Kowa yana cike da murnar dawowar aunty Shahudah a gidan amma banda ni, ba komai ya jawo hakanba kuwa sai irin tarbar dana samu daga gareta bayan dawowata aiki a randa ta dawo.
Cikin ɗokin ganinta da kewa na nufeta, amma saita kalleni cikin wani yanayi na wulaƙanci da ƙyama kamar yanda ta sabamin a baya, daga ƙarshe ta koma dariyar aikina. Hakan ba ƙaramin ciwo yayminba, musamman yanda naga harsu Mom sun biye mata suma suna tayata dariyar. Daurewa nai nima na tayasu, dan na ɗaukama kaina alƙawarin insha ALLAHU sun daina ganin raunina a yanzu. Sai da muka gama dariyar sannan na nufi ɗakina nabarsu, su Aunty Aamilah na bata labarin yanda akai nazama dss a yanzu.
Ina shiga ɗakina na faɗa saman gado na fashe da kuka, tabbas wulaƙanci bashida ƙyau sam a rayuwa, ƙasƙanci ga mutum abune mai muni, amma a wannan duniyar babu abinda mutane suke alfahari dashi kamar ƙasƙanta ɗan uwansu musulmi.
“Sai kaga mai dukiya yana ƙasƙanta talaka koda da magana ne, mai ilimi na ƙasƙanta marashi, mai mulki na ƙasƙanta mabiyansa, miji na ƙasƙanta iyalansa, ɗan uwa na ƙasƙanta na ƙasa dashi. koyaya mutum yafi wani saikaga yana hura hanci wajen ganin yayi tozarci ga wanda bai kaisaba, kaicon mutane da wannan ɗabi'a, kamanta ALLAHN daya baka shima bai manta da shiba, sannan badan ka fisaba ya baka shi ya hanashi, ikonsane wannan yabama wani ilimi yayi wani jahili, ya bama wani dukiya yayi wani talaka, ya bama wani haihuwa yayi wani babu ɗa, ya bama wani mulki yayi wani mabiyi, ya bama wani lafiya yayi wani mara lafiya, kowa a rayuwa akwai jarabawarsa, kaine wane bashike nuna kafi kowa ba, kai ka samu kaza ko kake da kaza bashike nuna ALLAH yafi sonka ba, nima ALLAH yana sona, kuma ina sake gode masa da yanda yayini aunty Shahudah.......”
Tun daga wannan ranar na sake jabaya ga kowa da komai na gidan, Dad dama bai dawoba, hakama Yah Qaseem yayi tafiya tun washe garin dawowar aunty Shahudah gidan. ko a wajen aiki bani da wata walwala, Ummie da wasu abokan aikina sai suka danganta rashin walwalar tawa da kewar Yah Qaseem da bayanan, dan zuwa yanzun mutane da yawa sun san alaƙar dake a tsakanina dashi.
Ni kuma a ɓangarena ba damuwar rashin yah Qaseem bane da lamarin gidanmu kawai kecin raina, akwai wani abu daban danaketa ƙoƙarin tureshi a raina, dan bana fatan gaskata zancen zuciyata koda da wasa kuwa.
★★★★★★★★
Yau data kasance juma'a dai-dai da dawowar aunty Shahudah da kwanaki huɗu Dad shima ya dawo, kowa yay murnar dawowarsa tamkar yanda muka saba, ya kuma samu tarba daga matarsa harma da Aunty Shahudah dake ganin wannan dawowar tatace. Nidai ina daga baya-baya dukda jana a jiki da Dad keyi, dan motsi kaɗan ya sako sunana a cikin zancensa, hakan na kula baƙaramin sosa zuciyar Aunty Shahudah ya keyi ba, hakama Mom. Dana kula abin zaiyi tsamari saina zare jikina na gudu ɗaki, dama dai muna zaune ne muna cin abincin dare.
Ban sake yunƙurin fitowaba kuwa har safiyar washe gari domin nima naji a raina yakamata na basu waje su gana da mahaifansu. duk da kasancewar asabar ce babu aiki ban iya komawa barci ba, dan narigada na saba yanzu da yanayin tashin sassafe. Ina zaune akan abin sallah tun bayan idar da sallar asubahi ban tashiba, na lazimci azkar nai karatun Qur'ani, rashin abunyi ya sakani tashi nahau gyaran ɗakina, hakan sai ya jani tsayin lokaci har kusan tara da wasu mintuna.
Sama-sama nake jiyo hayaniya kamar na kuka, kukan kuma yaymin kama da muryar Mom. Nai azamar ajiye tawul ɗin dana ɗauka zan shiga wanka na fita. Sosai gabana ya faɗi saboda cin karo da Mom dake kuka iyakar ƙarfinta, Dad na riƙeta, daƙyar na iya haɗa maganganunsu, daga ƙarshe na fahimci ƙanin Mom ɗine ALLAH yayma rasuwa mai suna Usman, tabbas naji suna yawan faɗar sunan Uncle Usman, sai dai ban sanshiba, ban taɓa ganinsaba, dan duk zamana a gidan ban taɓa zuwa gidansu mom ɗinba, bankuma cika ganin ƴan uwanta suna zuwaba, kowa dai yasan halin wasu ƴan bokon nan da aƙidar rashin son takura.
Nima dai tausayin Mom ya sakani bin sahun masu sharar hawaye, nan dai Dad ya cigaba da lallaɓata, kafin yajata sama, muma yace duk mu shirya domin tafiya can gidan. Hakanne ya saka kowa nufar ɗakinsa mu duka.