufa mata baya a in da ya nufi fada dan ya bada umarnin sarkin hatsi ya fito da abinci a girka dayawa a kai gidajen marayu, sannan su tabbatar sun girka abincin da zai kai a ciyar da gidajen prison dake garin gabaɗaya, su ɗauki tsawon sati guda suna ciyar da gidan prison and gidanjen marayu, su rabawa talakawa buhuhhunan abinci da kuɗi makudai dik dan murnar bikin Jawad and Chuchu, sannan su ziyarci asibitoci dan duba waɗan da za'ayiwa aiki kuma babu kuɗin yi, su biya masu kuɗin aikin, wanna hurumin sarkin fada ne, shi zai jagoranci zuwa asibitoci ya tabbatar ya biya kuɗin aiki da magungunar marasa karfi.

A wajen ɗaurin aure ma ya yi kyauta da kujerun makka sun kai 50, ya kuma yi kyauta da makuɗan kuɗaɗe ta hanyar raba check, anyi abubuwa da dama, King adalin sarki ne mai taimako sosai.

Wai ina maganar waɗan da suka karo masu hari? Muje dai zuwa.

Uncle Taheer ma fita waje ya yi ya bar uncle Abbas, Jawad and Chuchu kawai a cikin ɗakin.

Zaunar da Jawad a bakin bed uncle Abbas ya yi, sannan ya ja hannun Chuchu suka zauna a tare, yana a tsakiyarsu ya fara yi masu nasiha mai ratsa zuciya.

Shiru suka yi suna sauraronsa har ya dasa aya, sannan ne Jawad ya ce.
"Daddy please tell me yadda aka yi Jannat ta zama mallakina bayan ka ce mun Yah Rizwan dad ya bamawa?'.

Ajiyar zuciya uncle Abbas ya sauke, nan take yanayin face ɗinsa ya canza, alamar ya shiga damuwa, hakan yasa zuciyar Jawad ta kara karaya, dan bai san dalilin sauyawar face ɗin daddyn nasu ba.

Sun kasa kunne suna jiran jin me zai ce da su, ita kanta Chuchu ta fahimci uncle Abbas ya shiga damuwa a wanna tambaya da Jawad ya yi mashi.

"Rizwan ne ya sami dad ɗinku ɗazun da safe ya sanar da shi a ɗaura aurenka da Jannat ba da shi ba".

Zaro idanunsu a tare suka yi, they will not expect that at all, so they shocked.

"Dama Yah Rizwan yasan ina son Jannat ne ko dai kai ka gaya mashi daddy?". Jawad ya yi tambayar cikin ƙaguwa da san jin an warware masu komai dallah dallah!.

Girgiza kai uncle Abbas ya yi, sannan ya ɗaura da cewa.
"Ko ɗaya babu wanda ya gayawa Rizwan kana son Jannat, shi da kansa ya san da hakan?".

Sam Jawad bai san lokacin da ya furta. "How and when?". Ba.

"Lokacin da ya sanar da dad ɗinku ya sadaukar da soyayyarsa wa kai sai ya wuce room ɗinsa ya je ya fara haɗa kayansa zai koma Dubai, a time ɗin dad ɗinku ya kirani a waya ya ce dik in da nike na zo yana son ganina".

"Ban ɓata lokaci wajen zuwa in da yake ba, na same shi a room ɗinsa, I was so surprised time da ya gaya mun furucin Rizwan a kanku, ban iya haɗiye abin a raina ba sai da na bi Rizwan ɗakinsa dan na ji meyasa ya yi hakan".

"A lokacin da na shiga ɗakin nasa ya gama shirya echolac ɗinsa domin tafiya, ni na dakatar da shi na kuma umarcesa da ya zauna mu yi magana. Bai yi mun musu ba, ya zauna.
Da kallo ɗaya na yi mashi na fahimci ya sha kuka sosai, dan ga idanunsa har sun kumbura, ban nuna mashi kamar na gane yana cikin damuwa or ya sha kuka ba, na yi amfani da fifikon dake tsakaninmu na tambaye shi cikin hikima".

========================💔😥

"Rizwan meyasa kace ka barwa ɗan uwanka Jannat ya aura?".

"Babu komai daddy, naga hakan shi ne yafi dacewa da ni ne!".
Ya yi maganar yana sunkuyar da kansa ƙasa, baya san su haɗa ido da uncle Abbas, dan baya san ya gane yana cikin tashin hankalin da ba zai iya ɗauka ba a dalilin sadaukar da soyayyar tasa da ya yi.

"Ko zaka ɓoyewa kowa Rizwan bai kamata ni ka ɓoye mun na, shin ka manta nine daddynku ne?".

Girgi kai ya yi alamar a'a bai manta ba.

"To ka gaya mun meyasa ka sadaukar da soyayyarka ga Jawad? Shin ya ce maka yana son Jannat ne?".

Girgiza kai ya sake yi a karo na biyu, kamar zai rushe da kuka ya ce.
"Babu wanda ya gaya mun Jawad yana san Jannat a baya, da idanuna naga hakan, sannan kuma Auta ta tabbatar mun da hakan, har ɗakin nan ta zo ta gaya mun cewa Jawad yana san Jannat tun tana ƙarama, ta nuna mun video da hotunansu a wayarta a lokacin da suke soyayya, na kuma kara bincikawa na tabbatar da hakan ne, a binciken nawa ne ma na gane rashin lafiyan ɗan uwana nine sila, nine na yi mashi shamaki da abar kaunarsa yasa ya faɗi ciwo........."

Yaushe Auta ta gayawa Rizwan soyayyar dake tsakanin Jawad and Chuchu baiwar Allah? Allah sarki kila tin kafin ta mutu ta gina masu soyayyarsu dan su cigaba da kasakcewa da juna, ita kuma nata soyayyan shi ne ya zama ajalinta!!.

Cikin in ina ya idasa maganar sakamakon sarkewa da muryarsa take yi, ga wasu zafafan hawayen da suka cika mashi idanu, Allah sarki har wani zazzaɓi mai karfi yake ji tana ƙoƙarin kayar da shi. Dik taurin zuciya namiji soyayya tana sanya shi ladab, to ga dai Rizwan da ruwan hawaye saboda rasa Jannat da ya yi!.

Tun da ya fara magana tsananin tausayinsa ya kara dabaibaye zuciyar uncle Abbas, yau da yana da yadda zai yi ya raba Jannat gida biyu ya bawa ƴaƴan nasa da ya yi.

Matsowa ya yi ya rungumi Rizwan, zuciyarsa tana yi mashi zafi ya hau rarrashinsa a kan ya jure In Sha Allah zai samu wadda ta fi Jannat.

Murya a sarkafe ya amsa da. "Ba dai wadda ta di Jannat ba daddy, nasan ba zan samu madadinta bama bare wadda ta fita, Jannat ta dabance a zuciyata daddy, ka tayani da addu'ar Allah ya sassauta mun sonta a rai'na".

Tamkar ƙaramin yaro yake kuka yana magana. Hakika uncle Abbas ya fahimci irin tsananin sonta da Rizwan yake yi, abin ya wuci tunaninku, yanzu tsoronsa ɗaya shi ne kada wani abin ya samu first love ɗin nasa, dan a gaskiya soyayyar da Rizwan yake yi mata hakura da ita zai iya cutar da shi matuƙa.

"Babu abin da ya fi karfin Allah Rizwan, In Sha Allah zaka samu fiye da Jannat, ina tayaka addu'a a kan hakan, Allah Ubangiji ya yi maka albarka da sauyi na alkhari".

Sam soyayya ta rufe mashi ido, yaki yarda zai iya samun wadda ta fi Chuchu, gani yake yi ita ce karshe, daga karshe dai uncle Abbas shiru ya yi ya rabu da shi a mazaunin ba zai taɓa samun madadinta ba!.

Sosai Rizwan ya sha kukan da bai taɓa yin irinsa ba tun bayan rasuwar mahaifiyarsu, yau ya kara ɗanɗanar ɗaci a karo na biyu a rayuwansa, da kyar ya iya sarrafa hawayensa suka dakata da zuba, sosai zuciyar uncle Abbas ta karaya, yana ganin kamar tabbas wani abin zai faru da Rizwan, dan irin wanna kuka kai

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login