Showing 42001 words to 45000 words out of 397328 words
gwamanti, kai innalilahi Wa inna ilaihi raj'une ka duba ka ga irin zaryar da muka yi dan a tallafa mana da wani abin saboda ramin nan, amma aka yi mana shiru, tabbas ba zamu daina ganin laifin gwamnatinmu ba har duniya ta naɗe!"
Jam'in ƴan sandan ya ce" In sha Allah wannan ba zata gagaremu ba, zamu yi bakin ƙoƙarin mu har a sake su, ku mu je a gama saka su a motoci mu je a shirya su da wuri Allah ya jiƙansu."
Da wannan su Liman suka juya da gawarwakin, aka bar majinyatan a asibiti da masu kula da su, kusan kowa ta kansa yake yi a wannan lokacin sai ta wanda yake kulawa, hakan ya sa Yusrah a gadon da take kwance cikin dogon ɗakin dake ɗauke da majinyata, domin gefen talakawa futuk ne aka kawo su, a haka ɗinma suna kyautata zaton da wahala su iya biyan, ita ɗaya ce jal a kwance sai wani ɗan yalolon mayafi fari da aka rufa mata jikinta da shi, saukar numfashinta kaɗai ke nunin cewa tana da rai har yamma ta yi likitocin suka fara zagayen mararsa lafiyar dan cirewa masu karin ruwan da ya ƙare, ƙarawa wa'inda ya dace a ƙarawa, da dai duba yanayin mararsa lafiyan har Sakina ta zo kan Yusrah da mamaki ta duba yadda jini ya hau abun ƙarin ruwanta domin ruwan da aka ƙara mata har ya ƙare jini ya fara hawa sama babu wanda ya yi kiran likita dan a cire mata, hakan ya sa ta daga abin rufar tana faɗin" Wannan ina mai jinyarta ne bata kula da ƙarin ruwan nan bane har ya yi h..."
Ɗif maganarta ta katse sanadiyar fuskar Yusrah da ta gani, da sauri ta juya wajen matar dake faɗin " Wayyo baiwar Allah bamu kula ba da ya ƙare da mun yi kiran, ai bata da mai kulawa da ita baiwar Allah, iyayenta ne suka rasu da yayarta cikin hatsarin nan..."
"Yusrah? Innalilahi wa inna ilaihi raj'une." Sakina ta faɗa, da sauri ta kashe ta cire mata sannan ta fita, jim kaɗan ta dawo da masu aikin ɗaukan mutane da kujerar da ake ɗora mutum suka gyara Yusrah suka ɗorata tamkar matacciya suka yi can ɓangaren jinya na masu hannu da shuni aka shinfiɗata a wani ɗaki mai sanyi aka gyara mata kwanciyarta sannan ta fita ta nufi office ɗin ogan dan kuwa bata sanar masa ba ta aikata haka, abu ɗaya dai ta sani shine zai ji daɗi idan ya ga ta aikata haka dan sarai ta san ƙudirinsa a kan Yusrah.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*13*
A lokacin da ta ƙarasa office ɗin sa ta same shi da baƙi, dan haka ta dakata har suka gama suka fito sannan ta shiga, _'Kai, docter rashin gaskiyarsa ba kaɗan bace.'_ Take ayyanawa a ran ta, gashi da sake, lokacin da ta shigo ɗin takarda ce ta magani irin waɗanda yake karɓa yana siyarwa a saman table ɗin, wacce baƙin nan suka kawo masa bai ɗauke ba, shigowar ta ba da neman izini ba sai da ya saka shi ɗagowa a zabure yana dubanta.
Tsaki ya ja na bazatan da ta masa ya shiga ɗaukewa ya ce" Sakina, ki ringa neman izini idan za ki shigo office ɗina."
Murmushi ta yi na yadda ya tsora ta, a nutse ta ƙarasa ta haye saman table ɗin gaba ɗaya tana waina ƙafafuwanta cike da shaƙiyanci ta ce" Menene ban sani ba tun daga kan mai office ɗin har office ɗin?"
Bai saki fuskarsa ba ko ɗaya, hasalima fuskar a ɗaure ya dubeta ya ce" Amma kin san na maki ƙwaƙƙwaran kashedi a kan ire irin maganganun nan a cikin asibitin nan ko da kuwa daga ni sai ke ne ko?"
Yanayinsa ta bi da kallo, sai kuma ta taɓe baki a ranta tana ayyana _' Munafukin banza da wofi, ko wa zai ɓoyewa yana bin mata? A wannan halayya in dai kana yinta baka isa ka ɓoyewa mutane ba sai dai a bika da ido kawai dan abun da yake hannunka?'_
A bayyane kuwa sai tace" Dama zuwa na yi a kan maganar hatsarin nan da aka yi ɗazu da safe, waɗanda gini ya faɗa masu a anguwarsu."
Wani takaici ya sake kama shi, dan bai ga dalilin da za'a kawo masa wannan maganar ba, bai san uban da ya sa faƙiran mutanen nan suka rasa asibitin zuwa sai tasa ba, ace har yanzu sun kasa zuwa su biya kuɗin magunguna, shi ya faɗa masu babu wanda zai saka shi asarar paracetamol bare gadon asibiti! Sai an biya dukkan abinda aka yi aiki da shi ciki har da mutuwaren da aka kai wasu.
Sakina ta ce" A cikin su wacce ta rasa mahaifiyarta da mahaifinta da kuma yayarta YUSRAH ABDUL HAMID ce."
Da sauri ya juyo daga wajen jona cajin da ya juya, dan har cikin zuciyarsa sai da ya ji wani abu ya soke shi, amma sai ya zuba mata idanu yana sauraron ta tana ci gaba da magana.
"To da na je yanzu ne na same ta bata san inda kanta yake ba, kuma ko mai kula da ita babu, shine na kaita ɗakin categorie sannan na saka nurse biyu su kula da ita kafin na zo in sanar maka." Ta ƙarashe kanta tsaye, dan kuwa ta kula ƴan wulaƙancin a kusa suke da shi, ita kam tana mamakin a gidan duniya idan ka ga ya sassauta maka murya a lokacin da zai anfana da kai ne, daga wannan da kai da jaki ɗaya kuke a wajensa, kai Allah ya sawaƙa.
"Kina nufin categorie kika ɗauketa kika kaita? Da kuɗin wa?" Ya faɗa da ƴar tsawar da ta sakata jin tamkar ta aikata tashin hankali bayan ta zo da karsashin ta da ƙarfin ta dan ta sanar masa domin ita ko a kwalar rigarta wai dan ya nuna ya damu da wata macen bayan ita, domin dama rayuwar bariki ai ba ta sannin ciwon kai bace.
Dan haka tana dubansa da yanayi na ta fara sadakarwa ta ce" Gani na yi likitarka ce, sannan Yusrah ce fa."
Gaban goshinsa ya kama dan takaici ya ƙarasa ya zauna saman kujera ya ce" Har yaushe zan tsaya ina sake jaddadawa duk wani wanda ke ƙarƙashina cewar dukiyata tawa ce, babu mai ikon ɗaukan wani mataki a kan dukiyata ko wanene, amma dan baƙin wulaƙanci sai a ringa nemana da fitina? Da kike maganar Yusrah ce so what? Babu wani haɗina da ita da zata ɗauki adadin lokutan da ban san yawan shi ba tana zaune a ɗaki mai AC da ɗaukan magunguna a asusun banza, dan haka ki je ki mayar da ita inda kika ɗauketa su biya mata adadin abinda ta ci itama."
Da tsabar rudu da mamakin rashin tausayinsa da mummunar aƙidar sa take kallonsa, mutumin da ya yi tafiya mai gigitarwa wacce ake iya kiranta da *WATA TAFIYA* mai ɗauke da raunuka irin Yusrah duk wani mai imani zai dubeta, sai ga wannan salisainin dangin son kan ya aikata haka? Lallai ta ƙara ɗaurar ɗamarar tsakaninta da shi abinda ya haɗa su daga shi ba daɗi ba ragi. Baya ga haka ma, da ta ji yana ta kiran kuɗin shi, asibitin shi da dai sauran su... Shin yaushe asibitin nan ta zama ta shi? Bayan ta san ta Yayan sa ce Alhaji Aliyu Anza, e tabbas shi ma mai kuɗi ne kuma shahararre, saboda dukiyar su sun gada ne kuma suna nema suma bilhaƙƙi da gaskiya, amma dai asibiti kam ta Alhaji Aliyu ce, duk da za ta iya cewa tana tamtama, dan kuwa tamkar wanda ya shuka dusa haka yake wofantar da lamarin asibitin, ma'ana dai shi ba likita ba, kuma ba ya zuwa kawo ziyara, sannan babu ɗan sa ko ƴar sa dake aiki anan a duk cikin ƴaƴan sa, hakan ma ya sa wasu mutanen ke ganin kamar ya mayar da ƙanin nasa wato Doctor Hamat bawa ne, amma ita da ta san wanene shi, ta san shi kanshi Doctor zai wa masu masa wannan tunanin kallon mahaukata, dan bilyoyin da ya tara a asibitin nan ta hanyar munanan harƙallolin shi Allah kaɗai ya san iyakar su.
Juyawa ta yi rai ɓace da niyyar ficewa ta bar shi da masifar sa, ta kama ƙofar ta murda har zata fice ta ji ya yi wata gyaran murya ya kira sunanta, dan haka ta juyo rai ɓace ta tsaya tana kallonsa, wani ɗage kai ya yi yana tunani sai kuma ya sake kallonta ya yi murmushi ya ce" Ki barta, ki kuma duba da kyau ko akwai wani da ya shafeta da ya rage, sai a haɗe su a ɗakin ana kula da su har ta farfaɗo, itace da kanta zata yankewa kanta hukuncin ci gaba da samun lafiya da kuma yadda ya dace ko kuwa akasin haka."
Wani malalacin kallo ta biyo shi da shi dan ta gane manufar sa sarai, girgiza kai ta fara yi bakin ta a taɓe, kafin ta buɗe ƙofar ta furta "Na ji."
Da kallo ya bita, wato ita nan ya ɓata mata rai ne ko? Dan ta san anjima sun yi za su haɗu shiyasa za ta dinga yi masa wannan rashin kunyar? Sai kuma ya ayyana _'Ba damuwa.'_ Da zaran Yusrah ta ji sauƙi in dai ta yarda da sharuɗɗan shi ai ya kusa samun sabuwar cikar da zai dinga latsa wacce ya tabbata ta fi Sakina.
Ko da ta koma take tambayar na kusa da gadon da ta ɗauki Yusrah, su ne suka nuna mata ɗakin da Safwan yake, da ta je ta same shi sai ta ji ta ma fi tausayin shi fiye da Yusrah, dan shi likitan dake duban shi ya tabbatar mata babbar matsala a duka ƙafafun yaron, ko za'a dace kam gaskiya sai dai idan manyan likitoci kamar su Docter za su tsaya kan shi da gaggawa, idan aka ɓata lokaci kuma to tabbas sai an dangana shi da ƙasar waje ko kuma ya tabbata a haka, dan matsalar ta faro ne daga ƙashin bayan shi.
Da yamma wakilai ma daga gwamnati sun zo duba waɗanda iftila'i ya faru a kansu da ɗan abun hasafin da Yusrah ba su yi sa'ar samu ba saboda basu da wani a tare da su, sai wata mata da ta yi basaja kamar ita ke tsaron Safwan a lokacin da aka kusa isa bakin gadon shi, ko da aka bada nashi taimakon suka tafi ta sulale ta bar shi da murnar samun wani abun.
Kusan dai magriba Yusrah ta buɗa idanuwan ta da ko da suke rufe ana gane ɗan karan kumburin da suka mata, idaniyar ta ɗaya ce ta buɗe amma ɗayar a liƙe take gam, wacce ta buɗe ɗin ma haka take jin kamar an ɗebo ƙasa da gayya an zuba mata, dan da ta kai yatsan ta kan idaniyar ba ƙaramar ƙasa ta fito da ita ba tare da yana har saida ta tsorata.
Ƙafafunta da suka ma suka mata nauyi, ko ta ce illahirin jikin ta da take jin shi kamar ba shi ba ta motsa tare da sauko da su ƙasan gadon, yin haka sai ta ji kamar ta fama wani bala'en'en daɗaɗɗen ciwon baya da ta kwashi shekaru tana fama da shi, yadda ta ji abun ya soke ta lokaci ɗaya abun da baka taɓa ji a rayuwar ka ba yasa a bazata ta saki wata ƙara tare da furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Wayyo Allah."
Da sauri ta ɗora kanta saman ƙarfen gado da ta riƙe dan ya taimaka mata wurin tashi, ba ta ɗago tana shan wannan azabar raɗaɗin baya ga nauyin idanuwa sai da ta kusan kwashe minti goma a haka ita kaɗai, saida abun ya lafa mata sannan ta ɗago kanta a hankali fuskar ta tayi sharaf da hawaye, jiƙewar da sukayi ma har ta sa ɗaya idaniyar ta fara alamar buɗewa ita ma.
Ba tare da hawaye sun daina yi mata zuba ba ta ɗaga kai tana kallon inda take, kallo ɗaya ta ma ɗakin ta gane asibitin da ta bari ce jiya aka dawo da ita... Sannu a hankali kuma sai ta fara tuno wasu abubuwa da suka fara, ba ta san lokacin ba, ba ta san su waye duk akan ta ba, amma dai tabbas ta ji wata muryar na faɗin _"Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Shi ma malam Abdul-Hameed ya rasu yanzun nan daga jin ana magana akan rufe gawar matar sa da babbar ƴar sa, La'ilaha illalah, Muhammad Rasulillahi sallalahu alaihi wa sallam."_
Tabbas ta ji wannan kalaman, sai dai daga su ne bata sake sanin komai da ya faru ba sai yanzu, Maman ta? Baban ta? Yayar ta? Duk sun rasu ake nufi sakamakon wannan zubewar ginin? Wata sarawar kan ta ya yi da mugun ƙarfin da ya sakata dafe kan nata tana lumshe idanuwa har tayi nasarar liƙesu gam saboda gaba ɗaya ɗakin ne ke juya mata, a lokacin ji take ina ma wannan sarawar kan ya zo mata da bugawar zuciya irin mai fat ɗaya ɗin nan da sai dai a ce Allah ya jiƙan ka? Ita kam me ya rage mata a duniya yanzu? Me ya yi saura da za ta yi? Ya za tayi da rayuwar ta? Waɗanda suka zama gatan ta, ƙawayen ta, ahalin ta, nishaɗin ta, farin cikin ta, ace duk sun tafi sun bar ta, to me take jira ita? Me ta tsaya za ta yi? Me jinkirin nata yake nufi?
Wani irin kuka wanda ma fi aksari wanda basu da aƙida ne suke yin shi, wato kuka da gaba ɗaya zuciya cikin ɗaga iya sautin muryar da Allah ya hore mata, kawai ta saki maƙogwaronta ta fashe da matsanancin kukan da dole ya jawo hankalin nurse ɗin da ta gama sakawa wata Hajia ruwa a ɗakin kusa da na Yusrah.
Da gudu gudu ta shigo da tunanin wani abun ne ya faru, tana ƙarasowa ta kama kafaɗun Yusrah dake neman zubewa ƙasa ta yi birgima ta riƙe ta tana faɗin "Yusrah, Yusrah dube ni? Lafiya? Me ya same ki?"
Ture ta Yusrah tayi tana fizge jikin ta ba ta yi alamar za ta saurare ta ba, ba tare da jin ba daɗi ba ta sake matsowa kusan ta tana cewa "Yusrah, ba kuka za ki yi ba, ki wa iyayen ki addu'a, dukkanmu nan muna jajanta miki tare da tausaya miki, dan ko ba a asibitin nan ka ke ba ka samu labarin wacce a dalilin iftila'in ta rasa iyayen ta biyu da Yayar ta, dan haka ki yi haƙuri Yusrah, ki roƙi Allah ya baki juriyar cin wannan babbar jarabawar."
Cikin kuka mai tattare da hargagi Yusrah ta dube ta, duk da ita bata ma san ta ba tunda ma'aikatan dayawa kuma ba jimawa ta yi ba, amma haka ta daure take faɗin" Shin ni ma me ya sa ban bisu ba? Me ya sa ni kaɗai na rayu a cikin su? Shin dama ba sune ni ba kuma sune farin cikina ba? Yanzu da basa nan me zai faru da ni to? Me zan yi da wannan rayuwar da bayan ƙalubale babu abinda yake faruwa a cikin ta? Ni kam bana son na ƙara ko da minti ɗaya ne ina numfashi, ki wa girman Allah ki kasheni, ki samo allurar guba ki min na mutu n..."
Rufe mata baki nurse ɗin tayi tace" Subhanallah! Haba Yusrah, ya kina musulma wacce ta yarda da ƙaddara za ki dinga faɗin wannan maganganun? Kina so ki rasa imanin ki ne saboda waɗanda suka kawo ki duniya sun koma ga ubangijin su? Yusrah so kike ki kafircewa wanda da ke da duka waɗanda kike taƙamar da su shine ya halicce ku? Sannan ya karɓi kayan sa a daidai yanzu da suka gama miki komai a duniyar nan dan kawai ya jarabta imanin ki? Haba mana Yusrah, ki dinga tauna kalaman ki kar ki fita daga musulunci ba tare da sanin ki ba."
Jin tana shasheƙar kuka saboda ta yarda da abinda nurse ɗin ta faɗa mata ya sa cike da ƙwarin guiwa ta ɗora da" Za ki iya rayuwa Yusrah, kar ki manta akwai waɗanda mahaifiyar na diresu a doron duniya take tafiya ta bar su, amma ga dayawa da irin haka ke faruwa da su, sai ya zama godiya suke saboda ko ba komai ta riƙo hannun su ta nuna musu hanyar rayuwa da fafutuka dan inganta rayuwar, wasu kuma haka suke tashi babu uwa babu uba sannan babu wani tsayayyen mai kulawa da su cikin gata, Yusrah a ganin idan iyaye ne fatan kowa, me ya sa ubangijin da ya fi uwa tausayin ɗan ta zai yarda ya raba jariri da uwar da zata zama gatan nasa? A'a Yusrah, ubangijin ki, kuma ubangijin iyayen ki da ma mu duka, shine gatan kowa, ko da iyayen ki idan bai so ki yi tako ɗaya ba, to ba inda za ki iya takawa