Showing 390001 words to 393000 words out of 397328 words

Chapter 131 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70039

wata na goma har ma yana shirin ficewa, Aba da Aswan sun so ayi mata scaning dan ganin ko lafiya take, amma Anna ta ce tunda dai awon ta bai nuna wata matsala ba to kawai a bar wa Allah kayan shi, ita kam ba ta son gwanin ƙwaƙwaf ɗin nan ko a ce sai na'ura ce za ta maka lissafi, sam bata so.

Haka suka ci gaba da zubawa sarautar Allah idanu tare da addu'a duk sanda suka kai goshin su ƙasa kan Allah ya sauke ta lafiya. Kuma ita kan ta bayan kumburin ƙafafu da nauyi da jikin ta ya ƙara babu wani abun da ke damun ta, sai naƙudar tsaye kuwa da kullum take shan abar ta musamman ma ta baya wacce ta fi bata wahala sosai da sosai, amma cikin ta ma ba wani girman da za'ayi kwatance da shi ba ya yi, Anna ma ce dake uwa ce take ganin cikin nata yana da girma duba da shine na farko.

Wata sarautar Allah har Maryam ƙawar ta ma ta haihu wacce tana ɗakin mijin ta aka yi auren Maryam, haka ma tuni aunty Intisar ta haihu lafiya ta samu ɗan ta namiji sannan suka juya ƙasar da mijin ta ke aiki, yanzu haka ƴan amare ma babu wacce laulayin ta bai bayyana ba sai na Manal kawai, amma Abrar da Nawal har da su kwanciya asibiti.

Bilal kuma na nan da nacin nan na soyayya da jarabar ƙwallafa abu a rai, yanzu dai kam babu wata a duniyar shi sama da Nawal idan ka cire Hajia, to fa tunda ta fara laulayin nan Hajia lamarin ya shiga bata matsananciyar kunya, haka ta gagara zama da Nawal ɗin da taje da niyyar ta mata kwanaki har jikin ta ya warware ta tahowar ta, dole sai mai aiki aka tura mata ta musamman, dan fa shi kai tsaye yake abun shi shima yadda ka san uwa ɗaya ta haife su shi da oga AA.

Mukhtar ma dai haka abun yake, dan ma dai Hajiar shi na kwaɓar sa ne tana kuma masa izgili da haukan tuzurantaka ne ya taɓa shi, shiyasa yake ɗan sakayawa, amma fa ko flashing ya gani a kuskure a wayar shi kuma lambar Abrar ce, haka za ka ga ya miƙe a zabure yana sosa kai ya ce zai je ya dawo, haka Hajia za ta bishi da kallo sannan ta taɓe baki, wani lokacin har AA take kira a waya tana faɗin _"Ɗan nan nasan dama auren buzuwa in ji wani mawaƙi ya ce jidali ne, amma fa abokin ka hauka yake yi akan auren nan, ka dinga ɗora shi a hanya mana mace ba'a mata haka."_

Aswan kuma sai ya yi dariya ya ƙara tunzura Hajia da cewa _" Ai Hajia yaran nan sai a hankali, kinga da shi, da kawun ita Y. Turaki duk haka suke, suna ganin yadda ni nake tafiyar da iyalina, Hajia ban isa in ce a'a ta ce e ba, kallon ta kawai zan yi ta gane me nake nufi, amma su kam ai ba sa tsoron bin duniya a guje."_

Ai ko da ta ji haka ta yi ta zuba kenan sai su jima suna waya, da yana amsawa gaban Yusrah idan ya gama sai ya shiga rarrashi da nuna mata gigin tsufan Hajia ne fa, kawai dai a bita a hakane dan a rabu lafiya, daga ƙarshe sai ya daina amsawa gaban ta dan ba zai zauna kullum rarrashi ba.

Matar Humed ma tuni ta haihu, dan babu tazara sosai tsakanin ta da aunty Intisar, ta haifi kyakyawar ƴar ta da ta ci sunan mahaifiyar su Anna wato *Aisha*, kuma fir Anna ta ƙi su dinga kiran ta da alkunya, ta ce kawai su kirata da yadda aka raɗa mata, ita dai da take uwa gare ta kam tana kiran ta ne da Hajia wani zubin kuma ta ce uwata.

Yanzu haka dai Fatila da Yusrah ne kawai ake ta zuba idanu aga wacce za ta riga haihuwa, dan ita ma ta ɗan jinkirta, amma suna fatan jinkirin nasu ya zama alkairi ne.


*BAYAN WASU KWANAKI*


Yammacin ranar laraba Yusrah ma Allah ya sauke ta lafiya bayan gumurzu da aka sha, daga ƙarshe cikin sahalewar ubangiji sai ga *Aliyu Haidar* ya zo duniya har da ma wani baƙon a biye da shi da basu yi tsammanin zuwan sa ba, labarin haihuwar ta na riskar Aba da Aswan da suke tsaye cirko cirko daga bakin Anna, ita kanta dake tsaye bata san wa ya riga isar da goshin sa ƙasa dan sujadar godiya da ubangijin talikai ba, ita dai kawai ta gan su a ƙas suna godewa Allah, bayan Aswan ya ɗago ne ya dubi Anna ya rumgume ta sosai a jikin shi wasu hawayen farin ciki suk gangaro mishi, bubbuga bayan shi ta yi tana murmushi a tausashe tace "Barka, kai ma yanzu ka zama uba."

Ƙara rumgume Anna ya yi sosai a sanyaye yace "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Anna na gode, Anna ki tayani godewa budurwata."

Murmushi ta faɗaɗa sosai tana sake shafa bayan shi, a hankali suka ji Aba ya raba su yana jawo hannun Aswan ya dube shi ƙasa ƙasa yace "Kai, matata ce fa wannan ɗin..."

Sai kuma ya nuna mishi ɗakin da su Yusrah suke yace "Ga ɗakin da matar jikan Anza take ciki can."

Dariya Anna ta yi ta ɗan nuno Aba da yatsa tace "Kai ko?"

Juyawa ta yi ta bar su Aba kuma ya dubi Aswan dake faɗin "Aba twins fa aka ce Y. Turaki ta haifa min, ashe jinkirina alkairi ne?"

Jawo shi Aba ya yi jikin shi ya rumgume yana bubbuga ƙirjin shi yace "Yess, Allah ya raya mana su akan sunna."

Shiru ya yi na wasu daƙiƙu yana jin ɗumin jikin Aba kafin ya amsa da "Ameen Abana."

Cikin raɗa Aba yace mishi "Sai ka sa na ji ina marmarin sake haihuwa fa."

Da sauri ya ɗago ya zubawa Aba idanu yace "Me? Da Annan?"

Harara ya mako mishi yace "Ban sani ba, to da wa zan sake idan ba tawa budurwar ba?"

Dafe ƙirji Aswan ya yi yace "Wai Allah, dan Allah Aba ka daina min irin wannan wasan, ka cire wannan tunanin a ran ka kaji Abana, irin haka shi zai sa ka ji fa dole sai ka wa Nawal ƙane, idan Anna ta kasa baka kuma yanzu ka ce aure za ka yi."

Mazge masa ƙeya Aba ya yi yana faɗin "Na wuce auren ne to?"

Wani kallo ya sake jefawa Aban, sai kuma ya dubi Goggo Tidin da ta sake fitowa daga ɗakin da Yusrah take bakin ta har kunne, tana zuwa tace mishi "Ɗan Tidin barka, na zama kakar twins."

Murmushi ya mata ya ɗan jawota jikin shi ya rumgume na sakanni sannan ya dube ta yace "Momma, ɗayan takwaran Yayan ki ne dama tun azal, ɗayan kuma kina ganin ya dace a wa margayi takwara (mahaifin Yusrah)?"

Cike da goyon baya ta nuna masa ai hakan ma ya dace, sannan ta ɗora da "Hakan na nufin, sunan *AA* zai ci gaba da tabbata in sha Allah, Akhina AA (Aliyu Anza), kai ma kuma AA (Aswan Aliyu), sannan yaran ka ma AA babba (Aliyu Aswan Aliyu Anza), da AA ƙarami (Abdul-Hameed Aswan Aliyu Anza)."

Dariya Aswan ya yi yace "Hakane fa..." Sai kuma ya kalli Aba yace "Hakan na nufin suma sai matan su sun musu rashin kunya, dan tsaf za su kira su da AA bayan kallon idanuwan su."

Haka farin ciki ya lulluɓe duk wani da ya ji wannan labari, hatta Goggo Hinda da Alhamdulillah lafiya ta samu ta yi farin ciki ba kaɗan ba, dan dama alƙawari ne da Yusrah ta haihu ita za ta mata zaman jego, dan haka take ta shiryo kayan ta dreban da ya sanar da su labarin bai bar ta gida ba. Haka ma labari ya riski su aunty Fureira da duk wani dake funtuwa, haka kuma labarin nan ya isa kunnuwan Maman Nabihat wacce ta rasa gane baƙin ciki za ta ji ko takaici, dan sati uku kenan da Nabihat ta haihu take kuma aka ɗaura musu aure da Imran a gidan shi kuma aka yi suna, duk da ta ga dai ya yi iya ƙoƙarin shi wajen hidimar sunan nan kuma komai ya tafi kamar dai a gidan ta haihu duk da akwai ƴan tsegumi, amma kuma hakan bai mata ba ko kaɗan, dan ba haka ta so ba gaskiyar magana.



******************


Gaba yake yana amsa waya da AA ƙarami goye a gaban shi ita kuma tana biye da shi a baya da goyon AA babba tana ta duba jakar su dake bayan ta goye dan ta tabbatar madarar kowane na ciki da duk abubuwan da za ta iya buƙata, tunda fita ce da za ta jima, gidan Abrar za ta je da ta haihu jiya ita ma.

Sauko jakar ta yi a bayan ta ta tsaya gaban motar tana jira ya buɗe mata ƙofar, amma sai ta ga ya tsaya ya bata baya yana amsa waya kuma ƙasa ƙasa ita bata jin komai, ɗan ƙwanƙwasa gilashin ta yi dn ya buɗe mata da remonte, amma sai ya ɗan juyo irin kai tsayen nan ya ɗago mata yatsu biyu alamar ta jira shi minti biyu.

Da ƙaguwa dan tana so ta sauke AA babba ta zagaya dan ta karɓi makullin motar ta buɗe, amma sarautar Allah tana zagayawa sai kawai ya sake yin ƙasa da murya yace _"Zan sake kira anjima, ina hanya ne yanzu, zamu yi magana daga baya."_

Jin haka da Yusrah ta yi daga bakin shi yasa ƙirjin ta bugawa da ƙarfi, haka take ta ji yanayin ta ya canza zuwa gurɓatacce, kwana biyun nan dama ta fuskanci canji tare da shi, ya kan yi dare sosai kafin ya shigo gidan, sannan ya kan yawaita aiki da wayar sa wanda hakan da ba ɗabi'ar sa bace, indai yana gida basu cika anfani da waya ba sai dai idan kira ya shigo ko zasu yi mai mahimmanci.

Ran ta ta ji ya sosu ba kaɗan, ta so gane kalaman shi amma dai a dole shaiɗan ya fahimtar da ita ma'anar dai kenan, ya ce zai kira daga baya, sannan ina saman hanya ne, wai zasuyi magana daga baya, da wa kenan? Wata ya fara kalla a waje kuma? Bayan it... Subhanallah, take ta ji hankalin ta ya gagara ɗaukar yanayin da ta tsinci kan ta a ciki, dan kuwa sukar da ta ji a zuciyar ta har ta zarce wace ta dinga ji sanda ake ta haɗa mata shi da Nabihat, to yanzu ta gama da ƙalubalen Nabihat wata ce kuma da bata sani ba hala?

Take idanuwan ta suka rufe, ta gaza gane komai gaban ta, ta kasa bambamce daidai da ba daidai ba, kawai ta sakarwa sheɗan akalar zuciyar ta sannan ta shiga bin ta da jin duk yadda ta yi da ita ɗaya ne.

A sukwane ta koma cikin gida kai tsaye zuwa ɗakin baccin ta, tana zuwa makullin motar ta da bata cika aiki da ita ba ta ɗauko dan ba ya barin ta tuƙi, bayan kuma shi ya fara zama malamin ta a fannin tuƙi tun cikin ta na ƙarami kafin ya kaita makarantar koyo ta ƙware ta kuma samu lasisin ta a hannu, tana fitowa daga falon wajen motar ta nufa kai tsaye ta buɗe ta sauke jakar bayan ta ta shige sannan ta tayar ta kamo hanyar fita... Shi dai tunda ya aje wayar sai ya ga kuma ta koma ciki sai ya yi tunanin mantuwa ta yi, hakan yasa ya sake ci gaba da duba saƙonni masu mahiancin da suka shafi aikin da ya fara sabo ta WhatsApp, yanzu ma da yaron gidan wani hamshaƙin mai kuɗi ne suka gama waya, yaron gida ne dai haka da aka ajiyewa mata suke saka shi duk wani aiki na gaggawa, hakan ya sa ya san sirrin gidan sosai da sosai, dalilin shi kenan na maƙalewa yaron kuma yana samun yadda yake so daga gare shi.

Ƙa'idar aikin sa ce ko iyayen ka ba'a so su san me kake ciki? Me ka aikata? Me za ka aikata? Me kake shiryawa? Akan wa kake bincike? Da dai sauran su, shiyasa idan tana kusa da shi ya kan sassauta murya yadda ba lallai ta ji wani abun da gobe zai iya zama haɗari gare ta ba, shiyasa a ɓoye ba tare da sanin ta ba kariya yake bata ta ƙasa da ƙasa ita da yaran shi da baya fatan wani a cikin su ya cutu, a kowane sakan yakan san motsin su, inda suke? Me suke yi?

Yana tsayen nan ya ji ƙarar mota a bayan shi, ya juya dan ya ga wace motar ce kuma wa ye a ciki bayan shi ga shi? Sai kawai ya ga gilmawar ta da gudu inda mai gadi shi kuma tunda ya ga ta fito ya kuma san fita zasuyi ya ɗan buɗe ƙofar amma ba duka ba, yanzu da ya hangi tahowar ta tun daga wajen parking ne sai ya karasa wangale mata ƙofar ta fice.

Bayan hangen ɗan kwalin ta da ya yi ba wani tabbaci da zai iya bayarwa akan ita ce ta fita, hakan yasa ya ƙara juyawa bayan shi sannan ya sake bin ƙofar da kallo, sai kuma ya kalli AA ƙarami dake goye gaban shi yaron idanun shi biyu sai wasa yake da ƴan midil midil ɗin hannayen shi yana kai su baki, shafa kan yaron ya yi tare da sumbatar kan shi sannan ya buɗe motar shima ya shiga da tunanin bin ta a baya, hankalin shi duk a tashe yake saboda ba kasafai ya fiya barin tayi tuƙi ba, kawai bai yarda da ƙwarewar ta bane, shi dai sai ya ji yafi samun salama idan tana gefen shi yana tuƙa ta.

Saida ya ɗauki hanyar da ta yi ya fara ƙoƙarin dannawa lambar ta kira, da sauri kuma ya kashe yana ayyana _'Ai hankalin ta zai rabu biyu idan na kirata, ba kuma zan so haka ba gaskiya.'_

Dan haka ya ci gaba da bin ta yana mai cika da mamakin me akayi? Me ya mata? Jiran shi na minti biyu ne ba za ta iya ba? A gaskiya ba dan yaron nan dake tare da shi ba, yau da ya zama namiji ta hanyar shareta ya je muhimmin aikin dake gaban shi, idan ya so sun haɗu da dare a gida.

Saida ya ga tsayawar ta a ƙofar gidan Manal lafiya kaɗai hankalin shi ya kwanta, yana kallo ta shiga cikin gidan sannan ya kira wayar ta, kira ɗaya ba'a ɗaga ba, biyu ma haka sai da ya kira na uku ta ɗaga, da ɗan zafi-zafin yanayin yau da gobe da kuma aiki dake haɗe masa tunani wuri ɗaya yace _"Y. Turaki kan ki ɗaya kuwa? Me kike yi haka wai?"_

Ita ma dake tana ganin ya mata ba daidai ba sai ta amsa da _"Nawa ka gani a jikina?"_

Yanayin yadda ta bashi amsar yasa yace _" Tofa, lafiya? Wa ya baki izinin tuƙi kuma kika kamo hanya ke kaɗai? Haka kawai ki ɗauke ni wani sakarai ina tsaye ki kamo hanya ki tafiyar ki, me kike nufi? Shi wannan da kika bari a hannuna fa."_

Sai kawai ta ji ihu yake mata a kai, ranta ya sake ɓacewa, idanuwa a rufe ta bashi amsa da _" Sai ka kai wa sabuwar bazawarar taka shi ai, ko uban sa bane kai da za ka tambayeni ya za ka yi da shi? Kuma fita gani nayi baka da lokacina shiyasa na taho tunda na san gari nima."_

Da mamakin wannan halayen nata yace _" Wai ke kina lafiya kuwa? Me yake damun ki? Me aka miki? Kinga dakata, wallahi idan abinda za ki min kenan to maza ki koma gida, gwaramar da ke kaina ta fi ƙarfin na haɗata da kowace rigima bare ta ki, dan haka gani nan ƙofar gida maza fito na mayar da ke."_

Cikin fashewa da kuka Yusrah tace _" Wacece? Wallahi babu inda zan je, AA ba zan koma gidan ka ba, daga nan gidan Annata zan nufa, can ka ƙarata da sabuwar budurwar ka tunda ta fini mahimmanci."_

Ko da ta gama maganar ta ta kashe wayar ta ƙarasa cikin gidan tana share hawayen ta. AA kuma da mamaki ya bi wayar da kallo, sai kawai ya girgiza kai yana dantse leɓen shi na ƙasa ya yi ƙwafa, ƙara gyarawa ɗan shi kwanciya ya yi a jikin shi sannan ya tayar da motar ya kama hanyar gidan Anna ran shi shima a ɓace da wannan haukan, bai aikata laifin komai ba, bai san me ya mata ba? Haka kawai ta hukunta shi saboda taƙamar ta ita e duniyar shi? Dan tana alfaharin ko bata da gaskiya ya kan kwantar da kan shi ya rarrashe ta? Da wannan tunanin ya isa gidan Anna ɗauke da AA ƙarami a kafaɗa da kula abun goyon shi a hannu.

Kiciɓis sukayi da Anna za ta shiga falon Aba hannun ta riƙe da butar shayi, yadda fuskar shi take, da yadda suka gaisa ya kuma miƙo mata yaron tana kallon fuskar shi sam ba ta shaida wa ye ba a ciki dan kama suke tak tak babu bambamci ba, iyayen su dai ne tasan suna gane abun su, kallon AA tayi tace "Wanene a ciki?"

Ɗan murmushin yaƙe ya yi yace "A. Ƙarami ne Anna, ki riƙe shi ni zan fita wani aiki na dawo."

Da mamaki ta dube shi tace "To ina Maman shi? Ina kuma babban?"

A dake ya amsawa Anna da "Tana gidan haihuwa, za ta zo."

Daga haka ya juya ya tafiyar sa Anna ta bishi da kallo saida ya ɓacewa ganin ta sannan ta ƙara tallabe AA ƙarami tana shigewa da shi wajen Aba zuciyar ta cike da wasi-wasin ko me ya faru kuma? Me ya haɗa su? Faɗa sukayi irin na ma'aurata? Shine da laifi ko ita? Da ta shiga bata sanar wa Aba komai ba, dan tasan yanzu zai kira shi ya ce sai ya ji ba'asi me ya faru? Dan haka suka rumgumi jikan su tare da aikawa aka siyo masa sabuwar fida da madara da kunu na garin suya mai kyau da ƙara lafiya suka dinga ɗirka mi shi, har Safwan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login