Showing 87001 words to 90000 words out of 397328 words
ya ce" Yaushe rabon ki da ki yi sallah?"
Da sauri ta ɗaga tamkar ya tuna mata sunanta ba ma ibadarta ba,
ɗakin ta shiga kallo da sauri ta ce" Ko sallar asubahi ban yi ba, innalilahi wa inna ilaihi raju'un, bari in yi."
"Amma, kin ga dattin jikin ki kuwa? Kina cikin gari , ko bara kina iya yi ki tsaftace jikin ki sai ki yi ibada, idan har zaki amince, ki zo mu je wajen mahaifiyata, ki yi wanka ki yi sallah, sai ki ci gaba da tafiyar da kika ce." Ya faɗa a tausashe yana kallon ta.
Ido ta zuba masa tamkar ta ga sabon karatu, hakan ya sa ya sake sassauta muryarsa ya ce" Zan tafi da ke bisa amana, dan ki je ki yi ibada a cikin nutsuwa, kin san ai ibada bata yiwuwa da datti ko? Wajen mahaifiyata zan kai ki, na tabbata zata taimaka maki."
Ba dan ta ji a ranta cewa a tare da shi tana cikin aminci ba ta bi shi, hasalima a yanzu haka da take gaban motarsa a zaune a can cikin zuciyarta babu abinda ke iya ruɗa tunaninta wanda zai iya hargitsata sama da halin da take ciki, idan ya zamo wannan bawan Allah ya salwantar da ita ta tabbata addu'arta Allah ya amsa, addu'ar dake cikin zuciyarta mai girma ce, balle idan bata ga Safwan ba.
Tunda suka karyo kwanar gidan mai gadi ya buɗe ya danna motar cikin gidan gabansa ke faɗuwa sakamakon hangen alamun taro da ya yi a ƙofar ɗakin Hajiarsa.
Hajia Zainab mahaifiyarsa irin mutanen nan ne dake da matukar riƙo da abinda ya shafi sirrin su, idan na ce sirri, ina nufin dukkan abinda ya shafe ta ko ya shafi ƴaƴanta, hakan ya sa take danne dukkan wulaƙancin Tasneem tana faɗawa Allah da ƙoƙarin neman mafita cikin sirri ba tare da wani ya ji kan ahalinta ba, sai dai kashhh! Duk irin yadda ta kai da ɓoye abubuwan nan ya zamto duk duniya babu wanda bai san abinda suke ciki ba, an riga an san cewa ɗanta bai yi dacen macen aure ba, abinda suke ciki a bayyane yake a idanuwan duniya, wannan abin shi ya fi ƙona mata rai da fatan Allah ya nuna mata ranar da zata zamo yaronta ya fi ƙarfin matarsa.
Waje ya samu ya tsayar da motar ya zuba ido ƙirjinsa na dokawa, haka kuma ƙarara a bayyane yake tsoro ya bayyana a fuskarsa har sai da ihun bala'in da take zubawa ya lafa ya hangi fitar ta tamkar kububuwa sannan ya kalli Yusrah dake kallon waje ɗaya ya ce" Bismillah mu je."
Yawu ta haɗiya, har ranta ta gama yarda cewa maganar tsaro bata tare da ita a tare da namiji mai tsoro, sai dai wani ikon Allahn kuma wanda ya fi komai a duniya, a hankali ta idasa shiga falon bayan ta ɗauki minti huɗu da shigarsa.
A gurfane gaban wata dattijuwa yake riƙe da hannayenta, bayani yake yi mata dalla dalla na abinda ya faru, tana sauraronsa tana masa tambayoyi har ta gamsu sannan ta ɗaga tana kallon Yusrah da tabbatarwa kanta ƙwarai, in dai a haka ya ganta ko tana cikin hali na matsanancin taimako saboda an tsinci kai a matsanancin hali ko kuwa bata da hankali, domin yanayinta cikin biyun nan kawai take iya nema ta ajiye.
Huci ta fitar mai raɗaɗin ɓacin ran da yarinyar nan ta gama shaƙa mata, domin zagi babu wanda bata yiwa yaronta ba da alwashi kala kala a kan ɓarnar da suka aikata dan kawai an tsaya an yi yadda ya dace, tabbas ta yarda da bayanansa dan baya yi mata ƙarya, to wai menene Tasneem ke tunani? Lalle Tasneem na neman fitinar da ta fi ƙarfin ta.
A hankali ta miƙe, tana kallon Yusrah ta ce" Ƴata zo mana?"
Tamkar wata marar wayo ta ƙaraso ta duƙa tana kallon ƙafafuwan Hajia, a tausashe Hajia na dubansa ta ce" Ka taimaka mana da abaya , da abinda zai samu, ka yi ƙoƙari ka canza tufafin nan duk ya yage, Allah ya kyauta."
Daga haka ta kama hannun Yusrah a tausashe ta ce " Ƴata mu je ki yi wanka kin ji?"
Kai kawai ta iya gyaɗawa sannan ta bi mama a hankali tana kallon hannunta dake cikin na mama idanuwanta na hasko mata hannayen mahaifiyarta a duk lokacin da ta riƙe ta haka.
Saida ya ga ɓacewar su sannan ya miƙe shi ma ya fita yana jin ƙaunar mahaifiyar sa na ratsa shi wacce a duniya har yanzu ita ce mai share kukan shi bai kuma samu ta biyun ta ba, babbar kasuwa da ya fi kusa da nan ya tsaya, madadin abaya guda ma da Hajiar ta faɗa, sai ya ga ai yarinyar na buƙatar sutura musamman da ta ce iyayen ta basa raye.
Dan ma tsadar rayuwa da kuma abin da baka shirya ma ba ya sa ya ɗaukar mata abaya masu kyau da tsadar gaske har guda huɗu, sannan ya haɗa mata da wasu dogayen rigunan ƴan kanti har da riga da siket, sannan ya haɗa mata takalmi kala biyu da sabuwar jaka irin ta matafiyi da kuma ƙarama ta mata.
Hajia Mama kan ta saida ta yi mamakin ganin wannan uban kaya da ya tilo, amma sai ta ɗauki riga ƙwaya ɗaya a ciki ta kai ma Yusrah ɗaki dan ta jima da fitowa daga wanka, duk da dai taga wankan na yarinyar bai kwanta mata a rai ba, amma kuma ta lura da tana gaggawa ne, gaggawa take ko ta ci gaba da tafiyar ta dan fa ji take ba fashi sai ta je funtuwa.
A ƙalla dai ta haska, amma ita kan t ta san wankan da ta yi bai kai na dattin dake jikin ta ba, tunda gidajen su suka ruguje ba ta yi wanka mai sunan wanka ba, ko gidan su Maryam da ta kwana biyu ai tana dai yin shaf shaf ne ta fito, amma ita kn ta har mamakin yamutsewar fatar ta take yi duk ta zama kamar ba Yusrahn nan ba wacce ko b kwalliya dai Mamansu tana kulawa da duk wani sashe na jikin su.
Sallolin dake kan ta ta shiga ramawa, ta ɗauki tsawon lokaci har tana ma kanta karatun tanutsu akan ibadar ta, da ace Babansu na raye ya ji da gangan ta bari wata sallah ta suɓuce mata, ai ba ƙaramin duka zai mata ba wallahi, dan Baban su akan ibada kam ko Hannah dake babba sai ya daka bare ita dake ƙasan ta, daga nan kn salayya ta ɗauki alƙawarin duk matsin da za ta sake shiga ba za ta yarda ta yi wasa da sallah ba, saboda an koyar da su, kuma ta sani daidai gwargwado, kawai rikicin ne da ya zo mata bazata kuma abin da baka saba da shi ba, sai ya nemi zautar da ita gaba ɗaya, amma za ta yi ƙoƙarin kiyayewa ko dan ta kasance cikin nutsuwar ta da kuma haibar da ibada ke haifarwa duk wani bawa da ya tsayar da ita da kyau.
*A* yanzu da duhun magriba ya yi ita kan ta ta sani ba za ta fara cewa za ta fita ta kama hanyar Katsina ba, damma duk da haka cike da ƙarfin hali ta kalli Hajia Mama bayan gama cin abincin da ba wani ƙoshi ta yi ba tace "Mama, ina so zan ci gaba da tafiya, nagode sosai da duk alkairan ku gare ni, Allah ya saka da alkairi."
Zuba mata idanu dattijuwar ta yi tana kallo, irin tsofaffin nan ne da suke da miskilanci, kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta sauke numfashi tana murmushi tace" Ƴata, ai ko tafiya za ki yi kin bari dai wanda ya bani amanar ki ya dawo, sannan ina zaki tafi yanzu?"
Cike da kunya da ladabi Yusrah tace" Mama, Funtuwa nake son zuwa, amma idan Allah ya amince min ko Katsina na kwana da saf...e sa...i na."
Ba ta ƙarasa maganar ta ba saboda wani irin kallo da Hajia Mama ke yi mata mai kama da tuhuma ko kallon tsabagen rashin hankali, ita ma da ta ji bata ƙarasa ba sai tace" Funtuwa? Ƴar nan ba kya sauraran labarai hala? Ke baki san irin hatsarin dake tattare a hanyoyin nan bane? Da rana ma ya aka ƙarata dake da masu tsaro? Bare kuma yanzu cikin dare?"
Sai kuma ta girgiza kai ta tausasa murya sosai tace" Faɗa min ƴata, me za ki je kiyi a Funtuwa mai mahimmanci haka da ya sa kwata kwata ba kya tunanin hatsarin da za ki iya jefa rayuwar ki a ciki?"
Saida Yusrah ta ja dogon numfashi sannan ta sauke tana kallon Hajia Maman ta ce" Ƙanena, ƙanena zan je na nemo."
Cike da kulawa ta kafe ta da idanu tace" Ɓata ya yi ne? Ko dama ƴan asalin can ne ku ɗin?"
A hankali ta sadda kan ta ta shiga faɗa Hajia Maman yadda komai ya faru, daga ƙarshe da kuka tamkar ranta zai fita ta ƙarasa ma Hajia Mama labarin nan tare da ɗorawa da" Na sani ne, rashin samun alamtawa na cewa mutuwa ce ke tunkaro su ya sa basu bani amanar Safwan ba, amma ni na sani suna ji a jikin su ne indai har aka bar shi hannuna zai samu kulawa, lokuta da dama Babanmu ba ya kiran sunan Safwan, sai dai ya kira shi da *Yayan mu*, sannan ya kan yawan kallon mu ya ce mana _"Kun ga Safwan da kuke gani? Ku riƙe ƙanan ku hannu biyu, watarana ko bayan raina shi zai riƙe mahaifiyar ku sannan ya riƙe ku ko da kuna gidajen mazajen ku ne..."_, to yau sakacina ya sa na rasa Safwan, a wajen aunty Fureira kaɗai nake da tabbaci samun shi, idan anan ma baya nan... Idan ban samu Safwan anan ba... Ya zama dole na hukunta kaina ta hanyar tarar gaban babbar motar da bata da b..."
Da sauri Hajia Mama ta kai tafin hannun mai ɗauke da gajerar carbi da baƙin lalle irin na hausa ta rufe mata baki, sai kuma ta sa ɗaya hannun ta jawo kan Yusrah ta ɗora saman cinyar ta tana daddaɓa bayan ta, ganin Yusrah ba ta ganin fuskar ta yasa ta sa yatsa ɗaya ta share ƙwallar da ta gangaro mata na tausayin ta matuƙa, ta kasa cewa komai, ta kasa furta komai haka har saida Yusrah kuka ya sa baccin da bata samu ta yi ba ya ɗauke ta kan ta a ƙafar Hajia Mama.
Daga haka maganar tafiyar ta a ranar ta fasu, dan shi kan shi Jafar da ya zo gidan ya ci abinci dan sanin kan shi ne yau gidan shi babu abinci saboda faɗan da suka yi da Tasneem, ko ta dafa ma saboda yaran shi ne babu kason shi a ciki, dan haka ma har yanzu bai nufi hanyar gidan ba, kayan shi ma da ya canza ma a mota ya canza su, kasancewar yana yawan tafiya sannan yana bayar da wanki da kan shi, hakan ya sa baya rasa kaya spy kamar dai wasu daga cikin abubuwan da suka shafi kayan gyaran mota.
*WASHE GARI*
Lallai wata rayuwar ma rayuwa jarabawa ce babba, kamar yadda aka ce *tafiya* mabuɗin ilimi, gashi dai yau Aswan Aliyu Anza shine da wanke kwanon da zai ci abinci, bayan haka ya wanke ban ɗakin da dole dai shine zai yi anfani da ita, bugu da ƙari ya haɗa da sharar ɗakin da yake zaune ciki, wannan dole ne, dole dole ne kowa da ke nan sai ya yi kowace safiya, ba maganar jiya nayi yau ba zan yi ba saboda ba dattin. Ba wai dan bai taɓa yin aikin wahala ba, dan ko zaman shi Mali ai bai ma taɓa shan wahala a rayuwar sa kamar wacce ya sha a nan ba har da kuwa wajen horar da shi zama soja, amma dake an ɗan jima ba'a yi ba, yanzu hutu ne ya gama ratsa kowace jijiya da gaɓa ta jikin shi, sai ya zama ya gaji sosai da wannan aikin da ya yi.
Ya cire rigar shi zai shiga ban ɗaki dan ya yi wanka kamar yadda ake ƙwanƙwasa musu ƙofar ɗaki da kulkin dake hannun jami'ai masu tsaron aka bubbuga ƙarafan, juyowa ya yi a nutse yana kallon mutumin da shi ne ya tashe shi da safe, yana kallo har ya sa ƙaramin makulli ya buɗe ƙaramar ƙofa mai kama da window da aka yi dan zura musu abinci ba sai an buɗe ƙofa gaba ɗaya ba.
Faranti ne na silba masu kyau guda biyu akan babban farati da kofi da kuma gorar ruwa a gefe sai ƙwai guda ɗaya da tuffa a gefe, karɓa AA ya yi yana ayyanawa a ran shi _"Shiyasa idan wasu suka shigo gidan suke mulmujewa abun su, wanda aka tsare da sunan mai laifi sai ka ganshi ɓulɓul a nutse kamar ya zo daga Saudia."_
Yana karɓa ya aje akan wani table na benci dake ɗakin, ya ɗauka mutumin ya tafi shiyasa ma yana karɓa ya juya, amma kuma yana juyowa da niyyar shiga ban ɗaki sai ya gan shi tsaye, kallon _" Ya dai malam?"_ Ya mishi yana haɗe fuska.
Da idanu mutumin ya ma AA alamar farantin abincin shi, ƙurawa fuskar shi idanu ya yi yana karantar shi, da ya gane dai farantin yake nuna masa sai ya yi niyyar juyawa, gudun samun akasi sai jami'in ya gaggauta wucewa gaba saboda wasu za su iya gani har su gane akwai wani abu, AA ma da ya yi niyyar juyawa ya kalli farantin dakatawa ua yi da ya ga mutumin ya wuce da sauri yana ɗauke kai.
Dan riƙe haɓa ya yi yana shafa gemun shi yana tunanin tabbas faranti yake nuna masa, hakan na nufin akwai wani abu a ciki kenan? Gudun kwafsawa sai kawai ya kalli ɗakin dake kallon na shi ya ga mutumin da ke ciki yana cin nashi abincin, taɓe baki kawai ya yi ya shige ban ɗaki dan yin wanka ya ji sanyi a jikin shi.
Saida ya gama kimtsawa tsaf ya kuma zauna yana cin abincin, sannan ne cikin dabara ya ɗan ɗaga faranti na farko bai ga komai ba, ya ɗaga na biyu ma babu komai a ciki, dubawa ya yi sosai amma babu komai fa, sai kawai ya ji haushi har ya yi ɗan tsaki ya cire hannu a cin abincin... Ruwa ya sha ya nufi gadon shi ya kwanta yana kallon mutumin dake fuskantar shi yana ta gantsarar tuffa ɗin nan, idanun shi a kan shi amma yana wani tunanin daban na abinda ya kawo shi gidan nan, kwatsam...
Mutumin nan ya miƙe ya nufi ɗan wurin da aka keɓe ɗan tsugul daga cikin ɗakin dan wanke kwanuka da farantin shi a hannun shi, ƙurawa farantin idanu ya yi ya tabbatar babu kofi akan nashi, da sauri ya tashi ya nufi ƙofar yana sake kallo, ya karkata kan shi yana hangen ɗakin gaba da mutumin nan ma ya tsinkayi farantin wani da alama bai taɓa abincin ba shi ma dai babu kofi, sai kuma ya juyo ya kalli nashi, da sauri ya zo ya ɗauke shi ya duba ya ga shayi ne har yanzu da zafin shi kuma.
Ƙarasawa ya yi wajen wanke waken shi kawai ya zubar da shayi a ciki, ai kuwa sai ga wani tatsitsiyar ƙaramar kwalba ɗauke da ƙaramar kwalba a ciki, gefen shi ya juya ya ga ba wanda ya kula da shi da sauri ya dawo ya aje kofi sannan ya shige ban ɗaki inda babu mai ganin shi ya warware takardar.
Rubutu rubuce kamar haka _"Misalin ƙarfe 01:30 na dare Kofa zai ga likitan shi, ya rage naka ka san yadda zaku haɗu da shi."_
Wani salihin murmushi ya saki na jin daɗi saboda har ya gama hasaso yadda zai ga uncle ɗin nashi, yaga takardar ya yi ya jefa a watar ya kunna ruwa sannan ya fito daga ban ɗakin, a nutse ya shiga wanke kwanukan shi saboda jin an fara bi layi layi ana buɗe musu ƙofa zasu kai can inda ake ajiyewa su ajiye da kan su.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*24*
Zai iya cewa faɗuwa ce ta zo daidai da zama yau da ya zamana da rana an kawo musu wake matsayin abincin su na rana, haka AA ya ɓoye shi saboda targuet ɗin da yake son cimma.
Tun azal a rayuwar sa ba ya cin wake, kai zai iya cin tuwo ko da na masara ne ma ya kwana lafiya, amma wake dai ko a miyar tuwo aka saka shi sai ya saka shi jiri mai ƙarfin gaske haɗe da ciwon cikin da amai kaɗai yake saka shi jin daidai.
Amma yana sane yau ya aje shi har dare ya yi, da wuri ya yi nafilfilin da ya saba yi saboda