Showing 309001 words to 312000 words out of 397328 words
garzayo a yi da ku._
_*Farashin mai sauk'i ne* naira d'ari biyar (500) kacal, yan niger kuma dala d'ari ne (500fcfa) zaka samu wannan littafi mai *WATA TAFIYA* ta daban da zata birge ku._
_Domin tura na ka tura ta wannan account *2097292243 Lubabatu Shehu U.B.A Bank*. IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER 93 81 16 18._
_'Yan niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta wannan lambar *94-98-56-52*._
_Bismillahir rahamanir-rahim_
*77*
Ko suka shigo gidan shi da Arif da Mukhtar kai tsaye ya saka sojan dake kula da Sani dreba ya masa rakiya har sashen da suka kulle shi, da kula Arif ya dube shi yace "The boss, ba dai can sashen za ka maida mana wajen zaman mu ba? Ni fa na fi son waccen Alƙur'an."
Wani kallo ya watso mishi ya cira laɓɓan shi da ƙyar ya amsa da "Saboda anan cibiyar ka take? Ina ce dai gidana ne ko?"
Zaro idanu Arif ya yi ya kalli Mukhtar yace "Lahhh! Lauya kaji fa gorin gida zai mana? Anya the boss wani zubin kana tuna kai musulmi ne kuwa?"
Taɓe baki Mukhtar ya yi irin ko oho ɗin nan yace "Kaga ni ka daina sakani maganar ku, da kai da shi duk tsoron ku ya kamani."
Wata arniyar dariya Arif ya yi yana riƙe hannun Mukhtar ɗin yace "Kai wallahi mugun zabo ne, yo daga zane wannan ƙedarin banzan sai duk ka wani damu kan ka?"
Girgiza kai Mukhtar ya yi yana kallon Arif ɗin kawai bai ce komai ba, sojan na buɗe musu falon suka shiga dukan su suna ƙarewa falon kallo, riƙe haɓa Arif ya yi yace" Oga, nan kuma ina ne? Ka san da ni zan iya zama anan na ƙarar da rayuwata?"
Kallon Arif ɗin ya yi sai kuma ya kalli sojan nan yace" Yana ina? Fito min da shi?"
Da cika umarni sojan ya nufi ɗakin baccin yana buɗe ƙofar da makulli, hakan ya sa Arif ɗan sunkuyowa kusan AA ɗin cikin raɗa yace" The boss, hala wani arnen ka sake dafewa anan?"
Kallon shi ya yi yana ja baya yace" Arif masifa ne kai, kai ba zaka barni na ji da rikicin dake kaina ba wai?"
Sai kuma ya mayar da duban shi ga ƙofa da ake fitowa, ma sha Allah hutun da Sani dreba ke samu duk da ba cikin ƴancin yake rayuwa ba, amma wallahi shi da kanshi ya san ya yi ƙiba, dan tun yana cikin zulumin irin hukuncin da AA ɗin zai masa har ya kai ya darrafe ya daina saka haka a ran shi, abu ɗaya zuwa biyu ne suka fi damun shi wanda suma kuma basu hana cimar da yake samu fitowa a jikin shi ba, na farko iyalin shi da ya san dole suna cikin damuwar rashin shi, sai kuma tunanin yaushe zaman shi anan zai ƙare? Idan ya fita daga nan wace ƙasar zai koma da Alhaji ƙarami ba zai san yana can ba? Amma bayan wannan baya da wata damuwa, ba aikin wahala yake yi ba, ba'a takure yake ba, ya yi wanka a kawo masa ya ci ya sha, sai dai yana da lokacin ganin hasken rana ne kawai.
Sani na ƙarasowa kusa da shi ya tsugunna yana gaishe shi, haɗe fuska ya yi ya dakatar da shi da faɗin "Kaga, na sa an fito da kai ne saboda a yau za ka bar nan, Sani, na san kasan wa ye ni kuma ba za ka manta ba, ka sani shi kan shi uban gidan naka jira nake ya gama zagaye zagayen shi sannan na dafe wutsiyar sa, dan haka ya rage naka yin nesa da shi da duk wata sabgar shi, idan kuma ka fi so ni na mayar da kai ɗan wiwin, to mu zuba da ni da kai."
Hannu ya sa aljihun shi ya ciro envelope ƙarama ya miƙo mishi, jiki na rawa ya karɓa da ladabi yana aika masa da godiya, ɗorawa ya yi da" Kuɗi ne da zasu isheka ka kai kanka wajen iyalin ka, basu taɓa rasa abin ci ba tunda aka kawo nan, dan suma idanuna suna kan su, sannan akwai ƙaramar waya a ciki ɗauke da sabuwar lambar da za ka iya samun su a ciki, ina fata hakan ya zama gargaɗi gare ka."
Ko da ya gama faɗa masa haka ya juya zai bar falon, Sani da ya yi kasaƙai yana kallon shi da mamaki da al'ajab, sai ma ya rasa bakin magana wallahi, to shi wannan wane irin mutum ne? Suna da laifi, kuma hukuma ne shi yana da damar hukunta su ko sakawa a hukunta su, amma ya tsare shi cikin aminci, sannan ya kula da iyalin sa? Sannan yanzu ya masa wannan kyautar kuma? Sai kawai ya fashe da kuka ya bin shi da addu'a kala kala da godiya da yi masa alƙawarin ko wani ya ga zai cutar da iyalin shi yanzu sai inda ƙarfin shi ya ƙare, dan bai taɓa tsammanin rabuwar su ta zo a haka ba, sam bai yi wannan hasashen ba.
AA kuma da tuni su Arif suka rufa masa baya da mamaki bai ma san yana yi ba, yana danna wayar shi ne ƙarama yana ba wa amintaccen sojan dake tsaron gidan sa na sirri umarni kan ya ɗauko su Mani dreba da kanshi ya tuƙosu har cikin gari, saboda yaran shi za su fara zuwa makaranta suma, tare da bashi adreshin sabon gidan da ya siyawa Mani dreba ɗin matsakaici da zai ishe shi rayuwa shi da iyalin shi.
Ɗan daddaɓa kafaɗar sa Arif ya yi yace "Oga, waccen mutumin nace wa ye shi kuma? Me ya sa baka sa na zane shi ba?"
Wani irin kallon hagumce ya mishi tare da jan birki, sai kawai ya nunoshi da yatsa yace "Arif, in ba sa sojan can ya rufe min kai a ɗakin nan na kwana uku ba kace ni ba jikan Anza bane?"
Ƙasa da sama Arif ya kalle shi, sai kawai ya taɓe baki irin ba magana ɗin nan, har suka isa wajen motar da suka zo da ita Arif ɗin ya shiga ya zauna mazaunin matuƙi, AA kuma ya ce wa Mukhtar su yi gaba zai biyo su a baya dan zasu je ya kai gaisuwa ne wajen Hajiar su Mukhtar ɗin, wanda shi dai tunda ya ce zai je da kanshi ba tare da ya nema ba ma yake cikin zulumi, shi kam baya so suje ya zo ya samu yaran Hajia da bata juran a taɓa su yayi ta surfa, shiyasa duk ya kasa sakin jiki wallahi, kuma idan ma ya ce ba zai je ba ai a banza tunda ba iya ɗaure shi zai yi ba kuma ya san hanyar gidan.
Arif kam saida ya ga mai gadi ya wangale masa gate ɗin gidan ya daddafe sitiyari da ya tabbatar ko biyo shi zai yi ba zai kama shi ta sauƙi ba sannan ya sauke glass ya zuro kai ya kalli AA dake shirin shiga tashi motar yace "In ka isa ka rufeni Allah tsinen oga, kai nima fa sa kake gani ƙwallon ɗan iska ne, dabar mun yi ta ajewa ne mukayi da muka samu mata, kaima kuma ai auntynmu Yussy na zuwa nan da jibi ko? Za ka ga yadda za ta sauya maka suna daga Oga zuwa mijin Haji..."
Tunda ya fara maganar AA bai juyo ya kalle shi ba, ya dai yi saƙe ɗin nan ya ɗaga kai sama yana sauraren shi irin ya kai maƙura, amma da ya ji ya sako sunan hatsabibiyar sa sai ya juyo ya kalle sho, hakan ya sa shi danna hancin motar da gudun masifa suka fice a gidan yana ƙyalƙyala dariya yana cewa "Oho! Idan ka ganni gobe ka ce ubana goma sha biyu ne, ni da haɗuwa da kai kuma sai ranar raka ka ɗakin aunty Yussy."
Wata wawuyar ajiyar zuciya Mukhtar ya sauke yana girgiza kai, sai kuma ya kalli Arif da ɓacin rai yace "Kana ji ko? Na rantse da Allah idan kasan muna tare da kai ka daina hassala mutumin can, sannan ka daina gangancin nan da ni wallahi, kaga ina fa da burika dayawa da ban fara cika su ba, babban burina na yanzu kuwa shine naga na aure ƴar buzuwata (Abrar) na killace wallahi."
Dariya Arif ya yi ya daki cinyar Mukhtar ɗin yace" Kai kar ka damu fa, in sha Allah kafin ka mutu sai ka mori ƙuruciyar ka kaima, ba dai ƙanwarmu ba? Na baka."
Tsaki Mukhtar ɗin ya yi ya zuba tagumi yana kallon titi, tunani yake ko ya kira Hajia ya ce su fita unguwa da gaggawa ita da yaran, shi kam bai yarda da zuwan nan da AA zai yi ba gaskiya, Hajia kuma ba lafiya gare ta ba wallahi, kar ya je ya rikita musu gida sannan ya tahowar shi ya barshi da tashin hankali.
AA bai sauka gidan su Muktar ba sai da ya biya ta bakin kasuwa ya sayi huhun goro sannan ya bi ta wajen cinema ya sa aka datsa masa gasashen nama mai kyau da zafin gaske sannan ya ƙarasa da jus a bayan motarsa shaƙe.
Da ya ƙaraso yau samarin gidan Hajia biyu ne kawai suke nan, shi Attahir ya tafi aika, dan haka su suka kwashe kayan nan suka shiga ciki da su bayan sun masa gaisuwar da suka saba, shi kuwa ya kama hannayensu suka gaisa da kyau har yana masu yar fira.
Hajia na filin gidanta saman ƙatuwar tabarma daga zaunen da take su Arif na daga gefe suna ɗan zantawa amma kuma ta kan ɗagowa ta yi zage zagenta na ƴan matanta dake ɗaki suna shirin zuwa anguwa wai wajen aure, faɗi take tana ƙarawa idan aka gansu sun mayar da hankali yawo zasu je, in aka gansu kamar goron bakin sarki amma ɗakunansu kamar makwantar jakai, tana wannan mitar ne aka ringa shigo mata da kayayyaki hakan ya sa ta yi tsuru tsuru tana bin huhun goron nan da ido.
Murya ta rage sosai ta ce" Muntari, kar dai Babanku zai yiwa ɗaya daga cikin marayuna auren dole na shiga uku, huhun goro ai sai ɗaurin aure, ina Elhaji ne ni yau tunda safe ban ganshi ba?"
Muktar ya yi tsai shi ma ya kalli Samir zai tambaye shi wanene sai ga AA ya shigo yana sallama fuskarsa ɗauke da yalwataccen murmushi yana faɗin" Barka da warhaka jama'a, assalamu alaikum."
Hajia ta tsare fuskarsa da kallo ta ɗan dubi gefe da gefen ta ta ce" Kai Muntari kamar yaron nan mai takardar kuɗi ko?"
Muktar ya yi dariya ya ce" Shine Hajia."
Hajia ta miƙa hannu da maficin hannunta ta ce" Ya salam, ya razaƙu ya laɗifu, kai tashi daga nan bashi kujerar tashi."
AA ya ƙaraso yana cire takalminsa ya haye tabarmar Hajiar ya je daf da ita sosai ya zauna yana faɗin" Hajia ni a nan zan zauna, barshi ya yi zamansa a kujerar sa."
Hajia ta wani washe baki tana faɗin" To ai shikenan ɗan nan yi zamanka a gefena, bari in tashi in kawo maka ruwa, wani kala kake so? Kai Samir maza karɓi siyon na galan mai raɓa ya sha, shi yasa nake yiwa Alhaji faɗan ya ringa ajiye min ruwan galan saboda baƙin daraja, yanzu wannan ai ba zan bashi ruwan can na bakin can ba."
Daga Arif har Muktar baki suka saki suna kallon cin amana irin na Hajia,
Samir da kansa sai da ya tallabe baki yana kallon Hajia, Hajia fa bata bari a zauna mata saman tabarma, cewa take yi ina ita ina layuwa da ƙarti a tabarma guda? Cewa take yi sam ba zai yiwu ba, wai ba kyau, ƴan matanta kaɗai suke da wannan damar, yau sai ga mai damar nan na biyu ya bayyana, ƙiri-ƙiri ta yarda ƙato irin makashin mahaukacin soja ya zauna daf da ita har tana masa fifita?
AA ya katse maganar yana faɗin" Haba dai Hajia, can ɗin zan sha, to Hajia a gida ma bana shan na galan, sam ban ɗorawa kaina ƙarya ba gaskiya."
Hajia ta wani dafe kumatu ta ce" Ai ana ganin ka an ga ɗan aljanna, irin yaran nan ne da suke tsoron Allah, kai dai Allah ya maka albarka kawai, tabbas tsoron Allahn ka ya birgeni, Allah ya sa Muntari ya yi koyi da kai, shi fa ɗan ƙarya a motar sa ma cike take da ruwan kwalba, uhum Muntari ai akwai kashe kashen banza da wofi, Allah dai ya nunan ya yi aure in huta da Muntari, to ɗan nan goron nan na menene? Wannan abin mai zafi fa?"
Arif ya kalli Muktar Muktar ya kalli Arif ya tallabe ƙeya ya ƙara zubawa Hajia ido, AA ya janyo ledar ya buɗe yana faɗin" Wai Hajia ta hanyar cinema na biyo na ganshi ana ta gashi sai kawai na siyo, kar aje ma likita ya hana ki ci Hajia?"
Hajia ta kama masa suka buɗe da kyau ta ɗaga murya tana faɗin" Rihab, idan baki kawon ƙaton tiro na juye gashin nan ba nan da minti ɗaya yau in na kama dukan ki ko ubanki ba zai sheda kamanninki ba..."
Sai kuma ta dubi AA tace" Ɗan nan gashe ci muke da zarar ya samu, likita ai ba Allah bane, yo abinda idan ka ƙi ci ɗin ma mutuwar zaka yi? Kai dai Allah ya sa mu cika da imani."
AA ya amsa da" Ameen Hajiata ameen, Hajia wannan goron kuwa fa na gayyata ne, ki gayyaci duk wani abokin arzikin ki dan jibi in sha Allahu jikarki zata tare."
Ya ƙarashe yana ɗan rufe fuska abin kunya, daidai Rihab ta kawo tire ɗin, Hajia ta karɓa tana rangaɗa guɗa ta ce" Allahu Akbar, Allahu akbar dole in yi gayyata yaron nan, in sha Allah zamu je mu ansheta da hannu bibbiyu Allah dai ya bada zaman lafiya ya kawo ƙazantar ɗaki, kai yaron nan abin arziki ya maka yawa, har da kunya gareka ashe?"
Arif ya kwashi kiran sallah ya salamce yana tafa hannu, Muktar ya amshe shi yana sake zuba musu ido
Muktar ya ce" Hajia yanzu yau ke ce kike yin guɗa bayan kin ce ba kyau?"
Arif yace" Kai ba ma wannan ba, wai wannan ne mai kunya? Inna lillahi wa inna ilaihi raju'un, ƙarshen zamani."
Hajia ta maka musu harara ta ce" Baƙin ciki zaku masa dan na yabe shi? Ai dole in yabi gwani sai dai rai ya ƙiya, aikin banza ku yi zuciya mana kuma a muku auren ku gani in ban yabe ku ba."
AA ya taɓe baki ya ce" Ah to Hajia gaya musu, Hajia yaushe zan kai ƙannaina can gidan Hajia su wuni ne?"
Hajia ta ce" Su Samir? to ku je yanzu mana."
Da ƙarfi Samir dake ɗaki kunnayensa a kansu ya sauke atishawa ya fito yana faɗin" Ba fa mu ba ko Baba?"
Gaba ɗaya sai da aka ɗago ana kallonsa AA ya taɓe baki ya ce" A'a Hajia su Rihab."
Hajia ta ce" Au, bawan Allah in sha Allah zaka ga Annabi, ka ce kaima kana son marayu? Allah sarki, in sha Allah duk ranar da ka shirya sai su je su gaishe da Hajiar, nima ai sai in je in kai gaisuwar in sha Allah, Allah dai ya kashe maƙiyinka ko uban wanene."
AA ya shafa fatiha yana faɗin" Fatiha ameen, Hajia mu ci."
Hannunsa hannun Hajia suke cin gashen nan, suna miƙawa sauran a hannu, hankali kwance suna fira yadda ka san sun shekara da sanin juna, sabon kuwa yadda ka san tunda aka haife shi suka saba, wannan lamari da ya girmami su Arif sai kawai suka yi gum suna ci suma da jus dan abin na yau idan magana zasu yi tabbas za'a rasa da yaren da suke yi tsabar firgita, Allah dai ya shirya jikan Anza da Hajia kawai suke fata a zuƙatan su.
Daga gidan su Mukhtar gida ya nufo tunda har anyi sallah isha'i ga kuma yunwa da yake ji, a kasalance ya shiga falon Anna yana nazarin da fa uncle Sulaiman na nan da yanzu can ya nufa, saidai ya samu abincin sa ya ci a can, ya ɗauki sama da minti biyar zaune a falon na Anna babu kowa, duk hayaniyar yana jiyo ta ne daga babban falo har da ta su aunty *Fadima* suma saboda shirin tariyar Yusrah jibi, wayar sa ya ɗauka ya kira lambar Anna, bayan ta ɗaga suka gaisa ya faɗa mata yana falon ta kafin cikin shagwaɓa yace "Anna, yunwa nake ji fa sosai."
Ɗan jim Anna ta yi kafin tace "Shikenan, bari na turo maka da abinci."
Tana aje wayar ta dubi ƴan matan ta ga wacece a ciki za ta tura, Nawal lalle ne tasa a yatsun ta take jiran ya bushe, Manal kuma na ta faman tsefe kai, Abrar kuma da bata komai ba za ta iya tura ta ba, haka ma Nabihat dake kwance kan kujera, sai kawai ta dubi Manal ɗin a harshen buzanci tace mata "Manal, jikan Anza yana falona ki je madafa ki haɗa abinci ki kai masa."
Amsawa tayi tare da tashi tsaye tana mayar da gashin ta baya, hakan yasa Anna faɗin "Idan kina son gashinki ki tabbatar kin rufe shi da kyau, idan ba haka ba a daren nan zai miki ƙwal kwabo."
Turo baki Manal tayi sai Nawal da ta yi dariya haka ma Abrar da tace "Ai kuwa Anna da an ga mata a wurin nan."
Aunty Fadima ƙanwar Anna ita ma dariyar tayi tace "Haba dai, Alhajinmu ma ba zai aikata haka ba."
Cike da tabbaci Anna tace "Ita ai ta sani, Aswan ɗin ne za ta kai ma abinci ya ga tsilin gashin ta a waje? Hummmm!"
Sai lokacin Nabihat ta fahimci abinda ake magana a kai, ai da sauri ta tashi zaune ta bi Manal da ta shiga madafa da kallo, sai kuma ta miƙe tana kama ɗan kwalinta dake shirin faɗuwa, ba wanda ya damu da ita sai ma harkar gaban su da suka ci gaba da yi, kafin Manal ta fito kiran shi ya sake shigowa Anna ta ɗaga, cikin nutsuwa yace "Anna, a faɗa ma Y. Turaki ta kawo min earpeace ɗin tab ɗin yarona, ta wani kama masa abu ta riƙe uwa ita ta siya."
A sanyaye