Showing 282001 words to 285000 words out of 397328 words
tumbin raɗaɗa yana wasu abubuwa, cabdijan.
Bai sakar masa fuska ba ya ce" Ke wuce mana ko sai na finciko ki?"
Daga shi har ita a zabure suka kalle shi, wannan shine wanda mijinta ya ɗauka fa, wanda ake masa ikirarin kaca, kaca ɗin nan shine idan uncle Hamat na so ya kirta wulaƙanci yake turawa ya kori mutum korar kare, kaca baya jin maganar uban kowa sai ta kuɗi da ta uban gidansa, yau kaca ne ke yin wannan abin a gaban Uncle Hamat?
Ganin ta ƙi fitowar ya sa ya shigo ya tankaɗo ƙeyarta dan kaca bashi da mutumci, shaye shaye ya gama yi masa huɗuba uncle Hamat ya ɗauko shi aiki, a tsorace uncle Hamat ya riƙo hannunsa yana faɗin" Kai, kana da hankali kuwa? Matar tawa ka yiwa haka? Kaca na kore ka, ka je na kore ka ɗan iska."
Kaca ya wani karkace baki ya ce" Zan bajeka a nan Alƙur'an, ka ji korarre dilla sakeni kar in idasa gawar da ba tawa ba, wannan ai yawa ne, ya ya uban] an iska zai ce a koreta kai kace a barta, ai mu aikinmu kala biyu ne dama, muna yiwa kuɗi biyayya da kuma iyayen gidanmu, wanda ya fita yanzun ai babba ne, wallahi biyayya sak ko ba sisin kwabo, mu je ke ɓace min daga nan kar in baje ki a nan."
Mutuwar tsaye uncle ya yi kafin ya juya a haukace ya nufi inda wayar talho take ya warta ya shiga daddanawa dan ya yi kiran Aba, dan ya sani Aba kaɗai ne zai cece shi daga wannan bala'in, ko irin sukar da ƙirjinsa ke masa baya ji dan wannan tashin hankalin, sai dai ga wani tashin hankalin an yanke layin ɗakin da yake, abinda yake yiwa mutane idan basu daidaita harkar kuɗin ɗaki yadda ya kamata ba shine yau ya sauka a kansa, yanzun kam da gasken gaske ihu ya saki na hauka dan zuciyarsa gaba ɗaya ta gama tsinkewa ta rabe gida biyu ta nemi bugawa, da ƙarfi ya damƙi ƙirjinsa yana numfashi da baki dan wallahi baya son mutuwa, duk rintsi baya son mutuwa, a da yana kwanta musu yana musu iya shege bai wani riƙu ba iya riƙuwa, a yanzu da ya ji wannan sukar da ta ratsa har ƙwaƙwalwarsa sai gashi a ƙasa yana neman taimako.
Zaune ya yi a mota ya kasa tashin ta bare ya fice a asibitin, wasa wasa maganar Yusrah da aka faɗa masa yana ambatar sunan ta ya tsaya masa a rai, haka kawai wasu abubuwa ke ta dawo masa a rai da son sai ya auna komai a ma'auni yanzu yanzu ko dan ya samu salama, haka kurum yake jin yana so ya san me ye tsakanin shi da ita da har ya yi zautuwar da yake son nuna shi mahaukaci ne a kan ta? So ne? Wace irin soyayya kenan? Irin wacce ya san da jimawa uncle ɗin nasa yana taɓawa ta neman mata, shi ma ba wani sosai ya bibiyi abun ba duba da kowa da irin rayuwar sa ai. In bai manta ba haɗuwar sa da ita ta farko tana kuka ne ta fito daga ofishin uncle ɗin nasa, me hakan ke nufi to? Wani abu ya mata? Ko ya faɗa mata? Ko akwai wani abu a tsakanin su? Sannan me ya sa ta gaggauta barin aiki a asibitin? Har take ikrarin asibitin azzalumai, sannan take kiran uncle Hamat tsohon najadu? Sai kuma rana ta ƙarshe da ya gan su tare, kusancin dake tsakanin su, bayan ya ture ta yadda shi uncle ɗin ya tare ta kamar dama mai jiran yi mata maraba... Kai ya Allah! Wai me ye haka? Me ye tsakanin sa da wacce a yanzu ake kiran ta da sunan *matar sa*?
Kamar wanda ke neman zarewa shima kawai ya cije leɓen shi na ƙasa kaɗan tare da yin murmushi ya ayyana _'Me ye haɗin ki da uncle ɗina Y. Turaki?'_
Sai kuma ya saki leɓen nasa ya sake faɗaɗa murmushi yana jin wani ƙwarin guiwar matse mata wuri har sai ya san ko ma menene daga gare ta, wayar shi ya ɗauka ya dannawa Aba kira, jim kaɗan Aban ya ɗauka ya kara a kunne, cikin ladabi yace "Aba, kaga jikan Haidar fa rigima kawai yake shi a dole wurin ka yake son zuwa yanzu, kuma gashi daga asibiti ne na ɗauko shi."
Da jin daɗin hakan Aba yace "To me ye a ciki jikan Anza? Ka kawo shi mana, nima nayi kewar sa ai, dama asibiti ne zan leƙa wajen Hamat, amma ka zo min da shi ɗin, idan ya sallameni ai sai na tafi ko?"
Wani murmushi ya saki yana ayyana _'Idan mun sallamekan ba kenan Aba.'_ A zahiri kuma sai ya amsa da" Shikenan Aba, gamu nan ƙarasowa."
Tayar da motar ya yi bai zame ko ina ba sai asibitin Dr. Siddik, anan ya ɗauko Safwan Siddik na ƙara kwatanta masa duk wani abu da ya dace a ci gaba da ɗora Safwan ɗin a kan sa, idan kuma wani abu ya ɗaure musu kai to a gaggauta dawo da shi asibiti dan ya duba shi, godiya ya masa tare da jadadda mishi zai dawo ya same shi daga baya in sha Allah sannan suka tafi.
Gidan shi ya fara wucewa ya ɗaukar ma Safwan ɗin kayan jikin sa yana faɗa masa za'ayi taro ne, sannan ya tarkato har su Meem a mota suka nufi gidan Aba kai tsaye.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
21/06/2024, 22:09 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*70*
Suna shigowa farfajiyar gidan ya kalli Safwan dake riƙe tab a hannun shi yace "Son, mu yi wata shawara ko?"
Da kulawa Safwan ya kalle shi ya gyaɗa kai alamar, ƙara gyara zama ya yi ya fuskance shi sosai yace "Idan muka shiga ina so ka wa Aba rigima dan kar ya fita, kaga asibiti fa yake so ya tafi ganin uncle, kuma idan ya gan shi shima zai iya kamuwa da rashin lafiya, dan haka ya zama deal tsakanin mu, zamu hana Aba tafiya ko?"
Da gamsuwa Safwan yace "Kai kai! Dad zan hana shi tafiya dan bana so wani abu ya same shi gaskiya."
"Good boy." Ya faɗa yana bashi hannu suka tafa sannan suka fito yana tura shi a kujerar shi bayan ya tayar masa ita tsaye, yana so ne ma sai sun shiga ciki sannan su ci gaba da tattakawa da shi.
Tunda ya shigo falon ya tarar da yadda kowa ke ta kai da kawowa na shirin wannan zama da za'ayi anjima, Nabihat kaɗai ya gani a falo zaune tana waya, da ganin shi ne ta aje wayar ta taso da fara'ar da a baya bata ma Safwan ita tana wani shafa jikin shi da tambayar sa ya jiki, shi di kallo ɗaya ya mata ya kawar da kan shi ba tare da ya ko tuna wai an kai kuɗin auren shi gidan su ba. Saida ta kalle shi bayan Safwan ya gama bata haushi ganin shi kanshi yaron bai saki jiki da ita ba sannan ta wani kashe murya kamar yadda ta saba tace masa "Barka da zuwa Yayana?"
Kallon ta ya yi fuskar sa a haɗe, kallon gargaɗi kawai ya aikata mata mai nuni da kar ta ma ce za ta fara masa irin haka a gaban ɗan shi fa yake, ita ko kunya ba ta ji wai? Sai kawai ya kawar da kai ya amsa mata da "Barka."
Tare da tura kujerar Safwan suka nufi falon Aba, a nutse ta shiga take masa baya tana sake rusuna muryar ta sosai tace "Yaya AA, dan...Allah...."
Yadda ya juyo ya zuba mata idanu ya sa ta kasa ƙarasa maganar ta, a ɗan gimtse yana wani basarwa yace "Me ya faru?"
Idanun ta sak a kan fuskar shi da duk wani sassa na jikin shi tana ta karairaya tace "Dama, lambar ka nake so Yaya AA, ka ga fa ko sau ɗaya baka taɓa kirana ba."
Ta ƙarashe maganar a mugun shagwaɓa har da turo baki, da mamakin abun ya dube ta sannan ya saci kallon inda Safwan yake, sai ya ga Safwan ɗin ba su yake kallo ba bare ya damu da hakan, wannan kuma ya sa ya yarda lallai iyayen ɗan sa na farko ba ƙaramar tarbiyya suka ba yaran nan ba, dan ko Y. Turaki da take masa rashin kunya son ran ta wallahi bata masa irin matsawar nan da maƙe murya idan tana magana, uwa uba ta zuba ma fuskar sa idanu haka kamar za ta nemo munin shi. Da ɓacin ran haka yace "Amma ba gaki anan ba, me ye na buƙatar lambar kuma?"
Da kafiya irin wacce mahaifiyar ta ta koya mata akan shi ta sake ɗan bubbuga ƙafafu ita a dole son birge shi take yi tace "To amma Yaya AA ni fa nan kusa kaɗan zan zama mallakin ka, kuma ace har yanzu bamu da lambar juna? Ai bai kamata ba ko?"
"La'ilaha illalah!" Wallahi da gaske abubuwa take masa masu kama da na ƴan iska, shi kam ko dan baya harkar da ta shafi mata, shiyasa wallahi ko ya mace ke irin haka sai ya dinga mata kallon kamar dai...haba mana fisabilillah! Ya yarinyar nan take son zubarwa da Chef mutumci ne haka, zai iya tuna tana da Yaya fa mace, amma wallahi yanzu haka ba zai ce ga kamanninta ba, kuma tabbas Yayar ta ƙawar Intisar ce kuma har gidan nan tana zuwa, amma me ya sa ita ba ta zama irin ta ba?
Ita ta yi shagwaɓar, shi ya ji mata kunyar har ta saka shi shafa ƙeyar sa yana ƙara satar kallon Safwan yaga dai da gaske ɗan shi baya shiga hurumin da ba nasa ba, sai kawai ya ɗago ya kalle ta da ɗan sakewar fuska gudun kar ta masa abinda ba shine ba a gidan nan dake da Anna a ciki da Aba ya sa hannu aljihu da niyyar ya ciro katin shi amma sai ya ji wayam babu, daga littafin check sai wallet da kuma waya, a nutse ya tara hannun shi ya mata alama ta miƙo masa wayar ta, da ya so bata lambar da uban kowa ma na iya samun ta, amma kuma sai ya rasa dalilin da ya sa shi shiga ratttaɓa mata lambar da iya makusanta da wanda muhimmin abubuwa ke haɗasu ne suke da ita, miƙa mata wayar ya yi ita kuma wajen karɓa har saida ta ɗan haɗa da hannun shi da tunda ya karɓi wayar take kallo ta ƙura masa ido tana ayyana _'Kuɗi masifa ne jama'a, iya yatsun masu kuɗin nan ma fita daban suke yi, ka dubi hannun gardi kamar wannan amma uwa na jarirai.'_
Haɗawar da tayi da yatsun shi yasa shi ɗaga idanun shi ya kalle ta, sai kawai ya tsinci kansa da sakar mata murmushi ba zaki gane waye ni ba yarinya har sai na nuna miki ɗaya fuskata da baki sani ba, sai kawai ya girgiza kai a hankali ya juya tare da Safwan suka shige falon Aba yana ayyana _'Irin wannan a ƙafa aka ɗaura maka ma ai ka kunce ka gudu, ko me ye duk wannan abubuwan da take yi?'_
Nabihat kuma na ganin shigewar shi ta daka tsalle ta wani juyi tana sumbatar wayar ta, sai kuma ta ji wani ƙamshi irin na Sol de janeiro ɗin nan na tafukan hannaye, shinshinar wayar ta ƙara yi tana furta "Shegiya ni, wallahi Mama na samo lambar, ashe dai kwarkwasa za ta kayar da kai ƙasa warwas."
Da wata irin isa da ƙasaita ta shiga takawa tana haurawa sama tare da saka sunan da ya dace da shi a lambar, tana shiga ɗakin ta ta aje wayar ta fara cire kayan ta dan ta shiga wanka, dan tayi niyya zaman nan da za'ayi ita ma za ta bayar da kyauta kamar yadda maman ta ta umarce ta, shiyasa ma za ta fita yanzu tunda azahar aka yi ta siyo kyautar, daga can za ta wuce wajen kwalliya dan bata son wanda za ta ma su Manal ta yi mata, ba ma za'a mata yadda take so ba a gaban su, kwalliya take so ta yi da za ta fasa taron ta zama kamar ita ce amaryar, ba dai suka yarda ta ga kayan da za'a saka wa Yusrahn ba? To ita ma kwatankwacin su za ta saka kuma kala ɗaya da na Yusrah, sannan ta ci kwalliyar da ta fi ta Yusrah ɗaukar hankali, uwa uba ta miƙa mata kyauta duk da bata son haka, amma a cewar Maman ta za ta ƙara siye zuciyar Aswan, zai yi mamakin ta ya za ta ba wacce ta rigata shiga gidan shi kyauta? Shi a ganin shi ai ba'a mata daidai ba, hakan zai sa ya yi ta tunanin hakan har ta zauna masa a rai.
Tunda aka yi la'asar ƴan matan ke ɗaki da mai kwalliya tana tsantsara musu, Yusrah kuma suna ɗakin gyaran jikin da Anna ta sa ake fara yi mata kafin a mata kwalliyar, Anna kuma tsaye take kan ƙafafun ta ita da aunty Intisar a madafa tare da masu aiki ana ta shirya abun taɓawa. Sai Aba da yau yake mamakin irin rigimar da Safwan ke ta yi masa, da ya motsa shi ma ya bishi cikin tafiyar sa ta koyo ya maƙale masa, har kuka yake masa na shagwaɓa wai kar ka fita Grand pa, hakan ya sa dai da yamma lis Aban ya kalli AA ƙasa ƙasa yace "Jikan Anza, wai ko dai wani abu ka ma yaron nan da ba ya so na bar ku tare?"
Buɗe baki AA ya yi yace "Lah! Aba ni kuwa me zan wa gudan jinina? Kawai ya ce dai kai yake son gani, wataƙila ko mafarkin ka ya yi Aba."
Sai kawai Aba ya sauke ajiyar zuciya jiki a sanyaye yace "Hakan sai ya fara tsoratani, ina tunanin dai ko ya hango min mutuwata ne a nan kussssss...."
Da wani irin sauri AA ya rufewa Ab baki yana lumshe idanu, saida ya yi ƙoƙarin haɗe kukan da ya ji take ya zo masa sannan ya girgiza kai yana kallon Aban yace "Please Aba, mu canza topic."
Murmushi Aba ya yi yana girgiza kai shi ma a ranshi yana ayyana _'Jikan Anza kenan, ina tsoron idan wannan rana ta zo ka zama ƙane ga ƙannen ka, dan na sani ne za su fika iya jurar wannan lamari da yake tilas ga kowa.'_
A zahiri kuma sai ya kalli Safwan yace "To aboki, akan me ma muke tattaunawa?"
Safwan da ya ƙara narkewa a jikin Aba yace "Akan yaƙin sayyadina Aliyu."
Da irin kwarzanta abun Aba ya waro idanu yace "Wow! Ka ce wanda na ci sunan sa kenan?"
Jinjina kai Safwan ya yi alamar e tare da cewa "E papy, kai ma jarumi ne kamar shi, shine fa takobin sa take da harshe biyu, kuma malamin mu na islamiyya ya faɗa mana bai taɓa faɗuwa a yaƙi ba idan ya kara tsakanin sa da wani, aunty Yussy kuma ta ce min sayyidina Aliyu wai zaki ne."
Dariya Aba ya bushe da ita yana faɗin" Au! Wai ne ma? Kai baka yarda duk mai sunan Aliyu zaki bane?"
Dariya Safwan ya yi ya ɗan kalli AA dake kallon su da nishaɗi yana jin wani farin ciki, sai kuma ya ma Aba alamar ya kawo kunnen sa ya ji, duƙowa Aban ya yi Safwan ya raɗa masa" Na yarda, amma kuma Abana ne zaki, tunda ai shine soja ko?"
Riƙe haɓa Aba ya yi yana kallon shi yace" To, da alama kaima irin tunanin uban ka ne da kai, duk namijin da ba soja ba to a mata kuke kallon su ko?"
Sai kuma ya jinjina kai yace masa" To ka tambayi uban naka ka ji, Aliyu yana nufin Haidar ne, Haidar kuma yana nufin zaki, sannan duk jarumtar Baban ka a wajen ɗan Anza ya samo ta, ka tambaye shi ka ji."
Dariya AA ya yi yana girgiza kai cike da jin daɗin dramar ta ɗan sa da kuma Aban sa, sai dai bai ce musu ƙala ba har aka kira sallah magrib duk suka fita tare har da Safwan a masallacin Aba dake manne da gidan, su kam niyyar su sai ma sun yi sallah isha'i za su shirya tunda shirin su ba wahala ne da shi ba kamar na matan da ya tabbatar har lokacin mai kwalliyar nan tana gidan bata tafi ba.
Bayan sallar isha'i da kamar minti talatin AA ya nufi falon daga ɓangaren da aka sauke uncle Sulaiman, domin can yaje dan ya shirya, ya bar Safwan da Aba wanda tun ɗazu Aban ya sanar da shi suna falo fa, hakan na nufin zuwa yanzu duk an sauko falon kenan?
A nutse ya saka hannunsa ya buɗe falon ya shiga da sallama a saman leɓensa wacce duk suka amsa sakamakon ba hayaniya ba komai a falon sai ƴar fira ƙasa ƙasa da tagwayen Anna ke yi na takaicin