Unguwar kofar mata dake kwaryar birnin kano
Hadarine ya haɗo ta gabas gari yayi wani irin duhu ga iska na kaɗawa amma duk da hadarin nan magajiya ita da maƙarrabanta ko a jikin su wai an tsikari kakkausa suyar wainarta take gefenta dinana ne zaune yayi zaman dirshan a ƙasa sai aikin rubutu yakai
ture kaga tsiyarta ta gyara ta juya wainar'ta ta dubi dinana tace
"Dinana wai lafiya tun da ka shigo gidan nan kake ta aikin rubutu wannan ai takardar kampo ce me za kai da ita......?,
dariya ya sheƙe da ita ya ɗaga paper nan wacce take cike tab da rubutun chaina yace
"Uwar shagalallu wannan wasiƙa nake wa mara yar gidan honourable jiya ta yomin wasika cike tab da turanci kin ganta nan ya ciro takarda a aljihunsa ya ci gaba da cewa
shine nake bata amsa da chainanci tun da nasan kaf gidan nan in bake ba ba me iya fassaramin wannan turancin ke ma wallahi wannan turancin yayi miki tsauri......,
gabaki ɗayan su suka sa dariya ban magaji da ta haɗa rai sai ban kawa dinana harara take tace
"Dinana fitar min daga gida tun da abin naka rashin mutunci ne ina laifin ka tsaya iya kanka sai ka haɗo har da ni....,
abin juya waina ya dauka ya kwashe mata ganin tana shirin konewa yace
"to yar hau kina masifa wainar tana kokarin konewa.....,
fakar idonta yayi ya gutsire gefe kasa kasa yace
yar masara ina tare da ke kullum hayaki ba faɗeni ko rabin fafe ba zaki iya ban ba to bara inci ta haram
Ahayyye rasss wani ɗan daudo ya shigo yana wata iriyar rausaya da sauri kahu bulama ya fito da hannu ya nuna mai hanna yace
"Maza koma inda ka fito wallahi ba zan yarda da wannan iskancin a gidan nan ba.....,
rataya jakarsa yayi ya kama haɓa yayi wani fari da idanuwansa yace
"Kahu wa yake wallahi ina bakin ka gurin magaji nake zuwa ba gun Ka ba cin arziki ya kawo ni ato.....,
da sauri ya yo kansa matsawa yayi yace
"auzubillahi me zan gani shi yasa masifo sukai mana yawa ina mace kana ƙoƙarin taɓani innalillahi magajiya....,
sororo kahu bulama yayi magajiya ce ta taso gyara zanin da ta ɗora akan doguwar rigar ta tayi sai taunar chingum take ƙwai ta saki ya bada wani sauti ƙasss ƙas tusssh tace
"ki rabi ba ruwan ki wannan fa kahuna ne kai kahu ba ruwan ka da rabi ciniki tazo tai min a unguwar nan ba akwai masu sai da waina ba amma ta tsallake ko ina ta zo guna gaskiya kahu ka dinga jan girman ka.... kullum sai kai faɗa da wa'yanda suke zuwa guna....,
Zani rabi ya bankaɗe yace
ato faɗa mai kullum yana mana kallon hadarin kaji gurin wasu yan mata dake kan tabarma suna hura taba suna caca ya zauna yana taunar chingum
babbar rigar'sa ya gyara yace
"to nace ba ....dan Allah zan sami wannan wainar sai ki ci gaba lissafi duk ranar da muka koma Maiduguri lokacin da komai ya lafa sai in biya ki..akwai huluna na dana saka mantawa nayi ban dauko suba lokacin da muka tawo gudun hijira garin nan zan in siyar in baki bashin ki.....,
da sauri ta kallesa tace
"Kahu...,
Na'am magajiyar ya'yan Allah ya shirya
Kahu.......kahu
hularsa ya gyara yawa an kifa lotsassiyar tasa yace
"Magajiyar karuwai ina jinki....,
cikin hausarta mara fita tace
"wallahi kahu ai kafin ta ƙarasa yace
"Haba yar gidan faɗimatu dan Allah temaka min.....,
kai dai wallahi malam Allah ya shirye ka me zanyi da abin da ya fito daga hannun yan daudo da karuwai da yan sane wata mata ta fito tana masifa
jin dan shin huka tayi a huyanta jiyowa zata yi taji waya sa mata huku ji tayi ance
Kina jiyowa sai na burburma miki huƙa a hanci ta huce ta maƙoshin ki magajiyar kike faɗawa haka yana wani cije baki alamar rikakkan ɗan daban
Wata uwar buɗa magajiya ta saki tace
Manjagara sauke huƙarnan wallahi nasan in har ina tare da ku bani da sauran damuwa maza sauke'ta kallonta yayi yace
"Magajiya da kin barni da yar hau wallahi in ci kutumar....ubanta la'ada waje yasin.....,
Manjagara nace ka sauke ta nace