Showing 192001 words to 195000 words out of 397328 words
ya zama jajirtacce kuma sai an yi zama mai kyau an daidaita komai, sannan sai yarinya ta bar aikin nan da take zuwa tunda a sauran matan babu wacce bata yi karatu ba kuma babu wace take aiki, sai ita isashiya? Hum! Ita mamaki yarinyar ke bata, idan ta hangota tana tafiya ɗaya kan ɗaya sai ta ce sai kace can dama ubanta wani ne? Yarinyar akwai shegen kinibibin tsiya da iya yi, bata son ta ga mace ne ma mai shegen kyau an ce namiji ya aura, irin wahalar da suke ba mazan ire irensu? Hum!
Shigowar kira a wayar yaya Mubarak ya saka shi duba wayar dake ajiye gefe ya ɗauka yana ɗaga kiran domin kira ne tun daga U.S na abokinsa, bayan sun gaisa da yaren turanci yake sanar masa albishir ɗin da ya saka yaya Mubarack ɗan zaro ido a bayyane yana furta" Alhamdulilah, alhamdulilah Alhamdulilah, eh ban buɗa email ɗina ba, ma sha Allah bari in duba yanzu yanzu, Freind ina fatan wannan karon da na madame ɗin ko?"
Amsar da ya bashi ya saka fuskarsa faɗaɗa da farin ciki suka yi sallama ya buɗe email ɗin ya duba, ai kuwa saƙo gasunan na maganar takardun da yake jira nasa da na Intisar, da fara'a sosai ya sanarwa Hajia cewar takardu sun fito.
Hajia har ta kusan fi shi farin cikin abin, da ƴan uwansa, haka suke taya shi murna suna taya shi farin cikin abin, ya miƙe yana faɗawa Hajia yana zuwa ya fice da sauri dan babban burinsa ya je ya sanarwa Intisar a yanzu ya ga farin cikin da zata nuna, yana fita Hajia ta girgiza kai tana dafe haɓa ƙasa ƙasa ta ce" Ni dai na shiga uku, mu a zamaninmu kallon kirki ma basu cika yi mana ba mazan dan kar ace sun cika rashin kunya, idan ka ga namiji ya kalleka a cikin mutane dan ya baka umarni ne, umarnin ma da faɗa faɗa, amma yau na zo zamanin da idanuwana ke ganin rashin kunya kala kala, zuwa ne zai yi ya faɗa mata, bayan ya taɓa samun takardar nan dan tata bata fito ba ya nuna ba zai je ba sai idan tata ta fito? Allah ka sawaƙa, Allah wadaran naka ya lalace."
Bilal ya yi wata ƴar dariya ya yi kwanciyarsa saman doguwar kujerar nan ya ciro wayarsa dan ya ga ko Yusrah ta gama wayar da auntynta ko bata gama ba? Wato yana tausayawa lamarin Hajia ne kawai idan ya tuna shi fa tana iya kamawa ya goyi Yusrah idan tace ba zata iya taka ƙafafuwanta ba gaskiya, Allah dai ya bada tsayin rai da lafiya, abu ɗaya da ya sani, ba zai taɓa yarda macen aurensa ta wulaƙanta masa mahaifiyarsa ba, kuma zai yi iya yinsa dan ya kiyaye abinda zai ɗaga mata hankali, domin a ranar da ta ganshi riƙe da jakar Yusrah sosai ta ɗaga hankalinta shine har ya yiwa Yayansa maganar, shi ya kwatanta masa fa ya kamata ya kiyaye duk wani abu da zai sa Hajia ta ji ta tsani matar da yake son aure, tunda Allah ya sa mahaifiyarsu mace ce mai saka ido sosai da jin kishi sosai a irin zamantakewa irin haka, har ya zamo ta ƙi su fita su shiga gidajen su a waje ta saka an yi part uku a cikin gidan saboda su zauna tare da ita da matansu dole zasu bi komai a hankali su guji ɓacin ranta su yi mata biyayya har Allah ya daidaita komai, tun daga lokacin bai kuma nuna rawar ƙafa a gabanta idan yana tare da Yusrah ba, kuma bai kuma riƙowa Yusrah jaka ba a cikin gidan su, yana kiyayewa sosai dan ba zai so Hajia ta tsani Yusrah ba, bai san ina zai saka ransa ba idan ya zamo mata biyu mafi daraja a rayuwarsa basa jituwa.
*Yaya* Mubarak da ya shiga ya sameta tana waya ya karɓe wayar ya yi wa Yusrah sallama ya ɗaga ta ya ɗora saman cinyarsa ya sanar mata albishir ɗin nan ya ga farin ciki tsantsa a saman fuskarta, hawaye kuwa suka ɓalle mata waɗanda suka sa ya ji tausayinta sosai, ya sani sarai ya san irin gagarumin jurewar da take yi na rashin ƴaƴanta a gefenta, ya sani bata yi masa maganar dan kar ta ɗaga masa hankali, amma ya san babu abinda ke ɗaga mata nata hankalin irin tunanin su, ya sani tana yin iya yinta ne tana rayuwa a haka, shi da kansa a kullum yana iya yinsa dan ƙanwarsa ta riƙe masa su dan Allah ko ba komai kar su rasa abinci, kar a hana su karatu tun daga na islamiyya da na boko, haka kuma Allah ya sa ƴaƴan kansu suke iya yin su dan su nuna masu lafiya lau ba komai.
Amma rayuwa kam suna ganinta ganin idanuwansu, wata irin rayuwar ƴan boko auntyn tasu ke zubawa da mijinta, tamkar ba ƴar hausa ba, tamkar ba musulma ba, dama bambamci tsakaninsu da ƴaƴanta sun sani ba ɗaya bane, wannan tun suna baƙi a gidanta ta kwatanta masu cewa ita fa idan zaman lafiya suke nema su taka a hankali su jitu da ƴaƴanta, abu kaɗan faɗa, aiki kamar jakai bata da masu aiki komai su suke yi ƴaƴanta na hutawa, ɗayan tashin hankalin a gaban idanuwansu sai mijinta ya kamota ya shiga taɓata har su hau kissing ɗin juna a gabansu, waɗannan abubuwan suna matuƙar ɗagawa yaran hankali, kuma sukan sanarwa mamansu kaɗan kaɗan ita kuma tana basu haƙuri da rarrashi da nuna masu ba komai in sha Allah komai zai wuce ne.
Yana dariya ya ɗago fuskarta ya ce" Kuka kuma? To na menene?"
Ita ma dariyar ta ƙwace mata, haɗi da hawayen ta saka hannayenta tana sharewa ta ce" Bab, na farin ciki ne, alhamdulilah Alhamdulilah."
Shi ma a hankali ya ringa furta Alhamdulilah ɗin yana kallon yanayin ta ƙasa ƙasa ya ce" Hakan na nufin, nan da kwana goma in sha Allah muna can?"
Ita ma ta sauke ajiyar zuciya ta ruƙunƙume shi tana jin cewa eh a yanzu kam alhamdulilah damuwarta zata kau, tashin hankalinta na tarbiyyar ƴaƴanta duk zasu kau, zata je ta rungume abinta ta basu tarbiyya ta kula da su har mai rabawa ta raba,
lokaci ɗaya kuma Yusrah ta faɗo ranta, a hankali ta ɗago daga jikinsa tana kallonsa ta ce" Bab, Yusrah fa?"
Ajiyar zuciya ya sauke, yana kallonta a tausashe ya ce" Ita ta fi damuna, tunanin inda zan barta ya fi damuna, at alll na ɗauki yarinyar nan ne dan ta ji daɗin rayuwa, dan ta samu sauƙin matsalolin rayuwa kuma har raina Allah yana gani na ɗauketa ne daga ita har ƙanin ta dan in riƙe har mai rabawa ta raba, tunda na amsheta aka bamu ita na fara fafutukar ajiye nata takardun ita ma, sai dai kin sani duk irin hanyar da gareka a kaɗan a ɗauki shekaru uku kafin a samu takardun..."
Ya ɗan dakatar da maganar yana sauke ajiyar zuciya ya ce" Har yaya AA na yiwa maganar yace zai waiwayeni idan ya dawo daga kai yaronsa, ta yiwu shi ɗin yana da wata hanya da zamu samu da wuri ta samu takardar, kin ga abinda yake damuna Hajia ce, Bab ban san yaya zan kwatanta maki ba, amma bana tunanin in har zata ji daɗin zama a nan ba tare da mu ba, kuma bana so ta zauna ɓangaren Zahra'u, sam bana so."
Ita ma ta jima tana tunanin nan, ta hanyar da zata yi masa maganar ne take nema ta rasa, amma ko ita yanzu haka babu yadda Zahra'u bata yi kan ta ringa zuwa wajen su sunna wuni ta ƙiya, sam ita ma ba zata so Yusrah ta je wajen su ta zauna ba saboda rayuwa, ko ba komai mutum an san halinsa sai a kiyaye, sheɗan kuwa ai babban malamin masu ta'amali da ayyukansa ne, sai ta ɗan ƙara sunne kai tana tabbatarwa kanta ba zata taɓa iya barin yarinyar nan a hannun Hajia ba, dan a bayyane yake Hajia bafa zata iya riƙe yarinyar nan ba gaskiya.
A tausashe ta ce" Idan har ba damuwa, in har ba zan ɓata maka ba, ka kai ta wajen Anna, ka ga ga twins ga kuma Abrar, kewa ba zata dameta ba, kuma Anna ba zata ƙi ba."
Shi da kansa abinda ya fi kwanta masa a rai kenan, sai dai baya so a ga ya amshi yarinya zai riƙe kuma ya ba wani riƙon ta bayan bata zame masa nauyi ba Allah yana gani yarinyar kuma bata da halin ƙyama sai na so, domin akwai addini, akwai girmama mutane, bata da ƙiuwa, gaskiya zamanta a waje baya da gundura ko kaɗan, shi yasa yake so ya san ya barta a hannu mai kyau kafin takardarta ta fito ita ma ta bi su, ko aure ya samu mai kyau a yi.
Ajiyar zuciya ya sauke yana rungume ta ya saka hannunsa cikin rigarta ƙasa ƙasa ya ce" Zan je na samu Anna da safe in sha Allah, idan ta amince sai mu shirya mata ɗakin ta a can tun kafin ta zo, ni idan na tuna abinda ke gaban mu, maslaharsu a kan riƙon Safwan gabana har faɗuwa yake yi, ko ya ya zamu ƙare da Akhi ɗin ki? Allah dai ya sakawa abin ruwan sanyi."
Haɗin kai ta ba mijinta suka shige ɗaka dan raya daren nan da farin ciki da kuma kaunar juna, da niyyar gobe in sha Allah su je gidan su samu Anna da kansu da Aba a kan maganar ƴar gaban goshin su.
*Washe Gari*
(U.S)
Yau ne ranar da za'a fito da Safwan daga comma idan har aikin da aka yi masa ya yi kyau yadda suke fata, hakan ya sa Abansa da Yusrah yin sammakon zuwa asibitin suka zauna a filin da aka tanada dan zaman jiran, domin tunda safen likita na ciki tare da likitoci suna kan Safwan dan idan aka tashe shi sai sun tsaftace shi sun shirya shi sosai sun ciyar da shi da komai kafin su fito da shi.
Tunda suka zauna alamun zulumi ke bayyane a saman fuskokinsu, sai dai babu wanda ya cewa ɗan uwansa ufan suke zaune ita da tedy a hannunta fara ƙal wacce ta siya a shigowarsu wajen likitoci dan ta yiwa Safwan kyautansa kamar yadda likitocin ke faɗa shi kuwa bai sayi komai ba, yana zaune dai suna waya da Aba har suka gama yana kashe kiran barista Mukhtar ya shigo wayar tasa dan haka ya miƙe ya ɗaga ya kara a kunnensa ya juya bayansa hannunsa ɗaya a cikin aljihun wandon sa yana amsawa da taƙamar nan da aji sosai.
A hankali ta ɗauke idanuwanta daga kansa tana tuna kwanaki biyar ɗin nan da suka shige sai da ta kwana uku cirr tana jinyarsa da amsa tambayoyinsa a kan rashin lafiyar Safwan, idan ya tashi kuwa ya mata sumul dan wulaƙanci, amma duka kaf ta jure ta mayar da komai ba komai ba dan ita ma burinta a samu lafiya su koma a amshi ƙanin ta a bata, shi yasa take ta ƙyale shi da halinsa ko me ya yi mata take kawar da kai tana masa uzuri, gashi yau da suka zo shine ya ɗau wannan wankan cikin baƙaƙen suit da farar riga tass a ciki, gaba ɗaya yake haske wajen.
Kuma abin takaici ita ma baƙar abaya ce a jikinta da farin takalmi, farar jaka, ta kuma yana farin gyale a kanta sai ta ga sam hakan bai dace ba, da ta so komawa ta canza ya sanar da ita ba zai taɓa jiranta ba tunda shi ba ɗan gidanta bane, shi ne fa ta ji haushi tun ɗazu sai ta juyo ta ƙare masa kallo ta ɗauke kai tana tunanin idan ma kace zaka yi faɗa da mutumin nan ina zaka kama? Sai kawai ta yi haƙuri tana zamanta tana jira.
Kusan ƙarfe goma na safe aka buɗe babbar ƙofar, basu yi tsammanin fara ganinsa ba sai gani suka yi kujerar nan tasa ta cillo kai kuma an miƙar da wajen zaman ya zamo kamar a tsaye yake sak tana tafe a hankali a hankali har ta fito gaba ɗaya sai Doctern a bayansa riƙe da ƴar commande ɗin kujerar yana murmushi da kallon mutuwar tsayen da suka yi suna kallon Safwan wanda fuskarsa ke ɗauke jage jage da hawayen wahala amma kuma bakinsa alamun farin ciki ke bayyane suka turo shi a hankali har kusa da su Yusrah da suka yi mutuwar tsaye, farin ciki ne ko menene? Sun dai kasa kataɓus suna kallonsa.
Da ƙyar AA ya sauke ajiyar zuciya bayan ya riƙe hannun Safwan a hankali ya furta" My son."
Safwan ya saki kukansa , Docter ya ringa faɗin ba ya hana shi kuka ba, to bari a maida shi kawai, hakan ya sa da sauri ya ringa share hawayensa yana faɗin" Dady."
Yusrah ta fashe da kukan itama a hankali ta ɗora kanta saman ƙafafuwanta tana rerawa tamkar an zaneta, a raunane sosai Safwan ya ce" Dady, aunty Yussy ta daina kuka dan Allah ban so, ka ji?"
Aswan ya kalli inda ta tsuguna ta haɗe kai da guiwa tana kukan nan ya kalli Safwan a hankali ya ce" Kukan farin ciki take yi, tell me ina ke yi maka ciwo boy?"
Safwan ya ce" Dady bayana na ciwo sosai, da kuma wuyana, kuma idan ina magna bakina kamar ba nawa ba, kaina ya yi min nauyi sosai shi ma."
Aswan ya ce" In sha Allah duka zasu daina ka ji? a hankali komai zai daidaita ka dawo tafiya da ƙafafuwanka ka ji?"
Safwan ya gyaɗa kai yana yin ƙasa da idanuwansa a hankali ya ce" Dady aunty Yussyna. "
Aswan ya dubeta da takaicin kukan da take masu, a dole ya duƙa ɗin ƙasa ƙasa sosai ya ce" Ke dallah yi min shiru ni kar ki rikita min yaro, kina gani fa an ce kar ya yi kuka shine kike wa mutane kuka? Dallah tashi."
Ta ɗago kanta fuska ta yi mata jajir da hawaye shaɓe shaɓe ta maka masa harara sannan ta ɗauke kanta ta miƙe ɗin ita ma ta je a hankali ta haɗe goshinta da na Safwan ƙasa ƙasa ta ce" Allah ya baka lafiya."
Safwan ya yi murmushi cike da farin ciki yana kallon su suka tura kujerar tasa aka kai shi wani ɗakin wanda yanzu gado ne kawai, likitan na tare da su ya ɗan ƙara komawa a tsayen nan cikin kujerar sannan a hankali aka mayar da kujerar zaune duka yana jiki kafin Aswan ya ɗauke shi cimak a hankali ya zaunar da shi saman gadon ya jinginar da bayansa jikin garu.
Likitan ya yi masu sallama da nufin bayan awa ɗaya zai dawo su tafi dan a sake saka shi hutu sosai kuma a kwantar da shi saman bayansa, daga nan a dole suka zauna gefe da gefensa hannun kowane a cikin nasa suka saka shi tsakiya sai fira suke masa yana basu amsa, abin kamar kishi kishi dai, idan AA ya masa wata tambaya ya bashi amsa ita ma sai ta yi masa wata ya bata su haɗa ido irin ka gani nima yana sona ɗin nan su ɗauke ido, har lokacin tafiyarsu ta yi suka fito AA ya saka direban taxi ɗin dake hidima da su nufar park da su inda zasu haɗu da ƴaƴan Intisar kamar yadda suka yi da mariƙiyarsu yau zasu haɗu.
Sai dai suna zuwa ya yi ta kiran lambarta bata ɗagawa, tun yana control ɗin kansa har abin ya fara bashi haushi ya yi kiran Intisar a lokacin suna gida wajen Anna, Yaya Mubarak na zantawa da su Aba da Anna ɗin ita kuwa tana gefe ta ɗaga da sauri da kuma biyayya ta yi sallama tana furta" Akhi Barka da warhaka?"
"Barka, ƙanwar mijinki tana da hankali kuwa? Ya ya zata ce min mu haɗu a park dan in ga yara na zo ina ta kira bata ɗagawa? bana son rashin hankali fa!" Ya faɗa a zafafe domin sun jima a nan ɗin yayi ta zagaye, ga wutsiyarsa duk inda ya saka ƙafa sai ta saka ita ma.
Da sauri Intisar ta ce" Akhi bari in tura maka lambar yaran sai ka yi kiran su, ko da basu iso bane sai ka ji, ka yi haƙuri dan Allah." Bai bata amsa ba ya kashe kiran, yana juyowa suka haɗa ido da Yusrah dake kallonsa tana tunanin to shi halittarsa ce bala'i ga dukkan alamu.
Irin yadda ya juyo bayan msg ya shigo wayarsa na lambar babbar *Mabruka* ya sakata dan ja baya kaɗan tana kallonsa, jim kaɗan bayan ya danna kiran lambar yarinyar, lambar ta fara ringin kenan ta ɗaga jikinta na rawa ƙasa ƙasa ta furta "Assalamu alaikum Dad2."
"Dan ubanki ban ce kar ki ɗaga kiran nan ba? Bani wayar nan? Nouncence!" Abinda kunnayensa suka jiyo masa kenan maganar da ƙarfi ƙarfi da kuma warce wayar da aka yi sai kashe kiran kuma ya biyo baya.
Ya ɗauki second talatin a tsayen nan da wayar a kunnensa idanuwansa ƙyam a waje ɗaya, juyawa ya yi ya nufi motar ya buɗe baya ya shiga kamar yadda suke yi ta bi bayansa a guje ta shiga ita ma ta rufo suna sauraro ya faɗawa mai taxi ɗin anguwar amma suka ji shiru, sai can ya danna kira, yanzun ma bata yi wani ringin ɗin kirki ba Intisar ta ɗaga.
Bai tsaya wani bayani da ita ba a haɗe ya ce" Adres ɗin gidan nake so?"
Intisar zuwa yanzu muryarta har rawa take yi ta sanar masa adress ɗin gidan, yana kashewa ta je da sauri ta zauna muryarta a sanyaye ta ce" Yaya, ina ga kamar ko zaka yi kiran sister ne? Akhi na kiranta bata ɗaga ba na bashi lambar Mabruka, ban san dai ya ya ba yanzu ya ce in bashi adress ɗin su kuma muryar sa dai ba yadda nake son jinta na ji ba."
Aba ya dube ta ya ce" Me yake faruwa ne?"
Intisar ta ɗan sosa kai ta ce"Aba dama Akhi ne