Showing 51001 words to 54000 words out of 397328 words
ƙwarin guiwar da ta zo da ita ta barta, ta ɗauki Safwan ta kai shi ina? Ina zata kai Safwan?
Bata tashin ba ta rarafa da sauri hannayenta a haɗe ta ce" Dan Allah kana ji, na ji, zan je na haɗo kan kuɗaɗen, amma dan Allah ka min uzuri ka bani kwana biyu, kafin in zo a ringa masa abinda ya dace zan kawo kuɗaɗen kaf da za'a masa aikin, in sha Allah zan je yanzu yanzu in nemo."
Shi dai da takaicin ta yana kallonta har ta gama ta miƙe ta fita sai tare kukanta take ta koma ɗakin su sannan ya girgiza kai ya ja tsaki, a fili ya ce" Tabbas zan sake matse maki guri, idan har kika tardo shi a waje zaki sadaƙas tunda kema ai mutum ce kamar kowa, dole firgici zai saka ki damuwa da fita hayyaci harma da aikata aikin da kike ikirarin ƙyamata! Shirmen banza da wofi, da kyan ki, da komai zaki tsaya kina wahala a kan abinda kyanki ke iya magance maki? Mu zuba mu gani ni da ke wanda ya fi wani taurin kai!"
*Tunda* Yusrah ta fara yiwa Iya bayanin abinda ake ciki hankalin Iya ya tashi, tana kallon ta ta ɗaga kai ta bi ɗakin da suke ciki da kallo, sannan ta sake dubanta ta ce" Yusrah, me zai hana mu ɗauke shi mu tafi ta gwamnati da shi? Wannan asibitin ai ya fi ƙarfinmu, ki ga fa suna maganar mollioyin kuɗi? To mollioyin kuɗi mana Yusrah, ina muka ga kuɗaɗen nan?"
Yusrah ta sauke huci mai ɗacin gaske ta ce" Iya, abinda yake faruwa, yanzu idan muka nufi asibitin gwamnatin zamu je mu bi layin duban mutanen dake zaune jiran ganin likita, idan aka ce maki wani ya yi wata biyu a nan kar ki yi mamaki, ga ciwo ga rashin muhallin da za'a jinyaci ciwo mai kyau, domin a nan cikin runfunnan nan ake wuni a kwana, sauro da ranar garima tamkar ya ɗauke mutum ya gudu balle idan dare ya yi, ba maganar ƙazanta da rashin hutu, idan aka samu aka ga likitan ya bada gwaje gwaje nan ɗin ma kashin kuɗin ne ai, yin gwaje gwajen ma wani tashin hankalin ne, samun result ɗin ma haka, sannan mu dawo mu sake bin layin ganin likitan in mun ganshi amsa ne zai yi ya bamu lokacin da zamu koma, ya yi nazarin ciwon ne ya kuma saka ranar da zai iya yi mana aiki, Iya yaya zan iya zuba ido ina kallonsa a wannan yanayin tsayin lokaci haka? Idan fa ba'a kula da lamarinsa da wuri ba Safwan na iya zama gurgu kuma masaki har ƙarshen rayuwarsa, domin bayan nan gaba zai ringa ci ya zamo yunƙurin kashi ma zai garere shi zuwa gaba."
Iya cike da tashin hankali ta rafka tagumi hannayenta bibbiyu, kai subahanallah! Wani abun idan ya taso sai ka ji tamkar ka yi ta zunduma ihu kai ɗaya a zaune, astagfrullah, astagfrullah yanzu yaya za'a yi? Aina Yusrah zata samo kuɗin nan? A ina?
Iya ta fitar da huci mai zafi na tashin hankali, gashi a wajen makokin ya su ya su ne dangin mahaifin yaran, anya kuwa dangin Mahaifiyarsu sun san da rasuwarma? Domin Ita Mama dama ta ƙauyen Katsina ce, sukan yi fira da ƴan uwanta ta wayar Hannah ko ta Yusrah, tunda aka yi abin nan wa ma ya tuna wata aba wai waya balle har a nemi inda suke? Ta kai ake yi yanzun tukunan, a sanyaye ta ce" Ki je ki yi iya yin ki, amma maganar ɗaya ce dole ta gwamantin zamu nufa, dan bana tunanin kuɗin nan zasu samu, yaya zamu yi? Dole ai za'a je a bi layin, dole ce ke saka kowa bin layin, haka Allah ya hukunta."
Jinjina kai Yusrah ta yi ta ce" Iya, zan fara zuwa wajen Goggo Hindatu, akwai filin su da ya rage da suke maganar siyar da shi, to zan mata maganar idan ya so sai a siyar a nema masa magani, tunda dai yanzu mune magadan Baba, kuma Safwan yana da kaso ma fi yawa a ciki, ni kuma nawa na yafe masa duniya da lahira."
Da tausayawa Iya Abu ta ce" Allah sarki Yusrah, hakan ma wata shawara ce, ki je ki jaraba ɗin."
Jinjina kai ta yi ta ce" To Iya, sai dai zan qake bincikawa naga inda zamu samu kuɗin, dan gaskiya ba lallai kason Babanmu ya zama zai iya ɗaukar nauyin aikin Safwan ba."
Jinjina kai Iya Abu ta yi ta ce" Ba damuwa Yusrah, sai dai ina so duk rintsi ki dawo gobe saboda da yamma zamu juya gida, zan je nima in ga inda zan bar baffanku, in samu in barshi wajen wani in kuma bar masa ɗan na abinci sai in dawo, ki yi ƙoƙari ki dawo da wuri goben sai in je nima in dawo mu shiryawa dukkan abinda ya dace mu tafi mu yi jiran, ba komai innalaha ma'asabirin."
Yusrah ta gyaɗa kanta ta ƙarasa ta duƙa gaban gadon Safwan da ya samu barcin wahala ta kama hannayensa, a sanyaye ta ce" In sha Allah zaka warke, ko da aikatau da dako zan yi dan in kula da kai zan yi, sai inda ƙarfina ya ƙare, sai dai in mutu a hanyar nema amma ba zan dawo ba sai na samo abinda za'a kula da kai, Allah ya baka lafiya Babbanmu."
Daga nan ta miƙe ta amshi jaka da ashirin ɗin da Iya ta bata ta fita daga ɗakin ta ɗauki hanyar babbar ƙofar dan tafiya gidan su, gidan da yau kwananta uku rabonta da shi, gidan da idan ta je bata san a yadda zata tarda shi ba, gidan da ta tabbata tunda hasken dake ciki ya guje ba zata taɓa ganin haskensa ba har ta bar duniya, a haka tana ta tunani ta shiga adaidaita sahu ta nufi anguwarsu kanta a ƙasa.
Ɗaiɗaikun mutanen dake zaune ƙofar gidan ta gaishe da su har ƙasa suka sake jajanta mata da mata fatan samun lafiya ga Safwan, ba wasu ƴan uwan su a dai wurin da ta gani, ba ta kuma yi mamaki ba tunda ta san mahaifin ta talaka ne, haka ta shiga cikin gidan jiki a sanyaye tana sallama ƙasa ƙasa da kallon zubin gidan.
Gaba ɗaya inda ɗakunan su suke yanzu sai fili da tarin lakar da ta zuba, ɗaya katangar da ita ce ta shamake su da waje ma ita ma ta duƙa baya sosai alamar jiran taɓi take, haka ta ƙarasa tsakiyar gidan a cikin tsohuwar rumfar su da ɗaiɗaikun matan ke zaune.
Goggo Hindatu ce dai zaune ke karɓan ta'aziyya, sai wasu tsiraru daga cikin dangin mahaifin su dake ƙauye da suka zo tun jiya wasu kuma da safiyar yau, sai wasu dake nan gari sai dai da sun zo ba wani wuni suke yi ba suke tafiya, musamman ma da ba addu'a ake yi ba.
Da kallon tausayi waɗanda ke nan suka bita har ta zauna suna mata ta'aziyya da kuma tambayar jikin Safwan? Amsawa ta dinga cikin sanyin jiki har ta dubi Goggo Hindatu da ita ma tace "Yusrah ya jikin naki? Har kin warware ne kika taho? Ina cewa anjima in je in dubo ku."
A tausashe sosai tace "Jikina da sauƙi Goggo, jikin Auta dai ne sai a hankali."
Da alamar jimami tace "Allah ya bashi lafiya, su *Kadiri* sun je jiya ba ki farfaɗo ba, su suke gaya min jikin Safwan ɗin ba daɗi."
Jinjina kai ta yi alamar e amma ba ta ce komai ba, shiru ne ya ɗan biyo baya sai ga ƙanwar Kadiri ma'ana ƴaƴan Goggo Hindatu *Safiya* da sallama, amsawa aka yi kai tsaye ta nufo mahaifiyar ta tana duban Yusrah tace mata" Sannu."
Iya abinda ta faɗa mata kenan, wanda ya sa Yusrah ɗauke kai daga barin kallon ta ta ɗan motsa baki amma ba ta amsa mata ba, ko ba komai tana gaba da ita a shekaru tunda kusan shekara biyu ta bata, a ƙalla ko dan wannan za ta iya gaishe ta da girmamawa ai, sannan ta dubi halin da take ciki wanda ko Docter Hamat da bata da maƙiyi kuma wanda ta tsana a yanzu sama da shi, ai ya jajanta mata da addu'ar Allah ya kyauta, bare kuma ita da ke ƴar uwar ta?
Safiya kuma sai take ganin ita fa dama wannan wulaƙancin ne bata so na Yusrah, girman kai gare ta da share mutane, shiyasa ba ta shiga harkar ta ko kaɗan, ita ma ɗauke kai tayi tana taɓe baki ta kalli Maman ta tace "Mamma, aunty *Khadi* ta ce wai mai wane adadi za'a zuba?"
Kallon ta Goggo Hindatu tayi tana ɗan nazari, dake nan babu walalar wuri da inuwar da za'a dafa waken sadaka ya sa ta nemi alfarma a maƙwabtan su da abun bai shafa ba aka je ana girkin. Bayan tunanin da ta yi ta kalli Safiyar ta ce" Ki ce mata ta saka 1 litre."
Da sauri Safiya tace" To wallahi Mamma Zeinabu litre ɗaya da rabi ta zuba a tukunya, shine kafin a saka albasa aunty Khadi ta ce in zo in tambaya."
Yusrah na sauraron su, Zeinabun fa da ta faɗa gatsau sunan kishiyar ita Goggo Hindatu ne, ma'ana dai abokiyar zaman maman su wacce ita ma ya kamata a ce da Mamma ko aunty suke kiran ta, kuma abun takaicin hakan da suke yi tarbiyyar Goggo Hindatun ce, bayan kuma ita Zeinabun ba haka ƴaƴan ta suke kiran Goggon ba.
Cike da hargowa da masifa Goggo Hindatu kasancewar ta irin matan nan masu ƙiba sosai kuma sun saba da hargagi saboda ƴar kasuwa ce ta gidan gaba, kusan ma za'a iya cewa ba abin da ba ta siyarwa kuma duk a cikin gidan ta, kamar za ta cinye Safiya da ta faɗi saƙon tace "Kan buru'uban nan, Zeinabun wa da za ta min iyawa a harkar da ta shafeni? Ni ban aike ta aikin nan ba bare ta min iyayi, maza je a rage min man nan ko ke ma ran ki ya ɓace."
Gidan tsit ya sake ɗauka duk da dama ba hayaniyar ke akwai ba tunda ba mutane sosai, bugu da ƙari kuma ba kaɗan ba rasuwar ta girgiza zuƙatan su. Kaɗan dag halayyar Goggo Hindatu kenan, ba za ka san wacece ita ba sai ka zauna tare da ita na wuni ɗaya ma, mace ce dake da matuƙar son abun duniya, sannan take masifar tsanar a mata wasa da harkar kasuwar ta, take kuma da mugun kaushi ga wanda ya mata ba daidai ba ko mai ƙanƙantar ba daidai ɗin ba, sannan tana da ƙarancin ragowa har ma ga ƴan uwa ko ƴaƴan ƴan uwan, wanda wannan dalilin mai ƙarfi 'e ya sa ko alama Yusrah har ma da margayiya Hannah ba su cika shiga shirgin ta ba, ƴaƴan ta biyar kuma aunty Khadi da yaya Kadiri ne kaɗai suke fahimtar junan su tare da ƙaunar juna matsayin su na ƴan uwa.
Cike da rashin girmamawa Safiya ta juya tana turo baki da faɗin "To ni kuma da nayi me? Daga faɗin saƙo sai na zama mai laifi."
Wani irin kumtumemen tsaki Goggon ta yi tana faɗin "Aikin banza kawai."
Sannan ta yi shiru tare da ci gaba da jan carbin ta, sun ƙara ɗaukar minti biyu a haka, kafin Yusrah ta kalle ta sosai cikin ladabi da tausasawa tace "Goggo, dama magana na zo muyi akan aikin da za'a ma Safwan ne, ko zamu koma gefe?"
Kallon Yusrah ta yi, sam kallon ba tausasawa a ciki, tunda ta ji ta ambaci aiki sai wani tunanin na daban ya zo mata, amma sai ta ɗauke duban ta daga gare ta tare da yunƙurin miƙewa tana bismillah, saida ta tashi sannan Yusrah ta miƙe ta bi bayan ta suka koma bakin katangar ban ɗaki da babu kowa a can saboda ma rana da ta ƙwalla wurin, da sadda kai sosai Yusrah dake wasa da hijabin da Sakina ta kawo mata take faɗin "Goggo, dama aikin da za'a ma Safwan ne zai ci kuɗi masu yawa, saboda tsarar bayan shi ta raunata har ta shafi ƙafafuwan sa duka biyu, kuma aikin na buƙatar gaggawa Goggo, idan ba haka ba cikin biyu za'ayi ɗaya, in ma ya rasa ƙafafun nashi har abada, in ma kuma ta kaimu matakin da sai a ƙasar waje za'a masa aiki..."
Numfashi ta sauke ta kalli Goggon da tausasawa tace" Goggo, shine na zo muyi magana akan filin ku ke da su Baba da na yake yawan magana akan shi zaku siyar sai ya yi gyaran gidan nan amma Allah bai nufa ba, idan da hali Goggo a gaggauta siyar da shi ɗin sai a ba ni iya kason na Babanmu, sai na kai a masa aikin kafin lokaci ya ƙure mana."
Ba wani kwalo-kwalo Goggo dake ta duban ta tace" Yusrah, yanzu dama kin san da maganar filin nan ke ma? Kai amma dai Abdul-Hameedu bai da sirri a rayuwar sa, yara ƙanana ka tara su ka na faɗa musu komai da ya shafe ka?"
Sai kuma ta ja tsaki tana gyara tsayuwa tace" Ba ma wannan ba, yanzu Yusrah akan filin da ni dai nasan ko an siyar kason mahaifin ki ba zai biya kuɗin maganin Safwan ba, a ɓata kuɗin a banza ku baku mora ba kuma ke dake mace ba'a siya miki ko kayan ɗaki ba, tunda dai ai aure zakiyi nan kusa in Allah ya ce, kina ganin ta ya zan taya ki mu ɓata goma biyar bata gyaru ba?"
A ladabce Yusrah tace "Goggo, in sha Allah ma hakan ba za ta faru ba, Safwan a yanzu shi kaɗai ne ya rage min, zan iya yin komai dan ganin ya samu lafiya, sannan Goggo kin san komai game da shi, yaro ne mai hazaƙa, kaifin basira da wayo, mu taimake shi Goggo kar sanadiyar wannan abun ya rasa ƙafafuwan sa bayan rasa iyayen sa."
Taɓe baki Goggon ta yi cike da wofantarwa tace" Hmmmm! Shikenan, dama ai filin a kasuwa yake, tayin da ake ta mana ne bai mana ba shiyasa har yanzu bamu sallama ba, amma zan wa dilallin magana akan matsalar ki dan ya ƙara hanzartawa wajen samo wanda zai ƙara mana ko da wasu ɗaruruwan ne a sama."
Fuskar ta da alamar jimami tace" Goggo har zuwa yaushe kenan zai iya kai wa?"
Girgiza mata kai tayi tace" Ba lokaci Yusrah, sai dai na tabbata nan da sati ma ba zaki samu yadda kike so ba."
Buɗe baki Yusrah tayi cike da mamaki tace" Sati Goggo? To ai aikin Safwan ba'a so ya wuce kwana uku ko huɗu ma su zuwa."
Da irin ƙaguwa Goggo ta kawar da kai tace" Taɓɓ! Kinga kuwa sai ki haƙura kawai."
A sanyaye ta girgiza kai tace" To goggo me zai hana tunda ke nasan ba za'a rasa kuɗi ko kadara a wajen ki ba, Goggo ki taimaka ko aron kuɗin ki bamu, idan aka siyar ko yaushe ne sai ki ɗauki abun ki."
Da ɗan ɗaga murya Goggo tace" Wa? Ni Yusrah?"
Sai kuma ta girgiza kai tare da ɗata baki tace" Ƙarya haram Yusrah, ban da wannan kuɗin aje gaskiya, haka kuma ban da kadarar da zan iya siyar da ita ma a ƙananan kwanakin nan da kike magana a kai."
Shiru Yusrah ta yi tana tunanin mafita, ya za ta yi yanzu? Me ye abun yi? Ba su da wata kadarar da za su iya ɗagawa, basu da tsayayye a dangin su da zata ce bari ta je ya taimaka mata, ƙanin mahaifin ta ma ba za ta ce ga rayuwar da yake gudanarwa a ƙasar waje ba, bayan kyautar kuɗin da yake aikowa mahaifin su a duk watan azumi idan ya kama...
"Kinga, ga wasu darori da kwanuka can da Maman ku take ta wa Hannah tariya, da ƙyar aka ɓanɓaro su daga ƙasa duk kwalayen sun lollotse, amma wannan ba matsala bane dan su basu yi komai ba, idan kin yarda zan iya ɗaukar su na tafi da su gidana, a can zan iya samun mai siya, wataƙila idan aka harhaɗa ki kusa samun ko hamsin."
Tunda Goggon ta fara magana take kallon ta da mamaki sosai, duka kayan ɗaki da Maman su take ta siyawa aunty Hannah a gurin Goggo Hindatu take siya, ta taɓa jin Maman ƴan biyu ta nan unguwar su tana faɗa mata kayan Goggo Hindatu tsadar masifa ne dasu, kuma duk da alaƙar su ba ta ragewa Maman ko da sile, ita kuma kunya da kawaici ya sa idan ta kawo take ɗauka kawai ta ce tana so, sauƙi ɗaya bashi take bata kuma tana ɗaga mata ƙafa har ya kai kusan wata biyu saɓanin mutanen gari da take basu wata ɗaya.
Yanzu haka kayan da ta yi magana za'a iya haɗa kuɗi sama da jaka ɗari, amma shine take maganar hamsin, duk da ta san idan buƙata ta sa ka fito da abun ka dole a kassara maka, amma kuma abun ya yi yawa sosai.
To amma ba ta da yadda za ta yi, idan ta aje kayan me za ta yi da su? Ita ba saurayi gare ta tsayayye ba bare ta ce zatayi anfani da su nan kusa, hasalima ta ji Iya Abu na raɗe-raɗin riƙon su ita da Safwan zai koma hannun Goggon ne, dan haka kawai ta dubi Goggon tace "Shikenan Goggo, a siyar ɗin, amma suma na filin zamu buƙace su sosai, dan Allah ki taimaka mana a gaggauta siyarwa dan mu taimaki Safwan."
Da wata irin kagara ta yatsina fuska tace "Na ji."
Sannan ta juyo ta baro Yusrah can tsaye, a saiɓance ta biyo bayan ta suka dawo nan, har ta ce za ta koma asibiti aka ce ta jira ta tafi da abinci, dan haka ta zauna jira ba kuma jimawa aka fara shigowa da abincin cikin manyan kula.
Aunty Khadi na shigowa ta ga Yusrah da fara'ar ta ta nufota tana faɗin "Lah! Yusrah, yaushe kika zo gidan?"
Ɗan satar kallon Safiya ta yi, wato ba ta faɗa mata ta zo ba? Girgiza kai ta yi tana murmushin yaƙe tace "Aunty Khadi ina wuni? Ai na ɗan jima."
Zaune aunty Khadin ta yi kan dutsen dake kusa da Yusrah tace "Lafiya lau Yusrah, ya kike? Ya jikin naki?"
A tausashe ta amsa da "Alhamdulillah aunty Khadi."
"To ya jikin Safwan?"