UK (LONDON)_*
........Kwance yake rai-rai a madaidaicin gadon nasa da mutanen Nigeria ke kira da 6-by-6. Sai dai wannan yaji katifa mai shegen laushi da bedsheet fari tas shima mai laushin gaske da ko'a ido ka kalla zaka shaida hakan. Yanda yake ɗan furzar da numfashi sama-sama da huttai ga zufa da tai ma jikinsa jagab zai tabbatar maka da ga training ya fito. Dan wandone na jc ƙarami da ya tsaya masa a fin rabin cinya da rigarsa. Sai takalma da aka san ƴan ƙwallo da su a ƙafarsa. Jikinsa ne a saman gadon ƙafafun zube a ƙasa. Iska mai nauyi ya sake furzarwa tare da buɗe idanunsa da launinsu ke a surke. Sam babu fara'a a tare da shi, dan fuskar nan ɗam take fiye da yanda kowa ya sanshi da rashin walwala acan baya....
Cikin kuzari da ke nuna cikakkiyar lafiyar gangar jiki ya tashi zaune da ƙyau, ƙaramin tsaki ya ja tare da yamutse fuska ya fara saɓule takalman ƙafar tasa. Anan ya zubesu tare da miƙewa gaba ɗayansa ya kama rigar jikinsa ya cire cikin kamar yanayin jin haushi ya jefar da rigar ƙasa. Dogon glass ɗin da ya kasance kamar bango guda a haɗaɗɗen bedroom ɗin nasa ya nufa. Ya kai hannu ya danna wani ɗan maɓalli green. A hankali glass ɗin ya shiga raba kansa biyu har ya bada ƙofa. Shiga yay nan ma kamar a ɗan fusace, lafiyayyen toilet ne ya bayyana da ni kaina na zama baƙauya a kallo, kai tsaye ƙarƙashin shower ya nufa ya sakarma kansa ruwa yana mai jan wata nannauyar ajiyar zuciya...
Aliyu Mika'il Idris Mawashi kenan da ke amsa sunan Smart Mawashi a duniyar ƙwallon ƙafa. Duk da dai kwata-kwata watanninsa uku kenan da dawowa ƙasar ta UK a London yay signing a club ɗin Queen City. Du da kasancewar ƙaramin club ne muna fatan ya zame masa wani tsanin kaiwa inda ba'ai zato ba. A yanzu Smart da muka sani na baya mai shiru-shiru da rashin sakewa da jama'a ya sake zarce hakan. Dan yanzu ba shiru-shiru ba, har miskilanci ma ya koyo. Hakan kuma ta faru ne a sakamakon faruwar shuɗaɗɗun abubuwan da suka faru a cikin watanni ukun nan da suka wuce. A gaɓar da tafi kowace gaɓa muhimmanci a tarihin rayuwarsa. A lokacin da ya gama shiryawa da tsarawa kansa gina rayuwa mai ban sha'awa da birgewa tare da matarsa. A lokacin da yay shirin ɗaukar dukkan yarda da amanar kansa data rayuwarsa domin damƙa mata. Sai labarin ya canja da ga yanda ya rubuta shi a zuciya zuwa rubutun ƙaddara.. Matarsa ta kufce masa a yayinda da burinsa na zama ɗaya da ga cikin ƴan ƙwallo a wata ƙasa ya cika. A hankali komai ya dinga dawo masa a zuciya dalla-dalla tamkar a yanzu ne yake faruwa. _(Bayan fitarsa gida a waccan ranar ya nufi gidansu cike da damuwar halin da ya jefa Lulu a ciki. Ya samu Asma'u taje aikan da Ammah tai mata gidan Aunty Bilkisu. Sai Maryam kawai da Ammah. Ko zaman kirki baiyi ba a daddafe suka gaisa da mahaifiyar tasa ya sanar mata yazo ɗaukar ɗaya daga cikin su Maryam ne dan Mawaddat babu lafiya. Hankalin Ammah ya tashi, ko neman Abba bata tsaya yi ba tace ya ɗauki Maryam suje idan Abban ya dawo zata sanar masa, dan ita a nata zaton ko ciki Lulun ta samu. Cikin sauri Maryam ta kimtsa tare da ɗibar kunun gyaɗar da sukayi domin tafiya da shi can su karya dan itama ko karyawar basu yi ba. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso kasancewar safiya ce babu yawan go slow a hanya. Sai dai me tun a yanayin da sukaga ƙofar falon a buɗe da littafin da ya gani ɗazu a saman gadon Lulu yashe a ƙofar shiga falon alamar an yarda bisa kuskure gabansa ya faɗi. Amma sai ya dake cikin ƙarfin hali suka shiga, a falo Maryam ta zauna shi kuma ya nufi bedroom ɗinsa yana faɗa mata taje ɗakin Lulun yana zuwa. Maryam ta amsa masa da to, yayinda shi kuma ya nufi ɗakin nasa. Bai wani jima ba sai gashi ya fito. Ɗan turus ya tsaya ganin Maryam kamar a ruɗe tana kai kawo. “K lafiya? Ba canai ki shigaba ina zuwa”. Da sauri Maryam ta juyo gareshi tana bashi amsa da “Yaya ai Auntyn bata nan ciki fa. Har toilet na leƙa babu kowa a ciki, hakama kitchen, sai dai duk an harmutsa wadrobe ɗinta an ɗiba kaya harma da akwati guda da aka bari kamar sauri ya hana a ɗauka”. Wani irin duka ƙirjinsa ya dinga yi, sai kuma ya nufi ɗakin da sauri shima. Kamar yanda Maryam ɗin ta sanar masa haka ya gani, sai dai shi nashi idon ya ƙara masa ganin duk wani abu mai amfani a ɗakin ma babu shi. Ƙafafunsa ne suka fara rawa, sai dai cikin dakewa ya cigaba da ƙarfafa kansa. Takardar da idonsa ya sauka kanta a bisa gado ya ƙarasa ya ɗauka. Na tsaneka Aliyu, bana son sake ganinka a rayuwata, amma kaje na barka da ALLAH azzalumi. Ashe wa'azin naka duk na yaudara ne kaima baka aiki da shi. Ka manta da ni har abada, dan ko'a hanya nai maka tazara irin ta sama da ƙasa, gabas da yamma. Idan ka wahal da kanka a nemana kai ka so, dan babu wanda ya isa sakani sake zama da kai koda Uncle Yousuf ne. jiyay jiri na nan ɗibarsa yay saurin kaiwa zaune yana ambaton sunan ALLAH. Ya jima a wajen zaune kansa na yamutsa masa har Maryam ta gaji da jira ta shigo ɗakin. Hankalinta ya tashi da