Showing 12001 words to 15000 words out of 397328 words
ya iya furta masa" Aswan, tashi mu tafi gida?"
Hannayen shi dake kan guiwowyin shi ya gyarawa zama, cikin dakusashiyar muryar da ba za ka iya fahimtar halin da yake ciki ba duk da kuwa yana jin yunwa, yana jin bacci sosai, sannan zazzaɓi ya fara rufe shi wanda bai rasa nasaba da na cizon sauro, hka kuma ciwon kai na buƙatar sa, amma taurin zuciya da baya son nuna kasawa ya sa baya so ko a muryar sa a fahimta a daƙile yace "Ka je gida Dad, ba yanzu."
Ƙara matsawa yayi kusan shi yayi tsugunno irin na maza ya ɗora hannun shi a kan damtsen shi da rarrashi yace "Please Aswan, ka tashi mu tafi gida, ka cinye wa'adinka ai, tunda dare ya raba, me ye marabar yanzu da kuma safiya?"
A taƙaice yana kallon fuskar Dad ɗin yace "Ni ma haka na gani."
Matse baki Dad yayi saboda fahimtar abinda yake nufi, ɗan haɗe fuska yayi a kausashe yace "Aswan tashi mu tafi, ba zan bar nan ba sai tare da kai, kar ka min taurin kai."
Ƙara ɗaure muryar shi ya yi sosai cikin harshen buzanci yace "Oukou iguiwane ghass (ka tafi gida kawai), Adi nassa iguiwane nak da (Nima zan dawo)."
Da ɗan kausasa murya sosai har ɗakin na ɗan amsawa shima da harshen na buzanci yace "Warque wale dak oum moss war tahede kay (ba inda zan je ba da kai ba)."
Girgiza kai Aswan ya yi tare da ɗauke kan shi daga kallon Dad ɗin, hakan yasa Dad hassala ya miƙe tsaye tare da harɗe hannaye yace "Fine, zan nuna maka duk abinda kake ji a kaina ka ɗiba Aswan."
Gyara tsayuwa ya sake yi sosai har yana ɗan bubbuga ƙafa alamar ba zai matsa ba kenan, shiru ɗakin ba wanda ya sake magana, sai AA dake ɗan satar kallon Dad ɗin saboda sanin da ya yi ba zai iya jurar zama ɗakin nan na minti ashirin ba ma, Dad kuma ƙarfin hali ne kawai, amma yana da hawan jinin da zafi ke masa illa sosai, bayan haka ma mutum ne shi da tun yarintar shi ya kasance mai tsananin son sanyi, dan haka ma duk in da yake to akwai ac a wurin kuma baya tsagaita ta. Sannu sannu Dad ya fara buɗe bakin shi duk sanda zai yi numfashi, saboda numfashin nashi kmar zai sarƙe, Aswan na lura da haka ya sake kallon shi ba alamar sakin fuska yace "Daddd! Please go back home, i wil be there in sha Allah."
Wani kallo Dad ɗin ya mishi, sai kawai ya ɗauke kai shi ma yana so dole ya nuna masa iyakar shi, sun sake ɗaukar minti biyu haka Dad numfashin shi ya fara barazanar ɗaukewa, take idanun shi suka fara ƙoƙarin rufewa wanda hakan ya haddasa masa yin baya luuuu! Da wani irin azama AA ya riƙo hannun shi sannan ya tallabo bayan shi da ɗaya hannun, a nutse ya shiga takawa da shi suka kama hanyar barin ɗakin yana ɗan faɗin "Shine abinda nake faɗa maka Dad."
SK dake tsaye tare da Chef da azama suka rufo kan su, SK na riƙe Dad ɗin Aswan ya ɗan sake shi da niyyar juyawa ya koma ciki, ba fa zai fito yanzu ba, amma sai dad ya ƙara riƙe hannun shi gam ya ƙi saki, haƙa idanuwa sukayi sai ya ga idanun Dad ɗin kamar da ruwa ciki, kuka ne zai masa ko me? A hankali ya feso iska daga bakin shi ya ɗan girgiza kai irin _"Dad kenan!"_ Bayan motar aka buɗe musu ya taimakawa Dad ɗin ya shiga, farar jallabiya Chef ya miƙo masa ya karɓa ya zura sannan shima ya shiga, saida suka fara tafiya har sun fita daga compgn. Ɗin AA da har lokacin Dad ya ƙi sakin hannun shi ya kalle shi yace" Dad, me ya sa ka fiya dagiya ne wai?"
Ba Dad ba har SK saida ya ɗan karkato kan shi ya saci kallon AA ɗin, wai kura ce zata ce da kare maye? E shi yasan waye mai gidan shi a harkokin waje da dama, amma ko ma menene ai AA ya fi shi kafiyar tsiya, Dad kuma taɓe baki yayi yace" Ni da kai duka mu canza to, kai ka dinga jin maganata, ni ma na dinga jin maganar ka."
Wani ɗan malalacin murmushi AA ya yi ya ɗauke kan shi, bai ce komai ba Dad ma haka bai sake cewa komai ba, ana kawowa gidan shi ya ce zai sauka anan, ba dan Dad ya so haka ba suka sauke shi, amma saida Dad ya raka shi har bed ɗin, yana shiga ya cire rigar ya nufi banɗaki yana cewa "Saida safe."
Da kallo Dad ya bishi yace "Ba ka jin yunwa ne? A kawo maka abinci ko?"
Ba tare da ya juyo ba take ya bashi amsa da "No Dad, bacci zanyi."
Da mamaki Dad ɗin yace "Bacci?" Dakatawa yayi ya juyo ya kalle shi a nutse sosai cike da ƙwarewa a harshen buzancin shi yace "Aidaze a gue (na gaji ne)." Yna faɗa ya shige banɗaki, girgiza kai Dad yayi yana murmushi yace "Saida safe yarona."
Daga haka suka wuce na shi gidan tare da SK, yana zuwa Anna ta farka ta tambaye shi yadda aka yi, nan ya sanar da ita komai da ya faru, murmushi tayi ita ma tana girgiza kai tace "Aswan Anza."
Murmushi yayi shima yana cire jalabiyar jikin sa da niyyar canza wata yana faɗin "Yaron ki kenan." Dariya tayi tana kallon shi har ya cire rigar ya saka wata ash color sannan ya feshe ta da turare sannan ya kwanta yana jawo lallausan bargo ya rufe jikin shi.
*ANZA PALACE*
Duk da a mugun gajiya yake da maɗaukakin baccin da ya cika mishi idanu, hakan bai hana shi sake fitowa falon ɗaure da towel a ƙugun shi ba cikin kasalalliyar murya yana kiran sunan "Meem! My angel?"
Shiru ba wanda ya amsa, tsaye yayi tsakiyar falon yana ɗan dudduba ko ina da mamakin ina kuma suka shige, motsin da ya ji kaɗan ya sa shi yin murmushin saman laɓɓa ya karkata akalar shi zuwa hagun shi ya nufi ƙofar madafa, yana buɗa ƙofar ya kunna hasken wurin, wasu ƙosassun maguna manya guda biyu farare sol suka tashi tsaye daga kwancen da suke sun haɗa kawuna suka kalli ƙofar, suna ganin wanda suka sani ne, wanda suka saba da shi tun buɗa idanun su, wanda yake basu su ci kuma su sha sannan suyi wasa a jikin shi, da wani irin gudun dake nuna karsashin su ya ruɓanya sakamakon ganin shi suka taho a guje har tunkuɗar juna suke. Shi kanshi da farin cikin ganin nasu ya saki murmushi tare da ɗan ranƙwafawa, suna isa gare shi duk sukayi tsalle a jikin shi, haka ya ɗauke su tsaf kamar wasu jarirai ba tare da ya damu da wani irin gashi da ya rufe musu jikin su ba luf luf, ga ƙoshi da sukayi hakan ya sa ma ga yaro ba lallai ya shaida mage ce ba, dan kuwa gashin nasu na ƙasan cikin su har ƙsa yake ja, haka ƙafafun su a rufe suke ruf ba'a ganin su da kyau. Tafe yake da su a jikin shi bayan ya rufe ƙofar madafar yana shafa jikin su tausashe sosai yana faɗin "Kun yi kewata kuwa?"
Ƙwarai Allah da ya halicci dabba akwai anfanin d ya sa ya halicce ta, kamar yadda kuma kowace dabba ta duniya wacce aka sani da wacce ba'a sani ba tana da baiwar ta, sannan yau da gobe ta fi ƙarfin wasa, sarai sun gane me ya faɗa, damar mayarwa ne kawai babu, amma a haka magunan nan suka wani sake lafewa a jikin shi har da tagomashin wani marayan kuka kuka dake nufin suma fa magana suka mishi. Ƙara faɗaɗa murmushin shi ya yi ya sumbaci kowace yana cewa "Nima haka, na shiga wani rububi ne na kwana biyu, amma..."
Yana shiga ɗakin shi kan lallausan karfet ya dire su, amma da sauri dake sun san abinda zasu yi suka shiga tsalle tsalle har suka haye kan mazaunin abun dake gaban gado wanda shi kaɗai ɗin shi ma abun kallo ne da ɗaukar hankali, haɗa kansu suka ƙara yi bayan sun yi kwance suna fuskantar shi, zaune yake tsakiyar gadon ko towel ɗin bai cire ba ya ɗaga hannayen shi yayi addu'ar kwanciya bacci, sannan ya zura hannu ya kashe hasken ɗakin ya kalli fuskokin magunan da suka zuba mishi idanu yace "I love u."
Wani irin ƙara narkewa suke a jikin junan su alamar jin daɗi, sai shi kuma da yayi murmushi ya kwanta yana jan zani a jikin shi saboda fanka ce kawai ya kunna, amma dake ana yawan ruwa idan dare ya raba kuma sanyi saukowa yake, dan haka ma fankar kanta ba dayawa ya kunna ba saboda shi dai ya gaji da tashin hankalin nan, wataƙila ko dan Anna na yawan yi masa maganar ya yi aure ne, tunda ƙanan shi Humed ma har da yaro gare shi, to me ye a ciki? Lokacin Humed ne ya yi na aure shiyasa ya riga shi, ba kuma hakan na nufin shi ma ba zai yi bane, akwai abinda yake jira ne kafin ya yi auren, zai yi shima, zai yi in sha Allah.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨??👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*5*
*06:00* cif bayan shigowar shi gidan daga masallaci ya fara safiyar sa da motsa jiki kala kala, duk abun da yake kuma Meem da Angel na tare da shi, kamar yadda yake komai da tsari yanzu ma 06:30 na bugawa ya shigo ɗakin shi suna biye da shi sau da ƙafa, amma suna ganin ya nufi banɗaki sai suka tsaya cak har ya rufo ƙofar.
Wasar su suke yi a ɗakin, amma suna jin an murɗo ƙofa suka sake bazama sukayi kan shi, tun daga shafa lotion ɗin shi zuwa saka kayan shi na ciki bayan ya feshe su da tsadaddan turaren na bleue de chanel, duk da dai mutum ne shi da a ɓangaren turare bai da tsayayye ɗaya, duk wanda tsadar sa da ƙamshin sa suka mishi to ya kan siya ya kuma yi anfani da shi, sai dai ya fi anfani da turare irin na kamfanin Tom ford, duk da akwai turarukan da sukan yi wanda ko kyauta ka bashi ba zai karɓa ba, amma dai yana anfani da wasu daga ciki musamman ma oud wood da noir exterme.
Yana gama saka kayan ya ɗauki haɗaɗɗan lotion ɗin shi na kai wato sol de janeiro na maza ya shafe kan shi da shi wanda ke tall, amma ya san nan da sati da yardar Allah sai ya cika da gashin da zai fara damun shi, deodorant ɗin shi nivea white ya saka a hammatar shi kafin ya buɗa drower dan ɗaukar kayan da suka fi saka shi farin ciki ko ganin su ya yi.... Yana haɗa idanu da wani kaki ɗin na shi sai wani abu ya faɗo masa a rai, wato tsabar son aikin soja da shagala da sabawa da yayi duk safiya ya kan shirya ya tafi barrak ya sa ya manta da shekaran jiya an dakatar da shi daga aikin nan. Lumshe idanu yayi ba tare da ya janye hannun shi daga drower ba ya furta "Ya salam!"
Cikin rashin jin daɗi ya zura hannu ya ɗauko wata sleevless hoodie shirt tare da wando da ba zaka kira shi tree quater ba saboda iya guwan shi yake, yana gama sakawa ya ɗauki Creed ya fesa a rigar, sai lotion hand da ya ɗauka a cikin kit ɗin sol de janeiro ya matsa a hannun shi sannan ya juya zai fita yana shafe tafukan hannayen shi, wurin takalmin shi ya ƙarasa wanda ke jere reras daga sama zuwa ƙasa kan abun aje takalmin da musamman aka tanade shi dan haka, wasu baƙaƙen sfn slifas ya saka da suka fito da kyawu da hasken ƙafafun shi sannan ya fice daga ɗakin, duk abinda yake magunan shi na biye da shi suna kuma kallon shi.
Falo ya zauna duk yana jin haushin komai saboda yau ba zai tafi aiki ba, Meem da Angel kan su ganin yayi zaune cikin shirin da idan ba yana hutu ba yasa suke ta zagayen shi, ya ɗauka yunwa suke ji duk da kuwa ya aje musu kifi kafin fitar shi masallaci, amma sai ya miƙe a kasalance ya shiga madafa, madarar su ya ɗauko cikin wata farar kwalba tare da ƙaramin chines plate ya aje gaban su, zuba musu madarar ya yi sannan ya koma ya zauna, abun mamaki sai ya ga basu kula ba sai kallon shi suke yi suna ɗan kuka kuka, ɗan ɗaga musu gira yayi saboda mamaki da kuma son hasaso abinda yake tunanin shi suke nufi yace "Ina hutu ne my baby's."
Meem da a cikin su ta fi mugu mugun shaƙuwa da shi saboda ita Angel ta kan iya fita ko da yana gidan zaune ta ɗan yi tana wani irin kuka, murmushi yayi ya shafa kan ta tare da faɗin "T'inquiet Meem."
Daga haka suka tsugunna suka fara shan madarar nan, shi kuma ya ɗan tsare ƙofa da idanu yana kallo, tunani ne fal a ran shi, yanzu ya zaiyi da wannan abun kunya? Ya sani shi ya ja ma kan shi, amma sun mishi hukunci mai tsauri, da ya san haka abun zai zama da tun a gavan su ya nuna musu nadamar shi sanan ya nemi su sassauta masa hukuncin nan. Ko da yake Dad na nan, kuma ya san zai iya tsaya masa ai, da sauri ya aje filon kujerar da ya rumgume ya miƙe ya nufi ɗakin shi, yana shiga makullin motar shi ya ɗauko ya fito yana murza mundun dake tsintsiyar hannun shi na azurfa ɗauke da sunan *AA Anza* ya nufi ƙofa, da rige rige magunan nan suka bi bayan shi suna kukan da shi ya san me suke nufi, yana buɗe ƙofar motar Angel ta fara yin tsalle ta shige tare da haurawa ta zauna kujerar mai zaman banza, inda Meem ma ta bi bayan ta ta shige, yana kallon su saida suka zauna sannan ya shiga shima ya tayar da motar yana sake dannata, hakan ya sa mai gadi da kuma mai kula da cikin gidan suka leƙo suna hangen budurwar motar nan da wani talakan ya gan ta ko ya ji kuɗin ta baƙin ciki zai iya kama shi, amma a wajen yara irin su AA Anza mercedess amg ko mercedes benz ba wata abu ba ce, a haka wai shi ya na da tsantseni kenan. Mintuna ƙalilan suka kawo shi gidan da yake da tabbacin ba wanda ya fita zuwa yanzu, har ƙofar falon ya faka mota sannan ya fito shi da ƴaƴansa suka shige bayan ya tura ƙofar madubin, tunda ya ɗan fara jin hayaniya tun daga couloir ɗin ya san kowa n gidan na falo kenan, dan haka ya ɗan yamutsa fuskar shi ya haɗe sannan ya shiga da sallama ƙwaya ɗaya tak kuma sau ɗaya tak. Anna da take zaune kan kujerar dake fuskantar ƙofar kuma ta ga shigowar shi haka ma ta ga bakin shi ya motsa, dan haka a nutse tana mai ƙare mishi kallo ta amsa da "Wa'alaika salam."
Amsawar da tayi kuma ta sa sauran mutanen juya kawunan su, take Manal da Nawal suka yi tsit kowace ta sake gyara zaman ta, sai Abrar da ta tsare shi da idanu tana kallo, saɓanin mahaifiyar ta wato aunty Tidin da ta ɗan haɗe fuskar ta ita ma saboda ba wani gane wa juna suke da Aswan ba, matar Humed kuma da dama ai Aswan siriki ne a wajen ta tuni ta sadda kan ta ƙasa tana wasa da wayar hannun ta dan hatta mijin ta dake namiji a gareta kama kanshi yake a gaban AA, yaron nata ne ma kawai *Saiful-Islam* ya tarbe shi da gudu, ba tare da bayyanar murmushi a fuskar shi ba ya rusuna ya ɗauke shi ya saɓa a kafaɗa yana tambayar shi ya ya tashi?
Saida ya zo tsakiyar falon daya yi shiru tamkar mala'ika ya shigo, da azarɓaɓi Manal da Nawal har suna haɗa baki suka furta "Morning."
Kallon inda suke ya yi cike da shan ƙamshi, kafin yace musu uffan Humed ma ya jefo tashi gaisuwar kusan tare da matar shi da bakinta har rawa rawa yake na ɓari da shakkar AA, ita kam tasan Allah ya haɗata surukuntaka da shi ne, amma sam bata kai matsayin ba, tsoron shi take bilhaƙƙi da gaskiya, da gaske kuma tana tsoron haɗa sabga da shi da ta shafi ko da idanuwa ne bare