Showing 264001 words to 267000 words out of 397328 words
zai nemi jikan Anza ya warware shi, da kula ya ce" Ƴata wai kukan na abinda mamanki ta miki ne?"
Yusrah dake jin irin mintsinan da aunty Furera ke mata ta tsayar da kukanta dan dole, kanta sadde ta ringa gyaɗa kai, su kuwa suna fasarce me gyaɗa kan nata ke nufi kamar sarki da fadawansa, Aba ya sauke ajiyar zuciya a tausashe ya ce" Alhamdulilah, zan fi kowa farin cikin ki amshi auren nan, zan fi kowa farin cikin ganinki matsayin matar AA, ki yi haƙuri kin ji? Ki yi haƙuri ki daina kukan nan, kin san rayuwa kowani bawa da irin yadda yake gabatar da lamarin rayuwarsa, ki yiwa Goggonki uzuri, haka Allah ya halliceta sai fatan shiriya, ki daina kukan nan haka kin ga daga nan zan je asibiti in ga jikan Aliyu ta yiwu yau a bamu shi mu yi gida, kin ga kina zuwa zaki same shi a gida ko? Kuma wajen Annarku za'a kai ki fa sai an gama miki gyaran gidanki zaku tafi kin ji? Dan haka kar ki ɗaga hankalinki kin ji?"
Yusrah ta sake amsawa da eh kanta a ƙasa, Aba ya yi murmushi ya ce" Allah ya miki albarka, Allah ya sanya albarka a rayuwar auren ku."
Yanzu su aunty ke amsawa ita dai kanta a ƙasa, uncle Sulaimane ya dire kuɗin sadakinta shima ya ƙara da nashi nasihar sannan ya miƙe ya raka Aba, suna fita aunty Furera ta sauke ajiyar zuciya tana dungurar kan Yusrah ta ce" Da kika ce a sake ki yau ban san irin dukan da zan maki ba."
Yusrah ta fashe da kuka ta ɗora kanta a cinyar aunty Furera tana faɗin" Na shiga uku, da ma shi ne mijina? Aunty baki sun waye shi ba, inna lillahi wa inna ilaihi raju'un, ina Bilal ɗin yake ne toh? Hajia me na mata da zafi, dama ina jin vidion nan ta fita hankalina ya tashi, wallahi wallahi tun a lokacin sai da na yi kuka aunty ta ce kar ta ji kar ta ga na faɗawa kowa, ashe har sun ji?"
Aunty Furera ta taɓe baki tana faɗin" Kukan dai yau ina ga ba zai ƙare ba, to su ji mana, daɗin abin Allah ai ba na su kaɗai bane, Bilal kuwa ina ruwan ki da inda yake, shi mai iyaye ai gayanan ke ma Allah ne gatanki ya baki wanda ya fi Bilal ɗin sau million."
Yusrah ta taɓe baki a ranta tana ayyana _'Ni fa ban ga zaman aure tsakanina da mutumin da bai ma san me ye soyayya ba, babu abinda ya iya a lamarin nan, da ace dai faɗa aka ce da cin zali tsaf zai zama numba one, amma ace ko wacce suke soyayyar bata san waye ke soyayyar ba, bata san a soyayyar ana yi da ita ɗin ko ba'a yi da itan, kai bata ma san su nawa ne suke soyayyar ba balle ni da na faɗo yanzu, ai kar ku damu auren nan ni na san babu inda zai je, zai sau ni hankali kwance dan kamar yadda baya son takura haka nima.'_
Suna nan suna tare da su Manal dake ta son aunty ta fita su sakata a tsakiya ita kuwa ta ƙi fitar dan bata so Yusrah ko da wasa ta nuna musu bata son ɗan uwansu, ta fi so sai ta gargaɗeta sosai sannan ta bata damar kasantuwa daga ita sai su, Aunty Intisar ta ƙaraso cikin shiga ta alfarma sai walwali take yi walwalwal ɗauke da sakon Yusrah in ji Anna.
Tana zuwa ta ajiye saƙon Yusrah ta zo ta shige jikinta tana sakar mata kuka, Aunty Intisar ta saka dariya tana juyi da ita tace" To wai kukan bai ƙare ba? Haba amaryar mu."
Cike da shagwaɓa tace " Aunty har da ke? Ki rabani da su Manal Allah aunty."
Aunty Intisar ta ce" Kai ku ƙyale min ƴar lelena fa, tom, mu je ki ji labari saura wani ya biyo mu, aunty Furera bari mu je mu saka labule da *Yayata.*"
Aunty Furera ta saka dariya tana jin salama a zuciyarta ta ce" Yanzu kam ma ga waye aunty wace Yaya a tsakaninku." A ranta tana jin salama sosai, dan ta san in dai Intisar suka zauna zata rarrashi Yusrah kuma zata ƙara kwatanta mata cikin hikima, tana da yaƙinin zata sa ta gane abinda bata gane ba domin sun zauna ta san wacece Intisar ita da kanta tana girmama Intisar sosai domin shekarunta basu kai girman hankalinta ba ma sha Allah.
*PALACE ANZA*
A gidan Anna kuwa su Goggo Tidin ne ke kan komai na tarin sabgar bisa umarnin da Yayanta ya bata a jiya da dare bayan ta dawo daga gari ya sanar mata Anna fa ba zata je ta yi tsaye a kan komai ba bayan gata nan, ya damƙa mata komai ya kuma bata umarni dan ya isa da ita kan ya ganta a kan komai, ita da kanta bata san cewa wai ɗaurin auren da Aswan ne za'a yi shi ba sai yanzu da labari ya gama gari aka yi kiranta ana yi mata barka, ta ɗan jima da wayar a hannu kafin ta taɓe baki ta ja tsaki bayan ta katse kiran a ranta tana ayyana _'Lalle ƙiyayya ta yi tsauri tsakanina da Asalama, ace ana ɗaurin auren yaron nan yau sai dai in ji a duniya gani a cikin gidan ina mata bauta dan ita ce sarauniya? Ba damuwa a gama taron zamu zauna da Yayan a kan maganar nan zai tabbatar maki mu kaɗai ne shaƙiƙansa ni da Hamat, mune jininsa kuma a kanmu yana iya rabuwa da ke wallahi, dan Hamat na kwance bashi da lafiya ne ake wulaƙantani ko? Ba komai.'_
Nabihat na wajen mak'up ana tsantsara mata kwalliya mahaifiyarta ta yi kiranta ta bata umarnin ko me take yi daga inda take ta zo gidansu tana jiranta, ta yi haka ne saboda mijinta da ya dawo daga ɗaurin aure dan ya canza tufafi ya saka mararsa nauyi ya koma gidan amininsa yake tabbatar mata albishir ɗin auren fa da Aswan aka ɗaura, tunda har yanzu sun ƙi sanar masa ranar da suka yanke sai kawai ya sa aka ɗaura da Aswan yanzu, daga baya sai a yi na NABIHAT ɗin, shi ne suka kacame da bala'in da bai taɓa tunanin ta iya ba, domin duk kissarta a yau abin ya ƙwace mata ta ringa surfa bala'i, ita ba ta je gidan bikin tunda safe bane dan yanzu abin nasu ya ɗan ja baya da Anna, ta fi so sai kusan sha biyu haka ta ɗauki wankan da sai Anna ta raina kanta ta je gidan su ga juna ido cikin ido, sai gashi Chef ya zo mata da maganar da ta saka sai da ta faɗi dan juwa kafin ta riƙe zuciya ta shiga masifa da faɗin to wallahi ba zata bashi ƴar ta ba, dama tun da aka kawo kuɗin auren yarinyar nan ta gane ba'a son auren nan, shine za'a yi mata kishiya tun kafin ta shiga? To wallahi ba zai yiwu ba ko ya saki yarinyar ko kuwa a fasa aurensu da Nabihat.
Shine chef ya dubeta cikin ido yace da ita" Look maman Nabihat, bana son neman fitina da ja in ja a kan abinda ka san baka da ƙarfi a kansa, kuɗi? Au ko dai kuɗin ne ya sa kuke min nan da nan a kan maganar auren nan? Ke ki kula fa, ba dan kun fi ƙarfina na saurareku a kan maganar auren nan ba fa, na suarara ne saboda Yayarki ta nemi alfarma ta nuna min tana so su halarta har da mijinta da ƴaƴanta, idan kuka min garaje zan ɗaura auren nan a yau ta tare a yau in ga tsiya, ke kin san ai yaro yana da damar auren huɗu ba ma wai biyu ba, dan haka ki kula babu wanda zan ba dama ya wulaƙanta yaron nan, ko da babu alaƙata mai ƙarfi da mahaifinsa yaron kaɗai garin kansa ne, alaƙata da shi mai girman da zan girmama shi ne, ki kiyaye."
Daga nan ya shige ya cenza ya fito ya yi tafiyarsa, shine fa take ta tsefa balaki da alƙawarin sai dai a zaɓi ɗaya yau ko Nabihat ko wacce aka aura masa ta yi kiran ƴar ta tana faɗin ta zo yau su neme shi wallahi sai dai ya zaɓi ɗaya dan babu uban da zai haɗa mata yarinya kishi da kowa, ko ita uwarta ba'a yi mata kishiya ba balle ita?
Tana nan zaune ido ya gama kaɗe mata jajir Nabihat ɗin ta shigo ta sha mak'up ɗin ta da dakakiyar gizneer ɗin ta ta shigo tana faɗin" Mum, kina ina? Lafiya dai ko?"
Mahaifiyarta ta bi shigarta da kallo har ƙafarta kafin ta ce" Ke amma baki san abinda yake faruwa ba ko? Ina anfanin zuwan naki gidan can da zaunawa baki san abinda yake faruwa a gidan ba? Daga ina kike yanzu?"
Nabihat ta ƙaraso ta zauna gabanta na faɗuwa tana kallon mahaifiyarta ta ce" Daga saloon nake mama, tunda duƙu duƙu na tafi saboda sai an min kitso ga mak'up da nake so a min, kin ga yadda suke shirin auren yarinyar nan kuwa? Shine ni ma na je dan in musu ba zata."
Uwar ta ja uban tsaki ta ce" Ai kuwa kin ga bazata ganin idanuwanki, baki san da wa aka ɗaura mata aure ba?"
Nabihat ta ɗage kafaɗu ta ce" Wallahi ban sani ba, ta yiwu da Bilal ɗin ne ko mum?"
Rai ɓace ta ture hannunta tana ta harararta ta ce" Bilal ɗin ubanki, na ce Bilal ɗin ubanki, Bilal ɗin da ya fasa auren, baki san ba ma ya fasa ko? To ba Bilal bane kina cen kuna shashancin banza da wofi ban ma san uban da kike aikatawa ba a gidan har haka ta samu baki sanar da ni ba."
Nabihat ta yi saurin faɗin " Wai mama halan wani mai kuɗi ne aka aura mata? Ni abinda yasa ban sanar maki cewa an fa fasa auren nata da Bilal ɗin ganin sun ci gaba da shirin bikin su normal sai nace ta yiwu Aba ya samo mata wani mijin ko kuma shi Bilal ɗin ya dawo tunda ai abin ba'a fasa ba."
"Haka fa, shashashar banza da wofi, an fasa da Bilal an ɗaura da Aswan sai ki sanar min yanzu, banza da ace kin faɗa min a lokacin ai da mun bincika mun yiwa tufkar hanci, kika yi shiru gayanan yanzu ai an aurawa mijinki ita, iskancin banza da wofi , ki min kiran numbar yaron nan wallahi yau ya zo gidan nan ya za;a ke ko ita dan ba zan taɓa amincewa da wannan haukan ba, ya isa hakanan!"
Ta katseta rai ɓace tana miƙewa tsaye haɗi da tabbatar mata sai dai ya zo ya zaɓa yau, a ɗan birkice ta kalli maman nata tana nuna alamun bata ji da kyau ba, ta ƙara karkatar da kanta ta ce" Mum, wai ni fa ban gane ba."
Rai ɓace ta juyo ta ce" Me ye baki gane ɗin ba a ciki? Ɗaura auren na Yusrah da Aswan ko kuwa kiran nasa da nace ki yi ya zaɓa ke ko ita dan ubanki?"
"Wani maƙaryacin ne ya ce maki an ɗaura mata aure da Aswan mama? Aswan kuma?" Ta faɗa da ƙarfi tana miƙewa tsayen ita ma, mahaifiyarta ta kalleta ta buɗi baki ta ce" Ubanki ne ya f...."
Sai kawai ta ga luu Nabihat ta zube mata a ƙasa matsayin sumammiya, da karfi ta nufo ta tana ihun kiran sunanta haɗi da ihun kiran masu aiki, a rikice take jijigata tana faɗin "...
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
11/06/2024, 22:19 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*66*
A haukace mahaifiyar Nabihat ke kiran taimako, nan da nan masu aiki suka kama mata ita suka ɗora saman kujera sannan suka yi kiran likita, sai dai tun kafin likitan ya zo mahaifiyar tata ta kwaso ruwa ta maka mata, ta juya da nufin sake kawowa Nabihat ta farka a firgicen gaske idanuwa na yi mata yawo tamkar an shaƙe mage ta sake fasa wani kukan da kana ji zaka san daga can ƙasan zuciyarta yake fitowa.
A rikice ta ce" Shine aka fasa aura mata Bilal aka bata mijina? Da na kaiwa Hajia vidion nan ta fasa aura mata d'anta dan ta ga ba abar a ba mutumin kirki bane shi ni aka ba mijina, wallahi wallahi ba zai taɓa yiwuwa ba, sai na nemo wannan ƙaton da ya yi kiranta matarsa na nunawa AA ya saketa, ba zata taɓa wuni da sunan matar mijina a wuyanta ba, a yau yau sai mijina zai saketa, wallahi ina son AA irin son da ba zan taɓa iya bari wata ƴa mace ta so shi ba ko ta raɓar min shi ba."
Mahaifiyarta kanta sai ta dawo kallonta tamkar ta ga baƙuwar halitta, zantukan bakinta suka sakata kallonta da tsoron yanayinta, a ɗan hanzarce ta kori masu aikinta dake kallon kallo ta dubi Nabihat ta ce" Ke, wace vidio ce kika kaiwa Hajiar? Wace Hajiar?"
Nabihat ta yi tsittt da maganar da take yi, sai kuma ta kalli mahaifiyarta dan a irin wannan lokacin bata jin ko chef ne ke tsaye a kanta in zata ji tsoron sa, ido cikin ido ta ce" Vidion da yasa aka fasa auren Yusrah da Bilal ni na samota na kaiwa Hajiar Bilal ta fasa auren da ɗan ta, shine ni nawa sirikan da yake basu san abinda suke yi ba suka aurawa mijina ita, ga vidion nan, ki riƙe wayar zan je nan in dawo."
Ta ƙarashe tana miƙawa Mamanta wayarta domin dama ta fara maganar ne tana fito da vidion, da ƙarfi mahaifiyarta ta riƙo hannunta bayan ta fara kallon Vidion ta kalleta da wani yanayi na abin tsoro ta ce" Waye wannan namijin?"
Nabihat tace" Nima ban san ko waye ba, amma yanzu zan je in san ko waye ɗin, dan wallahi sai na nemo shi ko duka kaf dukiyata da na mallaka zan bashi ya tona mata asiri mijina ya saketa."
Rai ɓace ne? Ko tsabar fita a hayyaci ne? Ita dai ta san ta ɗauketa da mari a lokacin da bata yi tunanin zata iya marin ƴar ta haka ba, rai ɓace ta nunata da yatsa bayan ta maido ta ciki da ƙarfi ta watsar a falon ta ce" Ba zaki aikata aikin dana saninki ki sakani a ciki har ki aikata aikin haukanki ki sakoni a ciki ba, ashe ke kika janyowa kanki? Ina ruwanki da aurenta? Haukanki har ya kai ki can? To bari ki ji, ki zauna ki yi kukan kishiyar da ta rigayeki ganin mijinki kafin in yi tunani a tsanake da ilimi na sanin hanyar da zamu bi mu birne sunnanki a wannan lamarin, babu ke babu binciko ko waye a wayar nan dan kuwa wanda kike son binciko war shine mijin naki, banza duk ikirarin son da kike faɗin kina masa ba zaki ganshi ki gane shi ba? Wannan mutumin Aswan ne, kuma na tabbata a kan aiki ya aikata haka, idan baki san su waye iyayenki ba ki yi wasa da wuta, a nan zaki gane baki da wayo, abu ɗaya na sani wannan abu da kika aikata duk ranar da zai fito sai dai ya shafe ki ke kaɗai dan ba zaki taɓa haɗani da mijina ba, ya yafe ƴar cikinsa ya zauna lafiya balle ni, ki kula Nabihat ki kula."
Wani tashin hankalin ta ƙara shiga a lokacin da ta rarrafa ta warto wayar ta shiga duba vidion, a da bata ga kamar da zata sakata haɗa shi da AA ba, amma a yanzu kamar har ta ɓaci, a rikice ta fashe da wani irin kuka na tashin hankali da saka kai a uku, zuciyarta tamkar zata buga take ji, a yanzu idan ta ga Yusrah babu mai hanata shaƙe wuyan Yusrah ta kashe
ba zata taɓa iya yarda da wannan auren ba, wallahi sai ta fitine su.
*AA ANZA*
Suna zuwa gidansa suka baje a falonsa suka shiga cin abincin da aka kawo daga gidan Anna, girkin ya sha zabi ga jus a gefe da ruwan sanyi, miƙe ƙafa Arif ya yi bayan ya yi hani'an ya ɗan tallabe ƙeyar Muktar ya ce" Allah Ubangiji ya sa kaima ka yi aure, a yanzu tausayinka na iya hana ni barci, dan babu masifa irin rashin aure lauya."
Muktar ya kalle shi sheƙeƙe ya ce" To ai gwara ni da kai, ni ban yi bane kai kuma fa?"
Arif ya girgiza kai yace" Ba zaka gane ba, ni ai da sauƙi, kuma ni na ƙi ta dawo ɗakin ta saboda dan ƙaddara ta faɗa min an rufe ni iyayenta suka sake kai ƙarata sai na saketa, shine ni kuwa na sau