Showing 276001 words to 279000 words out of 397328 words

Chapter 93 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70024

Da yanzu ban san ya Annarmu take ba, ni kuma ban san wace proson aka sake kaini ba, dan ba abinda zai hanani likiɗawa Y. Turaki duka.'_

Bai ji buɗo ƙofa ba, amma wani tattausa kuma sanyayyan ƙamshi da ya kawo ma hancin sa ziyara ya shaida masa zuwan baƙo falon, ba ƙamshin da ya san ta da shi bane, dan wannan rikitarwa gare shi da wuyar fassarawa, dan sosai yake kama da turare irin na itace na wuta, wani sa'ilin kuma kaji kamar kana shaƙar ƙamshin turaren ruwa irin masu maiƙo ɗin nan masu masifar tsada da sanyin ƙamshi. Bai yarda ya juya ba sai ma basarwa da ya yi musamman da ya sake jiyo ƙamshin turaren da ya fi shaƙar shi wajen ƴan biyu, da dashi dukansu suke anfani babu bambamci, dan haka ya tabbatar idan ma ita ce to da rakiyar ɗaya daga cikin twins, dan haka kan shi na sadde har ya ɗan hangi alamar ta cikin wani zunbulelen hijab da ya rufe mata duka jikin ta sai hannayen ta kaɗai da suka sha lalle ake gani, sai kuma fuskar ta da ya tabbatar tana waje amma bai ɗaga ba bare ya gani dan gudun kwafsawa.

Cikin wata irin gagarumar kunya kamar ta ce ƙasa tsage na shige ta zauna ta ɗaga murya da ƙyar kamar wata mage har rawa rawan kuka take ta gaishe da Aba ya amsa yana ɗorawa da "Saki jikin ki mana ƴata, shin ni ba baban ki bane? Wannan kuma Yayan ki, kar kiji kunyar kowa dukanmu ai mun zama ɗaya ko?"

Ƙara noƙe kai Yusrah ta yi saboda tunda ta zauna sosai ta fara shaƙar mayataccen turaren shi na oud wood haɗe da versage tare da haɗin guiwar wani secret romantic Victoria, duk sai ya nemi hautsina mata lissafi kamar yadda ya haɗawa ɗakin nashi lissafi. Bugu da ƙari wata irin kunyar haɗa idanu da shi da ta ji ta kamata a yanzun ba zata iya ba, sai kawai ta sake sinne kai da Aba ya yi maganar ba ta ce komai ba ita dai.

Sai dai Aswan na jin abinda Aba ya faɗa ya yi wani lalataccen murmushi tare da girgiza kai yana ayyana _'Kayya! Aba ai nan kwantan ɓauna take yi tana neman hanyar da za ta cuceni.'_

Said ya ji Aba na faɗin "Matso nan ƴata, zo kin ji?"

Sannan ya ɗan ɗaga kan shi kaɗan ya saci kallon ta, da sauri ya sadda kanshi ƙasa yana furta "Hasbunallah wani' imal wakil."

Fuskar ta ya gani tana wani irin ƙyalli wallahi, sai kuma hakan ya kayar masa da gaba, shi kam anya ba maganar Aba gaskiya bace kuwa? Anya wata sheɗaniyar aljanar ba ta aure shi ba kuwa? Ko ya zama kamar ba namiji ba mata suna kayar masa da gaba? Ita waccen fiance ɗin tsoro take bashi, wannan kuma sai ya ji gaban sa ya faɗi, me ye haka wai fisabilillah kamar ba shi ba? Bai sake ɗaga kan shi ba saida ƙara nutsuwa da ya yi sosai yana sairaron nasihar da Aba ke yi musu na su manta komai da ya faru a baya, yanzu kawai yake so su dinga kalla idan har suna son ci gaba a rayuwar su, tare da tunatar da dukan su haƙƙoƙin juna dake kan su, da tsoratar da su akan duk wanda ya yi sakacin tauye haƙƙin ɗan uwan sa, to su sani ubangiji ba zai duba ta yadda aka yi auren ku ba ko ba kwa son juna ko baku jituwa, ubangiji zai yi hisabi ne kawai a tsakanin ku ba tare da ya duba alaƙar ku ba.

Daga bisani Aba ya ɗora da "Ku ji tsoron Allah, ku ji tsoron haɗuwar ku da shi, duk rintsi duk wuya kar ɗayan ku ya bari ya zalinci ɗan uwan sa, a rayuwar nan ta yanzu ka kwanta ba'a tashi da kai ba, ko kai kasancewar ka namiji ka fita daga gidan ka lafiya amma a dawo da kai a makara, kar ka yarda ka fita da hushin matar ka ko da sanin cewa ka ɓata mata rai, dan kana miji mai cikakken iko ba shi ya baka damar da za ka ma matar ka laifi sannan ka gagara bata haƙuri ba, duƙawa wada ba gajiyawa bane, sannan matsayin ka na namiji sai ka kasance kafi matar ka waɗannan abubuwan guda uku da zan lissafi, haƙuri, uzuri, da kuma lissafi yayin ɗaukar mataki idan ta maka wani abun, faɗa, bambami da kumfan baki ba sa gyara mace kamar yadda rarrashi da kwatantawa suke kayar da ita a ƙasa warwas, wani laifin ma ɗauke kai kake yi kamar ba ka gani ba, sai kaga da kanta kuma ta dawo ta gane bata kyauta ba har ta nemi afuwar ka. To hakan kuma ba yana nufin ke mata an baki cikakken iko bane na ki taka mijin ki son ran ki ko kuma ki masa yadda kika ga dama, idan ya fi ki abubuwan da na lissafa a farko, ke kuma sai ki fi shi da biyayya, yawan tuba idan kin masa laifi, da tausasa harshe yayin magana da shi, to idan kuka yi haka, zaman ku zai zama abun bayar da misali har a wajen jikokin ku ma, daga ƙarshe, ina mai gargaɗar ku akan kuyi taka tsantsan da wannan rayuwar, abinda ya faru ga auren nan wani babban darasi ne dake sake nuna mana mutane suna shiga abinda bai shafe su bane, tare da barik kiwon dabbobin su sukan yi na mutane, dan haka ku toshe kunnuwan ku daga duk wani suka ko zance da zaku ji marar daɗi, ni naji da kunnuwana masu faɗan auren huce takaici aka wa Yusrah, sannan na ji masu faɗin dama akwai wata ƙullaliya a tsakanin ku, to duk ko ma menene ina so ku kawar da kai daga duka wannan zantuka, idan ma kun ji ku ce e hakane sai ya ya? Sannan ku yi biyayya ga umarnina wajen zaman auren ku, ta yadda babu wani mahaluki da zai ji kan ku musamman ma saɓanin ku, hakan zai toshe babbar ƙofar kawo musu sukar juna..."

Tsagaitawa Aba ya yi ya ja numfashi na wasu daƙiƙu sannan ya ɗora da" Ba sai na faɗa muku idan kuka mana biyayya zaku ci riba anan duniya da kuma lahira ba, sai dai abinda zan faɗa muku shine idan kuka mana biyayya fiye da yadda muka yi tsammani, to shakka babu sai na sa kun zama ƴaƴan da za'ayi wuyar samun wanda zasu kama ƙafar su wajen samun gata da kulawar iyayen su, dan ko tari ko atshawa zan nemi yin yaƙi da ita idan naji ɗaya daga cikin ku ya yi, haka kuma bijirewa umarnin mu, kamar saka ƙafar wando ɗaya ne damu da nuna mana bamu isa ba, dan haka nima ba wanda ya isa ya hanani yanke hukunci ga ɗaya daga cikin ku dan dukanku na haife ku, kun fahimce ni?"

Yusrah dake ta sharɓan kuka amma ba mai sautin ba daga numfashin ta da kuma majina da take yawan ja ne za ka gane haka da ƙyar ta jinjina kai alamar e, sai Aswan shima da ya ɗan cira kai dan jikin shi ya mutu murus ya jinjina a hankali, dan haka Aba yace "Da kyau, Allah ya muku albarka, Allah ya wa rayuwar ku albarka, Allah ya haɗa kawunan ku, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyaba, Allah ya sa a ce auren nan gwanda da aka yi, Allah ya tsone idon maƙiya a kan ku ya kuma ɗoraku a saman su."

Yusrah ya kalla yace" Allah ya baki wuyan ɗauka ƴata, Allah ya ci gaba da shiga lamuran ki, Allah ya sa wannan auren ya zama mafarin karkarewar wasu wahalhalun ki na rayuwa, Allah ya sa maraicin ki ne ya zo ƙarshe sanadiyar wannan."

Cikin shasheƙa Yusrah ta gyaɗa kai bata iya furta amin ɗin ba ma, a sanyaye Aba cike da tausayin ganin kukan da take yace" Za ki iya tafiya, ki je ki ci abinci sai ki kwanta ki huta."

Saida ta share hawaye da hijabin ta taja majina sannan ta yunƙura tare da cewa" Na gode Aba, Allah ƙara lafiya da nisan kwana."

Miƙewa ta yi ta fita Aba na amsawa da amin, saida ta fice gaba ɗaya ya kalli Aswan da kanshi ke ƙasa shi kan shi maganganu akan haƙƙoƙin ta nan da Aba ya yi sun razanar da shi, da kuma tunin da Aba ya masa kan duk wani haƙƙi idan ya tauye mata shi ba shakka zai ƙone, yana cikin wannan firgicin na tashin hankalin abun Aba ya dube shi ya sake cewa "Marainiya, ban tsananta maka a gaban ta bane saboda mata ba'a musu haka, amma ka sani jikan Anza a babu aure ma tsakanin ka da ita ka cutar da ita Allah zai iya gaggauta hukunta ka ko ya yi hushi da kai, kakaninmu suna faɗa mana idan maraya ɗaya tak ya yi kuka, ko ba ka san shi ba idan ma a unguwar da marayan yake kai ma kake, to Allah zai iya saukar da hukuncin da zai iya shafar ka, to jikan Anza ina ga kaine silar zubar hawayen marayan, ina so ka yi wani abu, ka sa a ranka duk abinda za ka ma yarinyar nan da ƙanin ta za ka yi shine dan neman yardar Allah da kuma samun kusanci da Annabi Muhammad Sallalahu alaihi wa sallam, dan ya faɗa duk wanda ya saka maraya murmushi a duniyar nan, to zasu yi maƙwabtaka hakane ranar gobe ƙiyama..."

Ya faɗa yana nuna masa da yatsun sa biyu, sannan ya ci gaba da cewa" Ba'a ce ba za ka ɓata mata rai ba, ɗan adam ne kai, kuma yau da gobe sai Allah, sannan duk wani zama zo mu zauna ne zo mu saɓa, balle kuma zaman aure da dama y a gaji haka komai haƙurin da ake da juna, amma dai ina ƙara baka shawara ka kasanxe mai haƙuri da duk wasu kurakuren ta, idan kuma aka samu akasi ta maka abinda hankalin ka ya kasa ɗauka, ko ka gagara tausar kan ka akan haka, to kar ka ce za ka tattauna hakan da abokin ka dan neman shawara, ko ka kai ƙarar ta gurin aminiyar ta ko kuma magabatan ta, yawan kai ƙarar juna ga ma'aurata yakan janyo zubewar kima ne da ƙiyayya, dan haka ko me za ta maka ka zo ka sanar da ni, da kai da ita dukan ku ƴaƴana ne, ni zan sameta na mata magana ba tare da wani bare ya ji kan ku ba, ina fata ka fahimceni jikan Anza?"

Ɗaga kan shi ya yi ya kalli fuskar Aba yana jinjina kai, saida gaban Aba ya faɗi da ya ga idanun shi sun kaɗa sun yi ja haka, da kulawa Aba yace" Kai jikan Anza, kuka ne kai ma za ka yi yadda amaryar ka ta yi? Maza fa ba sa kuka, yaƙe baki suke yi na murnar sun yi ɗaki suma yanzu."

Wani murmushin kan laɓɓa ya yi ya ja majina sosai yana zaro tissue ya goge fuskar shi ya girgiza kai yace" A'a Abana, ba kuka nake yi ba, sai dai maganganun ka Aba...sun tsoratani sosai, yanzu nan fa Aba kusan ma ta fi ku haƙƙi a kaina kenan ko? Saboda ku bani nake ciyar da ku ba, amma ita idan na hanata abinci Allah zai iya ƙonani, sannan idan da ace zan fita nayi dogon kiwo bai waiwayeta ba nasan halin da take ciki, shima Allah zai ƙonani saboda ban kula da amanar da aka bani ba, a taƙaice Aba da *Y. Turaki* da *ku iyayena*, duka zan iya shiga wuta idan ban kula da ɗyanku yadda ya kamata ba, amma kuma ubangiji zai iya yafe min laifin da tsakanina da shi ne wannan idan ya so, amma ku da ita sai dole kun yafe min sannan zan samu rahama."

Cike da tabbaci Aba ya jinjina kai yace" Wannan haka yake *ɗan Zaki*, kuma naji daɗi da ka fahimci haka, kaga sai ka ɗauri niyyar kiyayewa da taka tsantsan wajen kula da duka haƙƙoƙin nan, ni dai matsayina na uban ka banda matsala da kai wajen sauke haƙƙina, matar ka ce kawai yanzu nake so nan da wasu shekaru ita ma ta maka wannan shaidar."

Jinjina kai ya yi a sanyaye yace" In sha Allah Aba."

Gyara zama Aba ya yi yace" Tom, mu koma maganata da kai, akan abinda ka ke aikatawa da ban san shi ba."

"Ya Allah." Aswan ya faɗa yana tsare Aba da idanuwa, sai kuma ya sadda kai ya yi shiru yana wani tunanin, da sauri Aba ya katse shi da cewa "Aswan, kar ka ce za ka min wasu dabaru ko sauya mana zance, ka faɗa min kan ka tsaye kawai ko mu samu matsala da kai, ina so na ji me ye kake haka mai mahimmancin da ya sa ka kira ƴar mutanen da ba komai a tsakanin ku da matar ka? Me kake aikatawa da girma da ya sa ka yi tafiyar sati ɗaya ba wanda ya san inda ka ke? Sannan ta ya kuka san juna da barista Mukhtar da kuma Arif wanda ni ban san su ba sai yanzu a cikin kwanakin da basu fi talatin ba zuwa arba'in? Aswan, me ya ɗauki hankalin ka da girma haka da har ya hanaka faɗawa uncle ɗin ka kayi adopten Safwan? Sannan me ya sa ka ƙi kwantar da shi a asibitin sa har ma ka fita U.S bai sani ba, oya! Ina jiran amsoshin ka."

A hankali ya lumshe idanu yana ta maimaita" Hasbunallah wani'imal wakil." A zuciyar sa, kafin ya ɗago dan bai da tsumi bare dabara ya kalli Aba a tausashe yace" Aba, zan baka duka amsoshin nawa, amma ka min alƙawarin ba za ka yi hushi da ni ba? Sannan ba za ka shiga damuwa ba? Please Aba?"

Tsura masa idanu ya yi yana kallo kamar mai nazarin wani abu sai kuma yace" Ka yarda za ka faɗa min gaskiya kenan?"

Jinjina kai ya yi yace" Na yarda zan faɗa maka komai Aba."

Da gamsuwa Aba yace" Kuma ka yarda da na san baka aje kaki ba ko?"

Kallon Aban ya yi yace" Abana, kaine fa abun koyina a rayuwar nan, ban da wani wanda nake kwaikwayo ko nake alfahari da shi sama da kai, na sani Aba dama za ka ganoni da wuri duk yadsa zan kai ga ɓoyewa."

Murmushi Aba ya yi yace" Aikin sa kai ne ko na gwamnati?"

Numfashi ya sauke yace" Aba aikin sa kai ne, amma da sahalewar gwamnati."

Taɓe baki Aba ya yi yace" Uhum! Aikin sirri ko?"

A hankali ya jinjina kai alamar e, dan haka Aba yace" Ka kammala ko da saura?"

A ladabce yace" Saura kaɗan Aba, in sha Allah saura ƙiris."

Dogon numfashi Aba ya sauke sannan yace" Shikenan, na haƙuri da jin ko ma menene yanzu, saboda ba zan iya maka alƙawarin hankalina ba zai tashi ba tunda ban da ikon sarrafa kaina yadda nake so, amma ka tabbatar idan ka gama koma menene ka sanar min da komai Aswan, ka ji da kyau?"

Da wani irin mugun daɗi ya jinjina kai yace" In sha Allah Aba zan yi hakan, in sha Allah."

Jinjina kai shi ma Aba ya yi ya jingina a kujera sosai yace" Shikenan, za ka iya tafiya, amma ku tabbatar kun je godiyar nan yanzu." Da karsashi ya jinjina kai alamar to tare da miƙewa yana wa Aba addu'ar Allah ƙara girma da lafiya har ya fice yana jin wani shaƙat har zuciyar sa.




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
21/06/2024, 22:09 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*69*




Bayan ya fita ne Aba ya tuno bai yi masa maganar kyautar nan ta yau da dare da ƴan uwansa na jini zasu yiwa amaryarsu, kyauta ce ta ƙara danƙon zumunci, kyauta ce ta irin yadda suka ɗauki amaryar gidansu da mahimmanci, suna da wannan tadar ne tun wajen kakaninsu, a gidansu idan aka yi amarya sukan yi mata irin kyautar bajinta gwargwadon ƙarfin ka ko ace gwargwadon irin yadda aka amshi amaryar, suna ba wannan kyauta mahimmanci sosai, ko Humed sai da suka yiwa matarsa wannan kyautar, idan kuwa mace ce zasu aurar yayunta na bata kyauta daidai da abinda Allah ya hore musu, ko Intisar ta samu kyautar nan ma sha Allah, shi yasa ita ma Yusrah suka shirya mata wannan kyautar.

Ya ɗan yi jim da ya tuna wannan maganar, lokaci ne da kowa ke ɗaukan wanka su zauna a falo mahaifiyar mijin ke sauko da amaryar ta amshi kyautukanta, yawancin lokuta zaka ga idan amarya ta amshi kyautukanta zasu wuce gidansu da angon ta ne, wannan tunani ya saka shi ɗan sakawa a ransa to ko Aba yana nufin daga nan zai wuce da ƴar nan? To amma ai Anna ta ce bata so a sakata a gidan nan ta fi so a sakata a sabon gidan da ƙarti basa zuwa lokacin da suka ga


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login