Showing 132001 words to 135000 words out of 397328 words

Chapter 45 - WATA TAFIYA COMPLETE HAUSA NOVEL

sajida   

26 Aug 2024

70042

ƙiri ƙiri Fatila ta ce" Umma, ni fa a yi duk abinda za'a yi matar nan bata shafi Yusrah ba, ina baƙar zuciyar ta yi over."

Yaya Mubarak ya sauke ajiyar zuciya, cike da tausayi da ƙarin jin burin taimakawa Yusrah har ransa ya ce" Shikenan, Allahn da ya amshi iyayenta ba dan sun masa wani laifi bane, kuma su da suka rigaye mu gidan gaskiya basu yi gaggawa ba, mu ma zamu amsa kiran nan ko ba daɗe ko ba jima, fatanmu Allah ya sa mu cika da kyau da imani, mutum kuwa ruwansa ya aikata alkhairi ko sharri, kowa abinda ya kwa;a shi zai ci, ni yanzu komai ya daina bani mamaki da lamarin duniyar nan, domin a bayyane take da abubuwan da manzon Allah Sallallahu alaihi Wa sallam ya zayyano na alamomin ƙarshen ta, Allah ya sa mu dace."

Da amen aka ringa amsawa, harda Yaya Jafar domin shi ma da kansa bai san haka ya faru ba sai yanzu, haba gaske Hajia a ranar sai da ta leƙa asibiti dan yanayin jikinta, kai Allah shi kyauta.

A nutse Yaya Mubarak ya dubi Hajia da Yaya Jafar ya ce" Hajia, da ina da wata shawara, ba dan na isa ba, ba kuma dan na fi kowa sani ba, a ganina, ya dace mu nemi danginta na ɓangaren mahaifiyarta, mu zanta da kowa, idan har aka bamu sai mu zo mu shirya a tsakaninmu, idan har da hali Hajia sai a duba a bani riƙon, ina roƙon a bani dan ina so in sama mata aiki, in kaita makaranta in kuma ja shara'a da wanda ya ɗauki Safwan, na karanci duk da ba aikin da nake yi ba kenan a yanzu, kuma mahaifin ita madame babban mutum ne da zai iya tsaya mana, in sha Allah duk inda yaron ya shiga za'a samo mana shi, idan har kin yarda Hajia zai zamo tana nan ne kawai na wasu lokuta amma kuma za tana zuwa wajen mamanta tana ganinki a duk lokacin da ta so, ɗan uwa ina neman alfarma in har da halin hakan a duba."

Ya ajiye yana sauke murmushin da ya sa Hajia ta sake dubansa da kyau, ƙwarai tun a jiya da ya kira ya sanar ta samu barci dan ta tabbata da ace wani sakarai ne ba ma zai neme su ba, kuma tunda suka zauna idan ya buɗi bakinsa tabbas maganarsa mai ma'ana ce da kuma tafe da tsoron Allah, duk da mutum na yau ba'a cika shedar sa ba, ita dai ta ji ya mata, balle kuma in har sirikinsa zai shiga lamarin ta tabbata sai dai in Safwan mutuwa ya yi, amma in dai yana raye tabbas za'a ga yaron, dan haka ta dubi Jafar ta kuma kalli Yusrah.

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" Amma, ya ya za'a yi a ga dangin nata na wajen mahaifiyar nata? Kuma su ɗin sa bar mana ita ne?"

Murmushi ya yi ya ce" Ina kyautata zato, in sha Allah in dai aka gansu zasu fuskanci abinda muke nufi, kin ga yanayin karatun Yusrah, takardar aikinta, rayuwarta gaba ɗaya ba irin ta can bace, in har sun yarda sun ganmu sun ga manyan mu, zamu nemi alfarma idan har ita ma Yusrah ta zaɓi hakan Alhamdulillah, in kuma ta ji ta fi son zama da su zamu amince mu bada dukkan gudunmuwar da ta dace, amma na san a yanzu ba zata taɓa iya binsu ba tare da ta ga Safwan ba, ni kuwa litinin na yi zan shigar da ƙara in je in kai takardar wajen dreban in yaso mu shiga kotu dan ba zan tsaya sauraron kowa a kan maganar batan ɗan mutum ba."

Wani irin sanyin daɗi ya ratsa zuciyar Yusrah wanda ya sa hawaye cika mata ido ta ɗaga fuskarta a sanyaye ta kalli Yaya Mubarak sannan ta kalli Hajia, a hankali ta fashe da kuka ta sake rungume ƙafafuwan Hajia, a sanyaye ta ce" Hajia, Allah ya sa a ga Safwan, wayyo Allahna ko yana cikin wani hali?"

Masu saurin kuka kam tunda ta fashe da kuka suka fashe da shi, sai da ya zamo mazan na bada baki sannan suka yi shiru Hajia a tausashe ta ce" in sha Allah za'a ganshi, kuma in sha Allah cikin hayyacinsa, muna ta addu'a bi'izinillah adu'armu ba zata faɗi ƙasa ba ƴata, kin ga Intisar a kawo karin ta karya sai mu juya domin mahaifin ita Tasneem yace wai yana son ganina zamu je mu zauna da su, ba komai Allah ya sa hakan ya fi zama alkhairi, ki daina kuka in sha Allah kin gama kuka, Allah na tare da ke, maza share hawayen, ni ina ƙawarki Maryama?"

Yusrah ta yi murmushi tana faɗa mata yadda suka yi, har aka kawo abinci aka zuzzuba suka shiga ci, mazan kuwa suka koma gefe suna ɗan ƙara sanin juna da canzawar lambobi dai da sauransu har suka gama suka masu rakiya wajen motarsu suka tafi da nufin ko me ake ciki zasu taɓo juna, Hajia kuwa tace zata dawo gobe da kayayyakin Yusrah.


Suna dawowa Yusrah ta nufi kicin, yanayinta tunda ta ji yadda za'a yi neman Safwan ya canza, ɗinkewar fuskar nan ta ragu sosai, har murmushi take saki bayyananne sai kuma ta sauke ajiyar zuciya.

Intisar cike da farin ciki ta ce" Bab, ina so mu je shopping da Yusrah please, ina so kuma a taɓo shagon masu kayan gadaje su canza mata komai da komai, nd ina so a..."

"Madame ba'a baki ba fa." Ya faɗa yana katseta da murmushi.

Turus tayi ta ce" Haba bab."

Ya yi ƴar dariya ya ce" Sai da yamma zaku fita, but kar ki manta ba'a riga aka baki ba, ko Hajia na tabbata da sauran rina a kaba, tana son Yusrah sosai."

Ta cuno baki tana ɗora kanta gefen hannunsa ta ce" Nima ina sonta sosai, Yawwa bab har gida zamu je in kaita wajen su Anna duka su ga nima ƙanwata sabuwa da suka ƙi bani ƴaƴansu."

Da mamaki ya ɗan zaro ido, ita kuma ta yi gaba tana dariya ta nufi kicin ɗin ita ma.



*******************



A lokacin da su Hajia suka ƙaraso gida, tun a farfajiyar gidan mai gadi da girmamawa ya sanar masu cewa sun yi baƙuwa bayan fitar su, kuma ta ce a ce wai ita maman Yusrah ce.

Hajia da mamaki ta tambaye shi maman "Yusrah kuma?" Tabbatar mata ƙwarai haka dai matar ta ce, da kula Hajia ta tambaye shi "Ta tafi ne?"

Shi kuma da girmamawa yace "E Hajia, dan da suka zo na faɗa musu ban san lokacin dawowar ku ba, sai ta ce za ta tafi amma za ta dawo ko zuwa bayan sallah magriba ne, har ta nemi alfarmar idan ta zo na barta ta shiga ta gan ki, duk da kuwa na sanar da ita an kwana da jimamin ɓatan Yusrah."

Ɗan murmushi Hajiar ta yi tace" Allah sarki, ka yi haƙuri fa na manta bamu sanar da kai an samu Yusrah ba, tun daren jiya aka kira aka faɗa mana an gan ta, shine muka tafi da safen nan, amma..."

Cike da bayar da umarni tace" Idan ta dawo anjima ɗin, kai tsaye ka shigo min da ita ciki, nima zan so na gan ta."

Da kulawa da kuma murna yace" To Hajia, in sha Allah zan yi yadda kika ce, ma sha Allah, na tayaku murna wallahi."

Saida suka shiga ciki Yaya Jafar ya ga zaman mahaifiyar sa dan tun a hanya ya ce kawai ta jinkirta kiran mahaifin na Tasneem, shi ba ma ya so a wahalar masa da mahaifiya akan wannan banzar matar da wallahi ko me za'ayi ba zai mayar da ita ba, kafin nan ya tafi zuciyar sa cike da son yi mata tambayar shin idan dangin Yusrah sun amince ta zauna anan? Za ta yarda ta bar wa su Intisar ita ne? E ƙwarai ya yarda suna da kuɗi kuma sun fishi kuɗin, amma daidai gwargwado zai iya kula da Yusrah shi ma, kuma ya kula kamar farin jini a jikin ta yake da klwa ke son ya zauna da ita. Haka dai ya musu sallama ya tafi Fatila ma tambayar da take son yi kenan amma ta kasa saboda bata so ta yi azarɓaɓi.



*INTISAR*


Tun jiya da Yusrah ta shigo gidan zuwa wayewar garin yau ba ta wani tsaya duba wayar ta da kyau ba duk da kuwa ta san tana da muhimman abubuwa da take gabatarwa da wayar, sai yanzu da ta ga su Hajia sun tafi babu Yusrah, sannan mijin ta ya ce su je siyayya anjima, tabbaci ne na shima ai zai sake dagewa kan aba su ita ɗin, sai ta ji nutsuwa ta zo mata da har ta ɗauki wayar na farko tana so ta ji lafiyar yaran ta biyu ƴan mata dake hannun babbar Yayar su Mubarak ɗin dake aure U. S, wanda take ta addu'a takardar da mijin ta ke nema ta fito a ce yau an turo masa gayyata zai je ce, hakan zai sa kula da yaranta ya dawo hannun ta ko dan ganin kalar tarbiyar da ake basu. Na biyu kuma Anna da kowace safiya take farawa da gaishe ta sannan su sha hira da labaran abinda ke faruwa, sannan ta fantsama ga harkokin kasuwancinta da take gudanarwa daga cikin gidan ta ba tare da wata doguwar wahala ba.

Murmushi ta saki mai ƙayatarwa tare da dannawa lambar Anna kira da ta ga ita ta kikkira ta, ta sani kuma jinkirik da ta yi ne wajen kiran ta ya kawo haka da kula son ta ji lafiyar ta, haka ma Nabihat ta kira ta saidai kiran bai fi awa ɗaya ba, da kuma wasu sauran lambobi haka.

Anna na ɗaga kiran ta yi sallama daidai da fitowar Yusrah da ta shiga taimakawa masu aiki wanke wanke da gyaran madafar, zaune ta yi kan kujera a ɗan tsome haka tana murmushi kanta a ƙasa saboda ganin auntyn nata na waya, kula daga yadda ta ji suna gaisawa har tana shagwaɓar ita fa jikin ta da sauƙi, sai ta ji a ranta wataƙila Maman ta ce, Allah sarki rayuwa. Haka ta gada dama yau farin ciki gobe akasin haka.

Jin Intisar na faɗin _"Anna, dama ina so na tambaye ku game da lamarin ɗan nan na Akhi?"_

Dan haka ta sulala ta miƙe ta bar wajen ta koma madafa dan ta baro dama suna wankin naman zabi ne ta basu wuri su gama kafin ta koma kama musu da wani abun, ita kanta Intisar sai ta ji daɗin haka dan gaskiya tana son jin ya akayi Yayan ta AA ya samu ɗa ne wai? Daga ɓangaren Anna amsa mata ta yi da _"Uhum! Ina jin ki?"

A nutse cikin tausasawa tace _" Anna, wai ta ina maganar yaron nan ta fito ne? Akhi dai bai yi aure ba, sannan ni ban taɓa jin labarin yana soyayya ba, sai kawai kuka faɗa mana ɗan sa kuke zuwa dubawa a asibiti."_

Daga wajen Anna dariya tayi tace _" Inti, ki kwantar da hankalin ki, yaron nan ɗan Yayan ki ne, abinda ya sa ban faɗa miki komai a kai ba shine, yanzu haka maganar yaron sa hannun alƙali ne kawai ake jira da zai tabbatar masa da ɗan sa ne kuma babu mai raba shi da shi, sannan shi ma Yayan naki ya ce a daina faɗawa kowa maganar yaron har a tabbatar masa da shi a dokance, ke hatta sunan shi ma yau da ya leƙo mu da safe tsawa ya ma su Nawal akan su daina faɗa, saboda wai yana so ya canza masa suna ma ta yadda dangin shi idan suka ganshi ba zasu taɓa shaida sa ba, wannan shine."_

Da matsanancin mamaki na abinda ke kai kawo a ran Intisar tace _"Anna, hakan na nufin Akhi y..."_

Katseta Anna ta yi da cewa _" Intisar, ki bar maganar nan nace miki, alƙalin da zai sa hannun ne ma ba ya gari shine dalilin tsaikon da aka samu, amma ana tabbatar masa da ya zama ɗan sa, zaki san komai da komai a kan sa."_

Ajiyar zuciya Intisar ta sauke tace _" Shikenan Anna, nima idan na gama daidaita lamarin ƙanwata zan zo na duba shi."_

Da mamaki Anna tace _" Ƙanwar ki? Wace ƙanwa kuma?"_

Murmushi Intisar ta yi tace _" Anna, ai yau gidan nan yaƙi nayi akan wata ƙawata, Anna mun fara haɗuwa ne a asibiti da ita kasancewar ta likita amma tana aikin stage ne a lokacin, to da fari Bilal ne..."_

Labarin Yusrah ta ba Anna, amma ba ta faɗa musu hatsarin da ya same ta ba saboda a tunanin ta su Anna suna da tsari akan komai, dan haka zata iya yin faɗa ta ce ta aje wacce bata sani ba gidan ta ba tare da ƙa'ida ba, dan haka sai ta ɗora da _" To iyayen ta da suka rasu a wani accident da tana hannun Goggon ta ne, to bata jin daɗin zaman shine kawai jiya muka zauna a kan ta, daga ƙarshe dai Anna an bar min ita a hannuna."_

Daga ɓangaren Anna cikin harshen buzanci tace _" Ha Yallah! Intisar rigima ko? Wato dan Mubarak yana miki duk abinda kike so ko? To kuma ke kin yarda da zaman ta da ke ɗin?"_

Da sigar shagwaɓa Intisar tace _" In sha Allah Anna ba komai da zai faru, ki ta min addu'a."_

Murmushi Anna tayi daga wajen ta tace _" Shikenan to, Allah ya tsare duk wani abun ƙi, Allah ya sa ta zamar miki alkairi, kika ce likita ce?"_

A nutse tace _" E Anna, likitar yara ce."_

Ɗan jim Anna ta yi saboda tuna AA ya mata maganar likita ya ce ya samu nurse da za ta raka su wajen yi ma Safwan aiki, amma a lokacin sai ta yi shiru tace _" Shikenan, wataƙila zan iya tuntuɓar ki akan lamarin ta, tunda tana da ilimin ta, za ta anfane shi in sha Allah."_

Da jin daɗi Intisar tace _" In sha Allah Anna, ni da Abban yara ma burinmu kenan samar mata aiki."_

Amsa mata Anna tayi da _" Allah tabbatar da alkairi."_ Kafin daga bisani suyi sallama, amma sai Intisar ta faɗa kogin tunani, Yaya AA da ɗa? Ɗan ma ana rigima akan sa? Har yana neman canza masa suna dan kar dangin shi su gane shi? Hakan na nufin mahaifiyar yaron fa kenan da ƴan uwan ta ko? Shin dama da Yaya AA ya ƙi yin aure abinda yake aikatawa kenan a gari? Ko kuma dai wannan ma ya faru ne a tsananin rabo da kuskure? Shiyasa ma har ya dage sosai akan shi haka har ya shiga kotu saboda yana da tabbacin gudan jinin sa.




*_SAJEERAH_*🖊️



*Alhamdulillah.*
23/05/2024, 08:39 - samiraharounayacouba: 👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕
*WATA TAFIYA*
👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕👩‍❤️‍👨🧕


_RUBUTAWA, TSARAWA_


*SAJIDA NIJAR*

_TARE DA_

*SAMIRA HAROUNA*


_VIVE LE NIGER_ 🇳🇪


*LITTAFIN KUƊI*


_Assalama alaikum masoya 'yan mutan niger, ga wata sabuwa da yardar Allah, *WATA TAFIYA*, hak'ik'a nasan kun san daga jin *WATA TAFIYA* tare da gwarazanmu a cikin wata sabuwar *TAFIYA* kun san abun zai ƙayatar, ba sai mun cika ku da surutu ba, kun san hannayen mutanen naku na Nijar, dan haka ku garzayo a yi da ku._

_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._

_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._

_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._



_Bismillahir rahamanir-rahim_



*36*




Nabihat ta kira dan suna yawan magana a waya dama, Nabihat na ɗaukar kiran ta fara rigima da _"Aunty Intina yau ko lokacina ma baki da shi kenan? Ni da na kira dan na faɗa miki zan kawo miki ziyara na huta da ƙorafin da ake min na ban zo bikin Zahra'u ba."_

Taɓe baki Intisar tayi tana murmushi tace _" Nabihat, ni za ki ɗauka shashasha ko? Abokiyar wasan ki zan zama kuma? Kullum ki ce min za ki zo kuma ba kya zuwa?"_

Dariya Nabihat tayi tace _"Yi haƙuri aunty Intina, wallahi zan zo miki in sha Allah, ni da ma nake so na zo nayi kwana biyu gidan naku, ki yi haƙuri mana."_

Nan ma ƙara taɓe baki ta yi tace _" Hmmmm! Kedai kika sani."_

Nabihat dai dake son dole sai ta shiga jikin su tace _" Aunty Nabihat kinga fa yanzu haka ina shirin tafiya gidan su Anna ne, suma kusan kullum ƙorafi suke min bana zuwa, kuma fa ina zuwa, ban fi sati da naje ba, amma wai Anna ta ce ban da kirki, shine na tattara kayana zan je can har sai sun koroni ma."_

Dariya Intisar ta yi tana miƙewa tsaye ta nufi madafa tace _" Babu mai koraki a nan ai kin sani, sai dai idan ba kya son zaman sai ki tafiyar ki."_

Jin ta yi murmushi ita kuma Intisar ta samu Yusrah zaune cikin masu aikin suna ta wankin naman nan filla filla ya sa tayi saurin cewa Nabihat _" Yaushe za ki zo? Kuma gaskiya nake so ki faɗa min?"_

Da tabbaci Nabihat tace _" In sha Allah aunty da naje gidan su Anna zamu zo jibi tare da su Nawal, idan ma basu zo ba zan zo ni kaɗai na."_

Da irin gaggawa Intisar tace _" Shikenan sai na gan ki, sai anjima ko? Zan yi wani abu ne."_

Ba ta jira cewar ta ba ta kashe wayar tana ƙurawa Yusrah idanu da mamaki tace"


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login