Showing 291001 words to 294000 words out of 397328 words
ɗaga maki hankali ki yi zamanki, kin ji?"
Da sauri aunty Intisar bayan ta zaro ido ta ɗan girgiza kai cike da matsanancin mamakin yaushe ma ya fita ya bar gidan daga zaman nan da aka yi har ya yi wannan ta'asar, la'ilaha illalah! Kai anya kuwa Akhi AA zai iya barin ƴaƴan cikin sa su yi zaman aure? Yanzu mijin Ule yake nufin ya zane kenan? Amma da sauri ta amsa ta ce" A'a Akhi, zan je in sha Allah ba komai."
Ya ɗan taɓe baki a ransa yana ayyana _' Banza mai son mijin tsiya.'_
A bayyane kuwa sai yace" Ok, idan kin san kin saka ƙafarki ki tabbatar da kin jure duk abinda zai faru, in ki ka yarda na ji Intisar decision ɗina za ta zama ta ƙarshe kuma ba zan waiwaya ba na rantse maki."
Intisar ta zauna bakin gadon tana jimƙe abin gadon ta ce" In sha Allah Akhi zan jure, Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana, Allah ya ƙara ɗaukaka da rufin asiri Akhi."
Ya yi ɗan murmushi yana ɗauke kansa daga inda Arif ke nuna alamun so ya yi su sumar da shi AA ɗin ya hana, ya rage muryarsa sosai saboda ƴan sa ido ya ce" Ita wannan na bar mata ɗana yau kaɗai aro ba dan halinta ba, ki faɗa mata ina bashi abinci ƙarfe goma saboda kar ya ji yunwar cikin dare, ina masa bruch da kaina, ina shirya shi barci, ina masa addu'a sosai ta tsari, kuma ina karanta masa story na manzanni da sahabbai na musulunci, ta tabbatar ta yi duka kaf har ya yi barci, ta daidaita sanyin ac kuma kar ta saki ta kwana gado ɗaya da ɗana, ban son shirme, sannan ta tabbatar da ta ci abinci kafin ta kwanta, kin fahimta?"
Intisar kam abin na daf da girmamar tunaninta, sai dai ko da wasa bata yi gardama ko jan zancen ba dan ta san ba wajen yin hakan bane, ita dai da girmamawa ainun take amsa babban yayansu har ya gama ya katse kiran, samun kanta ta yi da zubawa Yusrah ido wacce ta taƙaita doguwar addu'ar ta ta ta miƙe ta nufo aunty Intisar bayan ta cire hijabinta tana ninkewa haɗi da sakin fuskarta ainun ta ƙaraso daf da ita ta zauna tana faɗin" Aunty, baki tafi ba? Dama ina son yin magana da ke kuwa."
Aunty Intisar ta yi murmushi yalwatacce a ranta ta ayyana _' Ina da shakku a kan maganar haɗin auren nan, auren nan ba haɗi bane, auren nan tabbas da wani abu a ƙasa, ta yiwu faɗuwa ce ta zowa Akhi daidai da zama, na in yarda cewar Akhi baya ra'ayin auren nan, dan kuwa da ace baya ra'ayinsa wallahi babu wanda ya isa ya saka masa ra'ayinsa, ba wai ana nufin ba'a isa a saka shi ya amshi auren ba, zai amshi auren dan an isa da shi mutum ne mai biyayya wa iyayensa sosai sai dai idan har abin bai masa ba wallahi da kanta zata nemi ya saketa, dan kuwa sai ta gwammace kiɗa da karatu.'_
Fuskarta da murmushin nan ta ce" A'a ban tafi ba Aunty, faɗa min me na samu?"
Yusrah ta zaro ido sannan ta yatsina fuska ta ce" Kai dan Allah aunty ki rufa min asiri ki daina kirana da auntyn nan, yawwa dama cewa na yi ina so in nemi shawara, aunty kin ga kuɗin aikin nan da muka je kuwa? Ni kuɗin sai da suka tsoratani, Yaya Mubarak ya ce duk lokacin da na nutsu sai a saka a bankina yana cikin ƙoƙarin daidaita lamarin bankin ne, aunty ga albashina na ɗauka shi ma da kauri sosai, bayan wannan *wai shi wannan mai neman rigimar* ya kuma saka min kuɗin kula da shi da na yi a can da ya yi rashin lafiya, aunty ga waɗannan kyautukan dai ni na rasa ma waɗannan kuɗaɗen sai kace wacce ake bani rabona? Yanzu dai shawarar da na ce zan nema aunty a kan Aunty Furera ne da kuma Iya Abu da dai dangi, ina so su dangi a musu ihsani mai kyau wanda zasu ji daɗi, aunty Furera kuwa aunty bata da ƙarfi sosai, wallahi ƙoƙari ne take yi sosai da sosai, shine na ce me ya dace a yi mata a cikin kuɗaɗen? Ita kuwa Iya Abu jari ne na ce zan ƙara mata in har kuɗin sun isa."
Aunty Intisar ta yi dariya a tausashe ta ce" Ma sha Allah, ƙwarai kin yi tunani mai kyau Yusrah, dama Allah ya ce idan iyayen ka sun gushe kar ka daina hidimtawa ƴan uwansu, in sha Allah ba zaki taɓa taɓewa ba, Yusrah kuɗaɗen nan fa suna da yawa gaskiya, na wajena da na wajen Yaya Humed Aba ya ce gida zai siya maki da su, na wajen twins ne aka ba Anna aka ce ta yi miki tanadin gold ki ajiye abinki saboda rayuwa, to kin ga kuɗin tafiyarki zasu isheki yin abubuwan nan da kika zana, ko ba zasu isa ba sai in ƙara, ina ganin aunty Furera jari za'a girka mata mai kaurin gaske sannan a samawa mijinta shima jari na kirki wanda in sha Allah rayuwa zata yi musu sauƙi, wannan kuwa aikin Akhi ne dan na ji Anna fa na faɗin sai sun zauna da shi kan abubuwan nan, kar ki wani damu in sha Allah komai zai je dai-dai, kin ji?"
Yusrah ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ɗora kanta gefen kafaɗar aunty Intisar, sai ga hawaye na tsiyaya daga gurbin idanuwanta, ta riƙe hannun Aunty Intisar muryarta a shaƙe ta ce" Ba zan taɓa gushewa da yi muku addu'a ba, tabbas Allah shine gatan bawa, na rasa iyaye da ƴar uwa, ya bani iyaye da ƴan uwa, Allah ya jiƙan su Baba Allah ya sa sun huta, ku kuwa Allah ya ƙara ɗaukaka da girma, ya tsare gaba da baya aunty."
Aunty Intisar ta yi ƴar dariya ta ɗagota tana share mata hawayenta ta ce" Ba zaki daina kukan nan ba ko? So ki ke yi Akhi ya wanka min mari a gabanki kuma ya ce ki yi abinda zaki yi ko?"
Ido ta zaro ta yi ƴar dariya kamar yadda Intisar ke yi ta ce" Mari? Ai wallahi ba ma zai tarka ba, taɓdijam!"
Intisar ta gyaɗa kai ta ce" Ba ki san wa ye mijinki ba, i swear baki san waye mijinki ba, sai ya tattakani in na yi wasa kuma babu abinda ubana da babata zasu yi, kin ji fa wai ko mijin Hauwa ya yi wani laifi ko an ɗan hukunta shi? Yanzu ya ke cewa in na san ba zan iya jurewa ba kar in je gidan, in na zauna hakan na nufin ya ƙara amsoni fa? Ko tausayin Yaya Mubarak Akhi ba ya ji."
Yusrah ta dafe goshi cike da mamaki ta ce" Aunty, ba wani an ɗan hukunta shi wallahi ya zane mata miji, a gabana ya ce ba zai yafe ba sai ya hayyace su fa, a gabana ya ce masa ok taƙamarsa ya shige america ya zama ƙwallon ɗan iska? Zai shigo Nijar wai fita sai ta gagareshi."
Intisar ta rafka tagumi ta ce" Na shiga uku da Akhi, yanzu ya ya zamu ƙare da mutanen nan?"
Yusrah ta yi shiru kafin ta ce" Ko in tashi mu je aunty?"
Intisar ta zaro ido tana miƙewa ta ce" Ki rufa min asiri, kin ji saƙon da aka ce in faɗa maki..."
Ta kwashe komai ta faɗa mata tana dariya ta ce" Ki yi zamanki ki rufa min asiri, bari in je ki tayani da adu'a Allah ya sanyaya fushin Hajia dan wallahi ƴar nan tata ta san lagonta sosai, ta san hanyar da zata bi ta haddasa maka fitina tana nesa ma balle gata ga Hajia, bari in je."
Yusrah kam jikinta a mace yake murus, tabbas ta san yau sai inda ƙarfin hajia ya ƙare, sai ta fitini kowa a gidan nan, haushin AA ya ƙara kamata dama da ta shigo da mugun haushinsa ta shigo, ga kuma wannan, sai kawai ta yi ƙwafa ta tashi ta yarda Safwan bayan ta zumbula hijabinta ta kama shi ya tashi suka nufi wajen Anna da tagwaye dan ya musu sai da safe domin so take yi ya kwana wajen uncle Sulaimane, tana so ya je masa shi ma ya dan ji ɗuminsa, ai kuwa tana zuwa Manal ta miƙe ta ce zata rakata, har da su ƙara fesa turare da su shinshinar baki sannan ta saka hijab ɗin ita ma suka fito suka nufi part ɗin da uncle Sulaimane yake, ita dai Yusrah ta yi dariya a ranta tana binsu a hankali so take yi sai ta gama kama su ta fashe su a fili kowa ya gansu.
*G. MUBARAK*
Aunty Intisar ta iso gida cikin minti talatin, yaran a gidan Anna ta barsu domin da ta sanarwa Anna sai ta nuna ta barsu a can kawai dan yaren kansu tunda auntyn nasu ta sauka a gidan suka zama basu da sakewa a can ko kaɗan, shi yasa duk idan zata taho take zuwa da su ta koma da su, yanzu kuwa Anna ta ce a barsu zata kirayi Mubarak ɗin da kanta ya sanar masa zasu kwana a nan, jiki ba ƙarfi ta nufi ɓangaren Hajia dan ta fi so ta fara zuwa Hajia ta yi faɗan ta ta more in yaso sai ta je ta yi wanka ta ci abinci, gashi cikinta ya fara turawa a yanzu ba komai take iya ɗauka ba nan da nan hankalinta ke tashi in aka yi wani abun.
A nutse ta ƙarasa part ɗin na Hajia ta yi sallama tun daga ƙofa sannan ta shige, dakatawa ta yi tana kallo da kyau, nan ta gane Hajiar ce zaune a filin gidan sai faman fifitu take tana kore sauro, tausayin Hajiar ya kamata, dan kuwa tunda Hauwa ta zo take ƙure ac sosai ita da ƴaƴanta da mijinta a falon na Hajia, Hajiar kuwa sai ta kasa zama ga ciwon jiki na sanyin ac ga tarin kunyar irin rungume rungumen da suke yi Hauwa da mijinta, ga ƴaƴanta basu da aiki sai rashin kunya kala kala kamar ba ƴaƴan musulmai ba, shigarsu kanta abin mamaki da tsoro ne, wai basa son zafi, Prince kullum cikin kuka yake shi a koma america shi baya son ƙauyen nan ba zai iya rayuwa ba a ciki, abu dai kuma da kamar wuya dan kuwa ƙauye ta zama dole inda zasu rayu a yanzu basu isa su koma america ba kai tsaye sai dai idan su sun girma sa je.
Duƙawa ta yi har ƙasa bayan ta cire takalminta ta hau tabarmar da kula sosai ta ce" Hajia ashe kece a nan ɗin, ina yini, ina gajiya?"
Hajia ta ɗauke kai bayan ta dantse leɓe, sai kuma ta saki ganin Yaya Mubarak ya shigo domin shigowarsu ta yi ta jira dama sai ta ga shiru bata je ɓangaren su ba shine ya fito da sauri ya nufo nan ɗin saboda abinda ke faruwa.
Hajia ta dube shi ta ɗaga murya sosai ta ce" Ai gwara da ka zo, yau so nake yi a yita ta ƙare Mubarak, Mubarak so nake yi matarka ta faɗa min abinda na kashe mata ita da danginta, Mubarak ina so Intisar ta sanar min abinda yake faruwa da ƙiyayya mai tsanani haka ta shiga tsakanina da danginta." Ɗaga Muryar da ta yi ya sa Hauwa fitowa da sauri, ƴaƴanta na biye da ita.
Hajia ta ci gaba da faɗin " Kana ji kana gani aka zo aka tirani kan auren yarinyar da kake riƙo, dan kawai na ce ba za'a yi ba shine Yayanta ya ɗauka ya aure aka haɗa ni rigima da auta, a yanzu auta kwanana biyu yau ban ganshi ba da idanuwana, an rabani da ɗana dan son zuciya, sannan aka zo aka zane min siriki? Me ake so da ni ne ake son ƙarar min da ahali? Shikenan dan an fi ƙarfin mu sai a ringa cutar mu? Shikenan dan ana riƙe da ƙasa sai a mayar da mu shashashu? Yau ina so Intisar ki faɗa min me na yiwa Yayanki da yake son kasheni da hawan jini bayan ni riƙe masa ƙanwa na yi da zuciya ɗaya, ina zaune da ke da zuciya ɗaya, ina son abinda kike so shine kika hannawa Bilalu yarinyar nan kika ba Yayanki?"
Hauwa ta tare maganar da faɗin" Hajia, ki bar maganar wai Bilal, Bilal saurayi ne cikakke ko wace ƴa ya ce yana so wallahi za'a bashi ne ba gardama ba komai, a yi maganar shubidy da Yayanta ya zane, wallahi Hajia zan rama a kanta idan yaso sai ya gane abinda na ji, zan rotsa mata wani abin da zai canza mata kamani idan ya so sai ya gane ba'a taɓa min shubidy!"
Mubarak ya kalleta da sauri cike da mamaki da ita da ƴaƴanta har yana kama haɓa, rai ɓace ya nunata da yatsa yace" Ashe rashin kunyar taki har ta kai can? Ashe baki da mutumci yarinyar nan? Intisar ɗin zaki daka a kan mashayi? Oh ko da yake ƙwaƙwalwar taki ta zama irin tasa ba zan yi mamaki ba Uwale, amma bari ki ji, kin san Allah ko zagi? Ko zagin matata kika yi sai na baki haƙdorinki a hannu, ke babu wanda bai iya rashin mutumci ba, albarkacin mai daraja kike ci ya sa nake kauda kai ina cin duk wani rashin ɗa'arki."
Ya sassauta ransa ɓace kafin ya ci gaba da faɗan sama sama ya ce" Duk wani shara idan aka kwaso ni ne ko Intisar, yau har ya zama ke ƙanwata ki ke cewa zaki daki Intisar? To bari ki ji da sai na rikita maki lissafi da duka a gidan nan kafin ki haɗu da sha kundum uban tafiya, Uwale ba zaki san ɗaga maku ƙafa ake yi ba sai kin taɓa lafiyar yarinyar nan, wallahi a nan zaki ga waye Yayanta a gabanki, Allah ba zai ji nauyin kowa ba zai shigo har nan ya canza maki kamanni kuma babu abinda aka isa a yi dan duk inda kike tunanin zaku kama ya rigayeku, ƙarshe tsaf zai miƙa wancen lajamun hannun sojawan amerika a kai shi ya yi kason wiwin da aka kama a motarsa!"
A zabure Hajia ta kalli yaya Mubarak, da idanuwanta a rufe suke ruf, yanzu ta buɗe ta kalle shi jikinta na kwasar rawa, shi kuwa ransa ya gama ɓacewa ya ce" Kuma idan kina tune nan ai ba gidan gado bane, ba zan kuma lamunta uwata a nan tana shan cizon sauro ku kuna ciki kuna bushe bushe ba, gobe da sassafe ku shirya zaku wuce gidan da zan baku ku zauna idan ya so sai ya yiwa ƙasa shawara ko ya nemi aikin yi ko ya ci gaba da rayuwar america, abinda na sani ɗaya ne ya riga ya haɗu da karnukan dare wallahi in dai ya fita cikin gari sai sun zane marar tarbiyya."
Aunty Intisar da sauri ta haɗe hannayenta a sanyaye ta ce" Yaya dan Allah ka bari, Hajia dan Allah ki yi haƙuri ki yafe mana, wallahi ban san da abin nan ba sai ɗazu, kuma in sha Allah zan faɗawa Aba zai yi masa magana ba za'a sake ba Hajia dan Allah ki yi haƙuri."
Mubarak cike da tausaya mata ya miƙar da ita ya ce" Wuce mu je ki huta."
Hajia ta sake zaro ido tana kallon ikon Allah, Intisar ta tirje ƙasa ƙasa sosai ta ce" Allah ya kiyaye, wani irin hutu zan yi yau ka yiwa Hajia abinda baka taɓa yi ba? A gabanta zaka miƙar da ni ka ce in je in huta? Hajia fa uwarmu ce, ta isa da mu yasa ta yi haka, wallahi ka rufawa kanka asiri ka rufa min mu bata haƙuri saboda bamu san ko ma waye ba."
Da sauri ta janye ta dawo ta duƙa gaban Hajia a tausashe ta ce" Hajia, dan Allah ki yi haƙuri Hajia, ki yafe mana."
Jikinsa ne shi ma ya mutu sosai, ya dawo jiki a mace ya duƙa gaban Hajia kansa a ƙasa, ya yi iya yinsa dan ya jure amma ya kasa a hankali ya fashe da kuka ya sake duƙawa sosai a gaban Hajia, hakan ya sa Intisar fashewa da kukan ita ma ta rintse idanuwanta kanta a ƙasa, muryarsa na rawa sosai ya ce" Hajia dan Allah ki yafe min idan na ɓata maki, dan Allah Hajia."
Hajia hankalinta ya tashi ainun, kuma yau ɗaya Allah ya nuna mata tabbas da ace Intisar bata nusar da mijinta da du haƙurin Mubarak da tuni ya aikata wani abin da za'a ce dama ba'a ƙure mai haƙuri, nauyi sosai ya dirar mata a zuciya
rabonta da ganinsa yana kuka har ta manta, anya ba tun rasuwar mahaifinsa ba kuwa?
Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Tana ji tana gani yarinyar nan zata sa ta ɓatawa yaron da ya fi tausayinta da taimaka mata a cikin ƴaƴa ta riƙe wa? Komai nata shine, duk wata wahalarta shine, yau har aka kaishi maƙura ya faɗi abubuwa irin waɗannan? Lalle ta kai Mubarak ɗin ta ƙarshe ta hanyar wulaƙanta matarsa, babu abinda ya fi girgizata jin wai ashe miyagun ƙwaya aka kama mijin Hauwa da shi ya sa suka yi fitar higa? Haba gaske yaron gaba ɗaya ke bata tsoro, laɓewa take yi in ya shigo dan tsoron sa take ji, kuma abinda ya bata tsoro ya ƙi neman danginsa sam, wai ya ce bashi da kowa, shin ina Hauwa ta lalubo wannan bawan Allahn ne? Ce mata fa ta yi wai sharri aka masa shine aka ce za'a kashe shi su kuwa suka figo suka gudo, ashe ƙarya Hauwa ta gillara mata?
Jiki a mace sosai ta ce" Mubarak daina kukan haka ka ji? Ku je ɓangaren ku Allah ya muku albarka, tashi ku je ƴar nan Allah ya raba lafiya, sannan maganar da na hanaka tafiya nan da kwana ukun nan ka je ka fara shiri na yafe maka duniya da ƙiyama Allah ya tsare ku yi tafiyarku Allah ya tsare ka ji ɗan nan."
Yaya Mubarak ya ringa sauke ajiyar zuciya ya ringa godiya sannan ya miƙe ya fara tafiya,