Showing 333001 words to 336000 words out of 397328 words

Chapter 112 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70099

Ba wata matsala Elhaj, Allah ya kaimu lokacin da alkairi, idan na shiga ciki yanzu zan sanar da su dan su fara shirin abinda za su yi, Allah ya tabbatar mana da alkairi."

Da" Ameen." Aba ya amsa tare da ɗorawa da" Sannan, ka faɗa musu da kuma kai ma bama buƙatar komai daga gare ku, Nabihat ƴata ce kamar su Nawal, dan haka ni zan mata komai da uba yake wa ƴa a lokacin auren ta, tunda kun hanani wannan damar lokacin bikin Fauziyya."

Murmushi Chef ya yi yana sadda kanshi ya kasa amsawa da komai, hakan ya sa Aba tsare shi da idanu a tausashe yace" Dan Allah Chef ka yafew yarinyar ka, rayuwar nan da bata da tabbas, shin ya kenan idan yau ka faɗi ka rasu ko kuma ita ta bar duniyar? Ta yi kamun ƙafa da duk wanda ta san zai faɗa maka ka ji amma ba ta yi nasara ba, ni kaina har na gaji da baka haƙurin akan lamarin ta, ya kamata ka sassauta zuwa yanzu duba da shekarun da aka ɗauka, Fauziyya har ta zama magidanciya da ƴaƴan ta da komai, sannan ta yi sa'ar samun miji na gari da ya riƙeta da amana, me ya sa ba zaku godewa Allah bisa wannan ni'imar ba?"

Ajiyar zuciya Chef ya sake saukewa kafin ya kalli Aba yace" Shikenan Elhaj, in sha Allah zan duba na gani, sannan muna godiya sosai da wannan karamcin da ka mana, Allah ya saka da alkairi, Allah bar zaman tare."

"Ameen ya Allah." Aba ya faɗa yana miƙo masa hannu suka sake yin musabiha kafin ya shige mota da Sk ya buɗe masa ƙofa suka bar ƙofar gidan shima Chef ya koma ciki yana nazari akan maganar ta Fauziyya.

Yana shigowa Nabihat na zaune kan doguwar kujera ta miƙe ƙafafun ta da wayar ta tana dannawa sai faman murmushi take yi, magana take da Imran ta WhatsApp da sanyin safiyar nan, a tiktok ya yi targin ɗin ta har suka fara magana ɗazu ɗazu, ta rasa me ya sa yake da daɗin zancen da har ya iya riƙe ta haka take ma kula shi, wata irin kulawa ce da kalamai yake mata da suka saka ta jin ina ma dai shine wanda za ta aura? Ai da ta more rayuwa, amma dai duk da haka ta tsaya tana biye masa ne dan ta rage lokaci, tunda ba wani tsayayye gare ta da za ta kula a wayar ba bayan tarkacen ƙawayen ta.

Maman ta na gefe tana kallon tv, haka ma ƙannan Nabihat din duk kallo suke yi, daga nan tsaye ya ƙare musu kallo dukan su sannan ya tsayar da duban kan maman su, ba alamar wata wasa dan ma kar ta ga damar shi yace "Yawwa sai ku fara shirin ku irin na mata da kuka saba, an tsayar da ranar ɗaurin auren yarinyar nan, in sha Allah nan da sati uku mai zuwa za'a ɗaura, kuma abun farin ciki Elhaj ya ɗauke mana komai da yake kanmu ni da ke, amma duk da haka ki min lissafin duk wani abu da kika san zaku buƙata sai ki kawo min ɗakina daga yanzu zuwa da safe."

Irin fa ya gama magana kenan ya kama hanya zai tafiyar shi, daga Nabihat har maman ta da kallo suka bishi musamman ma Maman da ta saki baki, saida ya ɓace ma ganin su Nabihat ta daka tsalle tana juyi da karkaɗa kugu uwa na tsaka tana faɗin ita ma lokacin ta ya yi, a tsawace Maman nata da jin haushin abinda Nabihat ɗin ke yi tace "Ke dallah rufe min bakin ki, shashashar banza kawai, kenan har wani daɗi kike ji kina ganin an miki gata ne?"

Sai kuma ta yi ƙwafa tare da miƙewa ta nufi ɗakin ta, tana zuwa ta kira wayar Yayar ta dake saudia, tsaf ta sanar da ita komai da ya faɗa mata ɗin yanzu, amma sai ta nusar da ita da mata tuni akan ai abinda suke so kenan, uwa uba ma Elhaj Aliyu Anza ya ɗauki nauyin kayan ɗakin Nabihat, ai kuwa darjewa zasuyi su zaɓa son ran su fiye da wanda suka ma ita waccen ƴar riƙon tasu, da wannan ne kaɗai ta ji sanyi a ranta tare da yin zaune ta fara lissafa abinda za ta ɓamɓaro daga hannun shi shima ko da ba za ta yi komai da su ba.


*GOGGO HINDA*


Ihun da Safiyar ta saki tare da kwasar salallami da ƙanen Safiya shima ya ɗauka yana ihu ya sa Goggo Hinda fitowa a guje guje da kuma sauri sauri saboda yanayin jikin ta, ganin tukunyar ruwan zafin kunun ta a ƙasa tafasashin ruwan sun watsa a ƙasa ga kuma Mika'il zaune yana ta ihu da yarfe hannaye ya sa ta zaburo tana nufo su da faɗin "Lafiya? Me kuka ja min haka asararraru? Ɓarik ruwan kuka min dan kutumar uban ku? Sabod..."

Cikin kuka da hargag Safiya ta nuna mata Mika'il tace "Haba Mama, dubi ƙafar shi fa ta sale dan ƙonewa, ko ta jikin sa ma ba kya yi za ki hau zagin mu? Dama ba saida muka gaya miki ba zamu iya sauke ta ni da shi ba, kika ce dai sai mun zo mun sauke."

Kallon ƙafar ta Mika'il ta yi, ƙwarai ƙafar har ta nuna salewar sosai, amma ina ba wannan ne a gaban ta ba, dan haka ta shiga faɗin" Kai ku ar ƴar iska tsinannu, abu komai ƙanƙantar sa ba zaku iya iyawa mutum daidai ba? Na shiga uku ni Hinda, wannan masifa d me ta yi kama jama'a? Tunda malam ya kama gaban shi abubuwa ke lalace min, ita ma wannan shegiyar matar tasa ta zo ta bi bayan shi, da tana nan da kun ja min wannan asarar? Da ke baku san ciwon kan ku ba kuk kasa gane da wannan sana'ar nake ciyar da ku ko?"

Safiya da ta ga dai abun nata gaya nan sai ta zabura ta yi ɗaki ta buɗa jug ɗin da aka siyowa Goggo ƙanƙara ɗazu, da gudu ta fito ta zauna kusa da Mika'il dake kukan wahala ta buɗe ƙanƙara ta shiga ɗora masa a ƙafar tana masa sannu, wannan bambamin Goggo ta ci gaba da yi Safiya kuma saida ta ga Mika'il ya rage kukan ta kamo shi suka koma ɗaki tana ta masa firfita a ƙafar da ta jima da ɗuran ruwa.

Zuwa yamma ƙafar Mika'il ta zama wata iri dan wutar nan ta cika sosai abun tausayi, dole ta sa Safiya kiran Khadija ta sanar mata, ita ce ta samar masa magani ta zo gidan ta kawo mishi, amma har lokacin Goggo ko kallon kirki ba ta ma yaron ba bare ta masa sannu, faɗan ta kawai an mata asara kuma ba ta yafe musu ba, ba wanda dai ya kulata duk faɗan nan da take yi har dare ya yi Mika'il ya samu bacci daga magungunan da Khadija ta bashi kafin ta musu sallama ta tafi gidan ta ita ma cike da tausayin halin da mahaifiyar tasu take ciki, dan a fili yake ƙwaƙwalwar Goggon kamar ta fara taɓuwa tunda mahaifin su ya rabu da ita ya kuma bar mata gidan ta.

Safiya na cin abinci Goggon ta kalle ta da tausasawa tace "Safiya, kin san wani abu?"

A tsanake ta kalli Goggon jin wani sanyi da ta yi lokaci ɗaya kuma, amma sai ta bata hankalin ta tana sauraron ta tace "Me zai hana gobe ki shirya da wuri ki je gidan su yaron nan Bilal? Kinga fa na ma Hajiar sa alƙawarin za ki je, na san kuma tana ta tsumayin ganin ki, kinga idan kika je aka yi sa'a kika siye zuciyar ta da ladubba, tsaf zaki ga ta nemi auren ki a gaggauce a yi komai a gama."

Turo baki Safiya ta yi tace" Gaskiya ni Mama kinga ban san gidan ba, kuma ni bana so naje a min kallon raini wallahi, me zai hana ki bari idan tana so na da auren shi ai sai ta zo nan ta nema ko?"

Da ɗan ɗaga murya tace" Ke rufe min baki, shashashar banza kawai, ana ga yaƙi kina ga ƙura, tunda mu ke so ba dole mu zamu je ba, kawai kiyi abinda na gaya miki, yanzu gama cin abinci ki ɗauko min jakar nan tawa da nake ajiyar magunguna na, akwai na farin jini da na bakali a ciki ke har da ma kwalli, duk zakiyi anfani da su kafin ki je, in sha Allah wannan yaron sai ya zama naki."

Ita dai ba dan haka ya kwanta mata a rai ba tayi ta turo baki tana tura abincin da duk ta ji ya fice mata a rai ma, tana gamawar ta ɗauko jakar ta kawo mata sannan ta shige uwar ɗaki ta zauna tana sauraron dandali a wayar ta ta bar Goggo a falon tana ta neman magungunan ta.




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
30/06/2024, 23:13 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*84*



Can kusan ƙarfe goma sha ɗaya da rabi sai ga baƙuwar mamaki, baƙuwar da ta jima bata tako ƙafafuwan ta gidan Anna ba, a yau kuwa sai gata kamar an jefo gidan Anna, fuskarta ɗauke da fara'ar saƙon da mijinta ya faɗa mata na maganar saka auren Nabihat, gaba ɗaya idan ka ganta zaka ga farin ciki a tare da ita, shi yasa bata tsaya ɓatawa kan ta lokaci ba ta fito da kan ta dan ta je ta ba idanuwanta kalaci ta kuma san abinda ke jiranta, domin ta san cewa yau ne tarewar Yusrah, duk tsiya kuwa ta zo da shirin zuwa ta ga komai dan idan ta tashi yiwa tata ƴar ko kan ta zata siyar sai ta siyar ta yi mata wanda ya fi na Yusrah kyau, bare ma da uban kuɗin ya ce zai yi.

Da fara'a da sakin fuska sosai Anna ta tarbeta, sannan ta sa aka kawo mata dukkan abun buƙata kafin ta ƙara ɗaga wayar ta ta yi waya da Abrar dake zana mata abinda suke da buƙatar a ƙara kaiwa ta ajiye wayar da fara'a a fuskarta ta ce " Hajajju manyan ƙasa, yaushe rabo?"

Hajia ta yi murmushi ta ce " Hajia ke da kika ƙi ni? Yau ai na zo da kaina ko dan murnar auren ƴaƴan mu da aka saka nan da sati uku."

Anna ta yi ɗan jim tana kallonta kafin ta yi murmushi tana kaɗe abin a ranta bayan ta ayyana _' Ikon Allah, har an yanke lokacin, kuma a zuwan sa yanzu shine har ta zo ta sanar min? Ni ai ban ma sani ba.'_

A fili kuwa sai ta ce" Au!Kai maman Nabihat ba ƴar jin kunyar nan? Ai kam nan da sati uku in sha Allah ta yiwu warhaka ana haramar ɗauko amarya, Allah ya nuna mana."

Maman Nabihat ta yi murmushi har haƙoranta na bayyana sosai ta amsa da" Ameen ameen."

Anna ta yi kiran mai aiki tana dubanta ta ce" Kin ga ashe ba'a ɗauki man girkin ba fa, sannan karas ɗin da aka siya kaɗan ne fa, a je a ƙaro a haɗe a kai musu can gidan amaryar."

Maman Nabihah ta yi caraf ta tare maganar da faɗin" Ai tafiyar tawa ta zuwa tarewar ƴar tawa ce, ina ce can za'a je? Ta ɗauko kayan mu je."

Anna ta ce" Eh can za'a je, amma da kin yi zamanki a nan ɗin ai mu yi namu a nan maman Nabihat." Anna ta ƙarashe dan bata ga dalilin da zai sa matar da ba ta zo auren ba, bata zo ta yi Allah sanya albarka ba, ba zuwa ba zowa kai tsaye ta ce wai zata je yanzu, kuma bayan wannan Fauziya na can, ita kuwa ta san ya ya suke da Fauziyar kar aje ta je ta ɗagawa yarinyar hankali.

Maman Nabihat tuni ta miƙe tana murmushi ta ce" Haba dai, to wani babba ke can bayan abu ya riga ya zama ɗaya? Bar ni in je can ɗin kawai, dama kuma kin ga muna maganar a je a ga gidan da za'a yiwa Nabihat jere dan a yi a saka odern gadajenta, sai kawai in yi tafiya ɗaya in faɗawa uban."

Anna ta sauke ajiyar zuciya ta miƙe ɗin ita ma tana faɗin" Ayya, ma sha Allah, kin ga kuwa ai ba gida ɗaya za'a saka su ba fa, bari in ɗauko sauran saƙon, sannu da ƙoƙari Hajia Allah ya saka da alkairi." Daga nan ta haye ta bar Hajia cike da tunanin ba gida ɗaya ba? Me kenan?

Har Anna ta sauko da saƙon ta bata suka wuce da masu aiki tana tunani har suka ƙarasa gidan bisa kwatancen mai aiki suka je shiga aka ringa musu tambayoyi suka samu shiga sai faɗa take tana faɗin ita uwar matar ogan nasu ce, su sun zata ma ko Hajiar tasu sabuwa ake nufi har suka samu suka shige ta tsayar da motar tana ta zagin masu aikin da masifa kala kala, balle da ta ga yanayin gidan sai hankalinta ya ƙara tashi, uban wa ba nan za'a kawo Nabihat ba? Inda ya fi nan za'a kai ta kenan? Ai wallahi ba'a isa ba, in an isa a kai Nabihat inda bai fi nan ba lalle ita ba ƴar halak bace!

Da wannan ɓacin ran da hura hanci ta ƙarasa falon, sai dai tana shiga wacce ta gani tsaye tana ba da umarnin yadda za'a shinfiɗa sababbin cafet ɗin gidan ya saka ta tsayawa da ƙarfi tana zaro ido, Fauziyar kanta sai da cikinta ya juya, a rikice ta zubawa mahaifiyarta ido gaban ta na faɗuwa.

Ƙafafuwan ta na rawa ta nufo ta dan ta gaishe ta, sai dai bata bata dama ba ta ja tsaki har da tofar da yawu a nan falon ta juya ta bar gidan gaba ɗaya, jiki a mace Fauziya ta kama hannun Manal da ta zo inda take bayan mai aiki ta shiga gyara wajen da Maman Fauziya ta tofar da yawun.

A hankali ta riƙe hannunta a tausashe ta ce" Aunty Fauziya, ki yi haƙuri kin ji? In sha Allah, Allah zai sanyaya maki damuwar nan kin ji?"

Aunty Fauziya ta sauke ajiyar zuciya ta share hawayen da ya zubo mata a hankali ta furta" In sha Allah ƙanwata, innalaha ma'assabirin."

Daga nan suka ci gaba da ayyukansu, a hankali har ta saku ita ma bayan ta ƙudurcewa ranta tana zuwa gida yau ma zata yi ta jaraba kiran numbobinsu, zata yi ta kira ta gani ko Allah zai sa a dace su ɗaga kiranta, a kullum idan ta kai goshinta ƙasa ta yi sallah tana yiwa Allah kuka a kan iyayenta, in azumi ta yi hakane, wani lokacin ta kan ji kamar ta kashe aurenta ta koma gabansu, sai dai a duk lokacin da irin haka ya taso mata tausayin mijinta sai ya lulluɓeta, babu abinda ya rageta da shi, kullum yana tare da ita in kuka take yi yana rarrashinta, tana fatan Allah ya sanyaya damuwarta, a dole ta sake saboda yaran babu wanda ya barta ta afka tunani, harta Fatila dake baƙuwarta sai ta ringa ƙoƙarin sakata fara'a, dan haka sai ta ware kawai ta bi su suke kai kawo.



*AA ANZA*



Kusan ƙarfe huɗu AA ya je gidansu ya ga Aba a lokacin Aba ya dawo yana hutawa dan yana shigowa daga sallar la'asar ya zo ya ɗan kishingiɗa yana hutawa, sun gaisa sosai ya kuma gamsu da sauƙin da Aba ya ce ya samu, dan haka ya ce masa zai je ya dawo.

Yana fita ya nufi asibiti bai nemi Anna ba dan yau ba dama tana can tana fama da jama'arta, yana tafiya Aba ma ya ji sha'awar tafiya ya gano uncle Hamat dan rabonsa da shi tun jiya, dan haka sai ya shirya kawai ya ficewarsa da motarsa shi ma ba tare da ya jira ya sanar da Anna ba dan ya san zata ce kuma wata fitar bayan bashi da lafiya? Shi kuwa bai cewa kowa bashi da lafiya ba sun sako shi a gaba da faman bashi da lafiya bashi da lafiya, gwara ma ya je ya gano Hamat ya ga in ya farka dan ya masa bayani a kan abinda abokin aikinsa ya faɗa a kansa.

Ya zamo ne AA na sauka daga motarsa da ƴan mintuna Aba ya kai tasa ya ajiye, da mamaki ya kalli motar dan wajen ajiyar motocin masu wajen ne kawai, dan haka ya gane AA nan ya nufo ashe, bai sani ba ai da basu fito daban daban ba, a nutse ya fita ya nufi ɓangaren ɗakin da Hamat yake yana amsa gaisuwar da ake ta yi masa a nutse, yana zuwa ya ga wata likita ta fito ta bar ƙofar a buɗe, bata kai ga rufewa ba ya ɗan tare zai shiga kunnayensa suka jiyo masa magana kamar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login