Showing 102001 words to 105000 words out of 397328 words
su, Hajia kuwa zama ta yi a hankali ta ɗauki carbinta ta ci gaba da ja.
Jiki ba ƙarfi ya ƙaraso ya zauna kansa a ƙasa jikinsa a sanyaye sosai ya ce" Hajia, ki yi haƙuri dan Allah, ban san tana nan ba da ban zo ba balle mu daga maki hankali, dan Allah ki yi haƙuri Hajia."
"Jafar, lokaci ya yi da zaka dubi y'ayanka ka dubi tarbiyyar su, a kullum ina fada maka ina yiwa iyalinka uzuri saboda yanayi ne kowa da irin nasa, amma a yau zan iya faɗa maka bani da wani uzurin da zan yiwa balagaggiyar macen da za'a kirayi sallah tana zaune, ita bata tashi ta yi ba kuma bata tsawatarwa ƴaƴanta kan su je su yi ba, shin wani riba yarinyar nan ke ci a duniya? Tir da wanda zai ringa sabon Allah ba jin kunyar Allah bale na mutun, tir da wanda son zuciya zai saka ya manta wanene shi ya ringa aikata rashin mutumci yana takama, idan ita ta yi nisa bana so ta saka jikokina a ciki, yaran nan ba zasu koma gidanka ba har sai na gamsu da gidan naka, bari ka ji Jafar ko makarantar boko ba zasu je ba dan na san zata je ta ɗauke su ne, zan je da kaina makarantar a gobe da safe in ga shugabar makarantar su, idan shekarar nan zasu yi asara dan in daidaita tarbiyyar su sai dai su yi, na shirya ja da duk wanda ya shirya ja da ni, shiru shiru ba tsoro bane ina kawar da kai ne dan bana so ace na zama tsohuwar banza, idan ƙarana zaka kai saboda wannan ka maida hankali, abu ɗaya na sani in ba raina ya bar gangar jikina ba ba zan bada yaran nan ba sai na gamsu da tarbiyyar su, da addu'a da nasiha da faɗa sai sun dawo min daidai misalin yadda kimtsatsun yara suke, ka tashi ka je Allah ya bamu alkhairi."
Kansa a ƙasa dai yake, matsanancin kunya da nauyin mahaifiyarsa sun fi komai damunsa a yanzu, domin a dama sau huɗu yana zuwa neman alfarmar ta amshi yara tana nuna ba zata amshi ƴaƴansu ba su dameta da rashin kunya, akwai lokacin da ya sanar mata gidansa ya zama banda a kunna kiɗa a wuni ana ɗirkar rawa sai iface iface da wasanni, babu wani abu da zai yi alfahari a tarbiyyar da matarsa ke yiwa ya'yansa, Allah ya azurta shi da y'aya mata amma babu wani abu da ake koya masu na ribar rayuwa da zasu iya ci ko da nan zuwa gaba, amma Hajia ta nuna masa ya ringa tsawatarwa yana yin faɗa da nasiha, ta tabbata zata daidaita dan ko da zata yiwa wani wulaƙanci ban da ƴaƴan cikinta, Hajia bata san wacece Tasneem ba, yau da ta gani shi Alhamdulillah daidai kenan.
Zai yi magana Hajia ta ce"...
*PRISON*
Aiki mai sunan ƙunar baƙin wake ya saka kan shi, ta wani fanni kuma mai sauƙin aiwatarwa kamar shan ruwa, haɗarin bai wuce idan aka kama shi za'a mayar masa da tafiya baya ba, sauƙin kuma shine yadda ya yarda da kan shi da jarumtar sa. Ba tsoro ko sanyin hali bayan gama cin abinci dama su suke mayar da kwanuka wanda hakan ma wani tattaki ne da akan saka su yi madadin zama kurum, dake dare ne kuma suna tafiya ne da rakiyar jami'ai ta ko ina.
Haka ya faki idanun mutane da dama da taimakon Arif da ya je da kan shi inda masadar wutar duka gidan take ya kashe, ƙa'ida dama ba'a ɗauke wuta anan, idan kuma akasi ya sa an ɗauke babban Gen. ke akwai dake tayar da kan shi, wannan ɗaukewar wuta na faruwa gidan ya kwashi wata irin ƙara irin ta agajin gaggawa tamkar gobara ce ta tashi, sakan goma zuwa sha biyar sai kuma ƙarar gimgimemen generator ya karaɗe gidan tare da gaurayuwar haske ta ko ina, a ɗan wannan lokacin, a wannan tsirarun sakannin tuni AA ya sumar da wani jami'i Arif kuma ya ja jami'in zuwa wata kusurwa dake da duhu wasu matasan biyu suka shiga yi musu gadin shi wanda suma harkar ƙwaya ce ta shigo da su gidan. Haka suka sake sajewa cikin mutane suka mayar da kwanukan su, suna dawowa kuma wata hanyar daban ake nuna musu suna bi ta farfajiyar ɓangaren su inda yau suma saboda nishaɗantar da kawunan su zasu yi wasanni kala kala, suna ƙarasawa daga ganin yadda yau aka gyara farfajiyar ya tabbatar musu da ball za su buga kenan? AA dai ko a jikin shi bai kuma yi musu akan komai ba, wasu har sun fara buga ball ɗin Arif ya kalli AA ya masa signa da idanu alamar waɗanda suka baro kafin a lura ba sa nan, jinjina kai ya yi sannan ya fara fakar idanun jami'an wurin har waɗanda suke saman benen babban ɓangare suna ta bada tsaro.
Tsaf ya sulale daga gurin ya samu matasan nan sun cire masa kayan jami'in sun bar shi da kayan shi na ciki, da gaggawa shima ya cire na shi kayan ya saka na jami'in sannan suka nufi filin ball shi kuma ya haura ta katangar da ta raba ɓangaren su da na manya bayan ya saka rigar shi da ya cire yana ware wayoyin dake iya raunata mutum a katangar, amma duk da haka sai da bayan shi ya yage da kuma damatsen shi duk da kuma yana da riga a jikin shi.
Wani irin sanyayyan iska ne ya fara yi masa maraba, da mamakin wannan tattausan iska ya shiga kallon shukokin da sune suka haddasa wannan ni'ima a wurin, yana shirin tsallaka shukokin ya fita wani jami'i ya zo gilmawa tare da wani babban mutum, ƙara lafewa ya yi a ciki saida suka ɓace ɓat ya fito, cikin sanɗa da taka tsantsan ya bi hanyar da yake tunanin nan ne hanyar shiga ɓangaren, ai kuwa yana shiga kwanar ya hangi ƴan firisna ɗin wasu a zaune kan kujera, wasu kuma suna buga irin ƙwallon nan ta hannu daidai da yanayin jikin su, wasu ma ball suke yi da dai sauran su.
A hankalce ya kula da jami'an ba wai suna tare da su bane daf, a'a suna shawagi ne lokaci lokaci kawai dan kulawa da su, wannan ya bashi damar tunkarar wurin zaman kai tsaye saboda yana sanye da kakin jami'an wurin. Wasu mashahuran mutane ya fara cin karo da su wanda wasu ma shi kam har ya manta da su a duniya, wasu kuma da ganin su kasan ba wai hukunta su ake akan laifin su ba, kawai dai an shamakance su ne saboda kar al'umma ta yi ƙorafi akan haka, dan wasu a sanin shi da su sun tsufa sosai, amma dake kulawa suke samu tsufan ya ƙi bayyana gaba ɗaya idan dai ba ciwo suke ba da bai kwantar da su ba. Haka ya ci gaba da shawagi kamar jami'an wanda idan suka kusa haɗewa da wani jami'i sai ya kawar da fuska ko ya kauce hanya har ya dangane da katanga, sai gashi ya gama dubawa tsaf bai ga uncle Kofa ba.
Da jin haushi ya juyo zai sake komawa ya kuma ƙara dubawa, sai ga wani dattijo ya fito daga ƙofar ɓangaren tare da jami'i bayan shi mai cikar kamala da haiba, *wata* irin nauyayyar ajiyar zuciya AA ya sauke saboda ganin fuskar uncle Kofa, duk abun nan da yake yi bai ji yana da yarda akan uncle ɗin ba sai yanzu da ya sake kallon sahihiyar fuskar shi.
Bai yarda ya gan shi ba amma haka ya dinga bin su har jami'in ya kai shi wajen shukokin nan da ya baro na farko ya zauna sannan ya ga ya bashi jarida, murmushin da uncle ɗin ya yi ya kalli jami'in bakin shi ya motsa ya tabbatarwa AA godiya ya masa, yana ganin jami'in ya bar wurin shi kuma ya tunkara har ya ƙarasa.
Gaban shi ya tsaya ya furta "Barka uncle?"
Da sauri ya janye jaridar da ta masa shamaki da ganin mutum yana mai zubawa wanda yake tsammani idanu, da ɗumbun mamaki ya kalli dama da hagun shi sannan ya kalli AA yace "Oga? Kai ne a nan?"
Wani salihin murmushi AA ya saki, uncle Kofa shine mutumin da ya saka masa sunan oga kuma yake kiran sa da sunan, a nutse ya saki jikin shi yana takowa kusan shi yace "Ni ne uncle, ya kake?"
Kawar da kai uncle Kofa ɗin ya yi tare da sake mayar da jaridar sa yadda take ya amsa da "Kamar yadda ka gani Oga, ya kake kai ma?"
A ladabce yace "Ba daɗi, sai yanzu da na gan ka."
Sai kuma ya tattaka ya ɗan tsaya nesa kaɗan da uncle ɗin tare da bawa uncle ɗin baya kamar ba magana suke ba yace "Ba lokaci uncle, dan kai kawai na shigo gidan nan, me ya faru da kai? Me ka aikata da ya sa aka kawo ka nan?"
Duk da ya ji mamaki amma bai nuna masa ba yace "Dan ni kawai? Me ya sa to?"
Amsa ya bashi da "Kawu bincike nake yi akan wata *badaƙala* dake faruwa wacce sam bata min ba, bincikena ya yi nisan da har aka tabbatar min kai ne mai ƙarƙare sa indai mun haɗu, please ka sanar da ni uncle kafin lokaci ya ƙure, na maka alƙawari fita daga nan idan har bisa zalinci aka kama ka."
Murmushi uncle Kofa ya yi kamar suna ganin juna yace" Me ka ke so ka sani Oga?"
Hannaye ya zuba aljihu ya daidaita tsayuwar sa yace" Wane kuɗi ne suke shiga da fita a asibiti? Sannan me ka sani da ake aikatawa ba daidai ba? Sannan me ye haɗin Alhaji Buza da kuɗin da suka fita daga asibitin Aba?"
Murmushi uncle Kofa ya yi na jin daɗi, ya sani dama komai daren daɗewa wata rana dai gaskiya za ta yi halin ta, kamar mai karatun jarida yace masa" Oga, wannan mummunan harƙallar dake faruwa ita ce ta kawo ni gidan nan, abinda yake tsakani mai yawan gaske ne, sai dai kuma a dunƙule yake cikin juna, sanin kan ka ne mahaifin ka bai da amini kuma abokin shawara sama da ni da kuma Chef, ina da sani sosai akan harkokin shi da suka shafi kasuwancin sa da siyasar sa, kaso mafi girma na kasuwancin sa a nan nine mai kula da shi, sai dai ban da asibitin da ƙanin sa Hamat yake kulawa dan ba harkata bace, amma kasan akwai wani abu da idan ubangiji ya so fito da shi kowa ya gani, sai ya yi walƙiya ya haska komai ɗin ya fito, haka ce ta kasance da wannan asibiti..."
Ɗan sauke jaridar ya yi kaɗan ganin AA ya yi gaba sosai saboda ganin tahowar wani jami'i, saida ya yi nisa sannan ya dawo ya tsaya inda yake a farko, dan haka uncle Kofa ya ci gaba da cewa" Oga Aswan asibitin mahaifin ka a yanzu dai na tabbata ba asibiti bace, a zahiri za ta iya amsa wannan sunan, amma a baɗini matattara aikata miyagun laifuka ce, Aswan ana zalintar bayin Allah masu ƙaramin ƙarfi da ma masu ƙarfin a wannan asibitin da sunan tiyata, a yadda mahaifin ka yake sakawa ana odar magani ba'a haka ake siyar da shi a asibitin nan ba, sannan akan ɗibi wani kaso ana siyar da shi ga ɓata garin mutane musamman ma kayan aiki, bugu da ƙari..."
Tunkarowar wani jami'i inda AA yake ya sa da gaggawa ya dawo baya yana cewa" Uncle Kofa duk wa ye mai wannan alhakin? Aba ne? Da sanin Abana hakan yake faruwa?"
Gyara zama uncle Kofa ya yi yace" Kai ma kasan mahaifin ka ba zai taɓa aikata haka ba, saidai wasu makusantansa ne da a duniya ba ya da sama da su suke masa wannan bita da ƙulli, hakan da na gano ne ya sa nayi yunƙurin sanar da shi, amma kafin na isa inda Elhaj yake har an tsareni a hanya cike da tuhumar ci da ceto da yarfen wai bankina ta damfara ce."
Da gaggawa AA yace" Uncle su waye? Su waye suke aikata haka?"
Girgiza kai ya yi shima da sauri yace" Ba zan faɗa maka su ba, amma ka yi bincike ka gano, sannan ka fara binciken nan tun daga cikin gidan ku, dan idan na faɗa maka rayuwar mahaifin ka tana cikin haɗari kar kayi gardama, sanin ba zan tanƙwaru ga uban kowa ba akan cutar da mahaifin ka ya sa nake nan a ɗaure, hankalina kuma kullum yana kan shi, amma yanzu tunda na san *ɗan zaki* ya shiga lamarin, to zan kwanta nayi bacci dan nasan ba abinda zai samu aminina da ahalinsa, ko iya haka ma ya isheni farin ciki."
A hankali AA ya fara tafiya yana ɗan taune leɓe yace" Uncle zan tafi, wataƙila gobe ko jibi bana gidan nan, amma ka sani ba zan manta da kai ba, zan yi duk yadda zakayi ka bar gidan nan ba da jimawa ba."
Murmushi ya sakar masa yace" Allah ya baka iko Oga, ka faɗawa iyalina kar zunɗen jama'a ya dame su, ban aikata komai ba, kuma gaskiya za ta yi halin ta in sha Allah."
"In sha Allah." AA ya faɗa yana ɗan ƙara sassarfa zai bar wurin, sai kuma ya juyo yana tafiya da baya baya yace "Uncle Kofa, Sani Galadima kuwa yana cikin gidan nan?"
Ƴar dariya uncle ɗin ya yi yace "Sani Galadima yana nan, sai dai yana cikin halin matsananciyar jinya, ko shakka babu suna cike takardun yadda za'a fitar da shi daga nan ne a damƙa shi ga iyalin sa tunda ba ɗaurin rai da rai bane aka masa, sun san kuma akwai babbar hatsaniya idan ya mutu a hannun su."
Shima AA dariyar ya yi yana ci gaba da barin wurin ya ɗago murya yace" Tabbas kuwa, dan ɗaya daga cikin ƴaƴan sa ma yana nan dan mahaifin sa ne kawai, sannan kuma *ga ni nima*, duk zamu hargitsa ko ina."
Hannu uncle Kofa ya ɗaga masa ya mishi bye bye shi ma kuma haka kafin ya juya da gudu gudu ya bar gurin cike da farin cikin ya samu abinda yake so ba tare da wata matsala ba.
Inda suka bar jami'in nan ya koma yana nan har lokacin, amma daga yadda ya ga Arif wurin shi riƙe da wani icce, sai kawai ya kalle shi ya masa alama da idanu _"Ya akayi?"_
Cike da wofantar da lamarin Arif yace" Shegen farkawa yanyi, shine na sake kwantar da shi."
Tsura masa idanu AA ya yi yana dariya kawai yana ganin wani mai kama da shi haka wajen ɗaukar kasada da rayuwa, cire kayan jami'in ya yi ya mayar da nashi sannan suka maidawa jami'in nasa suka bar shi nan yashe, suna isa filin da ake ball ɗin har an fara musu busa kan kowa ya kama hanyar ɗakin shi, tsaki AA ya yi a ranshi ya ayyana _"Mahaukatan banza."_ Sannan suka nufi ɗakunan nasu da rakiyar jami'ai shi da Arif.
_*SAJEERAH*_🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*28*
Zai yi magana Hajia Zainab ta ce" Ka je kawai, Allah ya tashe mu lafiya."
Ajiyar zuciya ya sauke ya juya a hankali ya fice bayan ya yi mata sai da safe, ɗakin da yaran suka shiga Hajia ta nufa, ƙirjinta har wani zafi yake yi da ƙuna na ɓacin rai, sai sunayen Allah take kamawa dan ta samu zuciyarta ta yi sanyi, tana shiga ta tarda su biyun na sallah ɗayar kuwa sai faman kokowa take da su suna dakatar da ita, tana ganin shigowar hajiyar ta tayar da sallar ita ma, a dole ta zauna ta tsare su dan ta tabbata idan ta fita ba sallar zasu yi ba, kai sallolin nasu kansu bata yarda da su ba, ta tabbata Tasneem bata da lokacin zama ta duba sallar yaro, ta abubuwan dake gabanta ta yi ko ta tarbiyyar ƴaƴa?
A ɗakin su Fatila kuwa tunda muryar Tasneem ta fara tashi sama sama suka yi tsuru tsuru suna sauraro, ba ma kamar Fatila da ta gama rayuwa da shakku da tsoron Tasneem, kuma a yanayin nan na Yusrah da take gani bata tunanin in har zata iya maganin Tasneem, idan har Allah ya yi Yayanta zai auri Yusrah kuwa tabbas sai sun taya ta yaƙi, dan kuwa Tasneem tsaf zata iya kashe ta, kai subhanallah! Ita bata taɓa ganin mace marar imani irin Tasneem ba, bata tsoron kowa bata shakkar kowa, to wacce ta shaƙi mijinta wa zata ragawa? Sun yi daki in daka da aunty Ummi, basa ga maciji da uwar amarya, ita kowama abokin gabarta ne abokin su raba hali ne.
Yanayin muryar Hajia da irin abinda ta faɗa ya saka Yusrah sauke idanuwanta ƙasa haɗi da sauke ajiyar zuciya, domin ba zata so Tasneem ta tardota ɗaki ta ɗora mata wani ɓacin