Showing 141001 words to 144000 words out of 397328 words
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUÆŠI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*38*
Cike da jin rashin ƙwarin guiwa Mani ya tabbatar masa cewar eh shi ɗin yake nufi, ya jima yana kallon Mani, har sai da Mani ɗin ya cire hularsa yana ta fifita sannan ya cire kansa yana mai rintse idanuwansa ya miƙe tsaye a hankali yana duban agogonsa yace" Ina fata ka fahimci abinda na yi maka kwatance?"
Mani ya gyaÉ—a kai yana mai tabbatar masa ya fahimta, bai kuma cewa komai ba sai waje da ya yi da sauri sannan ya ja ya tsaya yana kallon Mani sama sama kaÉ—an ya ce" Da ace ka bani haÉ—in kai mun yi magana da ina mai tabbatar maka sai na baka tukuici mai girman gaske, tunda har ka min haka baka duba girman amincin dake tsakanina da kai ba kace in bar maka gidanka kai yanzu birnin ma ta fita a ranka ko? Ba laifi na gode."
Mani dreba ya ce" Sai dai ka gode kuwa, ba zan taɓa iya wata magana da kai ba, ka je kawai kuma na faɗa maka babu ni babu kai, sai anjima."
Daga nan ya yi cikin gidansa shi kuwa ya ɗan tsaya irin da takaicin nan sannan ya ja kyaftu ya shige motarsa har ana bashi haƙuri irin ƴan anguwa ɗin nan ya ja motarsa ya fice da gudun tsiya idanuwansa na hango masa Sani cikin mutane masu kallo.
Mani na shiga ya samu matarsa ya faɗa mata komai da gaggawa, sannan ya sakata fara yin gaba, ba musu ta amince domin tunda abin nan ya faru sun zamo kamar mujiya a cikin garin, kai hatta gidansu idan ta je wajen mahaifinta kawai take jin sanyi, dan mahaifiyarta ta rasu, ido da ido ake ce mata yanzu sai a ga ƙaryar birni, mijinta ya daina zuwa aiki birnin sai a ga ta ƙarya, ita kuma bata ce masu komai dan ba wannan ya fi damunta ba kamar damuwar mijinta, kullum yana cikin zulumi da damuwa, idan ta matse masa guri sai yace ba komai kawai yana tunanin abinda zai kama dan su samu su fidda kansu ne, bayan ga gonaki ga komai amma baya iya aikin nan ya riga ya saba da aikin birni da wahala ya iya da na ƙauye.
Cikin ƙanƙanin lokaci ta ɗauki abinda ta san dole zata buƙata ta ɓoye a cikin jikinta sannan takardun ƴaƴansu da mijinta ya fitar ta yi dabara ta ɗaure a cikinta tam sannan ta ɗora hijabinta a sama, da ta fito daga ita sai jakar hannunta mai ɗauke da mahinman abubuwa ta ɗauki hanyar gidan ƙawarta, sai da ta shige ta jima sosai a ciki sannan ta fita cikin dabara ta dudduba ta ga wanda ke binta yanzu baya nan sannan ta ɗauki hanyar gonakin tana ta addu'a cike da tsoro har ta ƙarasa wajen motar, tana zuwa ta samu yaranta biyu har sun ƙaraso suna cikin motar ta shige suka laɓe sai addu'a suke yi da kallon hanya.
Sani kuwa yana juyawa bayan ya bi bayanta ya ga gidan ƙawarta ta je sai ya yi kiran Oga ya sanar masa kaf abinda ya faru yau, Oga kuwa ya ji daɗin haka ya tabbatar masa Mani ya ji kashedin sa shima ya shiga harkokinsa hankali kwance, shi kuwa Sani tun kafin ya koma can gidan tuni Mani ya fitar da yaransa kaf ya koya masu yadda zasu yi su je wajen gonaki idan sun je kar su ji tsoro ko jira su shige motar da zasu gani a nan, kasantuwar yaran ɗaya ne kawai mai shekara tara sauran duk sun tasa, mata biyu maza biyu ne sai ya zamo duk sun fahimta kuma sun aikata, shi kaɗai ya rage , shima yana fuskantar ya kai ya fitan ya fito a lokacin tuni duhun magariba ya shigo, ko sallah basu yi ba ya fito ya bar gidansa buɗe ham kamar yadda ya saba ya ɗauki hanyar gonaki, yana tafe yana ɗan waige, sam idanuwansa basu nuna masa da mai binsa ba, har ya kusa ƙarasawa motar ya ji wani irin ƙara irin na an daki mutum da ƙarfi a rashin sanin zai samu dukan nan ya saki irin ihun nan mai ƙarfi.
A tsorace ya juyo, sai dai yana juyowar ya ga Aswan ya tallabi Sani dreba ya masa wata mazga É—aya da ta fitar da shi a hayyacin sa sannan ya saka abin É—aurewa ya É—aure shi tam ya buÉ—e boot É—in motar kamar ya É—auko kayan wanki ya watsa shi ciki ya rufe.
Yana ɗagowa ya nufo wajen Mani, Mani ya ja da sauri ya ruƙumƙume motar daga gefen shiga ya rintse ido a tsorace, Aswan ya ɗan zuba masa ido, sai kuma ya girgiza kai kawai ya buɗe masa gaba ya shiga ya zagaya ya buɗe ya shige ya tayar da motar bai ce komai ba ya ɗauki hanya da matsiyacin gudu bayan ya kunna masu acn motar.
Yana daf da isa gidansa na cikin gari wayarsa ƙarama ta ringa kuka, a dole ya lalubo ya ɗaga yana daidaita muryarsa cen ƙasa ya furta" Ina gida Aba, in zo ne?"
Aba ya yi murmushi ya ce" Idan ka fito ka zo, ga lauya nan ya zo da takardun ɗan ka, Alhamdulillah an tabbatar da yaro naka ne domin hatta masu kula da kare haƙƙoƙin yara sun gama bincike sun yarda an saka maka hannu, daga yanzu Safwan ya zama Safwan Aswan Aliyu, halastacen jikana na wajen ka na farko kafin in maka aure jikan ANZA."
Murmushi ne ya ƙwace masa, wanda ya fito daga can ƙasan zuciyarsa mai tsada mai wuyar samu, wanda a tunaninsa a yanzu da wahala ya iya samunsa dan irin abinda ya daki zuciyarsa mai ƙarfin gaske, sai gashi mahaifinsa ya fitar masa da shi cikin sauƙi.
A hankali ya furta" Alhamdulilah dad, sai na shigo." Daga nan suka yi sallama ya sauka daga baban titi ya nufi gidan nasa.
Yana zuwa aka buɗe masa ƙofa ya shige da su, sai dai ya dakatar da motar daga bakin ƙofa ya buɗe suna fitowa ya masu alamar kar wanda ya yi magana, suna gama fitowa ya nunawa sojan nan da ya tsaya ko kaɗan ya ji alamun motsi ya sumar da wanda ke cikin boot.
Daga nan ya ja gaba suna biye da shi har suka je can ciki, falo na wajen uku sannan ya dube su, murmushi ya fara yi yana duban Mani ya ce" Alhamdulilah, a nan zaku kwana, gobe zan dawo in ɗauke ku mu je ku kama hanya, dukkan abinda ya dace a yi an gama daidaitawa, kar ka damu da iyalinka, komai zai zo yadda ya kamata, a nan babu abinda babu, inma da wata buƙata ga waya a jikin bango ka yi kira za'a kawo maka ko menene, maganar suturu za'a kawo, karatun yara ne ina bada haƙuri na ɗan lokaci, idan komai ya shiga tsari zan je da kaina in daidaita komai."
Mani ya rage tsayinsa sosai yana ta aikin godiya, haka ma iyalansa baki ɗaya, Mani na kallonsa ya ce" Yallaɓai, a ganina ka barmu a nan ɗin ma ya wadatar, dan in dai ba wani ikon Allah ba ai da wahala a san muna nan."
AA ya ɗan yi shiru, shi da kansa idan akace suna nan kusa kai kawo zai fi yi masa sauƙi, dan haka ya dube shi ya ce" Gidan nan ko mahaifina bai san da shi ba, sannan yana ƙarƙashin tsaron soja mai riƙe da bindiga mai harsashi mutum goma sha biyu, ɓoyayyen waje ne da na sha saukar shugaban ƙasa a cikinsa dan a ɓoye shi, waje ne da yake da tsaro sosai da sosai, misali in dai a nan ɗin zaka zauna mu je in nuna maka wani waje da idan aka leƙo aka ce ku ɓuya ga numbobin da zaku danna ku shiga, wajen ko harbin bindiga baya ratsa wa kowace irin bindiga ce kuwa, ba'a gane da ɗaki a wajen ma gaskiya domin bangon a shafe yake, mu je dai."
Binsa ya yi suka je ya nuna masa, shi da kansa sai da ya ji nutsuwa ta sake ratsa shi, sannan ya tabbatar masa zasu zauna a nan ɗin, daga nan ya fito ya masu sallama da nufin sai ya shigo gobe , ya shiga motarsa ya juya ya tafi sojawan kuwa suka ci gaba da aikinsu, domin wajen an masa mahaukacin gini ne da manya ke ɗaukar hayar wajen a ɓoye su samu ɓuya na lokaci ko su huta da iyalan su, sosai wajen ke da daraja fiye da tunanin bawa, ga tsaro, kuma a wajen ɓangare ɓangare ne, ba wai iya nan da ya kawo su bane, sai dai nan ɗin yana da tsaro sosai da sosai dan nan kaɗai sojawan nan goma sha biyu ke zagayewa.
Yana isa gidansa bayan ya shige can baya da motarsa ya buɗe bayan, bai tsaya wata wata ba ya jijigo shi ya ciro shi tamkar ya ciro abin wasa, bai kuma tsaya jiran komai ba ya cira shi sama sannan ya sake shi, ji kake kau ya daku da abin motar nan, bai bashi damar dawowa hayyacin sa ba ya daki marfin motar ya rufe da ƙarfi, wanda ƙarar rufewar ta saka shi sake firgicewa sai kuma ya sake tsintar kansa a hannayensa ya jijigo shi ya kuma miƙar da shi a kausashe ya ce" Zaka sanar min abinda nake son ji ko wahalar da kanka zaka yi?"
A rikice sani ya ce" Inna lillahi wa inna ilaihi raju'un, wayyo Allahna, Elhaji ƙarami dan Allah dan annabi..."
" Idan ƙazamin bakinka ya kuma kirana da sunan da ubana ke kirana sai na yi maka shaushawar da zata ringa haɗe maka yaren bakinka, tunda wahalar ka zaɓi ba kanka fine." Daga nan ya yi alamar a ƙaraso.
Wani ƙaton soja ne ya ƙaraso suka gaisa sosai, a nutse ya ce" Ka kai shi can ɗakin bincike, zan waiwaye shi, abinci in ta kama kawai zai ci sai sallah idan yana yi."
Daga nan ya yi tafiyarsa yana ji Sani dreba na ihun kiransa da oga yana faɗin dan girman Allah ya amshe shi har ya ɓacewa ganin sa ya daina jiyo shi gaba ɗaya, sojan nan ya masa wata dariya ya ce" Sakarai, rataye ka zai yi a nan babu ubanda ya sani shikenan saboda ƴan kudade ka sheƙa barzahu, mu je."
Ya ƙarashe yana tankaɗa ƙeyarsa suka nausa can cikin gidan, cikin Sani na ƙugin tsoro da tashin hankali dan kuwa kamar da wasa maganar ta zauna masa a rai, zai iya cewa ya yarda tabbas ana iya rataye shin dan wannan lamari ya shamace shi sosai.
Aswan sai da ya yi wanka sosai ya É—aura alwala bayan ya zubawa su Meem abincinsu yana masu nasihar su ringa cin abinci in an basu, ba suce sai in shine ya zuba masu ba, domin mai kula da su ya sanar masa an basu abinci basu wani ci sosai ba suka bari.
Sallah ya gabatar dole a ɗakinsa dan bai sameta a hanya ba, sannan ya sadda kai yana jin kansa na sarawa da tunanin idan fa a lamarin nan da saka hannun mahaifinsa? Idan fa abin nan ya yi nisan da sai ya yi kuka da hawayensa da dana sanin bincikawa? Kar aje tashin hankalin abin nan na iya dakatar da bugawar zuciyarsa? Idan kuwa hakane wane ya zaɓa a ciki? Haɗuwarsa ko ta wanda ke aikata aikin nan da Allah ko kuwa shiga wani hali a nan duniya?
Idanuwansa dake rintse ya buɗe kunnayensa na sake amsa amon muryarta a lokacin da take kiran zalunci, miƙewa ya yi ya ɗauko wayarsa ya kuma lalubo numbarta yau ma ya buga amma ita ma a kashe, tunani ya afka shin komawa zai yi ya nemi yadda zai ganta ko kawai ya haƙura da neman nata? Kar dai aje ita ma sun tsoratar da itan kamar yadda suka tsoratar da Mani? Tunda abin ya zama in aka ganshi da mutum ne ake jin tsoron kar aje ya faɗa masa wani abu? Gashi ita ma sun taɓa ɗan tsayawa a asibitin ranar da ta masa tsaki ko?
Sai kuma ya sauke ajiyar zuciya ya ajiye wayar ya ƙara baɗe jikinsa da turare ya ɗauki ky ɗin wata motar ya fice bai ɗauki komai ba sai ƙaramar wayar shi ya nufi asibiti.
Sai da ya fara zuwa wajen docter, ya nuna masa yana so a saki ɗansa, yana so nan da sati ɗaya zuwa biyu ya fitar da shi ɗin, a nan Docter ɗin ya taɓo babbar asibitin da ya dace su kai Safwan, aka haɗa shi da likitan yara a lokacin shi ma yana gidansa, suka sake tattaunawa ta vidio call ta computer din Docter ɗin, likitan ya ji komai da komai ya tabbatar masu sun saba yin irin aikin kuma sosai ana miƙewa, nan ya sheda masu eh nan da kwana goma su tabbatar da sun iso garin, ya kuma faɗa masu a tabbatar da an zo da nurse ko docter mai kula da yaron saboda yanayin tafiya da sauransu domin cikin jirgi wani abin na iya taso masa yana da buƙatar kulawar likitan yara, gaba ɗaya dai zaman da ya yi hatta kuɗaɗen da aikin zai ci masa da adadin lokacin da suke iya ɗauka da zaman hotel da kuɗin hotel da abinci da komai sai da aka irga a rubuce aka bashi, shi kuwa yace docter ya riƙe idan tafiya ta tashi sai ya saka komai, daga nan ya shige wajen yaronsa ya same shi yana barcinsa a nutse, nurse ɗin dake kwana wajensa yau tana saman salayya tana lazumi domin magidanciya ce kuma akwai addini, idan ita ke kwana wajen majinyaci takan kwana tana ibadarta ne ma sha Allah.
Ya ɗan jima kaɗan a wajensa, ya masa addu'a sannan ya nufi gidansu, kafin ya ƙarasa wajen Aba sun gama magana da wanda zasu yi siyayar kayan buƙatar su Mani da matarsa da ƴaƴansu, ya zamo yana hayewa yana kashe wayar ne ya samu Aban shi kaɗai yana ziga shayi, sai kawai ya yi zamansa suka shiga shan shayin suna fira.
*YUSRAH*
Aunty Fureira suka fara biyawa suka É—auka kafin Goggo Hindatu, dake Fatila na tsakiyar su ba wanda ya ce ma wani ko da ina kwana kamar dai yara su a dole gaba sukeyi, Hajia kam abun dariya ya dinga bata tana hangen fuskar kowace sai ta girgiza kai a ranta ta ayyana _"Allah ya kyauta."_
Da wannan suka isa gidan su Yaya Mubarak suka shigar da motar su har ciki, gudun kar ya kuma aikata wani laifin ya sa daga nan farfajiyar ya dubi Hajia da kulawa yace" Hajia, nace ko zamu je ɓangaren Mamata sai mu tattauna a can, duba da ina kyautata zaton yau dai zamu samu matsaya akan lamarin na Yusrah."
Da gamsuwa Hajia tace" Gaskiya ne, nima ina fatan haka, tunda ga Yayar Baban ta, ga kuma ƙanwar Maman ta."
Intisar da ke kallon shi a ranta kawai ta ji jiya bayan ya je wajen Mama akwai abinda ya faru da ya sa ya ce a je can, to ba komai indai za'a bata Yusrah, matsalar kawai bata so Mama ta kawo mata wannan bidi'o'in nata da zasu kawo cikas wajen damƙa mata Yusrah.
Haka suka rankaya zuwa falon na Mama bayan Yaya Mubarak ya sanar da ita baƙi za su shigo, haka suka shiga sabuwar gaisuwa ta ɓarke an ɗauki lokaci ana gaisawar kafin falon ya yi shiru, Yaya Jafar ne ya dubi Intisar yace "Ina ga sai ki kira mana Yusrah anan ko? Dan duk inda aka je aka dawo dole za'a so jin ta bakin ta ita ma."
Jinjina kai tayi da ladabi ta miƙe ta nufi nata ɓangaren, Goggo Hinda tunda suka shigo take ƙarewa gidan da komai kallo tana so ta ji ta yadda Yusrah ma ta iya samun damar sanin mutanen nan, me ye alaƙar ta da su? Me ya sa kuma har suke wani rigengenton son taimaka mata kamar wata zinariya?
*Sanda* Intisar ke gaba kaɗan Yusrah na binta a baya, hangen ƙofar Bilal take tana murmushi, wai dan rashin mutumci irin na Bilal tun shekaran jiya rabon da ya leƙo inda take, ba dan komai ba sai dan yana ganin yanzu ya dafe Goggon Yusrah, dan haka tana sanin inda take za ta tuntuɓe shi, shiyasa ya daina yi musu kai da kawo a ɓangare, shiyasa ita ma kuma da Yaya Mubarak duk suka share shi da niyyar ranar da ya shigo wajen su ya ga Yusrahn, duk da dai ta san akwai yiwuwar kafin a gama zaman ya leƙo tunda suna shiga gaida Mama duk safe kafin su fita, amma dai tana fata yau ba zai fita da wuri ba har su bar wurin.
Sanda aunty Fureira suka haɗa idanu da Yusrah, sun yi kuka har sun gode Allah, aunty Furera ta ɗaga fuskarta tana kallonta, shar cikin sutura mai kyau, ƙamshi ta ko ina jikinta, idanuwanta harda kwalli cike da tausayawa ta ce" Ki yi haƙuri, ki yi haƙuri, ki yi haƙuri, Allah ya jiƙan su Yaya, Allah ya sa sun huta, in sha Allah sun barki a hannu mai kyau domin ba zan