Showing 111001 words to 114000 words out of 403653 words

Chapter 38 - RAWANIN_ZALINCI BOOK 3

20 Dec 2025

86

face ɗinta kasan bata ji daɗin dawowar Leesharh ba, ta haɗe rai kamar hadari, ranta a ɓace matiƙa. Ta tsani Leesharh, bata so ace sun saketa ba, ta so ne su kasheta, amma sai Sharifat ta ce mata an dawo da ita, ta tambayi Dr Raj meyasa aka dawo da ita ya ce mata ta tambayi Yah Ramish, tana shakkar tinkararsa saboda baya ba da fuska, hakan yasa ta tambayi Bilal, shi ma ya ce ta samu Yah Ramish a wajensa zata samu amsa, tin jiya take san tamnayarsa, amma tana tsoron tinkararsa, da kyar yau ma ta samu kwarin gwiwar zuwa garesa da abin ya dameta, wannan ma sai da wannan friend ɗinta mai kibar nan ta kara mata kwarin gwiwar a kan ta je ta tambaya kada ta damu.

Idan baku manta ba a baya ita da kawar tata sun haɗa baki zasu kashe Leesharh ai, to shi ne da Ramish ya kamata sai suka ce ya hutasshesu, sai murna suke yi, rana tsaka kawai murna ta koma ciki, gaza jurar hakan suka yi har sai da suka zo dan tabbatarwa.

"Abin da kika zo tambaya kenan?". Ya jefa mata tambaua.
Wlh Ramish ya tsani Ummie kamar me, babu abin da ta yi mashi kuma, haka kawai bai yarda da ita ba wai.

"Shi ne abin da ya kawoni". Ta bashi amsa.............. Gyarawa ya yi ya kwanta abinsa, ya janyo bargo har zuwa saman jikinsa. "Zaki iya tafiya dan bani da alaƙa da wannan magana da kika zo mun da ita". Shi ne amsar da ya bata, yana gama maganar kuma ya jawo remote ya kashe wutar ɗakin tare da kunna lamps, sannan ya kara gudun Ac.

Tsaye ta yi tana kallansa, ta ƙasa tafiya. A hankali ya lumshe idanunsa kamar mai barci, zubawa face ɗinsa idanu ta yi tana kallo, nan take shaiɗan bakin azzalumi ya fara ƙawata mata kyansa da surarsa, take a wajen ta ji ta kamu da muguwar sha'awarsa. Tashin hankali!!.

Zuciyarta ne ya fara azalzalarta, kun san mutumin fa ba dai kyau ba, jinin Zuhair ai ba wasa ba, ƙasa kawar da kallanta a kansa ta yi, ji take yi kamar ta tafi ta faɗa jikinsa, shaiɗan sai kara rura wutar wannan bakin al'amari yake yi a ranta, ta yi matuƙar kwaɗaituwa da surarsa a wannan dare, dama ita ma idan ba iskanci ba me zai kawota ɗakin santalelen saurayi a cikin wannan dare? Bayan kuma shaiɗan yana nan a tsakani yana yawo tsakanin karya da gaskiya tsinanne.

Wlh ta ƙasa juyawa ta bar ɗakin, infact ta ƙasa iya dai'na kallansa, ga shi lamps suna haska fuskarsa da kyau, dan ta bakin bed ya kwanta, cikin dare ga fara kyakkyawar fuska haske na haskata ai kyau iya kyau, ni kuma na ce dik jarabarki wannan handsome guy na King ya fi karfinki In Sha Allah.

Sallamar da aka yi daga bayanta ne yasa ta yi wani irin razana tare da zare kallanta daga kan Ramish, jikinta har wani tsuma yake yi da sha'awarsa. Wajen da take tsaye a kwai ɗan duhu hakan yasa Sharifat bata gane wacece ne a wajen ba, ta dai ga mutum, sai ta yi tinanin ko Yah Bilal ne, dan haka sai ta ce. "Yah Bilal good evening".

Shiru Ummie ta ƙasa iya amsa mata, sai ma ta juya da sauri ta fice daga ɗakin tana haɗiyar yawun kyan Ramish.

Sam Sharifat bata kawo komai a ranta ba, bata san wacece bace, kawai ta wuce ciki dan ta kai mashi cappuccinon da ya buƙata.

A gaban bed ta durkushe gwiwowinta, kamar zata saka mashi kuka, murya a raunace ta ce. "Good evening Yah Ramish".

Sam bai amsa mata ba, bai ma motsa ba kamar ya yi barci, ita kuma tasan sarai bai yi barci ba, ga zara zaran eyelashes ɗinsa suna ɗan motsawa alamar bai yi barci ba amsawa ce kawai ba zai yi ba, dan haka sai ta ɗaura da cewa. "Yah Ramish dan Allah ka yi hakuri ka ji? Wlh ban san kai bane ka kirani a waya shiyasa na yi zafafan furuci".

Nan ma bai motsa ba, kamar babu shi a ɗakin. Miƙewa ta yi ta ɗaura mashi cappuccinon a saman table dake tsakanin sofar a cikin ɗakin, sannan ta nufi waje, dan tasan ko kwana zata yi ba zai amsa mata ba sai time da ya yi niya, gara mata ma ta tafi zai fi mata.

Tana tafiya tana waigosa cike da tsantsar kaunarsa, sansa ne yake kara ratsa zuciyarta, tana san cigaba da kallansa amma babu dama, dan haka ta wuce waje da sauri idanunta suna ƙoƙarin cikowa da kwallah.

Tana fitowa parlon ta ci karo da Yah Rizwan ya fito daga bedroom ɗinsa rike da cup a hannunsa, yana sanye da white arabs jallabiya, ya yi wani irin rama sosai, da alama daga jinya ya tashi, Allah sarki yana jinyar san Chuchu shi ma kuma Aneesa tana jinyar sansa.

"Lil daga ina kike a cikin wannan daren?". Cewar Rizwan.

Dakatawa ta yi da nufar waje, da sauri ta juyo garesa, bata yi zaton ya dawo gidan ba, dan bata gansa ba, rabonta da shi tin a kingdom of power ranar bikinsa, dik jinyar da ya sha bata sani ba, ba komai yasa hakan ba kuma face in dai ba wajen Ramish ba bata zuwa wajen kowannensu a part ɗin, ɗan gara ma shi Rizwan ɗin da yana sakar mata fuska wani lokaci idan ta rasa abokin hira tana zuwa bedroom ɗinsa su zauna.

"Wajen Yah Ramish na je kai mashi cappuccinon". Kamar zata yi kuka ta yi maganar. Gyara tsayuwarsa da kyau Rizwan ya yi, cikin sanyin murya ya ce. "Yah Ramish ɗin ya yi maki wani abin ne naga kamar kina kuka?".

Kai ta girgiza alamar a'a tana ƙoƙarin shanye hawayen dake san zubo mata. "Mayasaki kuka to?".
"Babu komai Yah Rizwan...........". Tana kai karshen maganar ta rushe da kukan da bata san daga ina ya fito ba, da karfi kukan ya kubce mata.

Da mamaki Rizwan yake binta da kallo, Sharifat kenan sarkin saurin kuka ga raunin zuciya. Da yaga da gaske take kukan sai ya matsa kusa da ita, a saman table na wajen ya ajiye cup ɗin hannunsa, sannan ya janyota jikinsa ya rungumeta.

Ita ma rungunesa ta yi tana kara rushewa da kuka. Baya cikin yanayi mai daɗi sam, amma haka ya daure ya shiga rarrashinta yana bata baki.

A haka Dr Raj ya zo ya wucesu ya shiga ɗakin Yah Bilal dan ya sanar da shi condition da Leesharh take ciki a yanzu, dama tin safe Bilal ɗin yake jiran wannan amsa daga garesa.

"Ki yi shiru kinji our lil, kinga fa ke kaɗai ce sistermu a cikin gidan nan, bai kamata ace wani abin zai sanya manake kwallah ba".

Kun san Yah Rizwan Allah ya yi mashi baiwar iya kalamai masu kwantar da hankali, dan haka koma yaya mutum ya kai ga ɗaukar zafi ko ɓacin rai cikin ƴan mintuna zai rarrashesa.

Haka ita ma Sharifat cikin ƙanƙanin lokaci ya rarrasheta har sai da ta yi shiru, sannan ya sanyata murmushi kafin ya raba jikinsa da nata, ya riki hannunta suka nufi bedroom ɗinta.

Sai da ya tabbatar ta kwanta tana farinciki sannan ya juya ya fito, kai tsaye ya koma bedroom ɗinsa shi ma.

A ɓangaren Ramish kuwa, sai da ya gama shan kamshinsa, ya gama jan ajinsa sannan ya tashi ya ɗauki cappuccinonsa ya fara sha cike da class. Kaɗan ya sha ya ajiye sauran, ya miƙe ya nufi prayer mad set. Dadduma ya ɗauko, already ya ɗauro alwalarsa tin ɗazun, salloli ya zo ya fara gabatarwa yana neman Allah da ya dafa mashi ya saukaka mashi binciken nan da suke yi a kan masu nikaf, nan da next month akwai wani taro da zasu sake yi, baya fatan har a kai ranar wannan taron bai kama masu kawo mashi hari ba, idan bai yi hakan ba za'a iya samu gagarumin matsala su sake kai mashi hari cikin taron kamar yadda suka yi a farko, za'a iya rasa rayuka, waɗan da basu ji ba basu gani ba zasu iya mutuwa, idan hakan ta faru ranza zai kuntata sosai, saboda dalilinsa ne mutane zasu mutu.

So sai addu'a yake yi da Allah ya taimakesa kafin next month. Dai'dai lokacin da yake kwarara wannan addu'a a dai'dai lokacin Leesharh ra farka bayan kwanaki uku tana sume kenan.

Dr Raj ya yi namijin ƙoƙari wajen kula da lafiyarta, ya nuna cikakkiyar kwarewa a ɓangaren aikinsa wanda hakan yasa ta farka a cikin hayyacinta. Hannunta da ya samu matsala ma ya sha ɗauri kuma ya sha kula sosai, haƙiƙa Bilal ya yi kokarin a wannan ɓangaren kam dik da bamu san menene ainahin abin da yake a cikin zuciyarsa ba.

Ta yi babban sa'a kafin ta farka daga doguwar sumar nan dik wasu raɗaɗin ciwo dake jikinta sun kau, dan haka bata ji wani azaba da ta farka ba, sai da ta zo motsawa dan ta miƙe ne gaɓɓan jikinta suka ce ina ai basu san wannan ba, dole ta koma ta yi lamo a gadan tana kallan saman celling tana ƙoƙarin fahimtar a wace duniya take ma tukun nan, dan ita dai tasan ta baro kanta a hannun Yah Ramish ya danki gashin kanta yana bugata da jikin bangon ɗakin da suke horas da masu laifi, tin wani buga mata kai da bango da karfi da ya yi har ta fara ganin dishi dishi, daga nan bata sake sanin a wani hali take a ciki ba.

Sai a yau da taga alamar kamar a gidan Abu Abdussalam take, amma ba halin tashi ta duba, dan haka sai ta mayar da idanunta da suke yi mata zafi ya lumshesu tana furta istigifari a cikin ranta.

•••••••••••KINGDOM OF POWER•••••••••••🔥

Baki ɗauke da sallama Momma ta shiga master room ɗin dearlyn love ɗinta, baya a cikin bedroom ɗin, zubar ruwa da ta jiyo a toilet yasa ta fahimci yana ciki, dan haka sai ta kwantar da babyn Khadija a saman bed ɗinsa, ta ɗauki wayarsa domin ta kira uncle Jahiz.

11:00 a lokacin, dare ya yi, sai ta mayar da wayar ta ajiye a zuwan sai da safe kawai su haɗu. Tana ajiyewa King yana fitowa ɗaure da towel a waist ɗinsa.

Da sauri ta miƙe ta nufesa, ƙayataccen murmushi ya sakar mata, da alama ya yi farincikin dawowarta sosai. Tana zuwa ta karɓi ƙaramar towel dake hannunsa ta hau taya shi goge jiki tana yi mashi barka da dare.

"Kin dawo lafiya?". Ya faɗa fuska ba yabo ba fallasa, yana ta kallanta cike da tsananin kauna mai zafi. "Lafiya lou na dawo har ma da tsaraba". Ita ma tana magana tana kallansa cike da kauna.

Kara sakar mata murmushi ya yi kafin ya ɗaura hannayensa a saman lallausan kumatunta. "Tsarabar me kika dawo mun da shi". Ya yi maganar ba tare da ya lura da babyn dake kwance a gadansa ba.

"Kamata ya yi ka tambayi ya na sami mutanen ya kuma na barosu kafin ka tambayi tsarabar ko?". Ta kai karshen maganar tare da manna mashi towel ɗin hannunta a face ɗinsa tana ɗan jan dogon hancinsa cikin salo na soyayya.

"To ni Rahilarh menene ya dameni da su da zan tambayi ya suke?"....
Ɗan ɗaure fuska kaɗan ta yi. "Kai ko kake da damuwa da su".

"Kamar yaya kenan?". Da ɗan mamaki ya yi tambayar.
"E kai kake da damuwa da su tin da sun baka suruka sun kuma bawa ɗanka mata".

"What?". Ya faɗa da ɗan ɗaga murya. Jinjina mashi kai ta yi alamar kwarai kuwa, sannan ta ɗaura da cewa. "Muje in saka maka kaya sai ka zo mu yi magana........."

A hanzarce ya katseta da cewa. "A'a Rahilarh, ki faɗa mun wasa kike mun kawai a yanzu ba sai na je ko'ina ba".

Ganin da gaske yake yi yasa ta amsa mashi da e wasa ne, dan tasan halinsa, dama tasan zasu kai ruwa rana kafin ya aminta da Mahnoor idan ya aminta ɗin ma kenan, ba zai yarda ƴaƴansa su auri wasu ba idan ba larabawa jinin sarauta ba, shi ma yana da kabilanci sosai kamar dai Akka, basa san wasu bare a cikinsu, a hakan ma dai ɗan gara shi a kan su Akka, shi kabilanci nasa a kan ƴaƴansa ne kawai!.

Har wani ajiyar zuciya ya sauke jin ta ambaci wasa take yi mashi, hannunta ya ja suka wuce dressing room dan ta taya shi shiryawa, suna tafiya yana yi mata gargaɗin a kan kada ta sake yi mashi irin wannan wasa baya so, shi ƴaƴansa ba zasu yi aure daga waje ba, a cikin gida zasu yi aure kuma ƴaƴan sarakuna kamarsa zasu aura.

Da okey kawai ta bisa har suka shiga cikin room ɗin. Soyayya mai tsabta suka shiga zubawa kafin ta fito mashi da kayan barci, kwana biyun nan ya yi kewarta saboda damuwowi da suke a ciki, daga wannan sai wannan, sai yau ne ya damu damar samunta tana farinciki, ba komai ya sakata a farinciki ba kuma face auren Jaish, ta ji daɗin wannan lamari kuma zuciyarta ta kaunaci Mahnoor fiye da tinanin mai tinani, dik wasu qualities da ake san mace ta haɗa Mahnoor ta haɗa shi, tana da tabbacin idan King ya ganta shi ma ba zai yi ja in ja da zancen ba, wuyarta ya yarda ta ganta ɗin ne kawai.

Sun ɗauki a kallah 30 mins a cikin ɗakin suna zuba love ɗinsu suna soyewa kafin ya sanya sleeping dress ɗinsa su fito rungume da juna.

A bakin bed suka zauna, sai a lokacin ya lura da babyn dake kwance a saman bed ɗin, cike da mamaki ya jefa mata tambayar babyn waye? Daga ina ta ɗauko shi?.

Gyara zama ta yi suna fuskantar juna, cikin nitsuwa ta fara zayyane mashi komai da komai har da zuwanta gidan bappa da abin da ya faru zuwa ga kawo mata baby da uncle Jahiz ya yi.

Girgiza kai King ya fara yi kafin ya ce. "Hakan ba zai taɓa yiwu ba! Jaish bai kai yin aure yanzu ba, kuma koda ya kai ɗaya daga cikin ƴaƴan uncle Rahab nike san ya aura, babu ɗana da zai auro mun mace daga waje, dik cikin gida zasu koma su yi aure, dan haka wannan aure ban aminta da shi ba, yazama dole a kwancesa.

Shiru momma ta yi tana sauraransa har ya gama faɗarsa, sannan a nitse ta ce. "Dik hukuncin da ka yanke dai'dai ne bana da ja a kan hakan, dan nasan ba zaka taɓa san abin da zai cutar da ƴaƴanka ba, dan gobensu ya yi kyau zaka zaɓa masu mata masu inganci, amma ina san ka mun wata alfarma"......... Ta kai karshen maganar idanunta a kan face ɗinsa.

A taƙaice ya ce. "Wace alfarma kenan". Fuska a ɗaure ya yi maganar.

"Ina san ka bani sati guda, ka yi shiru a kan maganar har na tsawon sati guda, sannan sai na gabatar maka da matar tasa, idan har bata da qualities da kake buƙata a tattare da matan da kake san ƴaƴanka su mallaka to zan aminta da ka warware auren a mayar da ita kasarsu!".

Momma mace mai hikima da dabara, ko me zata kulla masu ta buƙaci sati guda kuma? Mu je dai zuwa.

"Rahilarh bafa zan yarda da batun auren nan ba, ni bana ma san ganinta, ban buƙatar hakan kawai a mayar da ita kasarsu a raba wannan aure, dan bana da buƙata".

Ganin da gaske yake yi babu wasa kuma babu alamar zai yarda da Mahnoor gaskiya, sai ta fito mashi ta wata hanyar daban.

Matsawa ta yi kusa da shi, a saman jikinsa ta kwanta, cikin salon kauna ta fara jansa da wasa, sam bata nuna ta damu da kalamansa ba, dik da ta damu ɗin a cikin ranta, tana kaunar Mahnoor tin daga kallon farko, ba zata taɓa bari a raba wannan aure ba.

King sai wani ɓata rai yake yi yana wani ɗaure fuska, cigaba da yi mashi wasanni momma ta yi tana ɓalle botiran rigan jikinsa cikin salo mai jan hankali. Ai bai san time da ya saki face ɗinsa ya fara biye mata ba, dan dama ya kwana biyu yana dakonta kawai dannewa yake yi, ta ji matuƙar daɗin hakan, dama buƙatarta kenan, dan haka sai ta kara zagewa sosai wajen ganin tasa ya shiga wani irin yanayi kafin ta zuba kalaman da suke cikin ranta.

Sai da suka yi nisa King ya afka duniyar sama jannati har da yi mata rumfa da faffaɗar kirjinsa yana zuba mata kalamai, yana sarrafata cikin kwarewa. Sai da ta fahimci an kai point ɗin da ba zai iya yi mata gardama ba, a wannan gaɓa komai ta ce zai amsa ne kawai, sai ta ce. "Ban tari numfashinka ba a ɗazun, kuma bana ja da hukuncinka a garemu gabaɗaya, amma dai wannan alfarma na nema da kabani sati guda, sannan ka yarda bayan sati gudan nan in gabatar maka da yarinyar, idan bata yi maka ba shikenana".

Haba King ya shiga duniyar da ba'a iya magana sosai, sai kawai ya gyaɗa mata kai alamar ya yarda, da kyar ya iya amsawa da ya yarda. Wani irin daɗi ta ji da har yasa ta shiga kara rikita shi da kyau.
Haka suka kashe junansu da soyayya na tsawon lokaci har suka raya darensu kafin babyn Khadija dake kwance a gefensu ya fara kuka. Da kyar King ya iya saketa ya koma gefe ya kwanta yana jin wani irin farinciki, ita kuwa ta fishi shiga farinciki saboda ta samu ya amsa mata buƙatarta, ko ya dawo cikin hayyacinsa bai isa ya musa mata ba, saboda ya rigada ya amsa, ta nan momma take cin galaba a kansa a kullum, amfani da karfin sha'awarsa take yi ta cinma buƙatarta, ba faɗa bare ɓata rai da kunci, cikin ruwan sanyi.


(Ina team Ramish? Yanzu na gano a ina Yah Ramish ya koyo wannan iskancin na sanya sexy night sleeping dress, gadan jaraba aka yi,😅 da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login