Showing 189001 words to 192000 words out of 397328 words
ya ce a'a sannan ya fice, a tsanake ya fara shiryawa har ya gama sannan ya zauna dan cin abinci yana kuma latsa wayar sa. A tsanake har ya gama ya miƙe ya sake kitsawa sannan ya ɗauki abinda zai iya buƙata ya kama hanyar ficewa daga ɗakin, saida ya buɗe ƙofa ya fita zai rufe ta sannan ya hangi maganin nan, zubawa maganin idanu ya yi yana kallo kamar yana tunani, me ya tuna? Me ya gani? Sai kawai ya taho a sukwane yana faɗin _"Fitinanniya, kamar wani ɗan ta za ta bani uamrni, har da wani cewa *matsayina na likitar ka*, ni ɗin? Rainon wayo kawai."_
Maganin ya ɗauka tare da robar ruwa da ya sha ya rafe ya ɓalli biyu ya haɗiye sannan ya aje robar ya fita yana soka maganin aljihun suit ɗin shi dan yana tunanin ba zai dawo da wuri ba bayan ya duba ɗan sa zai wuce wasu uzororin.
*Ƙwarai* Yusrah ta ji rufe ɗakin shi, dan haka ta leƙa ta ƴar hudar nan kuma ta ga gilmawar sa cikin shirin, tana buɗe ƙofar dan ta tabbatar wai fita ne zai yi da gaske ya bar ta har ya shige lift sai wani azababben sanyayyan ƙamshin oud wood ɗin shi da ya bar mata alakoro, da haushi ta koma ta rufe ɗakin tana matso ƙwallar takaici ta nufi wayar ta da taji saƙonni nata shigowa, zaune ta yi tana dubawa ta ga aunty Intisar ce ta turo mata voice ta share hawaye ta danna tana saurarawa, amsar voice ɗin da ta tura ma Yaya Mubarak ne ta dawo mata da shi, ita kam ta faɗa musu gaskiya ne Aswan shine mutumin kuma bata musu ƙarya ba, shine yanzu aunty Intisar ta maido mata da cewa _"Yusrah in dai ina da daraja a wurin ki ki ɗauki kirana, wai me ya sa kike min hakane? Kin san da zan iya zane ki ko?"_
Saida Yusrah ta yi dariya sannan ta kira aunty Intisar da kan ta ta WhatsApp amma ba kira mai motsi ba, kamar tana jira kuwa ta ɗauki kiran tana faɗin _"Yusrah sarauta, Yusrah yanzu ni kike wa haka? Saboda me dan Allah?"_
Da tausasawa Yusrah tana murmushi tace _" Ki yi haƙuri auntyna, na rasa me zan faɗa miki ne idan na ɗaga, shiyasa, amma wallahi ki yarda dani, wa..."_
Da sauri ta dakatar da ita da cewa _" Kinga Yusrah, na fahimce ki fa, baki min laifin komai ba kuma ban ga laifin ki ba, abinda kikayi ko waye ma shi zai aikata, yanzu abinda nake so da ke shine, Anna ta ce na faɗa miki indai har Safwan ɗan Akhi shine ƙanin ki, to ki kwantar da hankalin ki, ki bishi sau da ƙafa kar kiyi abinda zai ɓata masa rai ko makamancin haka, Anna ta min alƙawarin kuna dawowa za'a zauna sai ayi sulhu akan yaro a sama muku maslaha in sha Allah, kin ji Yusrah?"_
Yusrah ta amsa da _" To aunty, in sha Allah zan kiyaye, na gode sosai."_
Hira suka ɗan taɓa tana tambayar ta yanayin garin bai mata komai ba? Ya jikin Safwan? Tana cin abinci da shan magungunan ta akan lokaci? Kafin daga bisani ta ce ta gaida Yaya Mubarak sukayi sallama. Sa'ar ta ɗaya waya ta hana ta kaɗaici, dan tana ta WhatsApp ɗin ta da su Maryam, Fatila, twins da Abrar da duk Intisar ta basu lambar ta, ga kuma aunty Fureira da ita ma ta samu lambobi daga gare ta na ƴan uwa, uwa uba kuma mai gayya mai aiki Bilal da suke ta shan wata irin soyayya da ita ta ƙi yarda soyayya suke a haka, a ganin ta har yanzu bata bashi amsa ba, amma shi kawai folawa yake da ita kogin soyayya suna shan hirar su.
*Dr. Hamat*
Kira na 12 kenan yana sake aikawa lambar Dr. Siddik, amma girman kai da jin ya fi ƙarfin sa ya sa da ya aika kiran sai ya yi gaggawar katsewa, har saida dai ya tabbatar ba sarki sai Allah sannan ya aika kiran ya rintse idanu bayan ya saka wayar a speaker. *Shi* kan shi Dr. Siddik ɗin mamaki da al'ajabin haka ya sa ya jima bai ɗaga kiran ba, dan ko aiki zai haɗasu da Dr. Hamat ya yi ta kiran shi kenan yana sharewa, shi kuma wallahi dangantakar dake tsakanin cousin ɗin shi (Yaya Mubarak) da kuma Hamat ɗin tasa yake shanye komai, ko ba komai matar sa Intisar tana da kirki sannan ba haka iyayen ta suke ba, har saida kiran ya yi kamar zai tsinke kafin ya ɗaga, dan saida ya shiga tunanin me kuma ya sa ya kira shi? Maganar asibiti ko ta gida? Kai duba ba ɗaya daga ciki da ta taɓa haɗa su, shiyasa ma da ya ɗaga ya yi sallama ya saurara ya ji da me ya zo.
Saida Dr. Hamat ya numfasa ya ja lokacin sa ya gama shan ƙamshi, kafin da izza da isa yace _"Yarinyar nan da ka turo consultation ranar, *Dr. Yusrah*, likita ce mai tsada Siddik, ta fi ƙarfin aiki a ƙarƙashin ka ko wanin ka bani ba, zan iya samun lambar ta ko adreshi?"_
Tunda Dr. Siddik yake bai taɓa jin an raina masa wayo ba irin na yau, amma sai ya jinjina kai irin yana daidai da zamanin shi ɗin nan, tunda shi bai san ana ɗaga masa ƙafa dan tsufan sa ba, to zai yi maganin shi, saida ya gyara zaman shi shima cike da ƙasaita sannan yace _"Allah sarki oga, ka ce nayi nasarar samun ɗaya a cikin dubu? Ni a sauƙaƙe ma na ɗauke ta da fari, hakan ya sa ban ko san makwantar ta ba bare lambar waya, amma yanzu da na ga irin su oga na rububin ta, zan sake kulawa wajen riƙe ta gam ko da ta hanyar mallaka mata duka abinda asibitin nan ta samu ne a matsayin albashin ta na wata ɗaya, anything else?"_
Da matsiyacin mamaki Dr. Hamat ya dubi wayar, wai har shi Dr. Siddik yake faɗawa haka? Shi fa? Ya manta ko wa ye shi? Shi fa kamar baban sa ne a harkar likitanci, shine har yake tambayar sa da kuma abinda ya rage? Lallai ma ya yarda *son Yusrah yake*, ba dan haka ba shi ne zai kira Siddik har ya faɗa masa magana? Da irin takaicin nan ya kashe wayar tare da cillata ta bugi sitiyarin mota sannan ta faɗa ƙasa, bai damu da wayar ba sai haɗa kan shi da ya yi da sitiyarin motar ya sake liƙe idanuwan sa gam yana feso wani irin zafi da zuciyar sa ke yi mishi.
Ya Allah! Ya Allah! Shine abinda yake ta maimaitawa a ran shi, tabbas yana cikin babbar jarabawa, a rayuwar sa bai taɓa tunanin zai iya son wani abu haka ba, ko maman su Jolie makaranta ta ganshi ta kuma maƙale masa, shi idan aka ce asiri ma ta masa ya aure ta ba zai yi mamaki ba, dan gaskiya ba ma irin ƙirar matan da yake so bane, amma yanzu da girman shi da komai ya ji kawai yana son auren wata ƙaramar yarinya, sannan ya ji ba abinda yake son gani kamar ita a yanzu a rayuwar shi, yadda fa yake ji kamar yafi son ganin ta ma akan ƴaƴan sa, wannan wace irin jarabawa ce?
*_SAJEERAH_*🖊️
*Alhamdulillah.*
30/05/2024, 21:23 - samiraharounayacouba: 👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕👩❤️👨🧕
_RUBUTAWA, TSARAWA_
*SAJIDA NIJAR*
_TARE DA_
*SAMIRA HAROUNA*
_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪
*LITTAFIN KUƊI*
_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*49*
Taɓe baki Nawal ta yi tana kawar da kai zuciyar ta na jin ita fa gaskiya bata ɗaukar irin wannan halayen, haka kawai! Yayin da Manal ta sake riƙe kayan da Nabihat ɗin ta kwaso daga drower za ta zuba a akwatin ta tana faɗin "Nabihat wai me ye haka? Ina za ki tfi kike ta haɗa kaya? Wani abu aka yi miki ne? Ko dan abinda ya faru ne tun jiya za ki tafi?"
Cikin shasheƙar kuka kamar wacce aka kawo wa saƙon mutuwar iyayen ta ta dubi Manal ɗin tace "Manal gida zan tafi, gidanmu zan tafi ni kawai, ki ƙyaleni dan Allah."
Da kulawa Manal tace "To ki tafi gidan ku da aka miki me anan ɗin? Kin manta sati kika ce zaki mana? Kuma Anna ta sa aka ƙara miki wani satin, me ya faru da zaki ce za ki tafi haka kina kuka?"
Saida ta sake zuba wasu kayan a akwatin sannan tace "Tafiya zan yi Manal, bana jin daɗin zaman ne kawai, ba'a min komai ba."
Jinjina kai Manal tayi tace "Shikenan, bari na faɗawa Anna ita zaki mata bayani."
Ficewa ta yi a ɗakin Nawal kuma ta sake gyara kwanciyar ta tana mai ba wa Nabihat ɗin baya yadda ba ma zasu haɗa fuska ba, tun jiya take jin haushin ta wallahi, yo duk lalacewar Abrar ai tafi son Abrar da Akhi ɗin su idan ma hakan zai yiwu, amma har ta tsaya tana nuna kishi akan shi haka wanda bai ma san tsiyar me suke yi ba dukan su.
Manal na zuwa falon Aba a nutse ta nemi izini Anna ta bata izinin shiga, amma duk da haka saida ta sake yin sallama sannan ta shiga ta durƙusa gaban su, da ladabi ta kalli Anna tace "Anna, dama Nabihat ce wai za ta tafi, shine nace bari na zo na sanar da ke, ina ta bata haƙuri amma ta ƙi haƙura."
Da mamaki duk suka kalle ta har Aba ya yi gaggawar tambayar "Za ta tafi ina kuma? Har hutun nata anan ya ƙare ne?"
Kallon shi Anna ta yi da kulawa tace "A'a, ai ko satin ba ta cika ba."
Sannan ta kalli Manal tace "Me aka mata to? Tana ina yanzu?"
Da girmamawa tace "Tana ɗakin mu, nima ban san me aka mata ba wallahi, kuka kawai na samu tana yi da haɗa kaya wai ita tafiya za ta yi."
Ajiyar zuciya Anna ta sauke suka haɗa idanu da Aba, sai kuma ta kalli Manal ɗin tace "Shikenan, je ki turo min ita nan?"
"To." Ta faɗa tana miƙewa ta fita, da mamaki Aba ya sake cewa "To me yake faruwa ne? Ko wani abun ake mata ne da bata jin daɗin sa?"
A nutse Anna tana waina masa idanu tace "Baba ga twins me kuma za'a mata da ba zata so ba? Bari dai ta zo sai muji."
Suna nan zaune Nabihat ta yi sallama Anna ta bata izinin shiga sannan ta shiga, gaban Annan ta durƙusa ita ma kamar yadda Manal ta yi tana ta murzar idanu, da kulawa Anna tace "Nabihat, Manal ta ce wai kina haɗa kayan ki, hakane?"
Da shasheƙar kuka kalar za ta haɗe rai tace "E Anna."
"To ina za ki tafi?" Anna ta tambaye ta tana tsare ta da idanu, amsa ta bata da "Gida nake so na tafi Anna, dan Allah kar ki hana ni."
Girgiza kai Anna ta yi tace "Ba zan hanaki ba, amma ki bani ƙwaƙwaran dalilin ki na tafiya, idan na gamsu sai na bar ki."
Sunkuyar da kai ta sake yi tace "Ba komai Anna, kawai ina kewar gidan ne, ina so ne na ga Mama."
Sosai Anna ta zuba mata idanu tana kallo kafin daga bisani ta jinjina kai tace" Shikenan, tashi ki je zan neme ki, amma ki dakatar da haɗa kayan nan, kin fahimta?"
Jinjina kai ta yi alamar to sannan ta miƙe ta fita daga falon, shiru ne ya biyo bayan fitar ta na wasu daƙiƙu, Aba ya fara cewa" Kina ganin gaskiya ta faɗa? Ni sai naga kamar akwai damuwa ko?"
Numfashi Anna ta sauke sannan ta shiga faɗa masa abinda ya faru jiya da dare tsakanin Nabihat ɗin da Abrar, da kuma abinda take tunani akan Nabihat ɗin na son Aswan ne wanda shi kuma bai san da haka ba, buɗar bakin Aba sai yace" Dan wannan ne za ta dinga kuka haka? Mu kan mu ai babu abinda muke so kamar ganin auren jikan Anza, dan haka yau ba sai gobe ba zan kira Chef ya same ni muyi magana akan su, wannan ai ba wata matsala bane."
Yadda yake maganar ka rantse da Allah kuwa ba wata matsalar bace, sai dai Anna tana ganin kamar ya manta da wa ye Aswan Aliyu Anza, baya ga haka shi kan shi Aban da zai yanke hukuncin nan sannan Aswan ya nuna a'a ba ya so fa, tana da tabbacin ba zai tilasta masa ba, tunda ba yaron da za'a ma auren dole ko na haɗi bane, Aswan fa a arba'in da biyar kaɗan ne bai cika ba, da kuma aure ya yi da yanzu kusan saurayi ko budurwa ce a gaban shi, kawai wataƙila rabon sa ne ke nesa. Amma a yanzu ba za ta ce komai ba, dan haka tana sauraren shi yana ci gaba da nuna ai ba wani abun damuwa anan ita dai ba ta ce komai ba.
*G. MUBARAK*
Zaune suke a falon Hajia babba su uku ƴaƴanta maza, da yaya Mubarak, da ƙanensa suna taɓa hira, wacce yawancin hirar Hajia na yi masu sharar shanye da nasiha a kan harkar girman nauyin ta dake kansu, da nunin cewa kar su yarda su saki matansu su ɗauke hankulan su da yi mata hidima, idan suka yarda wannan tsinantaka ta same su sun kaɗe a duniya da ƙiyama, Yaya Mubarak ya yi murmushi ya karɓi zancen a tausashe sosai ya ce" In sha Allah Hajia, Allah ya taimake mu, daga Zahra'u har Intisar ɗin Allah ya sa ƴaƴa ne da suka san darajar iyayensu, shi yasa a kullum nake ganin kyautatawa daga wajen su zuwa gare ki, Allah ya ƙara basu ikon kyautata maki domin ni dai abinda Intisar zata min kawai ta birgeni kenan, kuma tun tana amarya da na faɗa mata cewa Intisar ba boka ba malam idan farin haƙorina kike so ki so Hajia ta kuwa so ɗin shi yasa nake kyautata mata sosai a zamantakewar mu."
Hajia ta ɗan taɓe baki ta cira hannu tana furta" Kayya! aa kayya!"
Shi kam Imran danne dan'en wayarsa yake yi da ƴan matansa, karatun nan na Hajia gaskiya shi bashi da time ɗin sa, ya gama shanye karatun nan ba yau ba, shi da Hajia sai dai ido idan tana wannan maganganun, shi bai san me hajiyarsu ke so ba, tsinannun sirikan da irinsu ta samu da an shiga uku, ma sha Allah, Allah ya wanke ya bata amma kuma kullum cikin mita da nuna na banzan aka bata take yi, shi kam bashi da bakin magana a kan lamarin nan, ko zaman nan da ta ƙirƙiro yi masu yanzu yana takura shi, sai dare ya yi sai kawai ta sa su zo ta saka su a gaba ta yi ta mitarta, yau kwana huɗu kenan da bai yi yawon dare ba abin ya fara damunsa sosai fa.
Bilal da ya rafka tagumi idan Hajia ta fara magana sai ya ɗago yana kallonta har ta ajiye, in yayansu ya ɗauki maganar shi ma sai ya ɗago yana kallonsa har sai ya ajiye sannan ya cire kansa ya fitar da huci a hankali ya ce" Hajia, ni dai ina so idan Yusrah ta dawo a yi maganar aurenmu, mun gama fahimtar juna da ita mun gama yarda zamu yi aure, yau kwananta huɗu a can, saura kwana goma a irgena, dan Allah idan ta dawo a yi a aura min yarinyar nan kafin wani ya ce yana so min ita ya ɗaga min hankali."
Yaya Mubarak ya yi tsuru tsuru yana kallon Bilal, Hajia kuwa dan takaici ta dafe goshinta ta kasa furta ko da a ne, har sai da yaya Mubarak ya yi dariya yana girgiza kai ya ce" Ja'iri, kai baka jin kunya ne? To sai na ga dama zan baka, ka ci gaba da yin sallar dare kawai kana faɗawa Allah, Allah ya sa in yarda in baka."
Hajia wani takaicin ya ƙara ɗaure mata zuciya, ta cira kai tana fitar da huci ta masu gum bata basu amsar komai ba, domin ita kaɗai ta san irin yadda maganar nan ke ci mata tuwo a ƙwarya, ta rasa gane inda zata duba ta riƙe ta ce mariƙin abin kirki ta yi a tafiyar nan ta autanta da yarinyar nan, wallahi kamar yadda maƙociyarta kuma ƙawarta ta faɗa ne, mutum fa katse ire iren abubuwan nan yake yi idan ya ga iya shege ne, ta yaya za'a yi tana ji tana gani zata ga kashi da rana da dare ta zo ta saka kafa? A bayyane yake in dai ta aminta da wannan tafiyar sunan ɗan ta shashashan namiji, namijin dake riƙowa mace jaka ba mahaifiyarsa ba ba komai ba? Me za ta ce ta yi kenan idan har ta yarda aka yi wannan abin? Hum! In dai abin nan suke so a yi to kuwa sai ya zama gagara