Showing 378001 words to 381000 words out of 397328 words
mota suna kallo saida motar ta ɓacewa ganin su kadai suma suka fara haramar barin wurin.
Daga nan Aswan makarantar su Safwan ya nufa ya ɗauko su tare da yaran Mani dreba su biyu da suke karatu anan, gaba ɗayan su ya kai su gidan kamar yadda Yusrah ta nemi alfarma ya kawo mata su zasu taya ta hira, haka ya kai su can ta kuwa samu abokanan hira, su Meem ne dai da zai fita ya bar ta da su yace "Saura su princess ɗina suma zan kawo miki su."
Shagwaɓe fuska ta yi tace "A'a fa AA, gaskiya bana son mage ni ko kaɗan, bana so ta taɓani a jiki, kuma bana so su yakusheni."
Riƙe haɓa ya yi yace "La'ilaha illalah! Y. Turaki ƙatuwa dake matar ƙato za ki zauna tsoron mage?"
Turo baki tayi ba ta ce da shi komai ba, hakan ya sa ya ja dogon hancin ta yace "Kullum ƙara fahimtar da ni kike nine kaɗai kika raina a duk faɗin duniyar nan, saboda ni kaɗai kika iya cin kwalar rigata ba tare da kin nuna kina jin tsoron Allah ba."
Ƙyalƙyalewa tayi da dariya ta ɗan faɗa saman ƙirjin shi a tausashe tace "Kasan me rohi? Wallahi a waccen lokacin ma tsabar gigitar da nake ciki ce ta sa na iya yin haka, amma fa a lokacin kar ka so ka ji yadda ƙirjina ke bugawa, gani nake kawai za ka ɗaukeni ka jefa ta window iskan sararin samaniya ya yi gaba dani."
Shi ma dariyar yake yi ya riƙe ƙugun ta yana cewa" To ai ni kasa aiwatar da komai nayi saboda kallon mai aljanu nake miki, amma da na jefaki ta window da yanzu wacece za ta kawowa Aliyu takwaran shi?"
Murmushi ta yi cike da jin kunya tana sinne kai tace" To ai nima ban tɓa cire ka a layin ƴan wiwi ba a wannan lokacin, saboda ban yarda da kai ba."
Zaro idanu ya yi yace" Lahhh! Wiwi fa kika ce?"
Jinjina kai ta yi alamar e tana dariya, raɗa ya mata" In kuwa hakane yau da dare za ki ga aikin wiwi, dan sai nasa kin yi ihun da zai karaɗe gidan nan."
Raba kanta tayi da shi tana ƙoƙarin ja baya amma ya riƙe hannun ta, kukan shagwaɓa ta saka mishi tana faɗin" Wallahi AA bana so, ka sake ni na tafiyata, ka ji dai abinda nurse ta faɗa ai."
Taɓe baki ya yi yana ayyana _'Nurse ta ci gidan su, dan iskanci ita ce za ta dakatar da shi daga more rayuwar shi, wai wani cikin ƙarami ne sai an dinga ɗaga ƙafa.'_
A zahiri kuma ƙara jawota jikin shi ya yi yace" Y. Turaki da gaske ba kya jin kunyar kiran wannan sunan nawa?"
Tana kallon fuskar shi tace" Ina ji mana, kamar yadda kake jin kunyar kiran sunan Kakana."
Sagale haɓa ya yi yace" Ke Turaki fa ba suna bane, ki nemowa kakan ki suna na ƙwarai mana."
Ɗan dukan shi ta yi a ƙirji tace" Bana so AA, kuma ai na fi ka sani, sunan shi na gaskiya kuma Muhammadu, kawai suna ne waccen kamar inkiya."
Dariya ya yi yace" To kinga muyi wata yarjejeniya, ke ki daina kirana da AA, nima sai na daina kiran ki da Y. Turaki."
Rumgumo ƙugun shi tayi ta baya ta sakawa hannayen ta sakata tana wani rangaji a jikin shi tace" Oya, me za ka dinga kirana to?"
Shima yana tallabe da ita a jikin shi yace" Sunaye kala-kala, duk wanda ya zo bakina zan faɗa ne, irin su ƙoramata, ni'imata, hutuna, jin daɗina, gonat..."
Rufe mishi baki tayi da tafin hannun ta tana dariya tace" Waɗannan ai sai mun shiga ɗaki ne za ka faɗa ko? Ni so nake naji wanda za ka dinga kirana da shi ko gaban su Anna ne, amma fa suna mai alkunya da daɗin sauraro."
Dariya ya ƙyalƙyale da ita ya haɗa goshin shi da nata yace" Umm... To zan dinga cewa matar jikan Anza, ya miki?"
Kamar mai tunani tace" Ummm...wani dai na musamman haka."
Saida ya sumbaci laɓɓan ta sannan yace" To sai nace *ƴar dabata*, ko *jelata*, ko *my Dr.*"
Bushewa tayi da dariya tana nunashi da yatsa tace" Umm, sai dai Dr ɗin..." Sai kuma ta ɗan dangware mishi kai tana faɗin" Sarkin zazzaɓi kawai, ka wahalar da ni fa bawan nan."
Dariya ya yi yana ta son haɗa bakin shi da nata, hakan yasa ta janye daga jikin shi, dan tasan in ta yi wasa tsaf zai kaita ruwa da yara a gidan nasu, tunda jiya ba abinda ya faru saboda yanayin jikin ta duk ji yake kamar bai samu yadda yake so ba, hannun ta ya riƙe da ƙyar tana ta son kubcewa duk sai ya marairaice yace "Please, dan bani harshen na tsotsa ko kaɗan ne, i swear kamar ban da lafiya nima saboda jiya ban sha madara ba kuma ban baki kin sha ba kema."
Maƙale kafaɗa tayi tace "Um um, idan na baka AA ba zaka tsaya iya nan ba."
"Na yi alƙawari ba zan wuce ba, Allah." Ya faɗa kamar wani ƙaramin yaro, sai hakan ya bata tausayi da jin wani begen mijin nata ya baibaye ta, cike da shauƙi ta nunoshi da yatsa tace "Ka yi alƙawari?"
Gyaɗa mata kai ya yi yace "Na yi."
Dan haka ta ɗan turo harshen ta kaɗan tare da matsowa kusan shi ta miƙo masa harshen, dama jira yake dan haka ya jawota gaba ɗaya ya damƙi harshen nata a sanyaye ya shiga tsufa yana rufe idanuwa, ita ma lumshe idanun tayi tana karɓan saƙon mijin nata dalla-dalla sala-sala.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
12/07/2024, 12:06 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*96*
Ganin dai Imran zai sa wankin hula ya kai su dare ya sa ba ta da wani zaɓi da ya wuce neman shi da kan ta, ƴar barazana ta masa da cewa za ta je gidan su ta sanar da maman shi abinda ya aikata, shine kaɗai ya sa ya zo gidan suka tattauna akan auren shi da Nabihat, sai dai kuma ya nuna mata ba zai iya auren ta a kwana ƙasa da uku ba gaskiya, yana da mahaifiya mai wuyar sha'ani sannan yana da mata, kowanen su dai ya cije akan abinda yake so, dan haka suka tsaya akan zai yi shawara zuwa washe gari zai kira su ji yadda ya yanke.
Kwatsam sai wahalar dukan da Nabihat ta sha ya raba musu gardama sakamakon bayyanar ciki a jikin ta, hakan sai ya zama wasa farin girki, tashin hankali sabo da ba'a saka masa rana ba ya gayyace su, bayyanar cikin kuma shi ya yi sanadiyar da wasu duk sukayi laushi.
*Hajia* kunya ke ɗawainiya da ita da tashin hankali, bata taɓa tunanin zata kuma yin wani zama da Aban Intisar ba wanda ita ce zata roƙi alfarma cike da kunya tare da ita ba sai yau, lallai ɗan kuka mai jawa uwarsa jifa.
Gasu nan zaune kai a ƙasa cike da jin kunya da tashin hankali suna neman alfarma a kan masha'ar da ɗan su ya aikata, domin wajen Chef suka je kan maganar ya nuna su samu Aba duk abinda ya yanke shikenan lafiya lau ne, shi ba ruwansa yarinya kuwa dama tana gidansa dan shi ya ɗauketa ya maidata can da hannayensa.
Murya a tausashe Hajia ta ce" Elhaji, a yi haƙuri, a yi haƙuri, a yi haƙuri, tabbas ka haifi ɗa ne baka haifi halinsa ba, tunda nake ban taɓa sanin yaron nan haka yayi nisa ba sai da sakamakon nan ya bayyana, maganar da nake yi maka kwanana uku a asibiti, da ƙyar na samu kaina, Elhaji ni dai kamar yadda na sanarwa mahaifinta ina roƙon alfarmar a yi haƙuri a yi haƙuri, idan yarinyar nan ta sauka lafiya daga asibiti ma a yi ɗakin ta da ita, saboda ina so da zarar ta haihu a ɗaura musu aure a rufa asiri a kaita ɗakin ta ba tare da kowa ya ji ba."
Aba ya zuba shayinsa ya sha a nutse ya sake duban Hajia sannan ya sake kallon Imran dake duƙe kansa a ƙasa, sannan ya kalli Aswan dake zaune ya rafka tagumi yana kallon Imran yana tunanin ina ma ace za'a yarda a bashi shi ya masa kaciya dan ubansa, shi kam da ya gille abin cin ƙaniyar kowama ya huta? Shi yanzu baiwar da Allah ya bashi ce yake anfani da ita yana cika marar ƴaƴan mutane ko? Shege mai kyan ɗan maciji.
Aba a tausashe ya ce" Hakane, to amma ya ya za'a yi in ɗauki ƴa sukutum in ba lalatacce? Gaba ɗaya tsoron haɗa iri nake da ku Hajia yanzu, abin abun ɗaga hankali ne."
Aswan ya kalli Aba ya tsura masa ido, a ransa ya ayana _' To fah, ɗan Anza zai rama abinda aka yiwa ƴar sa Yussy kenan? To in ba wannan ba ai daga baya kenan lalata, ɗan Anza haƙuri zaka yi dan in baka aura masa ita ba ni zaka raruma, ni kuwa na rantse da huwa rahamanu mijin mace ɗaya ne in sha Allah, yo ni zan mata kishiya ta ringa sheƙa kukan nan ta kasheni? Tsaf zata yi fushi ta ƙauro nan da sunan ta yi yaji, ku kuma ku riƙe ta in shiga uku, kawai a bashi abinda tunda shi ya fara cin ƙaniyar ma zasu zauna asirin su a rufe ba tare da an ɗagawa junna hankali ba.'_
Hajia ta sadda kai
cike da jin kunya, tunda take bata taɓa tunanin cewa daga tsatson ƴaƴanta maza zata amshi bara gurbi ba sai yanzu da Allah ya nuna mata shike da duniyar ba kakanta wanzan ba, ita Hajia shi yasa take taka rawarta daidai da kiɗanta, amma yanzu da aka ganar da ita ita ɗin banza sai gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi kunya ta luluɓeta, Imran kansa a cikin tashin hankalin da yake ba'a magana, matarsa ta tafi gidansu ta yi fushi, ana ta fama a yi nan a yi can, gashi Hajia bata so magana ta fita sam bata so a ji, dan kuwa ko a anguwa tana cikin tsofaffin dake zagin ƴaƴan mutane, balle idan ƴar ki ta ɗan fara rashin ji to fa Hajia har gida zata zo ta maku tofin Allah tsine da faɗin wa zai auri ƴar iska? Shi yasa da ƙarfin ta ta kaɗe auren Yusrah, dan kuwa ai tashin hankalinta ne ace ga wacce Bilal ya aura, mai gaba ɗaya yanzu Bilal ance ko da nasara suke soyayya? Dan kuwa ba'a faɗa mata gaskiyar wacce Bilal ke nema ba, wato Nawal an ɓoye mata ne har sai yaya Mubarak yayi zuwa mai gaba ɗaya zai sanar mata, sai ga wannan lamari ya faɗo wallahi da aka zo akace Imran ya yiwa ƴar mutane ciki ashar ɗin da ta ɗura ya fi cikin kwondo, sai da maganar ta tabbata sannan ta dawo ta duƙa ta zubawa sarautar Allah ido bayan rashin lafiya da koke koke ta yanke shawarar nan ita da yaya Mubarak, shine ta zo neman alfarmar hakan.
A tausashe ta ce" Ka yi haƙuri Elhaji, in sha Allah abinda ya faru ba zai sake faruwa ba, gaya nan ai zai faɗa da bakinsa."
Ta talle ƙeyarsa tana faɗin" Yi magana mana banza."
Kai ya sake sokewa a hankali ya ce" In sha Allah Aba ba zan kuma ba."
Aba ya taɓe baki ya ce" Ku dai ku je kawai zan yi tunani."
Duk yadda suka so su tanƙwasa zuciyar sa ya ce su je zai neme su, a dole suka tafin, suna tafiya Aswan ya gyara zama ya ce" Amm... Aba, a yi haƙurin fa shi ya fi in sha Allah, ai tunda sun yi nadama ba komai a yi a haɗa su su tafi, Allah ya kiyaye gaba."
Aba ya dube shi kafin yayi murmushi ya ce" Tirzawa nake yi mana ko sun san darajar ta ko da kaɗan ne, ko da yake ita ma ƴar tawa ai ba kanwar lasa bace, daidai take da wannan tsohuwar, so nake in ɗan bata wahala, amma nima ai ba zan so maganar ta gama duniya ba, duk da bamu isa mu ɓoye abin nan ba fa, amma kuma tunda Allah ya rufa asiri ya sa mai abin ya ce yana son abinsa sai a bashi su je su ƙarata da addu'ar zaman lafiya, in sha Allah zan neme su da kaina in na gama jan zaren."
AA ya miƙe yana faɗin" Alhamdulilah, har na tsorata ai, to bari in je gida lokacin komawa yayi kar a shiga haƙƙin ƴar mutane."
Aba ya yi dariya yana girgiza kai ya ce" A gaishe da maman Haidar."
Aswan ya saki wani murmushi ya fice yana buɗewa dan in aka ce baban Haidar da maman Haidar ji yake kamar ya janyo Haidar ya fito duniyar nan a sha gwagwarmayar tare, kai Allah dai ya nuna wannan rana ta zuwan Haidar duniya, amen.
Alhamdulillah za'a ce, dan rayuwa na tafiya ne yadda ubangiji ya tsara ta, kamar yadda kowa ke tafiyar da rayuwar sa da girban abinda ya shuka, Aba dai da ake ta ɓoyen kar ya ji ko ya ga wani abun da zai ɗaga masa hankali, sai gashi cikin hukuncin ubangiji lafiyar sa rass, ya riƙe ƴan uwan shi da zuciya ɗaya, yana iya abinda zai iya wajen taimakawa talakawa, ya kula da haƙƙin iyalin shi dake kan shi, sannan ya riƙe salatin Annabi da istigfari a matsayin abinda suke sanyaya ran sa, hakan ya sa hatta da tsufan shi duk da yana jan mutum ba ka ganewa saboda wannan falalar da haiba da hasken annurin dake wanzuwa kaɗai a fuskar masallata, tsakanin shi da ƴaƴan shi sai san barka, ya ja su a jikin shi ta yadda babu mai ɓoye masa wani abu da ya dace a ce ya san shi, musamman ma babban ɗan sa jikan Anza da ya riƙa tamkar amini wani sa'ilin kuma kamar kaka da jika.
Haka ma Anna uwa ta gari ta kiyaye nata haƙƙoƙin da suke kan ta, sannan ta tsare girman ta matsayin ta na babba, wanda ta kai ta kawo yanzu Goggo Tidin ma ta kan gaishe da irin ladabin nan mai cike da kunya da nadama, bugu da ƙari har Goggo Tidin ɗin ta ce ta bar komai na auren Abrar a hannun ta tunda ita ce uwar Abrar ai, hakan ya sa Anna yarda cewa lallai Tidin ta sauko daga matakalar da ta hau game da ita, sai kawai ta basar ita ma ta rumgume ta aka ci gaba da harkoki. Yanzu haka auren wasu ƴaƴan ne na ahali ake ta shiryawa kamar ba gobe, Manal da uncle Sul, Nawal da Bilal wace bayan ta shawarci waɗanda aunty Intisar ta bata shawara duk suka nuna mata sun amince da haka ita ma kuma ta amince in sha Allah alkairi ne, sai kuma Abrar da Mukhtar, shiri kowa yake yi kamar yanzu ne auren da za'a fara yi a gidan, ko dan ya zama na ƴan matan gidan ne da suka rage? Ko kuma dan ya zama sun haura ɗaya? Dan hatta Humed da Aswan shiri suke ba ji ba gani, shi kan shi miskilin kuma dodon nasu idan ya tashi halin nashi ko tsakanin sa da matar sa sai ka ji ya ce ai ya daina kashin kuɗi saboda auren ɗiya ne a gaban shi.
Ƙwarai kowa ya ga Aswan zai tabbatar ya ɗauki girman sa matsayin sa na babban ɗa, dan tsakanin shi da Intisar ya nemi shawarar ta sai ga kayan ɗaki kala uku ras ya siyawa ƙannan nashi, abinda ya saka Anna da Aba farin ciki matuƙa, sannan ya saka Goggo Tidin mamaki da riƙe haɓa tana sake duba lamarin, a gaskiya ta ji duk nauyin su ya baibaye ta, basu bar dangin mahaifin Abrar sun yi komai ba, haka ita ma sun hana ta saka kwabon ta, yi kawai suke ba ji ba gani kuma babu alamar gobe za'a ce ai mun yi miki, wannan abu ya faranta mata rai duk ta ji ta sauko daga inda ta hau, a dole ta nemi shiri da su har da AA ɗin wanda dama ba wani abu ya mata ba, kawai yadda yake mata da rainon da Aban ya mishi ne bai mata ba.
Sai dai a inda gizo ke saƙar shine ta ya za ta ce ma AA tana so su shirya? Sannan ta yi nadamar abinda ta yi ma a baya? Wannan ne ya sa har yanzu da bikin ke ta ƙaratowa bata samu ta yi magana da shi ba, saida ta ji a gidan ana raɗe-raɗin Yusrah na da ciki, anan ne ta kafa tarkon ta na nemi shiri da shi. Da fari gidan ta yi dirar mikiya da sunan duba Yusrah, hakan kuma ya ma Yusrah daɗi, amma shi da ya ji labari a wajen Yusrah sai ya taɓe baki yana neman tsarin Allah daga kaidin ta, dan a ganin shi wani sabon makircin ne ake son fitowa da shi kuma, bayan