Showing 183001 words to 186000 words out of 397328 words
zamu ringa yi dole, daga su zamu sallameku idan kun koma wajen Docter Siddik zai ci gaba, yanzu idan kuna so kunna iya leƙo shi sau ɗaya a wuni, idan ba kwa so ku yi zamanku, dan zuwan ma bashi da wani anfani dan ko kun zo daga nesa ne kawai zan baku wannan damar, zai warke sumul ku ci gaba da masa fatan waraka."
Aswan kam kasa gane abinda ake nufi ya yi, yanayin sa da tashin hankali ya ce" Docter, ka ce zai farka ɗazu, zan yi magana da shi, yanzu kuma kace a haka zai zauna har sai ya kwana biyar? Bai buɗa idanuwansa ba? Kun jajjona masa kayan aikin nan kamar matacce? Ƙarar injin can bana son ta, ku farkar da shi mana."
Yusrah ta sauke ajiyar zuciya, kasantuwar a jere suka zauna ita da kanta bata ankara ba su dai burinsu su ji bayanan likita ya sakata juyowa a tausashe sosai ta ce" Ka yi haƙuri, aikin haka yake dama, kuma nan na ga suna da abubuwan ci gaba sosai fiye da wani wajen, a haka fa yake baya jin zafin komai, idan aka farkar maka da shi yanzu yanzu zafin da zai ziyarce shi bana tunanin in kai ma zaka iya jurewa, a haka ɗin har zuwa kwana biyar ɗin ya fi, daga nan ɗin ma idan aka farkar da shi fa zaka ga duk yana neman fita a hayyacinsa, baya ne, in ba'a yi da gaske ba baya taɓa samun sauƙi, ka yi haƙuri in sha Allah idan ka jure zaka ga ya samu lafiya sosai, kar ka sa a tashe shi yanzu yanzu dan ta yiwu idan zafin ciwo ya sa ya motsa da ƙarfi sai sun mayar da shi sun sake aikin."
Wata irin ajiyar zuciya ta ƙwace masa ta shiga halin ruɗu, kansa ya ringa ɗaukan zafi, dama hanjin cikinsa ya wani irin kanannaɗewa ko ruwa fa yau bai sha ba kuma a tsaye yake a kan ƙafafuwansa, fargabarsa ma kaɗai ta isa ta dame shi, a hankali ya janye idanuwansa daga fuskarta yana ji docter na sake maimaita masa bayanan da ta masa da turanci, a saman leɓensa kawai ya iya furta" Allah ya bashi lafiya, thank you."
Docter ya miƙe ya basu damar sake jimawa da shi kaɗan sannan ya juya ya tafi, sun ɗan sake jimawar, cikin shiru idanuwansu a kansa sai addu'a suke yi masa suna tofa masa, a yanzu ya fita damuwa, shi bai karanci aikin asibiti ba, hakan ya sa yake kallon wannan yanayi da aka yiwa yaronsa kamar yaron na cikin mugun ciwo ne.
Ita kuwa a yanzu ta samu salama kaɗan sai fatan ganin farkawarsa gaba ɗaya, dan ta sani ne idan Allah ya sa ya farka gaba ɗaya in sha Allah shikenan sauƙi kam ya samu sai sauran abinda ya rage. Shi ya fara miƙewa ya ɗan kalleta sannan ya juya a nutse yana takawa.
Da sauri ta miƙe tana rarumar jakarta ta bi bayansa bayan ta rufo ɗakin ta ringa ɗaga ƙafa da ɗan gudu gudu dan kar ya ɓacewa ganin ta domin ta san idan ya ɓace mata a garin nan ta shiga uku, duk da ta san tafiya tare da shi ɗin ma a wata ukun take, sai dai gwara shi ɗin bahaushe ne kuma musulmi da waɗannan manyan turawan da take gani, mutanen garin manyan jiki gare su daga mazan har matan ma sha Allah.
A cikin accenseur ɗin hotel ɗin bayan sun iso ta ga ruwan sanyi a hannunsa a riƙe, ta so hana shi sha domin ta ga kamar ya jima bai ci komai ba, sai dai tunanin ai ba yaro bane, da kuma tunanin ko da ta hana shin ba hanuwa zai yi ba ya sa ta yi shiru har suka fito ya miƙa mata wani ky da wata takarda mai ɗauke da numbar hotel ɗin ya riƙe nasa yana gaba tana biye da shi tana karanta takardar kanta a ƙasa bata san ya tsaya ya kafa kai da ruwan nan ba ta zo ta gwara kanta da bayansa har tana sakin takardar hannunta.
da sauri ta raruma tana furta " Wasshhh, ka gwara min kaina."
Da mamaki ya kalleta dan tunda ta gwarun masan sai da abin butalin ya bugun masa leɓe, sai kuma muryarta tana faɗin ya gwarun mata, sake ƙyaleta ya yi, ya kai zuciyarsa nesa sosai, balle yanzu da wani irin gumi ke karyo masa jikinsa na neman ɗaukan rawa, juwa na son kayar da shi ga ciwon kai sai ya maida komai ba komai ba ya ƙarasa ya saka ky ɗin sa ya buɗe, masu aikin hotel ɗin na janye da akwatunansu aka shigar masa da tasa ɗakin sa, ita ma ta buɗe nata ɗakin bayan mai aikin ya nuna mata tana yatsina baki ta juyo zata yi masa magana a kan maganar zuwa asibiti ta ga ya jimƙe cikinsa da hannunsa ɗaya, da ɗayan hannun kuwa ya damƙi ƙofar ɗakin da ƙyar ya ja ƙafarsa ɗaya ya shigar ɗakin ya ja ɗayar ma ya shiga idanuwansa na neman rufewa ya duƙe a nan ya shiga murƙususu da amai a lokaci ɗaya.
A bayyane bayan ta dafe kai ta furta" Na shiga uku, ruwan nan da ya sha ne?"
Jin murƙususun baya raguwa ya sakata nufar ɗakin hankalinta na tashi, tana shiga ta ganshi nan ya cire rigar jikinsa ya haɗe jikinsa da ƙafafuwansa jikin ya ɗauki jajajir sai murƙususun yake yi da kakarin amai amma kuma aman ya ƙi fitowa.
Da sauri ta ajiye jakarta ta koma ɗakin ta ta ɗauko akwatin ta mai kayan aiki ta dawo bayan ta rufe ɗakin nata ta shiga nasa ta buɗe tana bincike sama sama ta shiga faɗa tana faɗin" Kai baka taɓa sanin idan an jima ba'a ci komai ba ba'a kafa ruwan sanyi a cika ciki ne? Akan me zaka buɗa ruwa ka kafa a cikinka ka tittila? Sai kace wani jariri yanzu ka zo kana min murƙususu, malam Allah ya sa na sako alluran zazzaɓi da na ciwon ciki saboda ni, da ace iya na Safwan ne aka saka da yau ka ji maza, Allah ya taimake ka kai dai."
Tana faɗan ta gama haɗa allurar ta je inda yake, a nan ta rasa ta inda zata iya kama hannunsa dan ta yi masa allurar, gaba ɗaya ma sai ta rasa yadda zata iya dubansa a haka, dan bashi da riga ya cire, da ƙyar ta iya daidaita dantsen hannunsa ta masa allurar nan sannan ta nemi waje ta zauna tana jira ta ga yadda zasu ƙare.
Abincinsa aka kawo, ganin da nata ta amshi natan ta ci, a yanzu wanka take da buƙata sai dai ba zata barshi a haka ta tafi ba, ko ba komai likita ce ita, dole zata ba da irin taimakon nan ko a wanda bata taɓa gani bane balle maƙiyin ta! dole ne kawai.
Ya jima sosai yana fama da ransa, a ƙalla ya kai ƙarfe biyu na dare kafin zufa ta yi ta karyo masa, ciwon cikin ya faɗa, sai dai zazzaɓi kuma ya karyo masa, shi yasa baya son saka damuwa a can cikin zuciyarsa, duk abinda zai taɓo zuciyarsa direct ya fi so ya fuskance shi, shi gaba ɗaya bai gane wannan juyawar da suka yiwa ɗansa ba?
Yana samu ya miƙe zaune ya zuba mata ido, ta ci abincin da aka kawo mata a saman cafet ɗin, ta bar kwano ɗaya a nan, jus ɗin bata sha ba, amma ta sha ruwan, barci ya kwasheta ta yi wata kwanciya a gefen hannu jiki a haɗe, ƙafarsa ya saka ya tura ta ta yana jin juwar nan sosai.
Cikin barci ta ji ana harbinta ta farka da sauri tana dube dube, ganinsa zaune ba riga ya sakata faɗin" Kai ina rigarka wai?"
Sai kuma ta ɗauke idanuwanta tana mayarwa gefe a ranta ta shiga mita _" Shirgegen ƙato da kai ka zauna a gaban mata ba riga? Wannan wace irin ɗabi'a ce?."_
"Ni na kasa ganewa, ta ya ya zasu barshi a juye a haka? Kina ganin ya kamata in canza masa asibiti ne? Ya ya zasu ce kwana biyar cif bai san inda kan sa yake ba?" Ya faɗa a jigace yana sake dubanta da kyau.
Idanuwanta ta ɗago a hankali ta sauke saman fuskarsa, a hankalin sai ta kalli agogon bangon dake kafe sannan ta sake kallonsa tana son ɓamɓara idanuwanta dake son haɗewa su rufe, ƙarfe biyu da mintina? Bayan ya miƙe daga zafin ciwo? maganarsa ta farko kenan maimakun ya nemi abincin da ta tabbata bashi da wata buƙata sama da shi a yanzu? Ya ya girman soyayar ƙanin ta a zuciyar wannan bawa? Da gaske kenan son Safwan yake yi har cikin ransa? Da gaske damuwar rashin lafiyar Safwan ce ta hana masa cin abinci? Da gaske abinda take gani a fuskar gagarumin namijin nan gaskiya ne? Sai ta ji wani irin abu ya tsirga mata a zuciya na tarin tausayi ne ko begen ganin haka ne? Ita dai sai ta ji har can ƙasan zuciyarta dole zata kula da shi ko dan Safwan ɗin ta da aunty Intisar ɗin ta.
Jiki ba ƙarfi ta miƙe tana ƙara gyara suturar jikinta ta ƙarasa wajen nasa abincin ta buɗe ta ga da zafinsu, dan haka ta ɗauko ta ajiye masa har da ruwan da jus ɗin, ƙasa ƙasa ta ce" Kar ka saka damuwa a ranka, idan ka kwanta yaron naka ya farka ya ya kake so ya ji? Ga zafin ciwo gashi ba ka kusa? Na ga soyayyar ka a fuskar Safwan, na tabbata idan ya farka bai ganka ba zai damu, yadda suka yi masa shine daidai a likitance sauran aikin kuma na Allah ne, Allah ya sa yana da rabon sake taka ƙasa zaka sha mamaki idan aka miƙar da shi, yanzu ka ci abincin nan ko kaɗan ne, sannan ka sha ruwa, kar fa ka fara shan ruwan, kuma kar ka cika cikinka sosai saboda ka jima baka saka komai a cikinka ba, idan kana buƙatar wani abin na magani ka buga ɗakina."
Daga haka ta miƙe, dama tana magana idanuwanta na kallon ƙasa saboda zamansa a haka ba riga, ita likitar yara ce, da ta fara bautar ƙasa a asibitin kuɗi na Hamat kuwa ta tsaya a ɓangaren karɓan haihuwa ne, bata ringa cin karo da manyan maza ba tufafin kirki ba gaskiya, shi yasa a yanzun ma duk da kasantuwar taimakon rashin lafiya ne take yi sai kunyar tsare shi da ido ke kamata, a hankali ta fice ta rufo masa ƙofar ko ta jakunkunan data shigo da su bata bi ba.
Shi kuwa bai ɗauke idanuwansa daga kanta ba sai da ta bar ɗakin ya maido dubansa kan abincin ya buɗe a hankali ya shiga ci, dan kuwa idan bai yarda da ita a komai ba ya yarda da ita a abu ɗaya, *in Safwan ya farka zai so ganinsa*, idan baya kusa kuwa tabbas zai damu, ta yiwu damuwar ta ƙara masa wani ciwon, gwara ya ci abincin nan ya miƙe, ya ɗan taɓa abincin sannan ya sha jus ɗin ko dan ya samu sugar ɗin dake ciki ko juwar zata bar shi.
Ya jima a zaune ya ji jikinsa ya daina rawar nan, sannan ya ji ɗan karfin jiki dan haka ya miƙe ya nufi bayi yana jin zazzaɓin nan akwai shi, wanka ya yi ya fito ya saka kayan barci ya ƙarasa gadonsa ya haye ya ja bargo ya lulluɓa dan sanyi yake ji ga zazzaɓin nan da ya rufe shi, a hankali yana jan carbin hannunsa yana jin barci barci na fuzgarsa du da zafin zazzaɓin jikinsa da kuma ciwon dake zuciyarsa.
Yusrah kanta ta jima a bayi tana wanka, da ta fito ta ciro rigar barcin da pant ta saka fara ƙal mai kyau amma mai kauri, sannan ta haye gadon ita ma da wayarta a hannunta ta duba tarin miss call ɗin Aunty Intisar da voice note ɗin ta masu yawa, sai dai ta kasa sauraro balle ta bata amsa, sai a lokacin take sake maidawa kanta ire iren zagin da ta yiwa AA a gaban aunty Intisar, tunani ya kama zuciyarta, ta rasa gane ta ina ya zama ɗan uwan aunty Intisar, ya ya aka yi ta ganshi da shigar nan tufafi a ciccire, kai mummurɗe, da bindiga da abubuwan yan daba? Furucin bakinsa irin na yan ƙunar baƙin wake, kuma yanzu ta ganshi da tufafi a jikinsa masu daraja, tare da ƙanin ta, a yanzun ɗauke da sunan yayan aunty Intisar? Shin me yake faruwa ne?
*DR. HAMAT*
Tana dai ɓalla bras ɗin ta ne, amma hankalin ta na kan shi ganin bai da niyyar tashi kamar ba shi ya gaya mata sauri ba yake yi yana wanda zai ma tiyata a asibiti, baya ga haka ita kan ta uzurin gare ta ya kuma yi alƙawarin rage mata hanya, amma ya yi wani baƙo sai kallon wuri ɗaya yake yi kamar mai hailala a zuciyar sa, bayan ta san ba haka bane.
Saida ta gama saka rigar ta tsaf ta gyara zaman mayafin ta sannan ta sake duban shi tana matsawa kusa da shi tace "Dr."
Iya idanun shi kaɗai ya wurga mata sannan ya tsare ta da su yana kallo da jiran jin me za ta faɗa, a nutse tace "Na shirya kai kawai nake jira, lokaci na tafiya fa."
Guntun tsaki ya saki tare da ƙara jan zanin gadon da ya rufe masa tsiraici sannan ya zura hannu ya ɗauko wallet ɗin sa, buɗewa ya yi ya zaro kuɗi ko ƙidayawa bai yi ba ya miƙa mata yana faɗin "Ki je kawai, na tafi daga baya."
Hannu ta sa tana karɓa amma da yanayin jin haushi tace "Na je fa ka ce? Ka fa min alƙawarin tare zamu tafi har ka rage min hanya?"
Da ƙaguwa ya dube ta yace "Na ce ki tafi Sakina, ba yanzu zan tafi ba."
Taɓe baki tayi tana faɗin "Gaskiya ni Dr. baka min adalci ba ko kaɗan, da nasan hakane wall..."
Kafin ta ƙarasa ya sake cewa "A'a, nace ki tafi ko."
Juyowa ta yi da mamakin yadda yake mata kamar ba shi ya gama yi mata murya ba da yake so ta zo ta same shi, jinjina kai ta yi tace "Na gode Dr. wallahi lamarin ka yana bani mamaki wani lokacin, idan kana da buƙata ga mutum shine yake cikakken mutum a wurin ka, akasin haka kuma banza ne."
Zuba mata idanu ya yi yana kallo ta kama hanya za ta fice, da sauri kamar wanda ya tuna wani abu yace" Sakina zo, zo mana."
Dawowa ta yi tana turo baki ta tsaya gaban shi, ba wata alkunya ko kara ga mutumin da bariki ta gama ratsa shi yace" Ni kam nace ya labarin ƙawar ki ne?"
Haɗe fuska ta yi sosai tace" Wace ƙawar tawa kuma?"
Murmushi ya saki yace" Yusrah mana, baki da lambar wayar ta ko inda take da zama yanzu?"
Sama da ƙasa ta kalle shi ba tare da jin zafin hakan ba, takaici ɗaya ne shine idan da Yusrah za ta amince masa tasan da ta wanke shi sosai saboda ta ga yana ɗan damuwa da lamarin ta, cikin taɓe baki tace" Bani da, kuma ban san a ina take ba yanzu, rabona da ita ma har na manta, lafiya kake neman ta?"
Da jin haushin ba ta san komai game da ita ba yace" Ba komai, za ki iya tafiya."
Ɗauke kai ya yi daga duban ta bai kuma sake waiwayawa ba har saida ya ji ta rufo masa ɗakin, lalubo wayar sa ya yi a kan gadon ya duba screen, ba kiran Sani dreba ba kuma saƙon kar ta kwana, buɗa tsaron wayar ya yi ya sake dannawa lambar Sani kira, amma dai jiya iya yau waya a kashe ba'a samu, da takaici sosai na damuwar da ta addabe shi kwana biyun nan ya cilla wayar kan gado ya dafe kan shi yana faɗin "Oh Allah! Wai me yake faruwa ne? Wannan wane shashanci ne?"
Sani yana masa anfani sosai da sosai, sannan ya san abubuwa da dama akan shi da ba zai so ya mishi nisa ba, amma ga dukkan alamu nisan yake yi masa da bai san dalili ba, duk inda yake tsammanin yana shiga ya sa a bincika masa amma babu labarin shi, sannan kuma waya a kashe? To yana ina? Rabon shi da shi tunda ya faɗa masa AA ya je ƙauyen su Mani dreba, kuma ai ya tabbatar masa da ya fito daga gidan ya tafi, to me ya faru daga nan? Anya AA zai iya zama wanda yake da hannu a ɓatan Sanin kuwa?
Wannan damuwar kuma ƙarama ce idan ya danganta ta da ta wannan yarinyar nan da ya rasa gane wace irin jarabawa ce wannan soyayya da girman shi ta masa irin kamun kazar kukun nan? Abu kamar wasa yana neman zame masa gaske, ya ɗauka kawai ƙuruciyar ta, kyawun ta, hasken fatar ta da kuma ilimin ta yake son ya mora kafin wani lokaci ya watsar, amma kuma sai yarinyar ke neman zame masa ƙarfen ƙafa, ƙiri ƙiri ganin Annabin tsohuwa tun ranar da ta zo da yarinyar da ya ma aiki hoton ta ya kasa ɓacewa a idanun shi, ya kasa cire surar ta a tunanin shi. Daga ƙarshe sai yake jin shi a dole ba na dare ɗaya ko biyu ko wasu tsirarun darare yake da buƙatar ta ba, amma na duka gaba ɗaya rayuwar sa yake da muradin kasancewa da ita, da gaske son ta yake yi kuma da aure, amma bai ko san ina take ba yanzu? Haka bai san ina zai ga ƙanin ta ba? Na ɗaya daga cikin dalilan da ya sa ma yake matse da son ganin Sani, dan ya masa aikin neman ta da kuma ƙanin ta, ko ƙanin aka fara gani shi a kawo masa ya masa aiki, ya san hakan ba ƙaramin farin ciki zai sakata ba ai, kamar yadda zai iya mata barazana da ƙanin akan auren shi, ya san dole ta amince. Wannan sune abubuwan da a yanzu suke dagula masa lissafi har wamwalar sa, karsashin