Showing 366001 words to 369000 words out of 403653 words
sai ka zagi momma a kai'na for what reason? Ka zageta kuma ka zaganmun iyayena, dik saboda kana san ɓoye laifukanka, just tell me wacece uwar Ramish kuma meyasa ka yaudari Aleezarh da shi? Me ya yi maka da ka ja mashi irin wannan bala'i da dik in da ya yi neman rayuwarsa ake yi? Laifin me ya aikata a gareka? Ka faɗa mun sannan ka bani amsar menene a tsakaninka da mahaifiyar Hoorain da har ka zage ka rabasa da Zunaira". Ɗan dakatawa ya yi yana mayar da numfashi kafin ya sake cewa.
"Dad kai azzalumi ne sosai, ka faɗa mun su waye suke bibiyar rayuwar Ramish, dan nasan tin da har ka iya yaudarar Aleezarh da Ramish a matsayin ɗanta to ba shakka kasan su waye suke neman kashesa, Raj shi ne kawai ɗan Aleezarh namiji sai Aneesa, Ramish ba ɗanta bane, kuma kai ka san uwarsa, dole kuma ka faɗa mun ɗan waye".
Yau ake yinta, Ramish ba ɗan mama ba, how comes to? Ya aka yi ita kanta bata san ba ɗanta bane? Kam bala'i lallai King shahararren ne, iyeeeee, ya aka yi Smart yasan dikka wannan sirrin wanda su momma basu sani ba? Sannan ya aka yi yasan suna da alaƙa da maman Hoorain bayan momma da ta yi tinanin ma bata faɗa mashi ba? Gaskiya Smart hegen kwaro ne, wato akwai badaƙala, wacece uwar Ramish to tin da ba mama bace? Amma da alama irin son da King yake yi mashi shi ne ubansa, tab QUEEN OF SURPRISED na fara baku a jikinku, yanzu kuka fara shan surprise ma ai, mu je zuwa.
King da ya gama nuna zallar hasala a face ɗinsa, abin da mutane suke cewa tabarmar kunya da hauka ake naɗeta, ya ɗaure fuska zai yi magana cikin tsawa kenan Chuchu ta afko cikin ɗakin a guje tana zunduma ihu, hakan yasa duk suka kai kallansu a kanta. Tana zuwa a haukace ta nufi King tana faɗin. "Daddy Auta ta rasu, Yah Abdussalam ne ya faɗa mata cewa Hoorain ɗin da take so ai ya mutu dan haka ta zo su yi zaman aure, shikenan ta faɗi ta dai'na numfashi!!".
Ai King bai tsaya jin karashin maganar ba ya nufi waje, saboda yasan dama ance zuciyarta gab yake da bugawa, to ga shi Abdussalam ya fasa abin da suke rufe mata, ai dole ziciyarta ta buga. Shi kuwa Smart tin da Chuchu ta ambaci Auta ta rasu ya rigasu barin bedroom ɗin ya nufi in da take. Yana shiga ya sami Abdussalam sai tattala mata tuwa yake yi a kanta yana ambatar sunanta, amma ko motsawa bata yi ba, da kallo ɗaya Smart ya yi mata ya fahimci tabbas babu rai a jikinta. Innalilahi wa inna ilahir rajiun.
Allah sarki kada ku ga laifin Abdussalam, shi bai san ciwon son Hoorain take yi ba, shi bai san ance kada a sanar da ita ba, da ta fito parlour tana sambatu a kan Hoorain ne ya biyo bayanta, a nan ya ji ashe san Hoorain ne a ranta, shi kuma yasan Hoorain ya mutu, shi ne ya sanar da ita ya rasu, hakan yasa ta yanke jiki ta faɗi zuciyarta ta buga.
A fujaje King ya shigo cikin ɗakin, tamkar ya haukace ya yi kanta zai taɓata, ai cikin wani irin kuna da fitar hayyaci Smart ya capki wuyarsa, dama ya faɗa mashi in Zunaira ta mutu to fa sai dai ayi gawa biyu wlh!!.
Page ɗin yau bai samu wadataccen editing ba, nasan zaku samu typing errors dayawa
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍
=======🔥🔥🔥=========
MALLAKIN🔥
P_R_I_N_C_E_S_S__T_E_E_M_A...✍️🔥🕊️
اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️
57
Daidai lokacin su uncle Abbas suka shigo cikin parlourn, dan Chuchu sai da ta je ta kira kowa na familyn, da alama Chuchu ta zauce, dan kalar kukan da take yi sai da uncle Jahiz ya kamata ya hanata dawowa part ɗin, ya miƙata ga Jawad ya yi mashi gargaɗin kada ya barta ta fita, saboda za'a samu matsala.
Kin yarda ta yi tana tigewa sai da Jawad ɗin ya sanyata a ɗaki ya rufe kofar da key, sannan ya kira Dr Raj da ya zo ya yi mata alluran barci ko zai samu hankalinta ya kwanta. Yau sai da aljannun dake kan Aneesa suka motsa saboda tsananin tashin hankalin da suka shiga. Uncle Jahiz and uncle Jahiz sun yi sun yi su zare hannun Smart daga wuyar King amma sun kasa, saboda wani irin damka da ya yi mashi na takaici da fitar hayyaci, shi kuma King like ruhinsa ya bar jikinsa saboda tashin hankali, bai taɓa zatan ɗan cikinsa zai yi mashi abin da Smart ya yi mashi ba ko da wasa, hakan yasa ya yi wannan sumar tsayen.
Ihun da guyson ya zunduma a lokacin da ya shigo cikin parlourn ne yasa Smart juyowa, Allah sarki, hankalinsa ya yi nisa wajen hukunta King ne, da ba zai taɓa bari guyson, Omaid and Obaid da Momma su ji batun mutuwar Zunaira a yanzu ba, dan abin zai yi mashi yawa, yasan ba zasu iya ɗauka ba, kazalika shi ma zai iya ɗaukar komai ban da tashin hankalinsu.
Ganin cewa labarin yana yaɗuwa a cikin gidan zai iya ja momma ta ji labari ne yasa ya saki King ba dan ya so hakan ba. Yana sakinsa King ya zube ƙasa a saman gwiwowinsa idanunsa sun kaɗa sun yi jajir, yau zuciyarsa ta karaya, ya shiga tashin hankalin da ko a mafarki bai taɓa zatan shiga ba, yana kaunar Zunaira tamkar ransa, idan ta mutu a gaskiya zai iya mummunar cutuwa. Ɗan uwa ɗan uwan ne my people's, uncle Abbas and uncle Jahiz ne suka rungumi King suna tausarsa dik da basu san me ya haɗa shi da Smart ɗin ba.
Shi kuwa Smart kan Auta ya nufa, Abdussalam yana rike da ita yana ta famar girgizata yana kwallah, ya tattala mata ruwa a kanta ya kai 5 bottle, hakan yasa suka yarda da ta mutu ɗin ne, ruwa ba zai tasheta ba sai dai ALLAHN da ya yi ruwan ne zai iya tashinta.
Wani irin gigitaccen tsawa da Smart ya dakawa Abdussalam har sai da yasa gabaɗaya waɗan da suke cikin parlourn suka natsu, a zabure Abdussalam ya ja baya da gudu. Bai bi ta kan kowa ba ya ɗauki gawarta ya saɓa a saman shoulder ɗinsa, cikin zafa ya nufi kofar fita, dik an rasa mai bakin iya ce mashi uppan. Har ya kai bakin kofa ya juyo ya kalli King ido cikin ido. "Ka jira dawowata, sai ka ɗanɗani irin azabar da ka ɗanɗanawa Zunaira a zuciyarta kafin mutuwarta, kuma sai ka faɗa mun dikkan amsoshina!!!". Yana kai karshen maganar ya ja hannun guyson da yake tsaye a bakin kofar tamkar an sassakasa, kamar wanda aka zarewa laka, tin da ya yi ihu sau ɗaya bai sake ko motsawa ba, amma ransa na jikinsa kuma ba suma ya yi ba.
Shi kuwa King Allah ne kaɗai yasan irin halin da ya shiga, ji ya yi tamkar bashi a duniya, Zunaira ta mutu? Ina kin yarda ya yi kamar yadda har yau commander Zafar yaki yarda da Hoorain ya mutu, an je an binne Hoorain, har kabarinsa su Ansar su je da shi, amma yaki yarda ɗansa ne, dan shi yana ganin Hoorain a gizo. To haka shi ma King a yanzu yaki yarda Zunaira ta mutu, ya shiga wani irin hali na tsakanin rayuwa ko mutuwa, wato shi ma a yanzu yana ɗanɗana abin da commander yake ɗanɗana, sai dai kuma dik da ta mutu wlh bai yi danasanin hanata auren Hoorain ba! Ko kaɗan bai ji mamar bai kyauta ba da ya hanata Hoorain tashin sense!!.
-------------------------------------🔥
Suna fitowa suka ci karo da Jaish and Omaid da Obaid suna biye da shi a baya. Cike da tashin hankali Jaish ya tambayi Smart me yake faruwa?. Ko dakatawa Smart bai yi ba bare yasa ran zai samu amsa daga garesa, kai tsaye ya nufi wajen motocin gida. Bayansa suka bi gabaɗayansu Jaish yana faɗin ina zai je da ita? Bai amsa mashi ba sai ya ce ya yi maza ya bashi keyn motarsa bari ya wuce da ita, dan ba za'ayi jana'izarta a nan ba, ran Smart ya ɓaci over.
Jaish bai yi musu ba ya ɗauki mashi keyn motarsa, sai dai a tare suka nufi airport, da jet ɗin Smart ɗin zasu yi amfani. In short kai tsaye ya ɗauki gawar Auta zuwa Dubai, rabonsa da Dubai tin wani zuwa da ya taɓa yi bincike a kan Ramish, tin lokacin bai sake zuwa ba, yanzu tsawon shekaru wajen 10, amma yau saboda mutuwar Auta ya wuce da gawarta can. Bai sanar da momma zai zo Dubai ba, babu wanda ya sani sai Jaish and guyson da suka tafi a tare, Omaid and Obaid ma sun barosu a kingdom ɗin sai kuka suke yi, ya ɗauki guyson ne ma dan yasan sai ya yi jinya, kada ya tafi ya barshi matsala ta afku da shi.
Tin kan su hau jirgi ya kira Ramish a waya, ya sanar da shi ya zo airport ya ɗaukesu, ya ɗan yi mamakin jin sun zo Dubai, amma sai ya shirya tsab cikin suit masu bala'in tsada, ya ce da Leesharh bari ya je airport yana zuwa. Da yake ita tasan me a gidan, tasan tana tare da bakar azzaluma yarinya mai ɓadda kama a matsayin tsohuwa, sai ta shiga tashin hankali da damuwa over, a tsorace take ya tafi ya barta da wannan tsohuwa.
Hannayenta ya riko cikin nasa yana kallan face ɗinta. "Aesh ba zan jima ba, babban yayanmu ne ya zo, shi kawai zan je in ɗauko kin ji?". Shiru ta yi kanta a ƙasa, kamar mai tinanin wani abin, tana zaune a saman bedside drawer ɗinsa, shi kuma yana zaune gefen bed ɗin suna fuskantar juna.
Kafin ya ankara sai ganin hawaye ya yi yana ɗiga a ƙasa, ashe kuka take yi da ta sunkuyar da kanta ƙasa.......... "Aesh lafiya kuwa? Meyasa kike kuka?"........ Shiru bata amsa shi ba, ita tasan bala'in da zata shiga idan ya tafi, tsoron matar take ji......... "To zaki bini mu je tare ne?". Ya jefa mata tambayar yana sakin hannunta ɗaya ya ɗago haɓarta. A gaggauce ta gyaɗa mashi kai alamar e zata bishi. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "To shi ne sai kin yi kuka? Ai da sai ki faɗa mun kina tsoron gidan ne mu tafi tare". "Kina tsoron mutanen da suka zo ɗin nan ko? Ba zasu sake dawowa ba In Sha Allah, so feel free and enjoy your life with your husband to be In Sha Allah". Ya kai karshen maganar yana ɗan leƙa face ɗinta.
Wani irin shessheƙa ta yi kafin ta kai hannu tana goge hawaye, ta kasa yin magana. Ƙasa sosai ya yi da murya wajen cewa. "Yau ɗaya naga abin da kike tsoro Aesh, dik yadda aka yi akwai abin da yake baki tsoro kuma yake ɗaga hankalinki a gidan nan! To faɗa mun menene sai in kawar maki da shi kada ki rinƙa jin tsoro". ....... KAI WATO RAMISH MA FA AKWAI ƘWAƘWALWA, A RANSA YA JI AKWAI ABIN DA YAKE BATA TSORO NA DABAN, BA WAI DAN MUTANEN CAN SUN KAWO MASU HARI BANE, AKWAI WANI ABIN DAI!!.
Da yake ita ma tana da basira sai rashin yin tinani kafin ta yi abu, sai ta ce mashi. "Yah Ramish tin da ka iya gano cewa akwai abin da yake bani tsoro, to ka gano ko menene da kanka ba sai na faɗa ba". "Haka kika ce?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e haka ta ce. Ɗaura yatsarsa a saman kumatunta ya yi. "Zaki gani, cikin ƙankanin lokaci zan gano". Ya faɗa yana ɗan ja baya kaɗan daga kusa da ita. Tab kunga Leesharh ta yi amfani da basira a nan ko? Tasa zai fara binciken me abin tsoratarwa a gidan, idan Allah ya taimakesa sai ya kama tsohuwar nan da hujja dumu dumu, kamar Leesharh tana highlighting ɗinsa a kan abin ne.
"Shirya ki zo mu je, saura bai wuce 20 mins jirginsa ya sauƙa ba". Ya faɗa yana kallanta. Miƙewa ta yi ta nufi waje ba tare da ta yi magana ba. Da kallo ya bi bayanta, idanunsa a kan mazaunanta dake motsawa a hankali, nisawa ya yi tare da haɗiyar siririn yawu kamar wadda aka ajiyewa kayan fresh marmari a gabansa!.
Tana fita suka yi karo da tsohuwar nan, gabaɗaya tray ɗin hannunta ya faɗi kasa abincin da ta shiryawa Ramish ɗin ya zube ƙasa. A razane Leesharh ta ɗago ta kalli face ɗin matar kafin ta mayar da kallonta a kan kayan abincin da suka watse a wajen. Idan ran tsohuwar nan ya kai dubu to ya ɓaci, sannan hankalinta ya tashi sosai, Leesharh ta lura da hakan, sai ta ce. "Mama kada ki damu ba sai kin ɓata rai ba, Yah Ramish ba zai ci abinci a gida ba yau, zamu ci a waje, ki gyare wajen kawai ki je ki huta abinki". Ta kai karshen maganar tare da wucewa zata bar wajen.
Ai tsabar ɓacin rai tsohuwar nan bata san lokacin da ta kai hannu ta damko wuyar rigar Leesharh ta baya ba, tana zazzare ido ta kasa yin magana. Ko kun san meyasa bata yin magana? Saboda muryan yara ne da ita, za'a iya gane ba tsohuwa bace, shiyasa ta yi acting matsayin kurma, yanzu kunga ne dalilin da yasa na ce maku tun da take kula da Leesharh bata taɓa yin magana ba?.
Da mamaki Leesharh ta juyo da kallonta a kan matar. A miliyan ta saketa tare da girgirza kai alamar tana bawa Leesharh hakuri kenan, mamaki kamar zai kashe Leesharh, me dan an ɓarar da abinci zata tashi hankalinta? Sai kace babu wani abinci a gidan? Abin da mamaki!. Alama tsohuwar ta nuna mata a kan zata iya haɗa masu wani abincin yanzu ba sai sun ci a waje ba!.
Shiru Leesharh ta yi tana san gane nufin tsohuwar nan a kansu, meyasa ta damu da abinci yau bayan a da ko ta kawo masu basu ci ba bata damuwa, wata rana ma a waje suke fita su ci, bata damuwa sai yau? To why? Leesharh ta jefawa kanta tambayar, lokacin guda ta ɗan ɗauke wuta. Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta saki wani ƙayataccen murmushi, kai ta jinjinawa tsohuwar a kan ba damuwa ta shirya masu wani abinci, a cikin ranta ta ce. "Zaki san da jinin Nigeria kike yi, yo mu da dik duniya ta jinjinawa kaifin ƙwaƙwalwa mu bare ke da iskancin naku ma bai da lasisi, mu kuma Najeriya dik iskanci masu iskanci sai ya jira, sai da suka sara mana, ni kaɗai na isheki ba sai Yah Ramish ya sa baki ba, zaki gane ke karamar ƴar iska ce, ba zan taɓa bari ki san nasan komai a kanki ba! Cikin ruwan sanyi zamu yi amfani dake mu kama iyayen gidanki, ai ke yanzu kina da amfani a wajenmu, zan taya shi bincike wajen yin amfani dake". JAMA'A KU TAFAWA NIGERIA!! KU TAFAWA LEESHARH!! HABA AI JININ NIGERIA BADAGA NAN BA, KOWA SAI YA JIRA ALLAH KUWA!!.
Wucewa ta yi tana tinanin in dai tana san yin magananinsu to dole ta kasance tana da kusanci da Ramish sosai, ta hakance zata sanyasu su da kansu su kama kansu. Da wannan tinani a ranta ta yi wanka ta shirya cikin haɗaɗɗen arabs abaya, ta ji yayansa zai je ɗaukowa, sai ta shirya da kyau dan kun san siririki ne Smart........... 😅
Ba karya ta yi fitina sosai cikin white abayan, ta yi rolling veil a kanta, ta ɗauki karamar fashion bag and flat shoe dik white color kalar rigar, sai tashin kamshi take zubawa ta nufi bedroom ɗinsa. Bakinta a ɗauke da sallama ta shigo cikin room ɗin. Yana zaune a in da ta barsa hannunsa rike da cup of cappuccino, yanzu tsohuwar ta kawo mashi cappuccinon da kayan abincin ta fita, har ta sake shirya masu wani kenan, yanzu ya ɗauki cappuccinon bai kai ga sha ba!!.
Ai tana gani bata san lokacin da ta ƙariso cikin room ɗin da sauri ba, shi kuwa yana ɗaura idanunsa a kanta ya kafeta da kallo, ta yi fitina sosai, yanzu a ƴan kwanan nan wani irin sihirtatcen kyau take karawa na musamman. "Yah Ramish cappuccino zaka sha?". Ta jefa mashi tambayar a ya yin da ta iso wajensa. Kai ya jinjina mata haɗe da cewa. "Aesh you're so pretty, zo ki sha cappuccino sai mu tafi ko? Lokaci na kurewa". Ya kai karshen maganar tare da kai cup ɗin bakinsa da nufin ya kurɓa.
Ai bata san lokacin da ta tafi kamar zata faɗi cikin dabara ta buge cup ɗin ya faɗi ƙasa ba, cup ɗin ya fashe cappuccino ya zube a ƙasa. A hanzarce ya ɗago kai yana ƙoƙarin yin magana sai faɗowa ta yi jikinsa mai gabaɗaya tare da fara salatin karya a zuwan zamewa ta yi ta faɗo jikinsa ba da gangan ba.
"Aesh lafiya kuwa?". Ya faɗa yana kallon face ɗinta, ta datse idanu wai irin ya zaci da gaske ne ma. Yunƙurawa ta yi zata bar jikinsa saboda shegen iya basaja. Rikota ya yi yana kallan face ɗinta. "Aesh yakamata in kai ki hospital a dubaki, naga kamar jiri yana damunki".
Ya bata satar amsa, sai kuwa ta ce. "Nima abin yana bani mamaki, kawai ina tsaye na ji jiri ya ɗebeni". Sorry ya ce mata tare da kai hannunsa ɗaya saman goshinta ya taɓa. "Ga shi jikinki babu zafi, amma dik da haka bari mu dawo zan ɗauki mataki". Langwaɓewa ta yi a jikinsa wai