Showing 216001 words to 219000 words out of 397328 words
mishi lambar sannan ta bashi yana ta mata godiya ta tafi shi ma koma ciki cike da farin cikin da ya baibaye masa zuciya.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
06/06/2024, 09:12 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕??❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*55*
*Kasancewar* jiya ma bai shigo da dare ba sai ta waya suka yi saida safe, yanzu kuma yana zuwa Aba ya zaunar da shi dan muhimmiyar maganar da yake ta son yi masa.
Yawancin lokuta idan aka yi irin wannan zaman da shi ya tabbata babban magana ne za'a kawo masa, zama ne suke yi ya zamo yana gabansu su kuwa su zauna a kujera ɗaya, to fa hakan na nufin za'a yi magana mai mahimmancin gaske ne, shi yasa a yau da Aba ya nuna masa ya hau sama zasu yi magana ya zauna ya nutsu yana sauraron su.
Ya kusan minti biyar a zaune a gaban nan nasu, sai dai daga Aba har Anna sun ƙi su buɗe baki su yi magana, kowane na ciki na ciki, Shi Aba kallonsa yake yi a ransa yana mamakin wai ace aure? Auren da zaka ga samarin yanzu da zarar sun fahimci anfanin anininsu a jikin su burin su su tara kuɗin sadaki a kai a kawo masu macen a kusa da su ko da kuwa basu da aikin yi, sai idan zama ya yi zama ne kuma wasu mai ke isar kan kaza, wasu kuwa duk rintsi babu gudu babu ja da baya tsakaninsu da mace kuwa sun ji sun gani har a mutu suna manne uwa cingan, amma ban da Jikan Anza, gashi shine babba, kuma shine ke tsawatarwa, amma yana kallo matar Humed yanzu haka ɗauke take wani cikin shi kuwa ko oho! Ko inma dan saboda ya yi aure ya haihu ake damunsa yanzu ai ba halin damunsa tunda ɗan ake so gashi ya kawo ko? Zantawar nan yana so idan ya yita jikan Anza ya gane ɗaurin aurensa a gaban nan bai fi saura sati biyu zuwa uku ba, ya kuma duƙar da kai ya yi godiya ya ce ya yi biyayya ne.
Anna kuwa a cikin zuciyarta gaba ɗaya wannan karon tamkar wacce aljannu suka kama, to sai ace aljannu mana, ace babban burinta? Burinta da ya fi komai damunta ya samu amma a yanzu da aka zauna dan a dasa ɗigo saman aya a shata layi sai ta ringa addu'ar Allah ya sa ya nuna sam ba ya so? Ba ya so fa? Me yasa take ire iren tunanin nan? Sam bata son abun nan, bata san dalili ba amma gaba ɗaya abin nan bai kwanta mata ba, bata ga mahaɗin abin ba, ba dan rashin kyau ko iyaye nagartattu ba, a'a fa, ta san cewa chef mutumin kirki ne da za'a so haɗa zuri'a da shi, kuma matarsa ba zata ce ga laifinta ba tunda suke babu abinda ya taɓa haɗa su na ɓatanci, amma kuma haka kawai sai take ganin kamar soyayar nan da wani abu da ya rage a cikinta, kalar bata cika cif ba, damuwa kan dameta sosai idan ta yi tunanin nan, sai gashi yau Abansu ya sako ta gaba kan a zo a fatattaki AA a kan maganar a nuna masa bashi da wajen kamawa a yau sai biyayya.
Tunaninta ne ya katse a lokacin da Aba ya yi gyaran murya ya ce" Cire tagumin mana Jikan Anza?"
Hannunsa ya cire yana dubansu a ransa ya ayyana _" Dole na yi tagumi, ban san irin tashin hankalin dake jirana ba, wannan shirin na tabbata abinda na aikata ba ƙarami bane, Allah ka sanyaya zuciyar *ɗan Anza*, dan kuwa ga dukkan alamu maganar tasa ce, da ta Haja Anna ce tun a waya zata sauke abinda ke ranta kafin a yi zaman sulhu ai._"
"Yaya maganar mu ta ka fitar da matar aure?" Aba ya faɗa a dake kuma kansa tsaye.
AA ya ɗan yi zuru yana tuno maganar tasu, inna lillahi! Wallahi ashe haka suka yi da Aba, kai ya Rasulullah sallallahu alaihi wa sallam, shin wai shi auren nan ba lokaci bane iyi? Kuma bayan wannan yanzu da shekarunsa a ringa irin wannan da shi? Shi dai ya shiga uku ya lalace.
A hankali ya soke kai bayan ya ɗan sosa ya ce" Ina kan aikin a kan hakan Aba."
Aba ya sakar masa harara ya ce" Kana kan aiki a kan me fa? Kana da wacce kuke soyaya ne?"
"Lah!" Ya faɗa yana rufe bakinsa, sai kuma ya saka hannayensa biyu ya rufe fuska ya ce" Aba Anna tana kallona fa."
Daga Aban har Annan sai da suka zaro ido suka kalli juna kafin su kalle shi, Aba ya ayyana _" Yau ga iya shege, yanzu jikan Anza ka rasa me zaka ce sai kana kunyar Annanrka ta san kana da budurwa? Idan ana cewa halina ya ɗauko ni abin sai ya ringa zuwan min wani iri, ni ai ba halina bane wannan gaskiya, iya shegen jikan Anza ya dame nawa ko a lokacin ƙuruciya."_
Anna kam sai ta taɓe baki ta jinjina kai sannan ta masa ƙuri tana ji a ranta cewa ɗan nan ko? Ire irensu ne kai da ka haife su in kana son su yi maka wani abu mai mahimmanci sai ka shirya zamanka da su kun yi kare jini biri jini sun gane sunne ƴaƴan kai ne iyayen zasu saddaƙo, iya shegen Aswan a kullum sabuwar paji ce ɗauke da sababbin karatu.
Aba ya ce" Ka kiyayeni, Jikan Anza ka kiyayeni ka bani amsa akwai wacce kuka yi alƙawarin aure da ita ne?"
Aswan ya sadda kansa a hankali ya ce" A'a Aba, a yanzun dai babu, amma ina kan aiki a kan haka in sha Allah."
Aba ya haɗe hannu ya watsa masa ya ce" Ungo nan, nace Ungo nan, to ni akwai kuma na shirya."
Da sauri ya kalli Aba, shi akwai kuma ya shirya? Ya shiga uku aure Aba zai ƙara? Sai ya kalli Anna ya ga yanayinta, da sauri ya ƙara kallon Aba da idanuwansa yake masa alamun kar ka ɓallo mana aiki, idan aure zaka ƙara ka bari mu tattauna, in ya zama dole ka ƙara sai mu mata roƙon Allah dai da sauransu sannan mu sanar mata, ba ka faɗa kanka tsaye ba ka sa uwata ta suma.
Aba kuwa ya ƙure idanuwansa da kallo ya ga kamar wanda zai tayar masa da bori haka? Sai kawai ya ayyana _"Yau ko bishiyar kuka zaka ɗora saman kanka sai na sanar maka maganar nan Jikan Anza."_
Dan haka ya haɗe fuska tamau ya ce" Eh, ina nufin na yi maka mata, kuma so nake yi nan da sati biyu ko uku a yi komai a gama."
Sai da AA ya sauke ajiyar zuciya ya dafe goshinsa
Aba kuwa ya kalli Anna ya mata alamun ta yi magana mana ita ma, ita kam wasu lokutan idan Aban AA na magana da shi sai ta ji kamar ta amshe maganar wallahi, yo duk da zaman da aka yi bata so ai ba shine zai sa a yi ta zagaye zagaye da yaro ba sai kace shi ya haife su ko? Sai kawai Aba ya ringa zagaye zagaye idan zai yi masa magana wallahi abin tarin takaici.
A dake Anna ta ce" Kai ka ɗago ka bamu amsa , ya ya ana magana kana wani dafe kai, ai ka ji abinda babanka ya yanke ina fatan zaka yi biyayya ne?"
Aba ya gyaɗa kai ya ce" Eh, da muka yanke dai ko Annar su? Muna fatan kuma zaka yi biyaya ne."
Aswa ya gyaɗa kai yana murmushi a ransa ya ayyana _" Ni gwarama a min auren dolen nan wallahi, tunda na kasa nemo macen Aba ai ya nemo min."_
A bayyane kuwa sai yace" To Aba Allah ya nuna mana."
Sai kuma ya sadda kai ya ci gaba da ayyana _" Ni ai kun tsorata ni ne, da ace Aba ne zai ƙara auren nan ai da na shiga uku, to yanzu fa da wata maganar ake yi ba wannan ba, da wani rikicin ai gwara wani, gwara ace ni ne aka yiwa auren dolen, ƙarƙarinta idan yarinyar bata yi min ba in zane banza in kaita gidansu shikenan, in kuwa ta min sai mu yi zamanmu, iya ruwa ai fidda kai, asirinmu a rufe da ɗan mu ko?_"
Aba ya kalle shi sororo, Anna ma ta masa wani kallon, Aba ya ce" Ban gane to ba?"
Aswan ya kalli Aba da mamaki, to me kuma ake so yace? Aba ya ce" Ka ga na fi gane maka idan aka yi sama aka yi ƙasa da kai, ya ya zaka ce to ko yarinyar baka san ko wacece ba? Sai kawai kace to? Kana nufin duk wahalar nan da na sha dan ka yi aure da tuntuni ma haka nace maka da tuni ka yi auren? Aslama kin ji wata tsiyar ko?"
Anna ta fitar da hucin " Hum." Tana kallon uban da ɗan, shima AA mamaki ya nemi kashe shi da halin Abansa, kai halayyar Abansa wani lokacin sai ya ga anya kuwa? Ko ba komai girman nan fa na Aba ƙara bayyana yake yi ta sigar rikicin sa, to jama'a, ka yanke hukunci an yi biyayya cikin sauƙi bai yi maka ba? Ana cewa ya yi rigimar Abansa ne aa shi ya san cewa shi ɗin banza? Bai isa ya kamo ƙafar rikicin Ɗan Anza ba.
A tausashe ya ce" Aba, na san ai idan zaka zaɓo zaka samo min mai nutsuwa mai hali mai kyau kuma mai kyau kamar dai yadda ka zaɓo Anna ne in sha Allah, to me yasa zan ƙiya? Na yarda, ka yarda da ni Aba."
Anna aka wani rauda kai ana wani cira kai an ce mai kyan hali ita, mai kyau ita, mai nutsuwa ita, shi da kansa Aban sai da ya wani hura hanci ya ce" Ai kuwa, yarinyar duka ta haɗa, ƴar gidan babanka ce, yarinyar wajen Chef, Nabihat, ai har mun yi magana da baban naka fa, kai kawai muke jira, zuwa dare zan sanar masa ka amince shikenan sai mu fara shiri, ma sha Allah."
Shi dai du yadda ya so hasaso kamaninta ya gaza ganewa, idan yaje gidan itace ke gaishe shin nan? Yana tunanin dai ita ɗaya ce ai yanzu a gabansu mace ko? Ko da yake ko menene ai ba wani abu lafiya lau ne, bari ya miƙe ya tafi zasu haɗu da Barista ne nan da minti talatin, domin sun yi zasu haɗu ƙarfe biyar na yamma kan case ɗin Humed.
A baje ya nunawa Aba lafiya lau ne kawai sannan ya miƙe ya masu sallama Aba har rakiya ya masa daidai ƙofar ɗaki yana washe masa haƙora, Anna kuwa ta bi shi da harara a ranta tana ayyana _"Kai kawai ba'a ci maka alwashi? Ga ranar ka nuna baka so ka murje ido kace sam baka so shine zaka yi mana biyayya? Maimakun ka ce baka so mu yi sama mu yi ƙasa ka nuna ina ba zaka taɓa amincewa ba sai kawai ka amince? hum!"_
Yana saukowa ƙasa daidai abin hawa na ƙarshe ita kuwa ta zo ɗauke da basket cike da kayanta na wanki da aka wanke mata a inji aka kai waje suka bushe, zata kai su ɗakin su ne ta adana ta ga AA ɗin yana saukowa.
Sam bata san ya shigo gidan ba, shi yasa da ta ganshi ta kasa ɓoye murnar ganinsa da ta yi, ta yi irin yadda take masa idan zata gaishe shi da ɗan rawar muryar nan da matse murya da wani fari fari haka na don a birge masoyi.
Tsayawa ya yi yana kallonta, tun daga fuskarta har ƙafarta, a nutse ya ce" Ke ce Nabihat?"
Nabihat ta ɗago da wani uban farin ciki ta dube shi jin sunanta a bakinsa, shi kuwa ya ɗan ja baya da sauri dan ɗagowar da ta yi gashin idon nan sai da ya ji kamar zasu kamo shi, gashi saka su da take yi ya sa ko da yaushe idanuwanta ja gare su, kuma fuskar kanta sai ya ga kamar an maka mata wani abu ta yi bum da ita.
Idanuwan da ya zaro bai sadaka su ba yana ƙare mata kallo har ƙasa ya zagayeta ya sauka ya sake juyowa ya kalleta sannan ya juya ya fice a fallon ya hangi su Manal da Yusrah suna zaune suna fira, ita Yusrah waya ce take amsawa, su kuwa suna shan fira ya wani tsaya ya ƙare masu kallo ya cire kai ya ƙarasa wajen motarsa ya shiga yana dafe ƙirji a bayyane ya ce" Wannan idan ka farka cikin dare fitilu a kashe ka kalli idanuwan nan babu abinda zai hana ka ihu, amma wanda ya ƙirƙiro wannan gashin idon duk inda yake aje a duba ko aljani ne ko yana da alaƙa mai kyau da aljanu sun bashi suffar su, lahaula wala ƙuwata, wai wannan ce Aba yake nufi? Taɓdijam!"
Sai kawai ya ɗauki wayarsa ya shiga whatsup ya danna voice note bayan ya yi alama an buɗe masa gidan ya narkar da murya sosai da girmamawa ya ce _" Asalamu alaika Abana, Abana yanzu yanzu na ga yarinyar dan Allah Abana ka cenza min ka ji? Wallahi ni tsoro take bani har raina, ka canza min ban ƙi a min auren nan da sati ukun ba amma dan Allah a canza min matar Abana, na gode Allah ya ƙara lafiya ya ƙara nisan kwana, na gode Aba na gode sosai."_
Daga haka ya tura ya tayar da motar ya bar gidan bayan ya kashe wayoyin, ya tabbata in an yi nisa a ɗau minti ashirin Aba ya duba saƙon, idan ya duba kuwa tabbas zai neme shi ne ko a gidansa ne, shi kuwa har ga Allah wannan yarinyar ya sani ne in dai aka aura masa ita ba zai iya zaman aure da ita ba, shi yo shi banda aukin farin babu abinda ma ya je da ra'ayinsa kuma baya son farar mace, a dai duba wata ko cigiya aka yi masallaci ai ba za'a rasa wanda yake da wacce ta rasa manema ba ita ma sai a haɗa su su taru su rufawa juna asiri, amma fa mai nutsuwa ba mai harare harare ba.
Da ya je suka haɗu da Barista suka tattauna a kan maganar kuɗaɗen nan sosai, Barista ya kwantar masa da hankali ya nuna masa ko yanzu ya gama bincikensa yana iya shigar da ƙara kansa tsaye, ya gama rufta Hamat a cikin maganar kuɗin nan, Hamat ya yi shirme sosai da yake rubuta kuɗi masu yawa haka ya ƙi saka dalilin fitar su, ya kuma saka hannu da saka hannunsa, sannan ya ba ɗan Yayansa uwa ɗaya uba ɗaya, idan har ya nuna zai saka Humed a cikin matsala saboda maganar kuɗin nan ya makaro, domin da maganar zai yi anfani ya saka shi shi a matsalar, idan aka yi duba da farkon zance familly mai girma irin wannan, aka yi duba da irin alkairin da shi Aba ya yiwa uncle yake cikin yi masa ba gajiyawa, har da su asibiti dake hannunsa, dan yau Uncle ya cire kuɗi masu yawa ya ba Humed saboda murnar aure, da murnar an masa haihuwa, da gudummuwar fitar da matarsa waje lokacin da ta yi rashin lafiya, da gudummuwar ginin gidansa da yake yi kamar yadda suka tsara shi barista ɗin da Humed ɗin a lokacin da suke tattaunawa da neman mafita ta abinda za'a raba fitar kuɗaɗen da daidai evenement ɗin da suka dace tsaf kuwa suka samu babu wanda zai yi mamakin yawan kuɗin ko dalilan fitar kuɗin, masu shi suna yiwa junansu kyautar da ta fi haka gigita tunani dan kawai isa da nunawa juna soyayya ta wannan hanyar, dan haka kuɗi sun fita kuma an ci an gama lafiya lau ne, ya kafta kan harkar bincikensa da ya dakatar saboda wannan dalilin, domin ba zai taɓa yin gigitar da zata saka shi kuka da hawayensa ba, yana so a samu mafitar ne dama kafin ya farma lamarin.
Bayan sun gama tattaunawa da farin cikin abin suka tashi, a tausashe AA ya ce" Am Freind, idan Aba ya yi kiran ka dan Allah kace baka ganni ba ka ji?"
Mukhtar ya dakata ya zuba masa ido ya ce" Me ka aikata?"
AA ya kalle shi da sigar harara ya ce" Wai a me ka ɗaukeni da kake min kallon wani iri? Me zan aikata kuwa ni? Me ma nake cewa ne ni ɗin?"
Mukhtar ya fitar da yatsarsa ya ce" Alƙur'ani ban yarda ba, ka faɗi me ka aikata ko in faɗawa Aba gaskiyar cewa yanzu muka rabu."
AA ya yi tsuru yana kallonsa a hankali ya ce" Wai auren dole zai min, kuma ni yarinyar ke bani tsoro, shine nace bana so, to ka ga yana iya nemana dan mu warwareta domin yanzu nace ina so, da na fito ne na ga yarinyar sai