Showing 318001 words to 321000 words out of 397328 words

Chapter 107 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70056

kar zazzaɓin nan ya kama ka sosai kuma bamu da ko da emergency box, please please please Dadyn Anna ƙarama."

Buɗa idanu ya ƙara yi ya kalle ta, wai ƴar mitsitsiyar nan shine za ta ma wayo? Ka ji wata sarautar Allah mana, ba tare da ya ɗauke idanun shi daga kan ta ba cikin wata irin daƙilalliyar murya yace" Har yanzu ba ki bani amsar tambayata ba, *matar ɗan Haidar*, har yanzu kina son Bilal?"

A zabure ta kalle shi tana girgiza kai da sauri tace" Haba mana *Aban Haidar*, ni fa musulma ce, kar ka fara ɗora ɗambbar zama dani da irin wannan zargin mai girma da aure ma yake lalacewa idan akwai shi tsakanin ma'aurata, wallahi tun ranar da aka faɗa min ba da shi aka ɗaura min aure ba, a nan take na goge komai da ya shafe shi a ƙwaƙwalwata, zuciyata da ma wayata, ba zan taɓa wannan kuskuren ba, ina kuma fata Allah ya tsareni da aikata hakan ko da kuwa a cikin munanan ƙadarorina ne."

Zuba mata idanu ya yi shi dai yana kallo, ko dan wannan abun da ta faɗa sai ya ji ba komai a yanzu zai yakice wannan a ran shi, amma fa... Sai kawai ya miƙe a nutse ba tare da ya ɗauki rigar shi ba ya kama hanyar wani ɗaki tana kallo ya buɗa ya shige, ajiyar zuciya ta sauke tana zaunawa kan kujerar gaba ɗaya ta zuba tagumi dan bata san me shirun ke nufi ba, ya haƙura kenan? Ko wani makamin zai ɗauko da zai gillare mata wuya da shi? Ko kwanciya zai yi har zazzaɓin ya rufe shi ya saka ta sintirin rashin madafa?


*MENSION ANZA*


Tun motar bata fita daga gidan ba Nabihat ta kwamtsa wata irin ƙara tare da durƙushewa ƙasa tana kuka wiwi kamar wata taɓaɓɓiya tana kiran "Me kenan hakan yake nufi? Ya tafi da ita gidan shi kenan? Shikenan yau za ta tare kenan? Na shiga uku ni Nabihat, wannan wace irin masifa ce? Mama, Mamana, Maamaa."

Yadda ta miƙe ta warta da gudu ciki tana kururuwa kamar wata ƴar maguzawa ya sa su Manal duk bin ta da kallo, Anna kuma sai ta daina mamakin abinda take yi ta sukwana da sauri ta yi ciki tana tura su Nawal gaba tana faɗin" Ku wuce muje ku riƙe min ita kar ta halaka kan ta, ya zama dole yau Nabihat ta tafi gidan su, wannan jaraba da me ta yi kama?"

Haka suka rankaya, sai dai kafin su hau sama Nabihat ta sauko da gudun da daga nesa kake jin sautin takalmin ta flate tana saukowa, ba wanda ya samu damar tare ta kawai ta bangaje su ta bi ta tsakiyar Abrar da Nawal hakan ya sa ta bige su sosai, kallabi da makullin mota kaɗai ta ɗauka ta fita bata ko kula kowa ba.

Nan ma dai da kallo suka bita ba wanda ya iya yin wani abu, hakan ya sa Anna girgiza kai tace "Ha Yallah! Wai me yake damun yarinyar nan ne?"

Sai kuma ta yi zaune kan kujera tana dafe goshi ta dubi Abrar tace "Abrar, bani wayata a ɗakina dan Allah na kira Aban ku na sanar masa wannan abu da ke faruwa."

Da ladabi Abrar ta amsa da "To." Ta juya da sauri, Anna kuma ƙwafa ta yi tana jinjina kai da faɗin "Jikan Anza, jikan Anza ni ko? Wallahi ka kuskura ka dakar min ƴa zan ci buru'uban ka a garin nan, yau ga iskanci, ɗan kwali ma fa bai bari ta ɗauka ba."

Ajiyar zuciya Manal ta sauke tana zama ita ma tace "Anna baki ga har takalmin ta suna nan madafa ba? Oh Allah besty, ina tsoron yau ta san wa ye Akhi."

Shiru Anna ta yi har Abrar ta kawo mata wayar ta karɓa ta kira Aba, yana ɗagawa Anna tace _"Aban yara, kuna asibitin ne?"_

Aba ya amsa mata da _" Gani daf da shigowa gida, na samu yana bacci ma yau da naje asibitin, sai kawai na dawo dan a bar shi ya huta."_

Amsawa Anna ta yi da _" To sai ka shigo, dan gaskiya na fi so mu tattauna ido na ganin ido, idan ba haka ba *zaki* zan tattargaɗa ɗan nan naka in jefar a banza, na rantse."_

Murmushi Aba ya yi yace _" Jikan Anza na farko ne ko?"_

_" Shi fa."_ Anna ta bashi amsa a tsaye, murmushin ya sake yi yace _" Gani nan shigowa."_

A ladabce ta amsa da _" A shigo lafiya."_ Sannan ta yanke kiran ta aje wayar tana ta sauke ajiyar zuciya a kai a kai, ba kasafai ka fiya ganin Aba a babban falon ba idan ba ranar da ya yi ra'ayin cin abinci da duka iyalin shi ba, amma yau kai tsaye nan ya shigo ya kuma zauna kan kujerar da Manal take zaune mai zaman mutum uku yana fuskantar Annan yace "Gani to, me ya faru? Me jikan Babana ya aikata kuma yau?"

Abin duk da ya faru Anna ta zayyane masa daga farko har ƙarshe, sannan ta ɗora da "Ana shirin tariyar yarinya gobe amma zai min wannan iskancin? Ka duba fa fisabilillah ba ɗan kwali ba takalmi haka ya ratsa min da ƴa cikin gari, me yake damun Aswan ne wai?"

Shiru Aba ya yi yana kallon ta har ta gama magana, saida ta dasa aya ya kalli yaran dake zaune ya yi murmushi, sai kuma ya ƙi umartar su da su basu wuri ya sake duban Annan yace" To yanzu me kike so na yi?"

Da mamakin tambayar ta kalli Aba, me take so ya yi? Da ta kira shi ba dan ya ɗauki mataki bane? Shine zai faɗa mata haka? Sai kawai ta turo baki gaba tana karkace kai tace" Kiran shi za ka yi ya dawo min da ƴata ko ni naje gidan, sannan ka masa kashedin kar ya sake rikita min ita, ba ka ga yadda take ihun a ceceta ba fa."

Girgiza kai Aba ya yi yace" Sai dai kiyi haƙuri gaskiya, amma ni ba zan kira shi ya dawo da ita ba."

"Saboda me?" Anna ta tambaya tana tsare shi da idanu, kai tsaye shi ma yana kallon ta yace "Saboda matar sa ce."

Numfashi Anna ta ja tace "To dan tana matar sa sai kawai ya kaita gidan shi shi kaɗai? Sai ta ɗauka an mata hakane dan bata da gata ai."

Gyara zama Aba ya yi ya ɗan sassauto da rawanin shi da ya ma naɗi irin na asalin bugaje, wanda dama ma fi aksari Aba in dai zai yi shirin fita ba mai jimawa ba musamman da sassauƙar sutura to ya kan naɗa rawani ne, saida ya fito da bakin shi gaba ɗaya sannan yace "Kina ji ko Annar yara, ni fa ban ga dalilin da ya sa kika ja lokacin kafin tariyar yarinyar nan ba, na yarda akwai buƙatar wasu shirye shirye duba da yadda auren ya zo, amma duk abinda aka yi yanzu abu ne da idan da kuɗi a kwana biyu zuwa uku an gama shi, amma ke kika riƙe masa mata har na wani sati uku fa, baya ga haka ni kaina bana sanin sun fita da ita wani lokacin, haka shi ma baya sanin fitar ta sai dai ya ji bata nan ko ya ga ta dawo, tunda kike da ita kin taɓa saka ta ta nemi izinin shi kafin fita? Ba ki taɓa yi ba fa Annar su, sannan a haka za ta fita ita da su da shiga kala ɗaya ita dake da aure a kan ta da su dake ƴan mata, shima kin taɓa tsawatar wa? Ba ki taɓa ba fa, sai yanzu kawai dan ya ga ba zai iya jura ba ya ɗauki matar sa sai a wani saka min yaro a gaba, kinga ni gaskiya bana cikin wannan rashin gaskiyar, ina ce dai gobe ne zakiyi hidimar ki ta tariyar ta, to ki yi duk abinda kika shirya, idan lokacin ya yi su mutanen su runguɗa su je can su same ta, dan ban ga wani anfanin dawo da ita nan ba sannan a maidata can kuma, ba addini bane dan haka kawai ku ba kan ku lafiya."

Yadda Anna ta yi saƙe kamar za ta tallabe haɓa ya sa Aba miƙewa yana warware rawanin shi yace" Zan samu shayi?"

Yadda ta wani firgita ta kamle shi ya sa Aba kallon su Abrar yace" Ƴaƴan Aslama, ku samo mana garwashin wuta da mangal, ku ɗauko mana shinfiɗa mu je can ƙofar gida mu ziga shayinmu, idan ba haka ba yau ran kowa zai ɓace a gidan nan saboda uwar gidan dai ta hassala, sannan babban ɗan gidan ma an rikita min shi, ni kuma tsoron duka biyun nan nake ba zan iya aikata komai ba."

Yanzu kam gaba ɗaya Anna sai ta buga tagumin ta bi Aba da kallo dake shirin ficewa, su Manal kuma miƙewa sukayi da jin daɗin yanayin nan da zasu shiga tare da Aban su suka nufi madafa dan yin abinda ya ce, dan ba yau ne zasu fara hakan ba, sai dai kafin hakan ya faru akan jima sosai, saida Aba ya kai ƙofa Anna ta ɗaga murya tace "Dan girman Allah Aban su ka kira shi ka ji to me yake mata a gidan? Ni wallahi ban yarda da yanayin sa bane? Ka fa san shi kai ma."

Juyowa ya yi ganin ba yaran ko ɗaya ya kanne mata ido ɗaya yace "Annar su, daga shi sai ita a gida zai daketa ne? Ki barsu dan Allah kar ki sa a katse musu hanzari, amsar tambayar da kike so a mishi za ta bayyana nan da wata goma zuwa tara in sha Allah."

Da sauri Anna ta miƙe ta nufi falon ta tana faɗin "Je ka Aban su, je ka kawai."

Dariya ya yi ya juya yana ayyana _'Haka kawai, ni fa na yarda da ɗana wallahi, kuma ni nasan takwarana zai fito ta tsatson sa ne in sha Allah.'_

Sassauƙan naɗi ya ma rawanin sa ya fice ƙofar gidan ya yi tsaye yana jiran ƴan matan su fito, ba jimawa kuwa suka dinga fitowa da kayan shayin da abun shinfiɗa duk suka aza sannan aka shiga ƙoƙarin hura wuta, hakan ya sa masu gadi da su Sk komawa ɓangare ɗaya suma suka dasa ta su hirar da shayin.



*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
29/06/2024, 15:18 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*80*



Tabbas yau da akwai jami'ai kan kowace hanya masu kula da sintirin mutane da babu abinda zai hana Nabihat fuskantar hushin su saboda gudun gangancin da ta yi ta kai kan ta gidan su, a ƙofar gidan ta aje motar ta fito a haukace ta faɗa gidan da gudu kallabin ta a hannu waya ma na mota bata ɗauko ba, tana shiga falon ta samu Maman ta tsaye da mai ɗinki za ta mata rakiya saboda jin daɗin ɗinkin da ta yi mata wanda za ta saka gobe, dan tayi niyyar shiryawa ita ma ta je gidan Anna ta ganewa idanun ta kalar tarairayar da Nabihat ke faɗa mata tsintacciyar magen nan tana samu a wurin su, da irin kayan alfarmar da ta ji an ce an watsa mata a ɗaki wai huɗu ne ko biyar yadda Nabihat ɗin ta faɗa, sannan kuma hanya ce da za ta gano kalar kayan, ƙarkon su, nagartar su, ƴan wace ƙasa ne sannan adadin kuɗin su ya kai nawa? Dan kawai ta san irin zazzagar dake jiran ta nan gaba, tunda ɓangare biyu ya ware saboda matan shi ai tasan komai iri ɗaya zai yi, dan haka ita ma sai ta cika mata ɗaki in ma goma ne kamar yadda aka ma Yusrah ko da za ta ƙarar da duk abinda ta mallaka a duniyar nan.

Yadda Nabihat ta faɗo ɗakin ya sa duk suka kalle ta a tsorace, Maman na ganin ta ta fahimci ba lafiya ba, kuma koma menene daga can gidan ne, sai kawai ta yi saurin yi wa mai ɗinkin alama da faɗin "Shikenan Hajia, na gode sosai, sai mun yi waya ko?"

Tana kallon Nabihat da take son tantance wai wannan ba ƴar Hajia Chafa'atun bace ta amsa mata da "To Hajia, sai na ji ki ɗin."

Ta juya ta fice har sake waigowa take yi dan gaskiya yadda ta ga Nabihat ba ta yi mai hankali da ita ba, Maman nata kuma hannun ta ta kama suka ƙarasa kan kujera ta zaunar da ita sannan ita ma ta zauna, har za ta kira mai aiki kan ta kawo mata ruwa, sai kuma ɗaya daga cikin ƙannan Nabihat ɗin dake maza ne ya shigo a guje da kayan ball jikin shi, daga zaune Maman tace "Mujahid bani ruwa a feidge?"

Shi sai lokacin ma ya kula da akwai mutane, kallo ɗaya ya Nabihat ya kalli maman tasu yace "Mom, wai ita aunty Nabihat me yake damun ta? Kinga yadda ta bar mota a waje? Ita kullum matsala, damuwa, kuka, wa ye wa ye dai..."

A tsawace Maman tace "Za ka bani ruwan ko sai na taka ka?"

Fridge ɗin ya nuna yana jik Nabihat na aiko masa da wasu mala-malan ashariya bai ko waiwaye ta ba, shi yake bi mata, kuma wallahi aka bar shi da ita tsaf zai yi kilishin ta a tukubar tsire, yo wacece Nabihat? Ruwan ya ɗauko ya kawo ya miƙawa Maman sannan ya nufi ɗakin shi ko ta kan su bai sake bi ba, ruwa ta bata ta sha tana faɗin "Sauke numfashi, a hankali a hankali, ki nutsu sosai, sai ki faɗa min me kuma ya faru?"

Jin tambayar Maman ta ƙarshe ya sa ta katse shan ruwan da ta fara har suna bulbulo mata a jiki tace "Mama, Aswan zai kasheni, Aswan zai kasheni da raina Mama, mama kinsan me ya aikata kuwa? Yarinyar nan fa ya ɗauka yanzu ya fita da ita wai ya tafi da ita gidan ta, har da cewa Anna idan tana buƙata zai dawo mata da ita gobe sai ta mata abinda za ta yi, amma dai yau a gidan shi za ta kwana, Mama wannan banzar yarinyar kenan za ta rigani kwana da As..."

Da sauri ta rufe mata baki saboda duk yadda suke da ita sai ta ji kunyar furucin nata, kwana da AA? Iya shi ne matsalar ta a yanzu? Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi sannan tace" Me ya faru to? Haka kawai tashen balagar tuzurancin nashi ya motsa ya kwasheta dan ya sauke? Ko kuma wani abun aka masa?"

A rikice Nabihat tace" Mama, ina ga fa ko kamata ya yi da tsohon saurayin ta Bilal a farfajiya suna zance, shine kawai ya hassala ya ɗagawa kowa hankali a gidan, ita ma haka ya jata ba ko shirin arziki a jikin ta."

Numfashi Maman ta sauke tana duban ta sosai tace" To, shine kika gigice kika taho min a haka? Nabihat tunda dai zaman ki bai yi anfani ba a gidan nan, kawai ina ga kin dawo gida kenan, ke da komawa can gidan sai kuma ranar da kika je gaishe da Aslama a matsayin ta na uwar mijin ki, amma yanzu dai zaman ki ya ƙare, abu ɗaya da za'a yi yanzu shine..."

Shiru ta yi sakamakon katseta da Nabihat ta yi da faɗin" Mama shikenan ba zan sake zuwa ba fa kika ce? Shikenan ya tare da mtar sa kenan ni kuma na zauna anan ko rana baku saka min ba?"

Da takaicin halin Nabihat ɗin ta girgiza mata kai tace" Chef ya yi hushi sosai ta yadda ba zai sake saurarata akan maganar saka ranar ki ba, amma abu ɗaya da zan yi shine gobe idan na je gidan zan sauko da kaina a gaban Tidin, zan zauna tare da ita mu yi hira, anan zan gabatar mata da ƙudirina na kuma tabbatar mata da na bar komai a hannun ta, ita kuma za ta wa Elhaj Aliyu magana akan saka ranar, kinga idan shi ya nemi Chef da maganar dole zai masa biyayya tunda ya zama kamar yaron sa, Tidin kuwa ko da kema ba ƙaunar ki take ba dan ta ƙuntatawa Yusrah za ta yi amanna da abinda na zo mata da shi, dan haka yanzu kawai ki kwantar da hankalin ki, na wani ɗan lokaci ki share Aswan da mutanen gidan su, na miki alƙawari nan da kwana biyu za ki ji labarin saka ranar ki ya fito daga bakin ɗaya a cikin ukun nan, Tidin, Elhaj Aliyu, ko kuma mahaifin ki da kan shi."

Wata wawuyar ajiyar zuciya Nabihat ta sauke ta faɗa jikin Maman nata tana faɗin" Mamana, ke ta dabance, shiyasa nake son ki."

Murmushi ta yi tana shafa bayan ta da ayyanawa a ran ta _'Dole naga na fita kunyar auren ki Nabihat, idan ba haka ba na tabbata ko Yayar ki (Fauziyya) ba za ta kasa yi mana dariya ba, musamman a yanzu da mijin ta ke ci gaba da zama


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login