Showing 204001 words to 207000 words out of 397328 words
daga kwance ya zauna, sannan in wani abin yake da buƙata yana yiwa kansa daga zaune a kan kujerarsa, yakan danna abin kujerar ta miƙar da shi in ya jima a tsayen nan sai kuma ya zaunar da shi, shi da kansa docter ɗin sa sai da ya jinjina masa, ya kuma yi masa kyauta na ƙwazonsa, sosai yaron yake da juriya kuma ƙoƙarin sa ya ƙara bada gudunmuwa wajen saurin haɗewar ciwonsa da komai.
Tun a ranar asibiti ta sallame shi, sai dai ba zai tafi ba sai washe gari da safe idan za'a kai shi wajen jirgi, ya zamo a hanyarsu ta dawowa da dare fuskar kowanensu ƙawance take da farin ciki da fara'a, kowane sai walwala yake yi, harda su aslama, domin sun saba da shi sosai, yaron akwai gaggawar sabo ma sha Allah.
*INTISAR*
Kwana huɗu kenan da suke cikin halin tashin hankali tsakaninsa da Intisar, duk inda ya san zai bi dan ta sauko ya bi amma ya gaza samunta yadda yake so, magana mai tsayi ma ta daina haɗa su, hatta abinci ba iya ci yake yi ba yadda ya kamata dan tashin hankali da zulumi, bai saba da rayuwar nan ba shi yasa sam baya iya ɓoyewa, abun har ya fara damun Hajia domin har ramewa ya fara yi dan sakawa rai damuwa sai dai ta ki saukowa domin dama aka ce ka guji fushin wanda baya yi.
Ko a yanzu ya gama yi mata dukkan bayanan da zai yi mata da nuna mata kenan Hajia bata isa ta mata faɗa ba? Sai kawai ta tashi ta shige ɗakin ta ta rufe, bata yi ja in ja da shi ba, amma tana kwanciya a ranta ta ayana _"Ƙwarai Hajia uwata ce, sai dai ita a wajenta kai kaɗai ta haifa ban da ni, Allah ya kai mu gobe Akhi ya iso, ba ma zaka san ya zo ba sai abinda ya yanke, gaba ɗaya rayuwar irin wannan ta fice min a rai, na gaji da rayuwar nan marar yanci."_
*Washe Gari*
Tun ƙarfe goma sha biyu na rana ta gama shiryawa, ta sani cewa ƙarfe shida akace jirgin su zai taso, kuma tun ɗazu da ta yi kiran Anna ta sanar mata zasu je aeroport ne ɗaukan su, shi yasa ta gama shirinta ta fito sai dai har yanzu bata ga yaya Mubarak ba, kuma bata san inda ya nufa ba, gashi yanzu ba tuƙi take yi ba, haka kuma bata saba fitar ba ma bai sani ba shi yasa take ta kai kawo har ta gama yanke hukuncin zuwa wajen Bilal dan ya kaita.
Ai kuwa tana sanar masa yau fa su Yusrah zasu zo shi da kansa ya ringa magiyar su je ta kuwa bi shi bata shiga ta yiwa Hajiya ba nkwana ba suka ɗauki hanya, ta ƙi ko da sanarwa yaya Mubarak ɗin suka nufi aeroport ɗin suma.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
01/06/2024, 10:52 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*52*
Ƙarar cokalin da joli ke ta dokawa a cikin abincinsa ke neman hawan masa kai, karo na biyar kenan yana saka hannunsa ya janye nata sannan ya yiwa mahaifiyarta alamun ta hanata cakalkalar abincinsa, amma uwar sai ta yi dariyarta ta bar ta dan hakan ba wani baƙon abu bane a wajen su, sun saba yin haka idan suna cin abinci, shekarun Joli ba na ƙaramar yarinya bane amma har yanzu halayya na ɓatanci da gatan da ya wuce misali suka sa bata bambamce abinda ya dace mai shekarunta su yi da abinda bai dace ba, shi yasa a yanzu ta kasa gane yanayin mahaifinta ba irin na da bane, haka kuma ya dace ta ba mahaifin nata sarari ya huta.
Sake mayar da cokalin ta yi ta takali abincin, da mugun ɓacin rai ya saka hannunsa ya doke hannunta mai riƙe da cokalin rai bace ya ce" Ke baki da hankali ne? Tashi ki bani waje kafin na saɓa maki, tashi maza."
A tsorace ta tsaya tana kallonsa ta ƙi tashin, sai dai ta tsorata ainun kuma ta masa ƙiƙam tana kallon fuskarsa, da mamaki matarsa ta ce" Ideal lafiya? Me aka yi da wannan ihu haka?"
Rai ɓace ya dakatar da ita da hannunsa ya miƙe yana nuni ta da yatsa ya ce" Ke wace irin daƙiƙiya ce? Sam baki da tunani, baki san lokacin da ya dace a bani waje in sarara ba, to na bar maku gidan gaki ga abincin idan kika cinye ki ƙara, shirmen banza da wofi."
Rai ɓace ya fice ya bar gidan ko karyawar bai idasa yi ba sai faɗa yake yi tamkar an aiko shi, galala ta raka shi da kallo hankalinta tashe, tunda ta auri Hamat basu taɓa samun saɓanin irin wannan na tashin hankali har haka ba, abin ɓacin ran take yi masa fa ya shanye ya ƙyaleta,
amma a kwanaki biyun nan ta kula abu kaɗan ke hassala shi, sai dai baya yin tsayi yake ha(ura, yau ɗin ne abin ya yi nisa har da zagi haka?
Da sauri ta miƙe ta nufi ciki dan samawa kanta mafita dan bata san wannan fuska ta mijinta ba, ta yiwu wani ne ya ɓata masa rai yake son hucewa a wajenta ko wani abin kuɗin sa ya hargitsa shi har haka?
Uncle Hamat na fita ya shiga motarsa bai yi jiran sabon direbansa ba ya samu waje ya tsaya ya yi kiran Yayansa dan tunanin dake damunsa a kan AA, sosai yake da fargaba a kan inda AA ya shiga kuma, ga tashin hankalin rashin jin Sani direba, idan yana tuna haka sai ya ji kar dai AA ya wa Sani wani abun? Amma kuma tashin hankalin da hakan ke haddasa mishi ya sa da ya fara tunanin sai ya yi gaggawar kawar da shi daga ran shi.
Ba ta jima tana ringin ba ya ɗaga, suka gaisa sosai kamar yadda suka saba, da sakin fuska a yanayin maganarsa ya ce" Akhi, wai ina son ne? Ni kam na bani, yaron nan sai wahalar da zuciyata yake yi."
Shi ma Aba nasa sai ya shiga tunanin to me yake faruwa har AA ya yi tafiya mai nisa haka ya dawo bai sanar da uncle ɗin sa ba? Lafiya kuwa? Sai dai ya basar a tausashe ya ce" Ban gane ba? Kana nufin baka san ya yi tafiya kai ɗan sa US ba? Har yau zasu dawo? Yanzu haka daga office zan haɗu da su Annarsu a aeroport mu tarbo su."
Da mamaki sosai ya ce" Ɗan sa? Wani ɗan kuma Akhi?"
Da mamaki Aba yace" Wai kana nufin har maganar yaron bai maka ba?"
Ya amsa mishi da" E Akhi, gaskiya bai min ba."
Aba yace" To! Amma garin ya haka? Ni ban sanar da kai bane saboda sanin ba ya ɓoye maka komai, amma ko da yake ba kowa ya san maganar yaron ba saboda bai da lafiya, sannan yana so sai ya zama ɗansa a shari'ance."
Da shiga ruɗu ya sake cewa" Wai wane ɗa ne haka Akhi? Na cikin sa ko kuwa?"
Aba ya ce" Ina wannan hatsari da aka yi gidaje suka faɗawa wasu bayin Allah waɗanda aka kai wasu daga ciki asibiti?"
Uncle Hamat gabansa ya faɗi yana zaunen nan ya ce" Eh...eee, na gane Akhi."
Aba ya ce" To akwai wani yaro a ciki sunansa Safwan, yaron bashi da kowa shine ya yi adoptern shi, yaron ya samu matsala a bayansa shine ya fitar da shi aka masa aiki, yau za su shigo in sha Allah."
Handchief ya ɗauka yana goge gumin dake tsatsafo masa a hankali ya ce" Ayya, ai ban sani ba, da ni zan kai jikana da kaina a masa aikin, Akhi zan yi kiran ka anjima kaɗan, sannan zan shigo gidan da kaina zuwa yamma ko gobe da safe."
Daga haka suka yi sallama, uncle Hamat ya rasa me yake yi masa daɗi, abubuwa suna neman haɗe masa tunani su saka shi a halin tashin hankali mai tsanani
ya rasa zuciyarsa dake buga masa idan ya tuna sunan yarinyar nan kaɗai zai iya kashe shi ko saƙe saƙe da tunanin ina Sani yake da kuma me AA ya sani a kansa ne zai kashe shin? Fargaba ta ninku a zuciyarsa hankalinsa ya tashi matuƙa, saboda tabbas wannan ma wata hanya ce ta tonon asirin sa, idan yaron da ya sa aka wulaƙanta ya zama ɗan AA yanzu? Hakan na nufin sun san abinda ya faru, shiru ne suka masa dan iskanci ko me? Amma kuma ai yaro ne, bai san me ya faru ba a asibitin, an dai fito da shi an ajiye kawai, dan haka ba zai iya cewa komai a kan sa ba, dole ya tayar da motarsa ya nufi gidan sheƙe ayar sa dan ya kwanta ko jininsa zai daidaita, tabbas zai je ya samu AA idan ya zo a daren yau ba sai gobe ba, sannan da yamma zai je ya samu Docter Siddik su yi magana ta gemu da gemu a kan maganar Yusrah.
*Aeroport*
Tun a hanya Intisar ta kira Anna take tambayar su sun sauka ne? Dan taga shida har ta ɗan gota da kaɗan, nan Anna ta sanar da ita e jirgin ya sauka sune dai basu fito ba, nan ta sanarwa Bilal ai kuwa ya ƙara gudu yana faɗin "Aunty ba fa na so wani ya fara kalle min Yusrah, ni nake so na fara ganin ta."
Murmushi dai ta yi tana ɗan ƙara gyara zaman ta a jikin kujerar motar dan bata jin daɗi sam na yanayin ta, suna isa a cikin sa'a suka same su kusa da motoci ana ta murnar ganin Safwan a kujerar sa.
A nutse ta fito ta tunkare su tana ƙarewa yaran ta kallo daga nesa Bilal na take mata baya, kyaɓe fuska ta yi sai ga hawaye sharrr! Daga nesa take hangen su, amma kallo ɗaya ta musu ta fuskanci canjik dake tare da su, yo americar banza da za ta sa ta kasa gane yaran ta, rainon da ta ma yaran ta kafin ta bayar da su ma na bugawa a jarida ne, sannan Anna ma sha Allah dake da jiki hakan yasa duk yaran gidan ma idan suna ƙanana zaka gansu kutuf kutuf da kumatu da ƙibar su ma sha Allah, Uka dama tun tana ƙarama da jikin ta ta tashi sosai da kuma tsayi na mahaifin ta, hakan ya sa tun suna nan kana ganin su za ka ga kamar kajin turai, amma yanzu wannan damatsan da kumatu na Uka duk babu, a haka wai suna turai ne?
Yusrah da tun tsayawar motar su ta kula ne ta nunawa yaran maman su, suna waigawa inda ta nuna musu da gudu suka ruga suka rumgume ta, rumgume su ta yi sosai a jiki tana kuka tana matse su kamar zata mayar da su ciki. Daga bisani kuma ta ɗago tana ta shafar fuskar su da sumbatar kumatun su tana tambayar suna lafiya? Suma kukan suke suna jinjina mata kai alamar e, har saida Bilal dake bayan su shi kanshi dake namiji ya ga canzawar yaran bare uwar su, da fara'a ya kamo hannun Anna ƙarama yace "Annarmu, come on my baby."
Da sauri ta rumgume shi ya sumbaci kan ta da ya sha gyara wajen Yusrah yace "Ya kike?"
A tausashe ta amsa da "Lafiya lau uncle B."
Kumatun ta ya ja yana murmushi yace "Good girl."
Uka ma kallon shi ta yi ta gaishe shi ya amsa yana dafa kan ta da rumgumata a jikin shi, lokacin Intisar ta miƙe tsaye ta nufi su Anna dake can ga Safwan suna shirin shiga mota. Kafin ta isa Yusrah ta tunkare ta suna haɗewa suka rumgume juna da murnar sake ganin juna, sannan suka riƙe hannun juna zuwa ga su Anna Yusrah na tambayar "Aunty Intisar ina Yaya Mubarak?"
A sanyaye Intisar tace "Mybe he was...i don't know Yusrah, muje dai kawai, ya jikin Safwan?"
Suna ƙarasawa su Manal suka gaishe da Intisar da ita kuma take satar kallon dodon ta wato AA, wallahi sai ka wa Aba laifi ka fuskance shi amma ban da bawan nan, yanzu haka tana ƙare shi da rawar murya tace" Barka da zuwa Akhi? Ya hanya?"
Basar da ita kawai ya yi akan laifin da ita ba nata bane kawai ya dubi su Anna yace" Muje."
Ba yadda ta iya haka ta koma motar Bilal ita da Yusrah da Uka, amma Anna ƙarama tana tare da Safwan da suke kamar tsara ne, ita a wurin ta ta samu aboki daidai da ita yanzu, dan haka tana maƙale da shi da kuma Dadyn shi da Anna da Aba dake gaba, sai motar su Manal daban da Abrar, Nabihat kuma tana gida bata zo ba, a wautar ta ta tsaya ne tarban future husband ɗin ta a gida da abubuwan bazata.
Suna isa kowa ya shiga fitowa ana ta rufe ƙofofin mota, amma AA sai bai rufe ƙofar da ya fita ba ya ɗan yi gaba kaɗan da tunanin ai *wutsiyar sa* za ta fito yanzu ita ma, hmmm! Sabo tirken wawa, kwana goma kuma ba kwana ɗaya ba, in dai zai fita a can kuma tare da ita to tana biye da shi ne yadda kasan wata uwawun shi, wannan sabon ya sa ya yi haka... amma sai ya ji ya yi tako biyu zuwa na uku dan isa inda zai taimakawa ɗan sa ya fito amma babu alamar ta a bayan shi, da ɗan mamaki ya juya irin ka ga ina nakan nan ya shiga? Sai ya ga wayam babu koma a wajen sai dreba da ya fito yana rufe ƙofar da AA ya fita.
Kamar dai mai neman ayi sai ya shiga ɗan yallara idanuwan shi da tunanin _"Ina kuma aka shiga? Ai dai ta fito daga jirgi, kar ta ja min jafa'i wajen Annnnnn."_
Bai ƙarasa faɗin Anna ba ya hangi Yusrah gaban motar Bilal daidai da Bilal ɗin ya ranƙwafo kanshi kusa da kunnen ta kamar raɗa yake mata, wai dan sharri irin na shaiɗan sai ya ga yarinyar nan da ba isassar lafiya gare ta ba tana murmushi har da rufe fuska da tafukan hannaye na wasu sakanni, sannan ta ɗauke hannayen nata ta kalle shi ita ma tana magana... Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Me suke faɗawa juna? Wane iskanci ne kuma haka? Kenan dai ita dama haka take ko? Ba shi kaɗai ta rena ba dama? Da kowa ma magana take yi kan ta tsaye haka da yaƙar haƙora... Mtssssss!
Anna dake kallon shi taga inda yake kallo tana jira ne ya zo ya kama Safwan, da ba wanda zai yarda ya taɓa shi ya yi laifi anan tace "Baban shi zo ka taimaka masa?"
Ruf! Ya rintse idanu da wani bijirarren takaici na me ye nashi a ciki na tsare su da idanu? Me ya sa har ya bari ma hankalin shi ya ɗauku haka, sai kawai ya juyo da kanshi yana taɓe baki ya nufi wajen Safwan ya shiga ɗauko shi ya ɗora kan kujerar sannan suka rankaya cikin gida har da su Yusrah da suka fito suma daga motar.
*15MINUTE AGO*
Zuwa lokacin ne kowa ke zaune wasu har sun fara taɓa abubuwan da aka zube gaban su na kayan marmari da abun motsa baki. Nabihat ma fitowar ta ta biyu kenan tare da masu aiki, ta ɗauki ado iya ado cikin doguwar rigar shadda kuma ta yi kyau, ga ƙamshi da take bazawa duk inda ta gifta sai an ji wucewar ta, sai dai wannan farantin na ƙarshe da ta ɗauko gaban AA dake zaune daf da Safwan yana bashi cream ta aje wanda ko kallon inda take bai yi ba sai ma tissue dake maƙale a wuyan Safwan da ya saka yana goge masa baki.
Tunda ta duƙa bata miƙe ba saida ta kalle shi tace "Yaya Aswan barka da zuwa? Ya hanya? Ya jikin Safwan ɗin?"
Kallon ta ya yi, shi wallahi ba ya son wannan gashin da mata ke sakawa a idanuwan su, kai dan fa yana soja ba cewa aka yi baya jin tsoro ba, akwai abubuwan dake tsorata shi, kuma tsaf yake da tabbacin idan yana farkawa a bacci suka haɗa idanun nan da Nabihat ba abinda zai hana shi ƙurma ihun tsoro, taɓe bqki ya yi a taƙaice kawai yana maida hankalin shi kan Safwan ya amsa mata da "Alhamdulillah."
Da takaicin amsar da ya bata ta dube shi, amma tunda da mutane a wurin sai ta haɗe kawai ta kalli Safwan ta masa murmushi tace "Safwan."
Sai kuma ta miƙe kawai ta koma madafa tana jiran mutane su fara ragewa ta haɗu da shi a yi duk wacce za'a yi, kusan kowa na falon na taɓa hira ne da na kusan shi,