Kuka yake sosai gurfane a gun wani kabari,wanda yanayin kukan nasa ze tabbatar maka cewa haqiqa yayi babban rashi,musamman yanda idanuwan sa suka kumbura sukayi wani irin jajur ta yanda duk wanda ya kalle sa dole se nashi idanun sun ciko da qwallah sbd tausayi_.
_A nn gurfanen da yake ne wani yazo shima se kukan yake ya tada shi ya rungume shi sosai a jikin sa,se rarrashin sa yake yana bashi magana,amma sam ya kasa daina kukan har se da yaja shi suka fita daga maqabartar_.
*Baya Kafin faruwar hakan*.
芦芦禄禄禄芦禄禄
Tsaye yake gaban mirror d'aure da farin towel a qugunsa yana taje sumar kanshi,wanda kallo d'aya zaka mishi kasan cewa hadadden guy ne shi,first class da sam bai aje kanshi kusa ba.
Sosai yake matuqar ji da kanshi sbd Allah yayi shi me tsananin kyau tamkar shi yayi kan shi.
Shiyasa sosai kyawawan en mata ke rubibi akan sa amma sam baya kula su,mace d'aya kawai yake kulawa wato "Sophie"wata classmate d'isshi da sukayi karatu tare a London wacce yanzu haka tana nn Nigeria ta biyoshi.
Bayan ya gama taje sumar kanshi ne ya tafi da cumb d'in yana qara kwantar da sajen fuskar shi dake kwance luf kan farar fatar shi tas wacce tamkar ka kwanta jini ya fito.
Sai da ya feshe jikin sa da body spray snn ya nufi kan bed inda ya ajiye kayan sawar shi da ya ciro,ya zauna tare da cire towel d'in jikinsa ya cillar gefe,ya janyo guntun wandon sa fari qal ya saka snn ya saka dogon wandon sa na suit silk fari,rigar ciki baqa yayi stocking da black belt,ya saka necktie fari,sucks baqaqe da takalmi baqaqe snn ya saka er samar shi fara,ya fesa turare kana ya d'auki briefcase d'issa ya fito bai zarce koina ba se 6angaren iyayen shi.
Ya sami mahaifiyar tashi ta fito daga kitchen tana jera breakfast kan dinning.
A natse ya gaida ta fuskar sa ba yabo ba fallasa,byn ta amsa yace am going.
Da sauri ta kalle shi tace"breakfast fa gashi har na kammala had'a komai ka d'an tsaya mana kaci ko kad'an ne"
Yace"No umma ina sauri ne"
Ba tare da ya jira me zata ce ba yasa qafa ya fita abin shi.
Ta bisa da kallo kawai tana mamakin yau ko Abban sa bai je ya gaida ba ko lafiya,nan se ga Abban na shi ya fito cikin shirin sa tsaf na fita,ta kalle sa tace kaddai kaima fita zakayi hakan nn baza ka ci komai ba kmr yanda saifuddeen ya fita.
Komai be ce da ita ba se d'an murmushi yayi had'e da girgiza kansa a lokacin da yaji tashin motar saifuddeen,kana ya qarasa gun dinning yaja kujera ya zauna yana fad'in"Halan me saifuddeen yace maki da zai fita?
Umma da ta janyo plate zata fara serving nashi tace"ce min yayi sauri yake"
Abba yace"haka dai ya gaya miki amma ba wani sauri da yake da akwai dalilin da yasa baya so mu had'u"
Umma tace"shi saifuddeen d'in?
Yace"shi d'in yaron da ko kad'an baya so in masa zancen aure amma jiya se gashi na ganshi da wata baturiya a office d'inshi yanda na gansu abun takaici matsayin sa na musulmi yana biye mata kan lalaci irin nasu na turawa.
Numfashi umma ta fitar snn ta zauna a hankli tana kallon Abba wacce da alama tasan saifuddeen na tare da Sophie ba yau ba amma se tace "kana nufin yanzu saifuddeen duk jiji da kanshi yana kula en mata.
Abba yace"Hm Mamn yusra knn ae duk namijin da kika ga baya kula mace to ba lafiyar sa qalau ba,amma irin kulawar da ake so shine namiji ya nemi mace da son aure ba irin shirritar da naga saifuddeen ya d'auko da wacce sam aure bazai ta6a shiga a tsakanin su ba,dan haka wlh sam bazan yarje masa wnn shashan cin ba,ni aure zan masa ko yana so ko baya so!
Yana kaiwa nn ya fara cin abincin da umma ta zuba mishi.
Umma dake kallon sa tayi shiru bata sake cewa komai ba,se abinci ta zubawa kanta ta fara ci cike da tunanin yanda zata shawo kan saifuddeen ya rabu da Sophie,dan ko kad'an bata son huld'ar sa da ita shiyasa ma bata so Abba yasan da ita ba.
Se da yamma liqis saifuddeen ya sake dawowa 6angaren su umma,sanye da qananun kaya a jikin sa,rigar fara ce tas me guntun hannu,rubutun jikinta baqi ne manya da aka rubuta *Being human*,wandon kuma fari ne tas tree quarter wanda duk da cewa fuskar sa ba annuri amma yayi matuqar kyau se qamshi ke fita a jikin shi sbd mutum ne shi da sam baya wasa da turare yana son qamshi sosai a rayuwar shi,shiyasa jinin sa ya had'u da Sophie dan haka take itama ko yaushe cikin qamshi take.
Umma dake zaune kan doguwar kujera hannun ta riqe da littafin addu'o'i ta kafe idon ta a kansa har ya qaraso ya zauna a kusa da kujerar da take zaune,still fuskar nn tasa ba annuri ya kalle ta yace"umma i will back to England"
Umma tace"meyasa?
Yace"kmr yanda suke buqata"
Tace"kmr ya u mean zaka kar6i tayin su ka koma can da aiki ka bar asibitin mahaifinka saifuddeen?
Yace"eh"
Da mamaki tace"why?
Muryar sa a hnkli can ciki yace"Abba yasa min ido umma ni kuma bana so"
Umma ta numfasa tace"saifuddeen knn idan Abban ka bai sa ido akan rayuwar ka ba to wa kake so ya kula da rayuwar ka ya nuna maka hanyar da ta dace kabi iye"
Shiru yayi kmr beji me tace ba taci gaba da cewa"saifuddeen kaifa musulmi ne bai kamata dan kayi karatu a qasar turawa ba kazo kana yin irin halayen su marassa kyau snn kuma a maka magana kaji haushi,ka sani fa ko kad'an Abban ka bai ji dad'in yanda ya same ka office kaida Sophie ba dan nasan ba makawa ita ce ya ganku tare tunda yace min baturiya.
A qufule yayi d'an guntun tsaki yace"umma bafa wani abu ya ganmu munayi ba fa,just ya samu tana kan laps d'ina muna magana shine kawai se ya balbale ni da fad'a wai kar ya qara gani na da ita,wat kind of this umma.
Umma dake kallon sa tace"Hum Saifuddeen yanzu kai a ganinka ba komai bane Abbanka ya ganka da mace kan qafafuwan ka,saif ae ko matar ka ce dole ka d'anji kunya bare Sophie wacce.....dafe kansa yayi sbd mgnr ta ishe shi,yace"umma plz a daina zancen nn haka is enough ni yunwa nake ji tun safe banci komai ba"
Ba yanda umma ta iya se ce masa tayi olryt me kake so kaci?
Yace"abu me d'an nauyi da zan iya ci.
Nan umma ta tashi a hnkli taje gun dinning wacce dama ta kammala girkin ta na yamma,ta d'ebo masa,tuwon semo ne da miyar agusi wacce taji naman rago sosai tayi kyau har ta gaji se qamshi ke tashi,ta had'o mishi ruwa da lemu ta kawo mishi ya kar6a tare da mata godiya snn ya fara ci.
禄禄禄
Da dare umma da Abba suna zaune a falo suna kallon labarai,Abba ne saman kujera umma kuma tana zaune a qasa manne jikin kujerar yayinda wata yarinya da bazata wuce shekara biyar ba wato wacce ake kira da yusra tana kwance kan qafafuwan ta tana bacci,umma na fmn shafa jikinta a hankli.
Abba yayi gyaran murya yana me kallon umma yace"Maman yusra wata magana nake so muyi"
Umma ta kalle sa tace"tou Allah yasa ba wani abu bane Alhj"
Yace"ba wani abu bane so nake ki amince na had'a auren saifuddeen da zarah.
Umma ta numfasa tace"cabd'i Saifuddeen da zarah fa kace Alhj?
Yace"Eh haka nace ko anyiwa zarah miji ne ban sani ba?
Aa ae kasan baza ma a fara ba baka ji ba amma dai kasan sam saifuddeen bazai ta6a yarda ya auri zarah ba ko.
Abba yace"Zarah bata da wani aibu da saifuddeen zai ce bazai so ta ba tunda gwargwado dei tayi karatu har gaba da primary"
To Alhj kasan fa zarah gabad'aya a qauya tayi rayuwar ta zuwan ta birni jefi jefi ne.
Abba yace"ae shiyasa nace ta dawo nn da zama dmn ki wayar mata da kai,na kuma sata a university taci gaba da karatu sannu sannu har su zo su saba ita da saifuddeen kafin nasa lokacin auren su.
Umma tace"gaskiya Alhj kawai da ka bashi za6i ya kawo wacce yake so dan bana tunanin saifuddeen ze ta6a sakarwa zarah fuska har sukai ga sabawa da juna bare har ace aure ya shigo tsakanin su abun da kmr wuya.
Yace"Maman yusra ba wani za6i da zan bashi Zarah nake so ya aura,dan haka abunda kawai nake so dake shine gobe ki shirya kije Rimin dako kizo da Zarah in yaso se kiyiwa inna bayanin komai nasan in taji baza ta qi ba inshaa Allah,ban sani ba ko dai ke ba kya son Zarah ta auri saifuddeen ne.
Umma tace"ba haka bane Alhj ae Zarah in taji nasan ba qaramin farin ciki zatayi ba dan dai sosai tana son zaman birni,a duk lokacinda naje ji take kmr ta biyoni.
Yace"to ai duk kece tun tana qarama ba yanda banyi ba kan tazo nn tare damu ta zauna kika qi alhali yarinya naso.
D'an murmushi umma tayi tace"uhm Alhj knn ae de yanzu komai ya wuce Allah ya nuna mana gobe lafiya se inje inzo da ita d'in"