Showing 342001 words to 345000 words out of 397328 words
zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*86*
Washe gari tunda safe Goggo Hinda ta saka Safiya a gaba har ta gama shiryawa ta sa ta yi anfani da kwalin nan na farin jini sannan ta laluba ta bata kuɗin adaidaitar tafiya tana sake jaddada mata cewar idan ta je ta tabbatar da ta yi biyayya ta kuma tunawa Hajia maganar ko da ita bata yi mata maganar ba, sannan kar ta damu da kuɗin adaidaitar dawowa ta tabbata in dai ta ga Bilal shine zai kawota da kansa da kyauta mai kyau.
Da wannan ta fita ta ɗauki ɗan sahu ta nufi gidan Hajia, a lokacin da ta je gidan Hajiar ta samu Hajiar da kanta ta fitar da rigunanta na shan iska zata wanke.
Bayan sun gaisa sosai ta kwaɓe hijabinta ta amshi wankin Hajia ta shiga yi ba ji ba gani Hajiar kuwa na shi mata albarka, bayan ta gama ne ita ce harda su gyaran ɗakin Hajia, gyaran kicin, gyaran falo aiki dai kamar zata kifa yi take ba ji ba gani Hajia kuwa tana gefe a zaune tana binta da kallo har Bilal ya shigo cikin shiri domin jirgin yau zai bi zuwa america wajen su yaya Mubarak.
Yana shigowa ta tsuguna har ƙasa tana gaishe shi da wani irin kisisina, ko kallonta bai yi ba ya amsa ya duƙa yana yiwa Hajia sallama, ta miƙe ta raka shi tana yi masa addu'a sosai da fatan nasara sannan ta sake dubansa da kyau ta ce" Auta ka cire damuwar nan a ranka ka ji? Kamar yadda kace baka so na haɗaka da kowa ba zan haɗaka ba, kuma ko wacce ka kawo in sha Allah ba za'a maimaita abinda ya faru ba ka ji? Allah ya maka albarka."
Da ameen ya amsa sannan ya tafi yana jin kewar mahaifiyarsa a ransa, kuma ya gama ɗaukan mata mai aiki gobe zata fara zuwa kawai bai sanar mata bane, haka kuma ita ma Hajiar bata ɗora masa diyar komai ba har ya tafi.
Hajia na dawowa ta samu Safiya na jiranta, bayan ta zauna safiya ta ce" Hajia yaya Bilal ina zai je?"
Hajia ta ɗan kalleta tana haɗe fuska ta ce" Tafiya zai yi, ina jin dai lafiya?"
Safiya ta kalli Hajia da mamaki ta ce" Kai, Hajia Goggo fa ta aikoni kan maganar da kuka yi ai."
Hajia ta dubeta sama da ƙasa ta ce" Allah ya kyauta, dama abinda ya kawo ki kenan? To ki faɗa mata gaskiya ba wannan maganar dan ya ce baya so, kuma ba zan masa dole ba."
Wani takaici ya tuƙo Safiya tana kallon Hajia ta rasa me ma za ta a ce mata, yanzu tunda safe ta zo take aikin wahala har rana ta raba kuma ta ce mata haka? Tsaki ta ja ta juya ta shuri hijabinta ta ce" Dama aikoni aka yi, na yi nan aikin banza kin tsufa sai masifa, ke da ni aka auro maki tsaf zan baki shinkafar ɓera a rage mugun iri dan babu tsohuwar najadun da zata saka min ido a gidana na aure ba wallahi, aikin banza."
Hajia har sai da ta yi kuka na maganganun Safiya tana faɗin" Ki je a gayasss, a haka zan aura maki Autan? Allah na gode maka da ban yarda an bani akuya a lulluɓe ba."
Adaidaita ta ɗauka ya mayar da ita gida ta shiga dan ta anso masa kuɗin sa, da ta shiga ta samu Goggo zaune jikin itace ta ce" Goggo kawo ɗari a ba mai mashin?"
Goggo ta miƙe da sauri tana faɗin" Mai mashin kuma? Ina Bilal ɗin?"
Safiya ta wuce ciki tana tsaki ta ciro kuɗin a ƙasan katifa ta fita ta ba mai napep ta shigo tana faɗin" Ni na sani ma ɗan ƙaniya? Kin ga wulaƙancin da uwarsa ta min? To ni babu inda zan koma dan ma ki ji, ba manema na rasa ba ai."
Goggo zata fara zage zage aka sanar da ita ana sallama a ƙofa, a dole ta zari gyale tana faɗin" Bari in zo in ci ubanki a gidan nan tunda baki da mutunci yarinyar nan, wato duk abinda na faɗa maki a banza ko? Bari in dawo."
Goggo ta fita sai bala'i take yi, sai dai tana fita sai da ta ji ta kalli baya dan mutumin da ta gani a tsaye jikin motarsa ya yi ruzaza ya turo hula gaban goshinsa, a birkice ta juyo idanuwanta na marmarmar na tashin hankali ta ƙaraso inda yake tana faɗin" Elhaji kaine da tsakiyar ranar nan? Sannu da zuwa Elhaji..."
"Ke zan yiwa sannu, nace Hinda sannunki, tsakiyar rana kuwa ai ke ke jinta, ina tunanin ko tsakiyar dare na zo nan babu wanda zai ce min dan me, yawwa, yaya maganar cikon kuɗin gidan nan da na bari ki cika shekara huɗu cif? Dan kin ga bana nan shine baki bada kuɗi ba? Dan kin ga na bar magana a hannun matata? Ai gani na dawo sati ɗaya na baki ki haɗa min kan kuɗina ko in kawo maki wanda kika bada ki bar min gidana!"
Duƙawa Goggo ke son yi tana haɗe hannayenta ta ce" Inna lillahi wa inna ilaihi raju'un, Elhaji bari ka ji, ka tsaya ka ji, wallahi damuwa na shiga shi yasa ban cika kuɗin ba, ka ƙara min lokaci ƙalilan in sha Allah zan haɗo kan kuɗin in kawo maka Elhaji kar ka fitar dani daga gidan nan ka tona min asiri, a yanzu yanzu bani da kuɗin haɗawa har million uku ama a hankali zan haɗa idan ka bani dama elhaji dan Allah ka rufa min asiri."
Elhaji ya taɓe baki ya shige motarsa ya ce" Ke kika gani shekara huɗu fa ba kwana huɗu ba, in na yarda Allah tsinen, ke ki haɗa min kuɗina tas ko ki bar min gidana wallahi, baki san waye ni ba, zan dawo nan da sati aikin banza aikin wofi."
Goggo na magiya ya ja motar ya yi tafiyarsa, da ƙyar ta iya saka kanta gida ta zube tana fashewa da kuka mai haɗe da ihu tana faɗin" inna lillahi, na shiga uku na lalace, wayo na shiga uku asirina zai tonu a min dariya, na haɗe jari kaf na ja jari kuɗi sun ɓace ɓatt, gashi bala'i ya kunno ashe Elhaji da ransa ya dawo neman dukiyarsa? Wayyo ina zan ga million uku ni Hinda? wayyo na shiga uku."
Yaranta gaba ɗaya suka zagaye ta suna kallo, babu wanda ya ce da ita ufan dan basu san me zasu yi mata ba, gaba ɗaya sai kuka take yi har maƙota na shigowa, faɗi take yi yanzu babu kasuwar ma bale ta ce ko sun fita tana da sana'a, in ma da sana'ar ta saida a ina? Ina malam yake? Duk rashin malam ne, tashin hankali dai da ba'a saka masa rana shi ta faɗa a wannan rana wanda ya dame sauran.
*AA ANZA @ Y.TURAKI*
Ganin yadda tun da asuba yake ta kiran Anna yana tambayar jikin Aba sai hankalin ta ya tashi saboda tunanin ko dai jikin ƙwarai ne? Shiyasa ma har ta shiga kicin dan ɗora abun kari sai kuma ta fito, kai tsaye ɗakin shi ta ƙwanƙwasa, jim kaɗan ya zo ya buɗe ƙofa, yana haɗ idanu da ita ya waina idanun shi yace "Da ma ke ce Y. Turaki? To me ya sa za ki tsaya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin mijin ki? Baki san yanzu ni da ke mun zama ɗaya bane?"
Sadda kanta ta yi ƙasa tana wasa da hannayen ta, kamo hannun ta ɗaya ya yi ya shigo da ita cikin ɗakin yana kama ƙugun ta cikin raɗa yace" Ko kin manta jiya a gauraye muka kwana? Da waɗannan..."
Ya dafa mazaunan ta, sannan ya dawo da hannun shi kan ƙirjin ta ya cika hannun nashi da nonon ta ɗaya yana faɗin" Da kuma waɗannan..."
Ture hannun shi ta yi tana faɗin" Abbbannnn Safwannn..."
Haɗa goshin shi ya yi da nata yace" Na'am, matar jikan Anza."
Sai kuma ta yi takwaf takwaf kamar za ta fashe da kuka tace" Dan Allah nace ko zamu tafi tare in ga jikin Aba? Wallahi duk na damu da son sanin halin da Aba yake ciki, please *chairman*."
Tsare fuskar ta da idanu ya yi sai kuma ya taɓe baki yace" Y. Turaki ni za ki cuta? Wa ya koya miki wannan lalatar idan kina son cin zalina?"
Ƙara shagwaɓe fuska ta yi tana bubbuga ƙafafu tace" Dan Allah fa nace."
Juya mata baya ya yi yana ƙoƙarin gyara ɗamarar wandon shi yace" Y. Turaki zan zure arzuzumina, in yi gaban ki ne?"
Wani kallo ta masa irin ta ji haushi ɗin nan kuma ta ƙi tanka masa, hakan ya sa ya sake taɓe baki yace" Shikenan, amma ki kwana da sanin kina gane min sirrikana wallahi ke ma sai naga naki, idan ya so a tashi ɗaya da ɗaya, haka kurum na shekara talatin da kusan takwas a duniya ko ɗan Anza ban yarda ya kalle min kaya ba sai ke?"
Cikin sako da hawaye tace" Ba za ka tafi da ni ba?"
Juyowa ya yi da kyau ya kalle ta zai yi magana, ganin tana hawaye sai kawai ya ji duk ba daɗi dai haka, sai ya kasa ce mata a'a kawai yace" Shikenan, je ki shirya."
Da farin ciki ta juya tana sakin murmushi tace" Na gode."
Ta buɗe ƙofa za ta fita yace" A dai ji tsoron Allah a yi shiga irin ta mata salihai Y. Turaki, ko a fasa tafiyar."
Jinjina kai kawai ta yi ta fice cike da murna, da gaggawa ta shiryo cikin riga da siket na atamfa da hijab ɗin da ya dace da kayan da takalmi da ƙaramar post ta fito daidai da fitowar shi shima, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai saboda ya yarda shirin ya mata kyau kuma shigar ta birge shi, tare suka fita gwanin sha'awa suka kama hanyar gidan Aba, bayan tazarar da suka kwashe sun isa gidan.
Duk da mamaki ne a fuskar su, amma AA bai kasa sakin murmushin jin daɗi ba ganin Aba a farfajiya shi da Anna suna ɗan yawatawa irin tattakin nan, daga zaunen cikin mota ya zuba musu idanu yana kallo wani irin farin ciki na kama shi kamar zai suma, idan ya ga Anna ta yi kalar jin kunya tana sadda kai sai ya juya ya kalli Yusrah da ita ma ta zuba musu idanu tana jira ya fita sai ta fita, cike da jin daɗi yake kallon ta sai yace "Ji dan Allah? Abun gwanin sha'awa ko?"
Kunyar ita ma ta ji ta sunkuyar da kai tana ayyana _'Allah ya shirya.'_
Sai kawai ya ɗan leƙa fuskar ta yace "Ke ma dai kamar Anna a jin kunyar nan."
Buɗe motar ya yi suka fito suna tunkaro iyayen nasu fuskokin su da fara'a, sai dai saɓanin Aba da ya haɗe fuska tun basu ƙaraso ba yace "Jikan Anza, lafiya na gan ka da safe haka? Lafiya? Kai me yake damun ka? Me ka zo yi min a gida?"
Haɓa AA ya riƙe da mamakin tambayoyin na Aba, sai kuma ya kalli Anna yana mata alamun _"Ji tambayoyin da mijin ki yake min Anna?"_
Ɗauke kai Anna ta yi irin _" Tsakanin ku ne."_ Sannan ta rumgumo Yusrah da ta nufe ta a jikin ta tana mata ya gajiya ya gida? Aswan kuma yadda Aba ya tsare shi da idanu alamar amsa yake jira ya sa dole ya shafa kai a ladabce yace" Aba na fa zo duba jikin ka ne?"
" To ni wa na gaya ma ban da lafiya? Shine za ka wani yo min sammako haka, bayan kuma amarya gare ka a gida?" Aba duk ya yi maganar kamar a hassale.
Da ladabi Aswan yace" Ka yi haƙuri Aba, ita ma fa kuka ta dinga yi akan sai na taho da ita, ko karyawa ba ta yi ba."
Kallon Yusrah Aba ya yi da kunya tasa kanta ke ƙasa, ajiyar zuciya ya sauke yana duban Anna da tace" AA, tund..."
AA da Anna ta faɗa bata ƙara da babba ko ƙarami ba ya sa da Aba da AA ɗin kallon ta lokaci ɗaya, murguɗawa AA baki ta yi tace" Da mijina nake, dama ba sunan sa bane ka ara."
Jinjina kai AA ya yi tare da yin ƙasa ƙasa da murya yace" Kalar zaran kalar kayan, ashe daga bakin matar Haidar ta koyi wannan ɗabi'ar."
Kallon shi Aba ya yi ya masa raɗa yana riƙo hannun shi yace" Hala kaima tana kallon fuskar ka ta kira ka da AA?"
Kallon Aban ya yi ya gyaɗa kai yace" Tsaf kuwa Aba, yanzu ma kafin mu fito sai da ta faɗa."
Girgiza kai Aba ya yi yace" Allah ya shirya su."
Anna da ta tsare su da idanu ne tace" To, idan kun gama yi damu muje sai ku karya anan tunda kun riga kun zo."
Tana faɗa ta ja hannun Yusrah zuwa ciki su kuma suka rufa musu baya, suna tafe Aba ya riƙe hannun AA gam yake faɗin" Kar ka damu dan ta kira ka da haka, kai watarana ma fa ni idan na mata laifi sai in ga kamar bakin ta na kirana da ɗan Anza, to ya zan yi? Ka ga dai su ba dakuwa suke yi ba, sai haƙuri kawai da lamarin su."
AA dai a tausashe ya amsa da" Hakane Aba."
Sai kuma ya ɗan jawo hannun shi sukayi kusa sosai ya masa raɗa" Ban fa ji daɗin zuwan nan naku ba jikan Anza, kai da na so a ce kana can kana rarrashi a daidai wannan lokacin, jikan nan fa sai ka bani shi ɗan Haidar, ka ji ko?"
Kallon Aba ya yi ya sagale haɓa ya kasa cewa komai har suka shige, yau kam har karin kumallo Aba tare da su ya yi anan cikin nishaɗi da raha, Yusrah dai kanta a sunkuye ba ta cewa komai idan ba murmushi ba. Saida suka gama Anna ta kalle shi tace" To maza ka maida min yarinya gida ta huta."
Har ya miƙe Aba ya ma Anna alamar ta sanar da shi maganar saka ranar auren shi da Nabihat mana, dan haka ta miƙe ita ma ta ce ya same ta falon ta, bayan ta ya bi a nutse suka isa falon, ko zaune ba ta yi ba sai shi da ya rusuna yana sauraron Anna tana gaya masa an saka sati uku in sha Allah, dan haka sai ya fara wani shirin sannan ya sanar wa da matar sa yanzu, duk da ta san da maganar amma ya faɗa mata an saka rana.
Gaba ɗaya sai ya ji wani ba daɗi dai haka, irin abun kamar bai kwanta masa ba, amma sai ya dake ya kalli Anna yace "Amma Anna dole ni zan faɗa mata da kaina?"
Ƙasa da sama ta kalle shi tace "To wa zai faɗa mata idan ba kai ba?"
Marairaicewa ya yi yace "Anna ki kirata dai yanzu ki sanar da ita, ni kam t...gaskiya..."
Shirun da ya yi ya kasa ƙarasawa ya sa Anna zama kan kujera ta ce "To kira min ita?"
Da sauri ya fito cikin nutsuwa ya mata magana suka sake komawa falon na Anna, zama ta yi ƙasa kusa da ƙafafun Anna shi kuma yana saman kujera yana kallon su, saida Anna ta taushi zuciyar ta da ƴan nasihohi da faɗa mata abu ne da ta sani dama to ya zo, ta ƙara da bata buƙatar ta tayar da hankalin ta ko wani abun, sannan ta yi haƙuri haka Allah ya hukunta, daga ƙarshe ta saka mata albarka sosai da mata fatan farin ciki da zaman lafiya a gidan ta.
Tunda Anna ta fara magana idanun ta ke lumshe saboda hawayen da suka zubo kan hijabin ta bata so su ci gaba da zubowa, amma ita kanta bata san dalilin haka ba, kawai dai ta ji gaban ta ya yi mummunar faɗuwa sannan zuciyar ta na harbawa ba daidai ba, hatta kanta ma fa ji take yana sara mata gaskiyar magana kenan, amma dan kar Anna ta gane ko bata ji daɗi ba sai ta tausasa murya sosai har tana rawa rawa tace "Allah ya sa alkairi, Allah kaimu lokacin, ba damuwa Anna."
Da jin daɗi Anna ta sake shi mata albarka sannan ta ce su tashi su tafi, sannan ta umarce ta da kar ta sake fitowa ita fa yanzu amarya ce, ta bari har ta gama cin amarcin ta sai su duba lokacin da ya kamata ta koma aikin ta.
Miƙewa duk sukayi tana jin kamar ta fasa ihu suka fito, su Nawal ma kasa sakin jiki ta yi suyi sallama yadda ya dace haka ta je ta shiga mota, yana zuwa ya shiga shima suka kama hanyar gida.
Ba wanda yake ma wani magana a cikin su, gwara ma shi ya kan kalle ta sai ya taɓe baki ko ya yi ƙwafa, saida suka kusa isa gida ya kalle ta cikin yanayin faɗa faɗa yace "Saboda liƙa miki ni aka yi ba kya so, shiyasa ma ko irin kishin nan da ake cewa mata na nunawa akan maaajen su idan zasuyi aure baki nuna ba, kawai kikayi wani ƙasa da kai wai _Allah ya sa alkairi..._, na ji to na kuma gode."
Ya faɗa yana jan tsaki ya ci gaba da tuƙin shi, kallon shi Yusrah ta yi tana share hawayen ta tace" Me kake so na ce bayan haka? Ba wacce ka ke so za ka aura ba? To Allah ya bada sa'a."
A zafafe ya dube ta yace" Ameen, na ce ameen kuma na gode."
Dama mai saurin kuka bare an jefe shi da kashin awaki, sai kawai Yusrah ta fashe da kuka ta haɗa kanta da guiwa kuka sosai