Showing 243001 words to 246000 words out of 397328 words

Chapter 82 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70089

huɗu da Arif da wani yanayi Arif ya ce" Baabaa, ɗan dakata, wai ba shi uban arnan bane ya ce ka zo dama ya sa muka zo yanzun?"

AA ya ɗan yi tsai, sai ya ɗauke kansa ya masa shiru, Arif ya tafa hannu ya ce" Amma ana ƙaniya a ƙasar nan, yanzu idan aka rufe mu fa? Ka ga wallahi ban shirya komawa wajen can mai kashewa mutum zuciya ba, yanzu zance ne muka zo a irin wannan lokacin?"

AA zai bashi amsa ya hangi an buɗe falon an fito, kansa ya ɗauke daga kanta yace" Yi haƙuri mu fita sai in gaya maka dalili."

Daga nan suka yi tsuru har ta ƙaraso wajen motar da nufin zagayawa ta shiga ta ɗaya ɓarin sai ta ga Arif zaune ya yi tsuru tsuru yana kallon ƙasa, wani abu ya ƙara riƙe mata wuya, yanzu da ace mahaifiyarta bata tafi ɓangaren mahaifinta ta barta tana jiran tsamanin ganinsa ba da bata san ko zata barta ta fito yanzu wajensa ba, tun ɗazu fa mamanta ta sa ta ɗau wanka ta sanar mata cewa wannan ce dama ta farko da zata fara haukata tunaninsa, hatta yadda zata ringa masa kissa sai da ta koya mata, har da su turaran baki aka fesa saboda idan ta yi magana ƙamshin bakin ya shiga hancinsa dan tsabar bala'in tun tana duban hanya har barcin wahala ya ɗauketa, a yanzu ba wai warin bakin abin barci ba hatta kwalinta ya haɗe a fuskarta sannan ya zo.

Ɓangaren nasa ta dawo ta gaishe shi fuskarta gaba ɗaya ba daɗi, amsawa ya yi yana kallon idanuwanta a ransa ya ayyana _'Wannan gashin ido nata kamar aljana.'_ A fili kuwa sai ya ce" Kamar barci kika fara ko? Bari mu wuce na dawo wani lokacin, ki koma gida sai gobe in sha Allah."

A ɗan zabure ta dube shi, haka ma Arif har ga Allah sai da ya zabura ya kalle shi, sai dai bata da damar tankawa, gaba ɗaya ji take idan ta buɗi baki tana iya zagin wanda ya fi ƙarfin zagi ya kakkarya banza ya fasa aurenta, shi yasa ta juya ta nufi gidan, shi kuwa ya tayar da motar ya fice a gidan.

Sun ɗan yi tafiya Arif ya tsayar da shi bayan ya cire uban tagumin da ya yi yana kallonsa ya buɗe motar ta fita ya ce" Jeka kawai, jeka Allah ya tsare, ni kam ka fi ƙarfina ubana ne kai wallahi, yanzu matar da zaka aura ce ka je zance ƙarfe ɗaya? Yarinya ta fito yanayinta na nuna ranta ɓace ka ƙi fita ka duƙa ka rarrasheta sai ma ka korata? Ka guji mata AA wallahi, ka guji ɓacin ran mata."

Aswan ya ja tsaki ya ce" Zaka zagayo ka shiga mu je ko in fito in ɗauke ka a saman kaina in saka ka boot mu je ne?"

Kiskirim ya yi ya gane faɗar da AA ya yi tabbas yana iya aikatawa sai ya koma ya shiga motar yana sake kallonsa, AA ya tayar da motar suka ci gaba da tafiya ƙasa ƙasa yace" Aba fa ya ce a yau sai na je, so ka ke ace masa ban je bane ya shaƙe ni? Kuma ba fushi ta yi ba, haka yanayinta yake wannan a kumbure ɗin nan."

Magana kasa fita a bakin Arif ta yi, ya yi zuru AA na zura gudu da su har suka isa gidansa suka shige dan dare ya yi kuma a nan zai kwana a ɓangaren baƙi, domin ya saba kawo masa kwanan dama tun da ya fito.


*Sati ɗaya da kawo kayan Yusrah.*


*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
07/06/2024, 18:12 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*61*



Tunda aka kawo kayan Yusrah gadan gadan suka shiga shirye shirye ba ji ba gani, siyayya Anna ke yi ba ji ba gani na kayan auren Yusrah, ɗinkuna kuwa ya zamo kusan kullum sai an kai dan aunty Intisar ita ke kula da lamarin tufafi da kuma gyaran amarya wacce a yanzu shirin gyaranta ake yi ka'in da na'in.

*A* ɓangaren Nabihat kuwa tun bayan an kawo nata kayan da kuɗin sadakin bayan sati guda mahaifiyarta ta gama shirin ta je gidan ta zauna na ɗan lokacin da zata kawo mata rahoton me mahaifiyar AA ke nufi da su da sauransu dai dan su san ta inda zasu hau maganar kuɗin nan, haka ɗin kuwa aka yi, ya zamo ita ma tana gidan zaune tare da ƴan matan gidan, sai dai wannan zuwan nata gaba ɗaya ta ƙara fice masu a rai saboda ire iren abubuwan da ta zo da su na wulaƙanci da ɗagin kai, ta sako Abrar a gaba da habaicin ta gani yanzu ita da AA sai dai hange, haka kuma sauran ƴan matan ko magana zata masu da wani jiji da kai tana nuna yanzu fa ita matar Yayansu ce dole su bita a hankali.

A zaman da ta yi ta ringa bin ƙwaƙwaf dan ta gane shin da gaske ne ita ce a vidio da hoton da aka saida mata a bakin boda an tare su matsayin ƴan ƙunar baƙin wake ita da wani ɗan iska? Idan kuwa ita ce lalle da za'a yi bur'uba a gidan nan, dan duk a wannan lamarin babu wanda farin cikinsa ya rufe mata ido irin na Yusrah, gani take yi yarinyar bata isa ta kai matsayin da ta kai ba
idan aka zo yi mata gyaran jiki na safe daban na yamma daban haka ranta ke ƙuna tana mamakin irin yadda suka ɗaukaka lamarin yarinyar da ko sani basu yi ba, wacce ta gagareta ɗaya ce ƙwal Goggo Tidin, ita ma ta tsaneta kamar yadda ta tsaneta ita ma , sam basa shan inuwa ɗaya, Anna kuwa babu abinda ya dameta irin yadda take mu'amalantarta a da haka take yi a yanzu, uwa uba shi oga kwata kwatan wallahi sai ya yi shigowa biyar gidan a wuni idan ya ga dama ya wuce ta inda take sau biyar ɗin nan ta gaishe shi ya amsa amma sai an ce masa wance ce fa, abin nan na dukan ƙirjinta fiye da tunanin bawa yana ɓata mata rai, balle idan ta kalli wani sabon salo wajen Abrar in tana waya, ta kuma kalli irin yadda Bilal ke bautawa soyayyarsa da Yusrah sai ta ga ai ta fi su gata da komai amma suka fita samun wannan farin cikin, a nan zuciyarta ke kitsa mata abubuwa daban daban a kan ƴan matan, wa'inda take da burin ganin sun daina samun wannan farin ciki har abada!


A yau da Yusrah ke zaune ita da aunty Intisar suna kallon ƙunshi a catalogue ɗin da aka basu ta zo ta zauna nesa da su kaɗan ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kallon su ranta na ƙuna, a irgenta auren Yusrah bai wuce kwana huɗu a ɗaura ba, shi ne aka haukata su da shirye shirye ba ji ba gani kamar za'a aurar da ƴar cikin Anna na matuƙar sake ɓata mata rai, anko kala kala, siyayya kamar ba da dukiya suke yi ba.

Sai da ta shiga Tiktok ta ga ƙwarai ya ɗora abinda ta saka shi bayan ta biya shi ta fitar da vidion, ta ƙara amon muryar vidion sama sama sosai a lokacin da AA ke maganar matarsa ce, ƙoramarsa, da lokacin da muryar Yusrah ke tashi tana rantsuwar bata san shi ba ke fitowa raɗau ya saka Yusrah ɗago da kanta a zabure ta kai dubanta inda Nabihat ke zaune ta zuba mata ido lokaci ɗaya ta kalli aunty Intisar idanuwanta a waje hankalinta tashe sosai ta sake juyowa a lokacin da Nabihat ta gama ganin reaction ɗin ta ta miƙe ta shiga takawa da nufin tafiya ta ce" Kai duniya ta lalace, aunty Intisar ji fa yan ƙunar baƙin wake a bakin hanya dan Allah."

Intisar ta amshi wayar hannun irin yannayin da Yusrah ta shiga, tana duba vidion Yusrah ta leƙa ita ma ta kalla, ai da cikinta ya murɗa ta miƙe da gudu ta haura sama, Intisar ma a tsorace ta zubawa vidion ido, tabbas in dai ka san Yusrah in ka ganta a haka ba zata ɓace maka ba, inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, AA nema ta yiwu yadda ya yiwa gashinsa da kuma irin shigarsa ba zaka iya haɗawa da shi ba tunda har fatar jikinsa sai da ya shafa mata abinda ya ɓatar da haskenta sai dai duk da haka su da suke nasa na jikinsa ba zasu iya rasa kamaninsa ba.

Jiki a mace ta ce" Nabihat ina kika samu vidion nan?"

Nabihat ta yi irin bata san abinda vidion ke magana ba ta dan ɗage kafaɗu ta ce"A Tiktok ne fa, ta yiwu jiya aka yi." Sai ta amshi wayarta ta shiga haurawa dan nufar ɗakin ta ranta fes tana tunanin lalle hakane ita ɗin ce, ai kuwa a yau ba sai gobe ba zata kai vidion nan da hotunan inda ya kamata.

Aunty Intisar ta je ɗaki ta samu Yusrah zaune bakin gadon ta tana kuka, zama ta yi daf da ita tana faɗin" Ke lafiyarki ƙalau kuwa? Kukan meye zaki zauna kina yi a nan kuma?"

Yusrah ta ɗago tana kallon aunty Intisar ta ɗora kanta saman ƙafarta ta fashe da wani kukan tace" Aunty an ɗauki vidion mu? An ɗauki vidion mu? Inna lillahi wa inna ilaihi raju'un, a Tiktok? na shiga uku aunty?"

Aunty Intisar ta ce" Ke ki yiwa mutane shiru kar ki ɗorawa kanki wani ciwo, sai me? Ai Allah ya sa hatta su Aba sun san da zancan nan dan dai basu san da waye aka yi ba."

Hankali tashe Yusrah ta girgiza kai tana faɗin" Aunty lamarin waya ne fa, wanda ma baya da ita zai iya ganin vidion nan, na shiga uku ni k..."

Tafiyar da suka ji ana haurowa sama ya sa aunty Intisar saurin rufe mata baki tace" Shiiiiiii! Wani yana tahowa, Yusrah kowa na gidan nan ya san maganar haɗuwar ki da wani mutum da ya yi silar shigar ki pg, amma babu wanda ya san Akhi ne, ni da ke ne kawai muka san haka, mu bar maganar iya ni da ke ɗin kawai, kin gane? Maza share hawayen ki kar wani ya fahimci abinda ke faruwa, kin fahimta?"

Jinjina kai ta yi tana share hawaye amma ba dan hankalin ta ya kwanta ba, su Nawal ne suka shigo tare sa Abrar niƙi-niƙi da kayan ɗinkin su da suka karɓo, nan suka shiga duba kayan da aka ma ɗinki mai tsadar mamaki iri ɗaya kowace na ƙoƙarin gwada nata, hakan ya ɗan saka Yusrah ta saki amma fa zuciyar ta a cunkushe take da wannan lamari.

*Nabihat* na shiga ɗakin ta ta ɗan ƙara shiryawa sannan ta fito da makullin mota da ta zo da ita daga gidan su ta fita ko Anna ba ta sanar ma ba, a nutse take tuƙi har zuwa gidan su aunty Intisar, tana zuwa ta ɗauko facemask ɗin ta rufe fuskar ta da shi da wani ƙaton gilashi, oda ta yi da ta saka mai gadi leƙowa, yana ganin nan ne ya fito da sauri ita kuma ta sauke madubin motar, duk da bai gane wacece ba ya gaishe ta, da izza cike da yauƙi tace "Hajia tana ciki ne?"

Amsa mata ya yi da "E Hajia tana nan."

Yatsina baki tayi duk da shi bai ga hakan ba ta sake cewa "Ok, Yaya Mubarak fa da Bilal? Ko aunty Intisar?"

Duk girgiza mata kai ya yi yace "E gaskiya su kam basa nan, amma dai Hajia tana can gidan su wajen shagulgulan biki."

Numfashi ta sauke ta kalli gaban ta na daƙiƙu, sai kuma ta ɗauko babban envelope ɗin da ta zo da ita da waya a ciki wacce ba komai cikin ta sai hotunan Yusrah guda uku da kuma vidion nan, miƙa masa ta yi tace" Yawwa karɓi nan, ka kaiwa Hajia ka ce ta yi ƙoƙari ta duba, saƙo ne mai mahimmanci."

Karɓa ya yi yana amsa mata da" To Hajia, yanzu kuwa."

Har zai shige ta kira shi ta mishi kyautar kuɗi ya karɓa yana godiya da addu'ar Allah ya tsare sannan ya shiga gidan ita kuma ta tafi, ba tare da damuwar komai ba ya sallama falon Hajia ya same ta da little Yusrah a goye tana ta zagaye ɗakin sai Zahra'u dake ɗakin Hajiar tana share mata, dan aunty Intisar ɗin dake yi mata kusan kullum yanzu sabgar gidan su ce a gaban ta, saida ta yi ta wannan mitar a gaban Zahra'u ita dai bata kula ta ba, dan har ga Allah ita ba zata dinga baro nata gidan ba dan ta zo ta mata sharar ɗaki ba alhalin akwai masu aikin da suke mata, to tunda ya raba ƙofar su da ta su Hajiar shigowa ma gidan ke mata aiki.

Saƙon ya bata yana bata amsar tambayar bai san ko wacece ba, amma dai ta tambayi Hajia uwar su Uka da Alhaji babba da ƙaramin mai gida, taɓe baki ta yi cikin sigar tsufa ta ƙwala kiran Zahra'u, amsawa ta yi da ladabi ta fito riƙe da tsintsiya duk ta haɗa zufa saboda ko banza Hajia dama sai dai ka buɗe window ka sha iska ko ka yi firfita, bare kuma ana shara ko lamba ɗaya ka kunna na fanka za ta fara faɗa da gorin dan ba ƴaƴan ka bane masu biyan kuɗin wutar.

Tana zuwa ta bata envelope ɗin tace "Buɗe min wannan takardar banza in ga me ye a ciki? Wai wata ta ce a kawo min."

Buɗewa Zahra'u ta yi sannan ta fiddo wayar ciki ta miƙo mata ta ce "Waya ce Hajia."

Karɓa ta yi tana jujjuya wayar ta ja tsaki tace "Aikin banza kai, wacce ta kawota yanzu ta ɗauko har yanzu ƙarama ce da ni? Ai tunda su Ule zasu tafi ƙasar waje aka ban wacce ta fi wannan, yanzu haka ba birgeni take yi ba siyar da ita zan yi na ba Bilalu kuɗin ko buhun shinkafa ya siya a ci, mtsssss! Na ɗauka wani abun arziƙi ne tunda an ga sabga ce da ni."

Buɗa envelope ɗin Zahra'u ta yi da niyyar maida wayar, sai kuma wata ƙaramar takarda ta faɗo daga ciki, ɗauka ta yi tana warwarewa ta ga gajeran rubutu ne kamar haka _" Ku fara kallon abin da ke cikin wayar, sannan kusan wa ɗan ku zai aura."_

Da mamaki ta dubi wayar dake hannun ta, sai kawai ta danna wayar ta shafa sai taga ba tsaro ba komai a wayar, tana shiga galerie ba komai sai hotunan Yusrah guda uku da Zahra'u na gani ta gane wacece, matsawa ta yi daf da Hajia ta miƙa mata wayar tace" Hajia ina ga fa ba wayar bace aka baki, kamar wani abu ake son nuna miki."

Karɓa ta yi tana dubawa ta kalli Zahra'u tace" Wannan ba yarinyar nan bace ta Bilalu?"

" Ita ce Hajia." Ta bata amsa tana nuna mata hotunan da ita bata ga komai ba saida aka je kan vidion, suna dannawa ya buɗe suka shiga wara idanuwa dan su gane abun da kyau, ga muryar Yusrah na ihun bata san shi ba da rantse rantse an tisa ƙeyar ta zuwa mota, ga kuma wani dake ta ikrarin wallahi matar sa ce, har da faɗan kar ta ɗaga buje gaban kwarata mana, wani irin salallami Hajia ta shiga rabkawa ta kalli Zahra'u da dana sanin nuna ma Hajia vidion ya fara kamata, dan wallahi da ta san abinda kenan a gaba da bata nuna mata ba tace "Nan ma ba ita bace? Kenan yarinyar nan mai laifi ce?"

Shiru Zahra'u ta yi dan ba za ta iya karanta mata irin rubutun nan da ake rubutawa akan vidio ba saman tiktok, ai da sauri Hajia ta shiga kwance goyon little Yusrah tana faɗin "Bani wayata gata can, maza maza bani wayata in kira wanda ya yi silar kawo mana ita gida, a gidan nan? Mugun iri? Ashe yarinyar nan an sha gwagwarmayar rayuwa? Jami'ai haka kamar a shirin film su tasa ƙeyar ta gaba, har da ma aure gare ta kenan? To bazawara ce ko mai takaba? Dan nasan wannan laifin da sukayi ba ƙarami bane."

Zahra'u ta sa ta kira mata lambar Yaya Mubarak, sannan ta faɗa masa ya kira Bilal su same ta gida yanzu yanzu, duk da ya so idan Intisar ta kammala da gida ne ya biya ya ɗauko ta sai su shigo tare, amma haka ya gaggauta zuwa kiran Hajian, Bilal ma dake can tare da abokan shi suna yawon neman gurin da zasu kama dan gudanar da gagarumar walimar da zasuyi ta ci da sha bayan ɗaurin aure, tunda aka ce Hajia na kiran sa yanzu gida gaban shi ya faɗi ya ji ya kama samun nutsuwa, haka dai ya taho tare da aminin shi da tunanin idan suka gama da Hajiar su je wani guri da aka faɗa musu can


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login