Showing 33001 words to 36000 words out of 397328 words
maida duban ta gare ta, da sauri tace "Mamanmu, wallahi ba yadda ban yi da su ba nace a'a, amma sai tsohuwa ta ce na karɓa ai abinci ne, sannan idan na zo na faɗa miki wai ita tasa na karɓa ba dan ina so ba, wallahi ko Mamanmu."
"Wace tsohuwa?" Maman ta jefa mata tambaya, da sauri Yusrah tace "Maman mijin wacce ta haihu ce."
Cikin faɗa Maman tace "Amma ai ni na hanaki karɓan wannan, Yusrah so kike ki fara cin haramun kuma ki kawo mana mu ci, na sha gaya miki duk wani da zai baki kyauta in dai akan aikin ki ne to baki cancanceta ba, ko ban faɗa miki ba? Yanzu shi wannan abun cin ban san a wane mataki zan ajiye shi ba, amma bana so kowa ya taɓa komai a ciki har sai Babanku ya shigo, idan ya yarje a taɓa kwa anfana da shi, idan bai yarda ba dole a fitar min da su daga gidana, kin fahimta?"
A nutse ta jinjina kai tace" E." Wucewa Maman tayi ta bar ta dole ita ma ta ja jiki a sanyaye duk tana jin ba daɗi, ganin Hannah tayi alwala a robar da Mama ta yi ya sa ita ma ta yi anan, sallayar da Hannah ta shinfiɗa ita ma ta tsaya anan suka kabbara sallah tare sai Safwan a gefen su.
Har sallah isha'i Baba bai shigo ba saboda har lokacin ruwa ake kuma ba yayyafi ba, ganin haka ya sa Hannah kallon Mamansu tace "Mamanmu, ko dai ruwa sun hana Babanmu shigowa gida? Gashi har an fara sallah isha'i."
A tausashe Maman dake kan sallaya ta amsa da "Ba shakka, wataƙila kuma suna tattaunawa ne kan ramin can na baya dake neman ruftawa da gidajen mutane, ya faɗa min za'a yi taro na duka unguwa dan a shawo kan matsalar, tunda an je gurin gwamnatin amma shiru ba wani taimako daga gare su."
Safwan ne ya kalli Maman yace" Mamanmu, ni dai na fi so Babanmu ya fara gyara mana ɗakunanmu, saura kaɗan fa su faɗo man..."
A tsawace cikin tashin hankali Maman ta katse shi da" Kai! Rufe min bakin ka."
Shiru ɗakin ya ɗauka kafin daga bisani Maman tace" Ka daina faɗin haka *Yayan su*, ba kyau ka ji? Ka yi ta wa Babanka addu'a ya samu kuɗi ya gyara, amma ka daina cewa zai faɗo."
Jinjina kai ya yi alamar to, a hankali Maman ta miƙe jiki a sanyaye ko sallah isha'i bata kabbara ba ta shiga ɗakin ta, sun ɗauka wani abun za ta yi ko ta ɗauko, amma suka ga shiru ba ta fito ba tsawon lokaci, duk da sun damu da haka musamman ma Yusrah da take tunanin kar dai Maman kuka ta shiga ta yi akan ginin nasu da kullum lalacewar sa ke daɗa yik yawa? Dan ta taɓa ganin haka daga gare ta.
Har sukayi sallah bayan sun idar Yusrah ta kalli Hannah tace "Aunty Hannah, ko za ki duba Mamanmu ki gani, ko motsi babu a ɗakin."
Girgiza kai Hannah tayi tace "Mu barta Yussy, wani abun sai ka keɓanta ka ke samun damar fito da shi daga ran ka, imma a suffar magana, ko a suffar kuka."
Shiru Yusrah ta yi tana kallon ƙofar ɗakin Maman da labule ne kawai ya rufe ƙofar, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tace "Hakane, Allah ya mana maganin dukkan matsalolinmu."
"Ameen." Hannah ta faɗa, wayar Hannah dake kan sallaya ce ta yi ƙara, Yusrah na ganin sunan da ya fito ta kalle ta da murmushi tace "Aunty Hannah kwana biyu ban ga Yaya *Jamil* y zo zance ba?"
Ɗaukar wayar tayi tana miƙewa tsaye tace "Kin manta Babanmu ba ya son yawan zancen? Ai shiyasa ko ya ce zai zo nake hanawa, amma dai mun yi magana yanzu akan duk juma'a zai zo."
Murmushi Yusrah ta yi tana bin ta da kallo har ta shige ɗakin su ita ma, daga ita sai Safwan aka bari, ba wani abu da take yi a wayar ta da za ta ce bari ta ɗauko ta duba, idan ta yi ƙara za ta ji, rabon da ta hau yanar gizo kuma saboda rashin isashen data har ta manta, kira ma ba wasu mutanen ne ke kiran ta ba idan ka cire Baba idan bata gidan ko shi baya nan yana so zai yi magana da Maman su, sai ƙawar ta Maryam kawai, bayan haka kuma sai irin samarin nan da zasu samu lambar ka baka san ta ya suka samu ba, ita kuma bata kula irin waɗannan dan gwara ka tarbe ta ka ce ta baka ya fi mata daɗi.
Sannu sannu ruwan suka fara ragewa zuwa yayyafi, suna nan zaune ita da Safwan har ta tambaye shi "Ba'a yi girki ba?"
Kai kaɗai ya girgiza mata shima bayan ya juya ya kalli ƙofar ɗakin Mama, doguwar ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin to idan dai ba'a yi girki ba, to tabbas rashin kuɗi ne ya kawo haka, wataƙila ma shiyasa Baba ya jima bai shigo ba, kenan ya za ta yi gobe wajen tafiya asibiti? Dafe goshi ta yi tana ci gaba da tunanin abun yi, kwatsam suka ji sallamar Baba, da sauri Safwan ya miƙe ya fita ita ma saida ta tashi, haka ma Hannah sai da ta yi sallama da Jamil ta fito duk suka tarbi Baban, ledar hannun shi ya ba wa Safwan suka shigo ɗakin, Yusrah dai cike da tausayi ta zuba mishi idanu saboda kayan shi a jiƙe suke sosai, tuni ƙwalla suka cika mata idanu saboda tausayin mahaifin nasu da kullum burin ta taga tana taimaka mishi, ba ya da namiji babba sai su mata.
Hannah ma da kulawa tace "Babanmu yau kun jima, ruwa suka hanaku fitowa?"
Murmushi ya yi duk ya shafa kawunan su yana cire hular shi, cikin taushin murya yace "Ruwa ne suka hanani Hannah, ina Mamanku?"
Safwan ne ya yi gaggawar amsawa da "Suna ɗaki."
Jinjina kai ya yi tare da nufa ɗakin yana cewa "Bari na cire wannan kayan, ma sha Allah yau mun sha ruwa."
Yana daf da shigewa ya juyo ya kalli Yusrah da bayan gaisuwa ba ta ce komai ba yace "Yussy kina lafiya?"
Jinjina kai ta fara yi alamar e kafin tace "Lafiya lau Babanmu."
Murmushi ya sakar mata mai ma'anoni da dama, da sosai yake hango tsagwaron tausayin su a idanun ta dake shirin sakata kuka, shiyasa ma bai tsaya wajen su sosai ba dan kar ta fashe masa da kuka.
Baba na shiga ɗaki ya tsaya turus, amma dan kar yaran su ji me ke faruwa sai ya ƙarasa a tsanake kusa da maman dake zaune kan gado yana kallon ta hankalin shi yana sake tashi matuƙa saboda tunanin me take ma kuka?
Da kulawa sosai yace "Ƙanwata, lafiya? Me aka yi kike kuka haka? Yaran ne suka miki wani abu? Ko jikin naki ne?"
Share hawayen ta fara yi tana sauke ajiyar zuciya da cewa "Ka yi haƙuri Yayana, ashe ka shigo? Ka yi haƙuri dan Allah na ɗaga maka hankali, ba komai wallahi."
Sai kuma ta gyara zama dan ta basar da zancen tace "To ya tattaunawar ta ku? An samu wata matsaya ne?"
Ƙura mata idanu ya yi yace "Baki bani amsar tambayata, me aka yi kike kuka?"
Shiru tayi tare da sadda kan ta ƙasa, ta ɗan ɗauki sakanni a haka kafin ta ɗago a hankali tace "Yaya, na ce ko zamu koma ɗakin yara, su sai su dawo nan ɗakin namu, gaskiya hankalina ba'a kwance yake ba game da lamarin ɗakin nasu, tsoro nake jiye musu wallahi."
Tunda ta fara magana ya zuba mata idanu har ta gama sannan yace "Ƙanwata, yanzu a ganin ki ɗakin namu ya fi nasu aminci ne?"
Ɗaga kai tayi tana ƙarewa kowace kusurwar ɗakin kallo, gaskiya ba wata maraba bace, gini dai ne na laka sai shafe shi da aka yi da simitin, shima dake abun ya ɗauki shekaru duk simitin ya kwaye wasu wuraren sai tsagwaron lakar a fili, ganin ba wani bambamci ya sa ta feso iska daga bakin ta tana kallon shi tace "To ya zanyi? Hankalina ne a tashe kullum, musamman ma idan suna cikin ɗakin sai naji na gagara nutsuwa."
Hannunta ya riƙe cike da tausasawa yace "Ki kwantar da hankalin ki, in sha Allah komai ya kusa zuwa ƙarshe, kar ki manta saboda nayi gyaran gidan nan na shawarta da ƴan uwana suka kuma yarda akan zamu siyar da filinmu ɗaya da ya rage mana na gado dan nayi wannan gyara, kuma in sha Allah ina saka ran fara aikin gidan nan a sati na gaba da zamu shiga, kinga kafin bikin Hannah ya tashi gidanmu ya zama sabo, ko ba haka?"
Tunda ya ambaci sati na gaba wata nutsuwa ta sauko mata, dan haka tayi murmushi tace" To Allah ya yarda Yayana, Allah ya tabbatar mana da alkairi, Allah ya baka iko akan wannan niyya ta ka."
Murmushi ya yi tare da miƙewa yana cire rigar shi yana faɗin" *Ƙanwar Abdul-Hameed* rigima, kawai sai kiyi ta kuka har da ƙoƙarin canza min ɗakina da na saba kwana a ciki? Hmmmm!"
Dariya tayi cike da jin kunya ta miƙe ita ma tana ɗaukar kayan da ya cire tana kakkaɓe su ta sagala a hannu dan ta shanya su tace" To me ba gashi kuma *Yayan Habiba* ya sakata dariya a bayan kukan ba?"
Dariya duk sukayi kafin ya ce mata" Yau ma dai sai kun haɗa da haƙuri ƙanwata, garin kwaki na nan da kayan haɗin shi wajen Safwan, ko iya yaran su gyara sai ku ci."
Da tausasawa tace" An gode Baban Safwan, Allah ya ƙara buɗi mai alkairi."
Har za ta fita daga ɗakin, sai kuma ta dakata take faɗa masa Yusrah ta zo da abinci, shiru ya yi na kusan daƙiƙa sha biyar tana tsaye tana jiran ta ji me zai ce, kafin ya kalle ta yace" Ku zuba mana mu ci, ubangiji ne ya ciyar damu daga gare su, sai dai ki sake faɗa mata bana so ta buɗe hanyar karɓan komi aka bata a wurin aikinta, wata rana za ta karɓi haram ta ci."
Jinjina kai tayi cike da gamsuwa tace" In sha Allah, zan ƙasa nusar da ita, ka yi haƙuri ba za ta sake ba."
Murmushi ya yi yace" Allah ya muku albarka."
"Ameen ya Allah." Ta faɗa tana fita daga ɗakin, akan kujerun ƙarfe dake falon ta shanya kayan kafin ta umarci Yusrah da ta karɓi garin ta gyara, ba ɓata lokaci ta shiga gyaran nashi musamman ma da ya zamana tana jin yunwa, saida suka gama gyarawa ta aje gaban Maman, ta ɗiba a faranti sannan ta basu sauran, ɗaki ta shiga ta kai wa Baban, jim kaɗan suka fito tare, kujera ta gyara mishi ya zauna ya karɓi farantin ya aje ya ce yaran su matso da nasu, haɗewa sukayi gaba ɗaya suka saka hannun su suna ci a nutse.
Saida suka cinye Baban ya kalli Maman yace "To yanzu a zuba mana wanda Yussy ta kawo ko."
Ba gardama ta tashi da kan ta ta ɗauko kwanon da leda, cikin kwanon da suka ci garin ta juye ashe miyar da ba komai a ciki sai zallar naman zabi da dankalin turawa yawa ne da shi, duk da abu ne da za su iya cewa daga sallah sai sallah suke samu, sai kuma ranar da ubangiji ya yi buɗi gare su suke iya samun nama a abincin su, dan mahaifin su kayan miya ne yake siyarwa a kasuwa, wasu lokuta ga kayan miya a gidan amma babu abun dafawa, ma'ana shinkafa, gero ko masara bare kuma ayi maganar makka. Amma haka daga yaran har iyayen ba wani wanda ya dinga haɗama ko zumuɗin zai ci, haka suka dinga jefa hannayen su bayan na iyayen su suna ci a nutse har suka cinye shi ma tass tunda miya ce babu mahaɗin ta, garin kuma dama ba kowa ne ya ƙoshi ba.
Ledar ma lemuka ne masu rai da lafiya da kuma kayan marmari a ciki, su ma Alhamdulillah haka suka sha har suka ragawa gobe, bayan hakane Baban ya yi hamdala sannan ya kalli Yusrah yace "Yusrah, nasan maman ki ta faɗa miki ba ta ji daɗin karɓan kayan nan ba? Kar kiga na ci, nayi duba ne da wasu abubuwa, amma dai ki kiyaye kin ji, mutumci ya zama shi ne sama da komai a wurin aikin ki, kin gane?"
Jinjina kai tayi tace "Na gane Babanmu, in sha Allah ba zan sake karɓan komai ba daga yau, kuma wallahi dan Mamansu ta yi magana ne ma na karɓa."
Jinjina kai kawai ya yi, da haka suka taɓa hira kamar yadda suka saba kafin dare ya ƙara yi suka shiga ɗakin su suka kwanta, sai dai Yusrah tun bacci bai ɗauketa ba aka sake ɓarkewa da wasu ruwan, tun tana juye juye har baccin ya ɗauke ta ita ma.
*AA ANZA*
A nutse yake haurawa sama, bayansa ƙannensa ne ke biye da shi dan kowace da maganar da take so su yi da shi, a nutse ya nemi izinin shiga ɗakin mahaifiyarsa, jim kaɗan ta bashi dama ta hanyar furta" Bismillah Rohi."
Domin ta tabbata shine, baya taɓa zuwa ya kwanta ba tare da ya zo ya yi masu bankwana ba, haka kuma yanayin doka ƙofar ma tasa ce, a hankali ya shiga da sallama a bakinsa ya sauke mata murmushi yana idasawa daf da ita a tausashe ya zauna ya furta" Barka da dare Anna."
Murmushi ta yi itama a hankali ta ce" Barka kadai yaro, ya gajiya?"
Kai ya girgiza a nutse ya ce" Babu."
Murmushi ta yi ta kalli ƴan matanta da ido ta masu alamun lafiya?Kowace ta yi tsuru suka kasa bata amsa, hakan ya sa ta dube shi ta ce" Ni wai, ina kake zuwa ne? Ya ya kuma maganar tafiyar yaran nan? Ka ce za ka yi bincike akan makarantar da suka zaɓada kan ka."
Ɗagowa ya yi ya dubeta, sannan ya dube su, kai ya girgiza ya ce" Su yi haƙuri da tafiyar har a kwana biyu."
Su da kansu da suka ji ya dasa aya haka basu tsaya jiran wani bayanin ba suka fita daga ɗakin dan sun san nacewa a kan lamarin ba zai kaisu ga ci ba face ma ɓacin rai da zai biyo baya.
Suna fita Anna ta dube shi fuskarta a ɗaure ta ce" Aswan, me yasa kake so a kullum ringa yi maka surutu a kan abinda ya shafi Goggonku? Wannan da kake gani idan ka raina ta mu ka raina, tana da damar ta yi maka faɗa in ta yi ra'ayi, ka kula bana son ina ganin kana yi mata abubuwan nan da kake yi mata ka ji?"
Kai ya gyaɗa da kula sosai ya ce" Ki yi haƙuri Anna, za'a kiyaye."
Anna ta yi murmushi, hakan ya saka shi sauke ajiyar zuciya a hankali ya miƙe ya yi mata sai da safe, dama ya gama da mahaifinsa tuni, dan haka yana fitowa ya kama hanyar sauka dan nufar nasa gidan, a saman matakala ta biyu suka haɗe da Goggonsu ita da Abrar, Abrar ɗin ɗauke da kular abinci jikinta sanye da doguwar riga ta bi jikinta masha Allah ta yi mata ɗass.
Tunda ta ganshi ta haɗe rai sosai, dan kuwa haushin sa take ji sosai kan abinda ya yi yau, Abrar kuwa sai ma ta so manta kanta a tsayen da take domin cak ta ja ta tsaya fuskarta ta yalwata da murmushi ta duƙa sosai murya a shaƙe ta ce "Barka da dare Yaya AA."
A saman leɓensa ya furta" Barka."
Barka ɗin da ya bada a jimulce daga ita har babarta sannan ya raɓe ya ƙarasa sauka ya fice gaba ɗaya daga falon, ba wai ya raina Goggo Tidin bane, hasalima shi mai girmama wanda yasan yana gaba da shi ne, kawai dai ta dinga yin wasu abubuwa ne da jimawa da suka tsaya masa a rai ya kasa fitar da su, tun bata haifi Abrar ba take gidan nan da sunan zawarci bayan rasuwar mijin ta, mahaifiyar ta tsakani da Allah take zaune da ita.
Amma a wannan lokacin ta ba wa mahaifiyar shi wahala, wahala dai irin wacce wasu ƙannen mijin suke ba wa matan yayun su, ƙiri-ƙiri har matsala ta dinga ƙirƙirowa tsakanin Anna da mahaifin shi, ya sha ganin Anna tana kuka a dalilin ta, makirci dai kala kala. Shi kuma dama bata taɓa nuna ƙaunar sa ba, ko shakka baya yi akan mahaukaciyar soyayyar da Aba yake masa ne, ba ta ƙaunar shi a yadda dai ya tashi ya gani, babu wani abu da take masa da yake nuna ita ƙanwar mahaifin sa ce wacce take zaune gidan su, tun yana yaro bai saba ganin fara'ar ta ba, shiyasa da ya mallaki hankalin sa gaisuwa dai tana haɗa su, amma babu mai shiga sabgar wani shi ko ita, kuma hakan ya fi yi masa daɗi.
*Da* wani mugun takaici ta zubawa Abrar ido, ita kuwa bata san tana yi ba har sai da ya ɓacewa ganinta ta juyo ta ga irin yanayin da mahaifiyarta ke kallonta, ɗan kauce dubanta ta yi ta shiga haurawa, ita ma ta mata shiru har sai da suka shiga ɗaki ta dubeta fuska a haɗe ta ce" Kina kallo ni da nake uwa a wajensa ya gaisheni tamkar gaisuwar saƙo da saƙo, amma ke kika duƙa dan ki gaisar da shi, ina fatan ba wani shirme kike kitsawa kanki a kansa ba, domin ki ji ni da kyau Abrar sai dai idan bayan raina, kin fahimta?"
Abrar ta yi shiru ƙirjinta na dokawa har mahaifiyarta ta finciki wayarta ta kuma ficewa, ita kuma ta ƙarasa ta zauna a hankali bakin gado tana jin kanta na neman tarwatsewa dan tashin hankali.
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️??🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪