Showing 78001 words to 81000 words out of 397328 words

Chapter 27 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70062

yi dan ya miƙar da shi ya fito da shi, sai ya miƙe tsaye da gaggawa ya zamo goshin polise ɗin ya daki ƙirjinsa, da sauri polise ɗin ya ja baya yana sake damƙe bindigarsa ya ce" Kai, wallahi ka nutsu nan gida sojawa muka kawo ka, in mu ka raina mu su tsaf zasu kashe ka kafin a kai ka shara'a su ce kai ka kashe kanka kuma babu abinda za'a yi."

"Namiji ya da haka kuma, gardama yake yi ne? Fito da shi mana ya ya zaka ringa cacar baki da mai laifi ne? Ni na sauka zan je gida in dawo gobe da dare Allah ya sa in samu wannan cikan, ga dukkan alamu yau gidan ire irin wa'mɗanda muke so ne." Daya daga cikin sojawan ya faɗa kansa tsaye.

Shi kuwa polise ɗin dama tunda ya ga sojan nan ya san in me mutumen nan ke taƙama da shi tabbas ga daidai da shi, domin babu waɗanda basu san *YARAN AA ANZA* ba.

Muryar da AA ya ji ya tabbata da ace a wajen da suke wajen haske ne tarrr tun a nan zai gane shi, subhanallah! A dole ya nutsu ya sake sinne kansa ya bada dama polise ɗin nan ya fito da shi ya sauko da shi sannan ya nufi ofishin da ake fara kai mutum a faɗi laifinsa kafin a san inda za'a ajiye shi.

Ana sauka da shi aka cicciɓata, kanta a ƙasa, domin tunda aka ɗagata aka wurgata bayan motar nan ta je kƙiiiiiii! Ta ƙuma bayan nata a jikin tayar nan dake ajiye a cikin motar ta fitar da wani marayan ihu sai ta yi laƙwas ta zuba idanuwanta a waje ɗaya ƙirjinta na ƙunar da bai taɓa yi ba, ranta a mugun ɓace yake fiye da kima, haka kuma tsoro ya gama mamaye mata ƙirji, ta gama sarewa rayuwa, subahanalla! Bata son tunanin cewa sun fa kaɗe kuma ya ɗarsu a ran ta, amma abin so yake ya zauna darr a ranta, ta kasa daina tunanin cewa an tafi da Aswan a bak'ar mota ita gata a motar polisai bayan babu abinda ta aikata, a dole ta ɗaga idanuwanta ta zuba a fuskar mutumen nan, wanda gaba ɗaya yanayinsa ya nuna ba yau ya fara shiga motar nan ba, ba yau ya fara aikata laifi ba, dan ƙiri ƙiri alamun sa suka nuna babu uban da yake tsoro a tafiyar nan, ta yiwu ya shigo motar nan ne kawai saboda bindigar da aka ɗora a kunkumin ƙeyarsa, wai itace matarsa? To kuwa wannan mutumen in sha Allah ko ita ko shi, gwarama ta aikata laifin mai dalili a san an kawota da dalili ba tsabar zalunci ba a kwasota a bayan motar nan dan kawai wannan yace wai matarsa ce ita, ita damuwarta wai me ya aikata da girma haka? domin ta ji ana batun shine, wallahi bindigar ce, Inna lillahi wa inna ilaihi raju'un! tabbas babu *tafiya* mai tashin hankali sai wacce bawa zai yi a duniya babu ran iyaye, Allah ka jiƙan iyayenmu, ka tsare mu a duk inda muke.

Da ƙafa aka buɗe aka turo ta ta shigo ofishin itama, sai dai tana shigowa ta ƙara sarewa duniya da tunanin to tabbas kuma ta yiwu lokacin ta ne ya yi ita ma, shi yasa Allah ya haɗata da wannan ɗan bala'in, domin a lokacin da ta shigo soja biyu ne suka saka irin abin dukan nan su biyun suka nemi kai shi gurfane amma ya saka hannayensa sumul ya suluɓe abubuwan dukan, hakan ya sa suka zaburo har babban nasu suka fito da bindiga ihu ya cika wajen suna faman faɗin" Harbeka zamu yi, kai tayar da kanka zamu yi idan baka bamu kulkin nan ba."

A rikice Yusrah ta ɗaga hannayenta ta duƙa kanta a ƙasa ta ware muryarta ta ce" la'ila ha ilalah Muhammadu Rasulullah, Sallallahu alaihi Wa sallam, Allah ka amshi shahadata ka sa auta na hannun salihan bayi, idan kuwa lokacinsa ya yi ka sa ya huta shima!"

Kusan kowa juyowa ya yi yana kallonta, harda AA da ya ji wani irin dariya ya ciyo shi, domin a bayyane ya gane wannan mental ɗin ai ji take lokacin ya yi ne, wato harbe su ne za'a yi, bata san wasa kawai yake son yi da abokanan aikinsa dan su yi gaggawar sada shi da inda yake son zuwa kar ace za'a yi ta riƙe shi a nan a ɗaukar masa lokaci bayan ya bar Boy a asibiti yana jiransa, "Wannan fa?" Chef ya tambaya yana kallon Yusrah, ga kuma bindigarsa a kan AA a kafe.

"Chef, matarsa ce ya ce." Sojan da aka faɗawa matsalar kafin a shigo wajen chef ya faɗa.

Haka kawai chef ya samu kansa da jin shakun maganar, domin matan ire irin waɗannan mutanen fa basu da tsoron mutuwa, mutanen da idan maganar mutuwar aka yi musu zasu yi murmushi kamar an ce zasu shige aljanna idan sun mutu, wato kamar suna da tabbaci, tsabar ɗacin rai da taurin zuciya ai ba hatsaniyar nan bace zata ɗaga mata hankali.

Sojawan da suka zagaye shi su huɗu suka sake tanƙwasa shi wannan karon saman kujera, hakan ya sa ba gardama ya zauna yana gyara hannayensa suka mayar masa da ankwa ɗin nan domin da farko da aka shigo kunce masa suka yi, basu taɓa tunanin bashi da hankali ba sai da ya nuna masu,

"Dawo nan ki zauna" Chef ya faɗa a kausashe sannan ya koma shima ya zauna saman kujera yana sake zubawa AA ido
haka kawai kamannin AA ke satar masa na fuskar wanda ya sani, sai dai ya sani a yi ruwa a yi ƙanƙara ba zai ga wanda ya sani ɗin a irin wannan shigar a wannan wajen ba, koda haukacewa ya yi tabbas da yana killace a wani wajen mai daraja, kai ina ANZA ba zai taɓa kasancewa wannan mutumen ba, dan haka ya ɗauke dubansa ya maida kan Yusrah da ta dantse leɓenta sai hararar AA take yi.

A nutse ya ce" Wacece ke, me ya haɗa ki da shi, idan ke ba matarsa bace? Me zai tabbatar mana da haka?"

Yusrah ta kalli AA dake lumshe ido, jajayen leɓunansa suna neman fitowa domin duk da ya ƙara bakin abu a jikinsu neman yin haske suke yi, kafin ta yi magana sai kawai ta ji tamkar mashayi a wani bige ya ce" Yaran mu uku fa, tana da ɗan taɓin hankali ne oga."

Yanzu kam sai da cikinta ya murɗa, ta kuma zaro idanuwa tana kallon baƙuwar jaraba, Chef kuwa ya girgiza kai ya ce" Ku kaita cel."

"La ila ha ilalahu, innalilahi, to, kai innalilahi, wallahi yallaɓai, yallaɓai ka ji na rantse maka ban taɓa ganin wannan dan..." Tsawar da sojan ya mata a dole ta haɗiye maganarta, tana ji tana gani aka nufi ciki da ita aka wuce wani waje mai duhu wanda ya raba hanya biyu, nan kunnayenta suka jiyo mata muryar wani namijin yana ɗure ɗuren zagi yana faɗin yau sai ya kashe kowa da kowa.
Hankalinta na neman barin gangar jikinta aka turata wani ɗakin aka rufo aka saka ky.

A tsorace ta juyo bayan an gama rufewa idanuwanta suka sauka a kan wasu mata sun kai su tara, abin tashin hankalin harda tsofafi biyu a ciki, da kuma budurwar da bata kaita a shekaru ba amma fuskar budurwar da ɗinki, sabon ɗinkin dake nunin ba'a jima da yi mata shi ba.

"Ke ba nace ki zauna ba? nemi waje ki zauna har a fitar da mu daga wajen nan, ba dai har yar gidan Sahabi ce ta yanka maki reza saboda saurayin da yake naki, sai dai in yi kasonta a kan ki!" Tsohuwar dake magana da ƙyar dan tsufa da ya gama mamayeta ce ke cin alwashin nan jikinta sai rawa yake tsabar ranta a ɓace yake, tana maganar ne tana nuna yarinyar dake tsaye mai ɗinki a fuska kamar an ɗinke kwarya, ɗayar matar ta ja uban tsaki, dan kuwa tsohuwar nan ta fara isarta kuma tana daf da sumar da ita ko ta basu lafiya su yi tunanin mafita, domin ita a nan yau dubunta ta cika aka gane cewar a gidanta ake ɓoye ƙwaya shine aka ritsa su a lokacin da suke rarrabawa masu sari. Kai a wajen dai kowa da abinda ya kawo shi kuma yake jiran sakamakon sa, wani yakan samu fita wani kuwa daga nan sai gidan gyaran hali , wani kuwa sai an yi ta kai shi shara'a ana maido shi, dan haka a hankali ta zagaye ta zauna bakinta ɗinke, ko yunwar dake cinta bata damunta kamar yadda haushin mutumen nan ya riƙe mata zuciya, ta tabbata idan aka bata bindigar da ta yi maganinsa fa cikin sauƙi kowama ya huta, yanzu shikenan ya sakata a halin ha'ula 'i, wanda ta tabbata ko shekara nawa zasu riƙe ta a nan babu wanda zai san inda take, babban tashin hankalinta shine SAFWAN, ya Allah, Safwan!


A cikin ofice ɗin chef ɗauki ba daɗi ake sha wace ta fara caja masu kai daga bakin lokacin da suka fahimci ba tsoron dukansu yake ji ba, ba kuma tsoron bindigar hannayensu yake ji ba sai chef ya daki teburin gabansa da ƙarfi ya ce"So muke ka sanar mana dalilin da yasa ka tari jami'in mu, ka dake shi sannan ka ƙwace masa bindiga?"

AA ya ɗan gumtse bakinsa da aka daka iya duka ya tattara jinin da ya tarun masa ya tofar a nan, a nutse ya ɗago idanuwansa ya saka cikin na chef, ya dantse leɓensa sannan ya cika ya ce" Kai, Ni sa'an yinka ne? Ai ka san ni ba sa'an yinka bane, me ka isa ka yi? Kana da wani abu da ka isa ka yi ne? An zane shin bai min bane kawai na ci zalinsa, kai ma idan ka yarda ka sake ni sai na je inda kake shan giya na zane ka."

A haukace sojan dake gefensa ya moɗa masa ƙaton abin dukan dake hannunsa a ciki, ya ƙara tafka masa a bayansa zai kuma moɗa masa chef ya dakatar da shi da hannunsa ya ce" Ku kai shi cel."

Daga haka ya juya ya ciro sigari ya kunna ya saka a bakinsa ya ja da ƙarfi sannan ya sake zuba idanuwansa hanyar da aka fita da AA kansa na neman hautsine masa abubuwa, kai yau gidan nasu nema yake ya rikice, dama yanzu suka gama kokowa da mahaukacin soja, wanda aka je aka kamo a anguwar mata ya tada rigima ta tashin hankali, abin haushin kasantuwarsa soja ya raina da yawa a cikin sojojin, domin a zuwa kamo shin sai da ya jinyata mutum uku da ƙyar suka ɗauro shi, suna tafe yana ihun zai diro daga motar ana riƙe da shi, kuma tunda aka kawo shi cel biyu aka cenza masa da ƙyar suka bar shi a cel ɗin wasu samari uku da aka kamo suma irin yaran nan ne mararsa jin magana da aka masu alƙawarin idan aka kuma kamo su a cel ɗin manyan masu laifi zasu kwana, da ƙyar aka haɗe su da shi bayan an karɓe duk wani abinda aka san zai iya jima cutar da wani da shi harta faratunansa sai da aka yanke aka rufe shi, sai ga wannan kuma an kawo masu yanzu, abin tunanin a nan an rasa gane ɗan iskan gari ne? Ɗan masu faɗa a ji ne? Ko ɗan ta'ada mai hatsari ne? Domin an bincike shi bashi a jikinsa babu wata sheda da zata gabatar maka waye shi, daga shi sai suturar jikinsa sai bindigar da ya ƙwace ta police, sai ko wannan da yace matarsa ce wacce ita kuwa da kuɗi a jikinta , ita ɗin ma babu wasu takardun a tare da ita koda na shedar y'ar ƙasa ce.

Wayar dake ajiye ya ɗauka ya danna kira, domin ba zai yi wasa da wannan mutumen ba, aje wani riƙaƙƙen ɗan ta'adda ne, zai yi yadda zai yi da shi, zai ga ƙaryar rashin kunya, idan ya je wajen da zai tarda waɗanda suka dame shi suka shanye zai gane ruwa ba shayi bane.


Mutum huɗu suka kai AA cel ɗin sa, a lokacin da ake buɗewa sai ya ga ukun nan sun daidaita bindigun su, ɗaya daga cikin su ya buɗi baki da ƙarfi ya ce" Zamu buɗe mu sako wani, idan ka yi gigin fitowa harbeka zamu yi a kai, umarnin chef ne."

"Da ku ɗin, da chef ɗin , kun ci kutumar uban ku." Wata murya da ta gama fashewa da ƙarfi irin na shaye shaye ta maido masu amsa harda buga ƙofar da ƙafa da ƙarfi, hakan ya sa suka kalli juna su dukansu ynnayin su na nuni da kamar hankalinsu na son tashi.

Shima AA da mamaki ya kalli ƙofar , sai kuma ya kalle su ƙasa ƙasa ya ce" Hala mahaukaci ne a ciki?"

Sojan nan ya zabga masa harara ya ce" Ban sani ba, ka samu daidai da kai ai, Allah ya sa ya lakaɗa maka duka mu ga ta iya shege."

AA ya taɓe baki ya ce" Ba amen ba." Sannan ya sake zuba masu ido, ganin sun dai buɗe ɗin amma kuma basu buɗe ƙofar babba ba, hakan ya sake tabbatar masa yau fa ta yiwu ya daku a ɗakin nan, koma a kai shi ƙiyama, Inna lillahi! Oh Allah dai ya ƙwaci maza kawai, amma idan ya cika a nan Allah ya isa tsakaninsa da wanda ya kashe shi.

Suna nan tsaye wani sojan ya zo, ɗauke da bindigar barkonon tsohuwa, AA ya yi tsuru yana kallon ikon Allah, sun ki buɗewar a yi mai yiwuwa dan haka ya kalli sojan nan ya ce" Ku buɗe mana."

Sojan ya sake kallonsa yana gya&a kai, lalle wannan bai san abinda ke bayan nan ba, kuma ya godewa Allah da ya zo gaba ɗaya baƙin sojawa ya tardo, yara yaran sojawan da suke baƙi, da ace ya tardo dakarun sojojinsu shi ɗin banza , han a cikinsu akwai wanda zai haɗiye shi ya kora da ruwa, da haushi haushi ya ce" Maza mu je."

Ai kam ɗayan ya buɗe sannan da ƙarfi ya afkawa wanda ya yi shiru yana sauraren su yana jiran su buɗe, abin takaici shima ana buɗewar yayi ciki da sojan, ai kam kokowa ya balle suka aniya doka masa bindigun su, da ƙarfin bala'i ya zamo AA da suka tiso ƙeyarsa sun manta da shi yana tsaye yana kallon ikon Allah da tarin takaici domin wani irin tsumi ke kuno masa yana dannar kansa dan gudun ɓata nasa aikin ta ƙarfi da yaji har suka samu suka kai korarran sojan nan ƙasa suka ta dukansa, amma bai daina ƙoƙarin ramawa ba, du sun jikkata juna, a ƙasan da yake da ƙarfi yana ihu ya ce" Ku yarda ɗayanku ya yarda in ƙwace bindigar hannunsa, in fara kashe shi, in kashe sauran da suke tare, sannan in kashe waɗannan ukun, sai kuma in kashe kaina."


A tsorace ɗaya daga cikin ukun da korarran sojan ya saka suka yi kneldown ya fashe da kuka ya ce" Shikenan babu shara'a, in ya kashe kowa ya kashe kansa da wa za'a yi shara'a? inna lillahi wa inna ilaihi raju'un! Attahiru sai da na ce maka kar mu je wajen wasan nan na tubawa na mota yau, kace mu je ai babu abinda za'a yi tunda wasa ne kawai da ƴan matanmu, gashi muguwar jarabawa ta sa mun shigo PG bayan kashedin da chef ya mana a gaban su Mama cewar in muka kuma yin rashin ji aka kawo mu wallahi ba zai badamu ba kuma sai mun kwana a ɗakin nan, ashe ashe yau zamu haɗu da ajali, wayo Allahna Mama."

Ya ƙarashe yana sake fashewa da kuka, Attahiru ɗin kuwa ya yi wani gilu gilu da kai ya ce" Hailala ake, hailala ake yi, yi haƙuri Samir in sha Allah ba zai kashe mu ba, kuma ba zamu ƙara aikata laifin da za'a kawo mu nan ɗin ba ma, yi haƙuri, Dauda ce masa ya daina kukan ka ji?"

AA ya gama ƙare masu kallo su ɗin ma ya gyaɗa kai a nutse ya shigo da kansa yana faɗin" Assalamu alaikum. "

Dauda dake ta salatin annabi, shima kansa a ƙasa ya ɗaga yana faɗin " Mala'ikan ne ya zo da sallama, ni kaɗai na ji sallamar?"

A tsorace su Samir suka dube shi, sannan suka kalli inda aka yi sallamar har AA ya ƙarasa ya zauna a wajen zaman da ya samu yana gyara zamansa da kyau yana kallon ikon Allah, Samir ya girgiza kansa ya ce" Mutum ne, mu duka mun ji sallamar ai, kai dai Allah ya fidda mu daga gidan nan lafiya."

Su kam sojawan sai da suka ga sun samu kan wannan mahaukacin sannan suka nemi juyawa a rikice dan kar aje ɗayan ya gudu, ga mamakin su suka ganshi zaune yana ƙare masu kallon da ya sa suka sha jinin jikin su, amma suka maze basu nuna ba.

Sai da suka gama daidaita fitar su, sannan mai riƙe da barkonon tsohuwar nan ya sakar masu guda suka ja ƙofar da ƙarfi suka rufe su a ciki da barkonon tsohuwar.

Tsaki AA ya ja da sauri ya lalubi bayan kunnen sa ya kunce ankwa ɗin da tsabar rikicewa suka fita basu cire masa ba, ya zaburo yana cire rigarsa ya dubi samarin nan da ƙarfi ya ce" Kai wani ya yi fitsari a nan!"

Kafin su gane me yake nufi har sojan nan ya fitar da abin nan ya yi fitsari a tasa rigar da ya cire, gaba ɗayan su sai tari suke ya laftawa barkonon tsohuwar ya zamo kowa ya yi nesa suna neman ransu, ba ma kamar samarin nan su uku kuka suke suna numfashi da bakunan su da neman iska ta ƴar ƙaramar window ɗin dake cen sama, sai dai tsayin su ba zai kai ba, a dole suka dunƙule abin tausayi waje ɗaya suna kukan ganin mutuwarsu ƙiri ƙiri.

Nan da nan hayaƙin ya tsaya, wanda ya ɗan fara saki kuwa da ƴan mintuna ya ɓace, sai kuma wanda suka shaƙa kowa ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login